OMAR KO FAROOQ?

120-121

by @nuceeyluv

® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓





120_121



"Saukowa yyi daga kan kujerar ya zuba dukkannin gwiwiwin sa a kasa sannnan ya riko imaan yana kallon ta yace imaan wallahi abubuwan da na fada maki gsky ne har cikin zuciyata ada kikewa wancan omar din kallon haka Amman a yanzu zanso kimin kallon omar sabo me matukar kaunarki inason dan Allah ki manta da baya mu fuskanci gaban mu dan Allah.. Ya karasa mgnr lkcn da muryar shi ta fara rawa. "Duk jikin imaan yabi ya mutu ko kadan bata taba zaton omar me shegen sham kamshin nan zai iya zuba gwiwowin sa a gaban taba, take zuciyar ta karye sosai harma taji wani irin tausayin omar yana shigar ta kota INA. "A hankali itamata ta kamo hannun omar ta damke shi da nata sosai tana kallon sa da murmushi a fuskar ta tace shikenan na yafe maka omar na yafe maka har abada Allah ya yafe mana gaba1, wow farinciki ne? Ko murna CE? Take omar ya jawo imaan ta fada jikinsa tuni ya matse ta tsamm a jikin sa haka nan yakeji kamar an dauke masa nauyi daya jima da daukar sa gefe guda kuma ji yake tamkar ya tsaga kirjin sa ya maida imaan ciki dan ya tabbatar mata d irin kaunar d yake mata., dakyar ya iya samun labbabn sa suka iya motsi a hankali cikin muryar farinciki ya fara mgn yace...


" _Kalaman baki basu isa su iya furta kalmomin dake tattare a qundun littafin zuciyata ba da har zai iya zayyane tsantsar farincika na a gareki da kuma dumbin godiyata a gareki imaan, saidai hakan bazai hana furta maki kalmar godiya ba, imaan na gode na gode d karmacin ki, lalle kin ciri tuta cikin mata dan ba kowa bane yake tamkar ki, imaan Allah ya saka maki da gidan Aljannatul-firdausi ameen_ "imaan tayi murmushi tace ameen mijina. "Omar ya ware ido sosai yana kallon imaan yace da gske kin ajiyeni a matsayin miji? Imaan ta bude baki da niyyar mgn sai jin bakin omar tayi cikin nata yana aika mata da wani kiss me zafi2.





****

6angaren mummy kuwa, imaan tana barin wajen, farooq ya kalli mummy bayan sun dan taba hira, ya kalli mummy yace ehmm... Mummy mgn fa zamuyi mummy tayi murmushi tace inajin ka. "Farooq ya dan shafo kansa sannan yace mgnr bro da imaan ce, take mummy ta hade rai tace akayi yaya? Farooq yace ehm.. Mummy da farko zanso na fara baki hakuri akan abubuwan da bro dina yyiwa imaan... "Mummy ta dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu tace kaga farooq kaima tunda sauran 6urbushin mutuncin ka a idona ka daina zancen nan tun kafin kaima naka mutuncin ya zube a yanzu. "Farooq yayi kasa da murya yace duk bekai haka ba mummy inason dan Allah ki dubi girman Allah ki saurari mgn ta koda ace bazaki amince min ba dan Allah. "Mummy tace toh inajin ka.

"Farooq yace _mummy nazo nan ne sbd bro dina ina kuma Neman dan Allah wannan fushin da kikeyi dashi ki sauke shi nasan yyi laifi Amman tashi guda kuma sai gashi yyi nadama akan duk abubuwan daya aikata, mummy tunda yyi nadama dan Allah ki basa dama ta karshe yanzu kiga iya gudun ruwan sa, mummy ko Allah daya halicce mu ai muna masa lefi, amman da mun rokesa sai kiga ya yafe mana, toh mummy shi kuma bro har saikin yafe masa kin daina fushi dashi kafin Allah ya yafe masa, domin duk wanda iyayen sa suke fushi dashi to Allah yana fushi da wannan bawan shin mummy bazaki kidena wannan fushin ba fisabilillahi?_

"Mummy tayi shiru tabbatas maganganun farooq ya shiga jikin ta. A hankali itama ta fara mgn tace farooq kenan ai badan komai nake fushi dashi ba saidan yanda yyi watsi da abunda muka bashi amana. "Imaan marainiyace bata d kowa sai Allah saimu kuma da muka taimaka mata, ta wajena na yafe masa komai ya wuce saidai bazan tilastawa imaan ta bishi ba kamar yanda na tilasta auren dan itama saida akayi sati da auren kafin tasan dashi kaga bada amincewar ta akayi ba dan haka banason na sake tafka kuskuren da nayi a baya idan yanason komawar ta saiya nemi izinin ta.

"Farooq yyi murmushin cin nasara yace yanxu mummy idan imaan ta yadda zata bi bro shikenan komai ya wuce? Mummy tace tabbas farooq yyi murmushi to shikenan sai muyi zaman jiran result, mummy tace wanne result kuma? Farooq yyi 'yar dariya yace bakiga har yanzu bata dawo daga aiken danayi mata ba? Oh sai yanzu mummy ta tuna ashefa farooq ya aiki imaan side dinsa., mummy tace eh. "Farooq yace toh inaga sakon ne ya riketa. "Mummy tace kamar ya? Farooq ki zuba ido. Mummy ta tabe baki kawai taci gaba da kallo.




******

Omar wasu zafafan kisses yake aikawa imaan, imaan tun tanajin kunya da nauyin sa har batasan lkcin data fara maida masa d martani ba, habawa tuni Omar ya sake birkicewa yana wani irin numfashi, sun dauki tsawon lkci a hakan kafin omar ya iya saita kansa, sannan ya sake matse imaan a qirjin sa, imaan kuwa tayi lamo kamar jaririya tana maida numfashi a hankali. "Honey omar ya kira imaan da wata irin murya daya sake birkita tunanin imaan., imaan tayi shiru, omar ya sake cewa honey imaan tace uhum. "Omar yace tashi muje kada su mummy suga mun Dade, tashin hankali ai sai yanzu ta tuna ma farooq aiko ta yyi shin da wanne ido zata kallesu? Imaan ta mike tana kallon kan fridge taga ba komai a wajen, omar yace me kike nema? Imaan tace ya farooq ya aikoni wai nazo kan fridge akwai Leda na kai masa, kuma ban ganta ba. "Omar yyi murmushi yace ai wajena ya turoki, imaan ta kalleshi d mamaki tace toh yaya akayi yasan kana gidan? Omar yace tare muka zo ai. "Imaan ta zaro ido tace Amman ya akayi banga shigowar ka ba? Omar yace lkcin kin tafi duniyar tunanin mijinki ya shafo fuskar ta lkcn daya karasa mgnr yana murmushi, imaan ta rufe kanta cikin kirjinsa tana murmushin itama dan tabbas gsky ya fada no wonder ya farooq yace ana ta zabga sallama ban amsa ba Ashe lkcin ya omar ya wuce kenan ma hada baki sukayi? Omar yace tunanin me kikeyi? Imaan tace INA tuna tsakanin ya *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓ wanne yafi wani wayo, omar yyi dariya yace uhum kinga tashi mu tafi gidan mu, imaan ta mike sannan omar ya salkaye hannun sa a cikin na imaan suka fara tafiya dan zuwa falon mummy.

"Suna 'yar hirar su har suka isa falon, imaan duk yanda taso ta kwace hannun ta jikin na omar abun ya faskara dan omar sake rike hannun ta yyi, "a hankali Tace ya omar dan Allah ka sakemin hannu kar mummy ta ganmu a haka. "Omar yace yaushe kika fara wannan kunyar? Imaan tace nidai dan Allah, omar yace haba inaa ai so nake mummy ta ganmu a hakan dan ta barmin mata mu koma gida, imaan a zuciyar tace ah lallema ya omar dinnan baida kunya wlhy, ahaka har suka bude kofar falon, suna yin sallama, mummy da farooq suka juyo suna kallon su.






Nuceey luv😘