116-117
by @nuceeyluv
® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
116_117
"Bacci suke sosai sai wajajen 8:30 omar ya farka da sauri yyi dabara ya zare imaan dake jikinsa a hankali, sannan ya tura mata pillow a hankali sannan ya dauki jakar sa cikin sanda ya wuce part dinsa, nan ma yana zuwa sharp2 ya shirya ya canja kaya yasan idan 10 tayi masa a gidan mummy zata ritsashi dan yasan ko shakka babu yanzu tana bacci, saida ya gama shirinsa sannan ya dauki jakar shi yabar side dinsa. Har zai wuce ya sake komawa dakin da imaan take anan ya dauki 'Yar karamar takarda da pen yyi short note sannan ya ajiye kasan pillow'n da imaan take yana murmushi ji yake kamar yyi kissing dinta saidai bayason tasan yazo gidan. Yana waiwayen imaan haka yabar dakin har yabar gidan yana tunanin imaan da jikin ta me matukar laushi tamkar audiga.
"Sai 10:13 imaan ta farka daga bccin da takeyi sai juyi take tana tunanin mafarkin da tayi da omar ba abinda yafi bata mamaki yanda ta farka taji gaba1 gadon ya game da kamshin turaren omar dan ko a mafarki bazata manta d daddadan kamshin sa ba take ta lumshe ido tana murmushi lkci guda ta jawo pillow dan sake rungume shi idanun ta a rufe, bude idon da zatayi taga 'Yar takarda a ninke a wajen cike da mamaki ta shiga kallon takardar tana tunanin kome ne a ciki, a hankali tasa hannu ta dauko sannan ta bude taga anyi rubutu kamar haka...
" _kullum_ _kara_ _kyau_ _kike_ _especially_ _idan_ _kina_ _bacci_ _have_ _a_ _nice_ _day_ _I_ _luv_ _yhu_ _Muahhhh_
"Tsananin mamaki ne ya kama imaan shin waye yayi wannan rubutun? _omar_ amsar da zuciyar ta bata kenan lkci guda, a fili tace toh Amman taya hakan ta faru? Yaushe yazo gidan? Wannan shine dalilin jin kamshin da tayi kenan? Take wani murmurshi ya kubce mata tana nanata kalaman da omar ya rubuta mata, ke imaan meke damunki? Wata zuciyar ta mata wannan tambayar lkci guda shin kin manta Wanda ya wulakanta kine a rayuwa? Duk wannan hudubar ta zuciyar tata takasa daina jin omar a ranta murmushin ma sai karuwa yake da wannan tunanin ta fada toilet tayi wanka.
"Mummy kam Sam batasan da zuwan omar ba saima hidimar gabanta da takeyi.
"Omar yana office sai 10 ya bada order a kawo masa breakfast koda aka kawo masa ma kadan ya iya ci yana tunanin imaan yanzu idan taga wannan rubutun yasan ma bazata daukeshi da wani muhimmanci ba shin yanzu meye mafita? Dole dai yaci gaba da bawa mummy hakuri har ta bashi matar sa.
*****
Kusan kullum omar yana kan hanyar zuwa wajen mummy yana Binta da hakuri Amman Sam mummy taki sauraran sa, bashi kuma da damar dazai je wajen imaan. "Gaba daya omar ya zabge lkci guda tun yana daukar abun a hankali har yazo ya fara damunsa, ada yana lallabawa yaje wajen imaan idan tana bcci Amman yanzu ya daina samun hakan sbd idan yazo kofar a rufe yake samunta.
***
Omar zaune a office yyi jugum yana tunanin mafita sai ji yyi an dafa shi, a dan tsorace ya dago kansa. "Farooq dake tsaye gabansa yyi murmushi, omar yace yaushe ka shigo? Farooq ya nemi waje ya zauna sannan ya kalli Omar yace kusan 10mins kenan nayi knocking harna gaji na shigo still bakayi noticing hakan ba shin meke faruwa ne bro? Omar ya sauke ajiyar hrt sannan ya danyi yake yace ah ba komai. "Farooq yace haba bro bekamata ka boyemin komai ba karka manta nifa dan uwanka ne tunba yau ba na lura akwai abunda ke damunka kwanannan meyasa bazaka sanar min ba? Idan na addu'ah ne ai saina tayaka.
"Omar yyi jugun yana tunanin shi bawai yaki fadawa farooq din bane dan wani Abu aa saima dan kunyar sa da yakeyi idan yaji dalilinsa na shigar sa halin da yake ciki yanzu dan baya manta ranar da yayi ta maimaitawa farooq cewar " _Na_ _tsaneta_ _bana_ _sonta_ _Har_ _abada_ _kuma_ _bazan_ _taba_ _sonta_ _ba_ shiyasa ya kasa tunkarar sa da zancen.....
"Farooq ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi yace bro kayi mgn mana.
"Omar ya sake sadda kansa kasa a hankali ya shiga zayyane wa farooq abinda ke faruwa tun auren sa da imaan... Sannan ya dago kansa fuskar nan tasa ta koma abun tausayi a raunane yace... Farooq na zalinci imaan na nuna mata tsana tun farkon haduwata da ita a rayuwa karka manta ba agida na fara sanin imaan ba na fara saninta ne a wannan hospital Din ta dalilin mahaifiyar ta...... Nan ya labartawa farooq komai sannan yaci gaba da fadin farooq wannan shine rashin jituwata da imaan INA mata kallon _kyama_ tana min kallon marar _imani_ sai gashi lkci guda Allah yyi mun kamu na fada tarkon son imaan Wanda tunda nake arayuwa bantaba son wata ba sai ita Wanda har abada bazan iya rabuwa da itaba. Gashi mummy tamin hukuncin da bazan iya daukar sa ba wai na saki imaan? Abunda bazan iyaba kenan.. Dan Allah ka taimakeni farooq do something plsss.... Ya karasa mgnr cike da muryar kuka lkci guda kuma hawayen da yake makalewa tun dazu yyi nasarar saukowa kan kumatun sa.
Nuceey luv😘