118-119
by @nuceeyluv
® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
118_119
"Farooq ya saki baki d hanci da kunne yana sauraron yanda bro dinsa ya nuna tsantsan rashin imani ga imaan, lkci guda kuma wani irin tausayin sa ne yake masa yawo a xuciya sbd yanda ya hango tsagwaron nadama a tare da bro dinsa... Saida ya danyi shiru na wani lkci sannan ya iya motsa labbansa yana kallon omar yace mgnr gsky bro ka tafka babban kuskure a zatona koba imaan mummy da daddy suka aura maka ba ya kamata ka dubi girman su ka rikesu amana...omar ya dakatar da farooq ta hanyar dafa hannun sa jikinsa yace tun tuni na fahimci haka bro na yada nayi kuskure yanxu shawara nake nema. "Farooq yadan ja numfashi sannan yace toh karka damu tunda yanxu mummy bazata saurareka ba insha Allah ni zanje da kaina wajen ta kaikuma sai kaje ka samo soyayyar ka wajen imaan.. Omar yace na gode broth buh kana ganin imaan zata soni kuwa? Farooq yyi murmushi yace haba broth karkace min tsoron tunkarar imaan kake, omar yadan shafa kansa yana girgiza kai yace bazaka gane bane banason abinda zai takura tane. Farooq yyi murmushi a karo na biyu yace ohk karka damu insha Allah imaan zata amince da kudirinka. Omar yace Allah yasa farooq yace ameen. Suna wannan firar har lkcin tashin su yyi. Sannan suka bar hospital din.
*******
A falo suka tarad da imaan ita kadai tana kallo, imaan da take zaune Sam bata San da zuwan su ba sbd duniyar tunanin data tafi. "Farooq ne ya kalli omar daya zuba mata ido har bayason kyaftawa yyi murmushi sannan ya dafa kafadar sa. Omar ya dawo daga tunanin daya tafi, farooq yyi mgn a hankali yace kaga tunda batasan d zuwan mu ba ka wuce side dinmu zan turo maka ita. Omar yace OK. Sannan ya wuce side din nasu. Yana tafiya kenan mummy ta fito daga dakinta daidai lkcin shima farooq ya sake maimaita sallamar sa. "Mummy da fara'ar ta tace a'a son Kaine a gidan sai lkcin itama imaan ta juya ganin farooq itama ta saki murmushi laa ya farooq sannu d zuwa. Farooq ya nemi waje ya zauna bayan ya gaishe da mummy y kalli imaaan yace ke tun dazu ana rafka sallama kin tafi duniyar tunani baki amsa ba. "Imaan ta zaro ido d mamaki tace yaushe kenan. "Farooq ya kalli mummy yace mummy weekend tazo miki ne mummy tace uhum. "Farooq ya kalli imaan yace af na manta jeki side dinmu cikin falona zaki ga wata Leda tana kan fridge ki kawo min. "Imaan ta mike tace toh.
"Omar yana zaune cikin falon farooq yana tunanin imaan can yaji kokarin bude kofa hakan ya tabbatar masa d imaan CE, "imaan ta shiga dakin tana 'Yar wakar ta sai ganin omar tayi zaune kan kujera ya zuba mata ido, saida imaan tadan tsorota dan batayi zaton d mutum a ciki ba, itama tsaya tayi tana kallon sa dan Rabon d su hadu sunyi kusan 2weeks kenan. "Omar tashi yyi daga zaman d yake ya taka a hankali har gaban imaan, imaan na tsaye sai ji tayi an rungume ta tsamm, kokarin kwatar kanta tayi Amman ta kasa dan yanda omar ya shiga shinshinar jikinta yana Shakar kamshin jikin ta. "A hankali ya fara matsowa d ita har suka kaiga zama kan kujera saidai ita yyi mata masauki a cinyar sa. "Imaan ta dago balabalan idon tana kallon omar daya tsareta da ido. "Omar ya fara mgn cikin tattausan lafazi yace..
" _imaan_ _Nasan_ _nakasance_ _marar_ _tausayi_ _a_ _gareki_ _na_ _nuna_ _maki_ _kyama na nuna maki rashin adalci ban rungumi maraicin ki ba na wulakantaki duk nasan da wa'annan saidai imaan yau Nazo da kokon barata dan Allah INA rokon ki da duk abinda na _maki_ _wanda_ _ya_ _bata_ _maki_ _rai_ _dan_ _Allah_ _kiyi_ _hakuri_ ki _yafemin_ _kuskure_ _na_ _dan_ _Allah_ _ki_ _dubi_ _girman_ _Allah_ _ki_ _yafe_ _min_ _wallahi_ _a_ _yanzu_ _banda_ _wata_ _mace_ _a_ _fadin_ _duniyar_ _nan_ _da_ _nake_ _kauna_ _tamkar_ _ki_ _imaan_ _INA_ _sonki_ _imaan_ _INA_ _matukar_ _sonki_ _imaan_ _dan_ _Allah_ _karkiyi_ _watsi_ _da_ _kudiri_ _na_.
"Imaan ta dago ido tana kallon omar tace......
"Ya omar kenan banajin akwai wasu zantuka naka d zasuyi tasiri a kaina na tabbata ko Karen hauka naci bazaka taba sona ba, na Dade d fahimtar mayudaran kalaman ka, Wanda zaka iya yin komai dan ka kubutar da kanka, yanzun ma sbd mummy na fushi da kaine dat's y kazo da wa'annan mayaudaran kalaman domin ka wanke kanka wajen mummy hmm ya omar kenan karka manta fah bawai jaririya bace ni kamar yanda kasha fada tun a baya...
"Tsabar rudani ma omar ya kasa furta komai saima kallon imaan daya shiga yi, sai yau yake nadamar karyar da yyi ta shiryawa mummy dan ya kare kansa yanzu gashi illar karyar ta sameshi alkcin da yake kokarin nuna asalin gskyr sa an dauketa a matsayin tatsuniya shin dan Allah meya kamata yyi dan ya nunawa imaan lallefa sonta yake bana wasa ba???
Nuceey luv😘