JIDDATULRAHMAN 1
_*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*_
*💫 JIDDATULRAHMAN💫*
~Daga Alƙalamin✍️~
_Asmau Abubakar Musa (Jasmine🌸🌸)_
*SADAUKARWA: HAUWA MUHAMMAD GANA*
______________________________________
DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINKAI
... A hankali na tura ƙyauren gidanmu na shiga bakina ɗauke da sallamar da ba ni da tabbacin za a ji saboda sautin muryarta ma bai fita ba, sai da na fara leƙa tsakar gidanmu daga soro na tabbatar mutanen da na ke tsoron su ganni basa nan kafin na sa kai na shiga gidan a saɗaɗe kamar ɓeran da ya yiyo sata. Kai tsaye ɗakin Ummata na shige ina kara yin wata sallamar a hankali, tana zaune a kan sallaya da carɓi a hannunta da alama tunda ta idar da sallah ba ta tashi ba, sallamar ta wa ta amsa sannan ta waigo ta dube Ni Ta ce"Alhamdu Lillah! Ba ku haɗu ba ko?"
Na kalleta cikin rashin fahimta Na ce" Da wa Umma".
"Mahaifinki da Innarki, tun ɗazu suka fice wai za su je makarantar su ɗauko ki don da alama ke ce bakya son dawowa gida saboda kar kije talla".
A gefen Katifarmu na zauna ina ƙoƙarin cire Safar ƙafata, na kalli Umma Na ce, "Ban haɗu da su ba, mun biya ta gidansu wata ƴar ajinmu da aka yi wa tiyata ne muka duba ta da jiki."
"Subhanallahi! Allah Ya bata lafiya." Umma ta faɗa tana ninke sallayar bayan ta miƙe, kana ta ɗora da cewa, "Ki hanzarta ki sauya kaya ki ɗauki tallar ki wuce, na san idan suka dawo suka same ki mahaifinki zai iya miki dukan rashin dalilin da ya saba".
"To Umma."
Cikin ƙanƙanin lokaci na sauya kayan makarantar da zuwa na zaman gida. Tare da Umma muka fita zuwa tsakar gidan, da kanta ta shiga madafi ta ɗauko wata madaidaiciyar robar fallasa da aka kusa cika ta da dafaffen ƙwan zabi ta miƙo min, kana ta ɗora da cewa, "Har kullum ba zan gaji da faɗa miki cewa ki tsare mutuncin kanki ba a duk inda zaki tsinci kanki, kada fargaba ko tsoron abin da wani zai miki yasa ki saɓawa Ubangijinki, duk rintsi ki kasance mai hakuri da miƙa dukkan lamuranki ga Ubangiji."
"In Sha Allah Umma zan kiyaye." Na fada ina ƙoƙarin ɗora robar a kaina.
Bakin zani Umma ta kunce ta fito da wata tsohuwar Naira ɗari ta miƙo min tare da faɗin," Ga wannan idan kinje ki nemi wani abu ki sanya wa cikinki kada ki zauna da yunwa".
Shiru nayi ina kallonta ba tare da na karɓi kuɗin ba, tunani nake yi a ina Umma ta samu kudi har Naira ɗari tunda dai na san ba wata kwakkwarar sana'a muke yi ba, sannan wanda ya ajiye mu kuma bai damu da ci ko shan mu ba.
Kamar ta san zancen da na ke yi a raina, tayi murmushi tare da shafa gefen fuskata tace, " Ɗazu Maman Jamila ta shigo, ita ta bani wannan ɗarin duk da na ƙi karɓa sai da ta ajiye ta tafi".
Nima murmushin nayi kafin Na ce, "Allah Sarki Maman Jamila, tana da kirki sosai ita kaɗai ke nuna damuwa da tausayi ga halin da muke ciki".
"Maza ki wuce, Allah Ya ba da sa'a Ya tsareki daga dukkan sharri". Ta faɗa tana kama hannuna zuwa soro bayan ta damƙa min kuɗin.
Sallama na mata sannan na fice daga gidan namu bakina ɗauke da addu'ar fita daga gida da Malamin Islamiyyarmu ya koya mana.
Hanyar tasha na nufa kai tsaye don nan ne na saba kai tallen a kowace rana, kuma ina ciniki sosai don wata rana ma bana jimawa nake siyarwa na koma gida.
Ina tafe ina tunanin wannan rikitacciyar rayuwa da muke ciki ni da mahaifiyata, ina da mahaifi amma ban kasance ɗiya a gare shi ba kamar yadda ya saba faɗa min lokuta da dama. Sai dai a kullum na kan ji tausayin mahaifiyata fiye da yadda nake jin tausayin kaina, watarana na kan faɗi cewa da wani yana sauya ɗabi'un wani lokaci guda, to babu shakka zan sauyawa mahaifiyata wasu daga cikin ɗabi'unta, ba wai don sun kasance marasa kyau ba a'a sai don ina so ita ma ta ƙwatar wa kanta ƴancin da kowace macen aure take da shi a gidan aurenta.
Duk da haƙuri abu ne da addini ma ya ƙarfafa yinsa sannan kuma duk mai hakuri zai ga sakamako mai kyau a gaba, amma na kan ji cewa haƙurin mahaifiyata ya zarce wanda ake faɗin ya kamata a yi.
Ummata ba ita kaɗai bace matar sa Babana ke aure, kamar yadda nima ban kasance ɗiya ɗaya da Babana ya mallaka ba sai dai ni kaɗai ce ɗiya mace, sauran ƴan'uwana uku da abokiyar zaman Ummata ta haifa duka maza ne.
Kamar yadda watarana Ummata ke bani labari cewa, ita da mahaifina sun haɗu ne a kasuwar hatsin garinsu inda yake zuwa sai da hatsi duk ranar sati da ake cin kasuwar, a wajenshi suke siyan kayan abinci duk sanda aka aiko su kasuwa ita da ƴar'uwarta. Hakan yasa suka saba sosai har zuwa lokacin da soyayya mai ƙarfi ta ƙullo a tsakaninsu.
Babu jimawa Mahaifina ya buƙaci tura magabata gidansu, bayan bincike da duk wani abu na addini da al'ada daga ƙarshe mahaifinta ya lamunce a ka sanya ranar aurensu.
Babu daɗewa aka yi aurensu, danginta suka rakata zuwa gidan aurenta.
Da fari suna rayuwa ne cikin aminci da kwanciyar hankali, Baba yana sauke duk wasu haƙƙoƙinta da suka rataya a wuyarshi.
Har zuwa lokacin da aka haifeni, tun daga wannan lokaci ne kuma abubuwa suka fara sauyawa saboda haɗuwar da Baba ya yi da wata bazawara da lokaci guda ta sauya al'amura da yawa a rayuwarsa.
Bansan abubuwan da suka faru bayan haka ba saboda Umma ta ce sai na ƙara girma sannan za ta fahimtar da ni wasu abubuwan, abin da kaɗai na sani shine na taso ne cikin rashin gata da kulawar mahaifina. Bai san ci, sha da suturata ba don watarana a gabana ya faɗa wa Umma cewa babu wata ɗawainiya da zai sake yi da mu bayan muhalli da ya ba mu. Don haka ne tun daga wannan lokacin Umma ta dage da sana'o'in aikatau na cikin gida irinsu wanki, guga, surfe da daka da sauransu duk don ta nema mana abin da za mu sanya a bakin salati.
Da taimakon ƙananan sana'o'in da Umma ke yi na shiga makarantar Firamare ta Gwamnati lokacin da na isa munzalin, da fari Babana ya so hanawa amma a lokacin sai Umma ta nuna mishi cewa a wannan karon idan yaƙi amincewa za ta kai ƙararsa hukuma, da wannan ta samu tudun dafawa har ya barni na ci gaba da karatun har zuwa yanzu da nake aji uku na ƙaramar sakandare.
Mafarin fara zuwa talle Tasha kuwa ya samo asali ne tun wani lokaci da Innarmu (bazawarar da Babana ya aura) ta fara kiwon zabi, dake Allah Ya sanya musu albarka sai suke yin ƙwai sosai wanda hakan yasa ta yanke shawarar fara saidawa kuma tana samun alheri sosai kasancewar ƙwan zabi ya kanyi wahala saboda ba kowa ke kiwonsu ba. A haka mutanen dake zuwa siye suka ba ta shawarar cewa ta dinga dafawa ana kai wa Tasha saboda mutane matafiya suna nema sosai za ta yi ciniki sannan mutanen gari ma za su siya.
Bansan me ya faru bayan haka ba sai watarana ta dafa ƙwan da yawa, muna zaune a ɗaki ni da Ummata Babana ya kirawoni ya faɗa min cewa daga wannan ranar kullum Inna za ta dinga dafa min ƙwai ina kai wa talla tasha, na yi kuka sosai kamar raina zai fita saboda a duniya babu wani abu da na ƙi jinin na ga ƴa mace tana yi kamar talla, ko da Umma ta nemi hanawa sai cewa ya yi matuƙar ta hana ni to zai dakatar da karatun da nake yi sannan kuma zai sake ta kuma ta tafi ta bar masa ni tunda ni ƴar sa ce yana da iko da ni. Wannan dalilin yasa Umma ta bani baki tare da yi min nasiha sosai na fara kai tallen a kowacce rana bayan na dawo daga makaranta ƙarfe ɗaya na rana, a ranakun mako kuwa tun ƙarfe goma na safe nake ɗaukar tallar.
Bansan cewa nayi tafiya mai nisa ba sai da na ji hayaniyar mutane, nan na farka cewa na iso tashar. Gurin da na saba zama a kowace rana na nufa, gefen wani gidan mai ne da matafiya ke yawan zuwa sannan akasari mutanen tashar a nan suke hada-hadarsu, Ni kaɗai nake zama a gurin saboda da yawa daga cikin masu talle basa tsayuwa a waje guda sun fi gane su dinga bin motoci suna nuna abin da suke siyarwa, a nawa ɓangaren kam ba zan iya haka musamman da na fuskanci cewa mutane da dama sun san wajen zama na kuma har inda nake ake zuwa a iske ni a siya.
Ban jima da zama ba naji an yi min sallama da wata sanyayyar murya da na kasa tantance mace ne ko namiji, sai da na ɗaga kaina na kalli wanda ke sallamar. Wata matashiyar budurwa na gani tsaye tana yi min murmushi, kallonta nayi sosai kuma na fahimci babu shakka ta fito ne daga gidan masu ƙumbar sosa, duba da yanayinta da kuma kalar suturar da ke jikinta, ga kuma ƙamshin jikinta da ke sintiri a kafofin sadarwar hancina.
"Nawa kike sai da kwai?". Ta katse tunanin da nake.
"Guda ɗaya Naira Hamsin". Na ba ta amsa.
Tana ƙoƙarin buɗe jakar dake rataye a kafaɗarta ta ce, "Ba ni guda huɗu", ta miƙo min wata sabuwar ɗari biyar da ta ciro a cikin jakar.
"Ba ni da canji, yanzu na iso ban yi ciniki ba tukun". Na faɗa ina kallonta.
"Ba damuwa bari na zauna a nan ɗin kafin a gama gyara mana mota, kila kafin nan za a samu canjin." Ta faɗa tana zama dakalin da nake zaune.
Nayi tunanin a wajen za ta ci ƙwan, amma da na ba ta sai na ga ta buɗe jaka ta ciro wata leda ta saka ƙwan a ciki ta maida cikin jakar.
Muna nan zaune lokaci-lokaci mutane na zuwa siyan ƙwan, ita kuma ta ciro waya a jakarta tana latse-latse. Can ta ɗago ta dube ni tace, "Dan Allah mene ne sunanki?".
Ba tare da tunanin komai ba na amsa mata da cewa, "Suna na Hauwa amma Jiddah ake kirana".
Murmushi tayi kafin tace, "Suna mai daɗi, na ga kiyi min kama da wata fuska da na taɓa gani ne amma na manta ko waye".
Ƴar dariya nayi kaɗan kafin na ce, " Kinsan kowane ɗan Adam yana da mutanen da suke kama da shi a duniya".
"Haka ne, amma ke kam kamar na taɓa ganin mai kama da ke a masarautarmu". Ta faɗa tana ƙara jinjina kai.
Haɓa na riƙe ina kallonta kafin na ce, "Ashe ke sarauniya ce".
Dariya kawai tayi, ta kawar da maganar ta hanyar yi min wata hirar daban.
Mun jima muna hira kafin wani dattijon mutum ya iso inda muke ya faɗa mata an gama gyaran motar ta zo su tafi.
"Ƙanwata ga shi zan tafi bansan ranar da za mu sake haɗuwa ba kuma, amma naji daɗin hira da ke sosai." Ta faɗa lokacin da ta miƙe.
Nima duk sai na ji babu daɗi saboda yadda muka saɓa cikin ƙanƙanin lokaci kamar dama mun san juna tun da daɗewa. Kila ganin yadda yanayina ya canja lokaci guda ne yasa ta cewa, "Karki duk sanda na zo wucewa ta garin nan zan neme ki mu gaisa kinji".
Dariya na ɗan yi kana na mata gyaɗa kai na ce, "Toh ki gaida gida, Allah Ya kiyaye hanya".
"Amin" ta faɗa, kana ta ƙara da cewa, "bari na miki hoto da wayata saboda watarana".
Yanayin da tayi maganar ya ba ni dariya sosai, bansani ba ashe hoto take min ina dariya.
Ta sunkuyo saitina ta nuna min hotonan, sun yi kyau sosai har naji da ina da waya da na tura. A haka tayi ta mana hotona har sai da dattijon ya sake dawowa kafin ta wuce tana ɗago min hannu.
Gaskiya naji daɗin hirar da muka yi da Falmata, kamar yadda ta faɗamin sunanta a cikin hirar da muka yi. Zan iya cewa ita ce mutum ta biyo bayan Ummata da na taɓa sakewa muka yi hira haka, abin da ya bani mamaki sosai saboda ban kasance mai yawan sakewa da mutane ba. Kodayake ban samu nutsuwar yin hakan bane saboda yadda kullum nake cikin fargaba da tunanin makomar rayuwata.
Sai bayan La'asar ƙwan ya ƙare, dan haka ban tsaya ɓata lokaci ba kamar koyaushe na miƙe na nufi hanyar komawa gida.
******* A ɓangaren Falmata ita ma mamakin yadda suka sake da Jiddah take yi sosai, Kodayake mutane da yawa suna faɗa mata cewa tana da sauƙin kai da kuma saurin sabo da mutane, sannan ba ta da girman kai ko kaɗan duk da kasancewarta jinin sarauta. Ta kan yi dariya ne kawai duk sanda wani ya furta haka a gareta, a ganinta hakan ba wani abu bane da za a kuranta tunda dai duk Allah ne Ya halicci mutane sannan talaka, mai kuɗi, mai mulki ko muƙami duk Allah ne ya ba su, shiyasa ba ta wani ɗagawa ga duk wanda Allah ya haɗa ta zama da shi.
Shiyasa ko a cikin Masarautar ba su cika shiri da ƴanmata sa'aninta ba saboda yadda suke da jiji da kai da nuna su ƴaƴan masu mulki ne, mafi yawan lokuta idan ba ta aiki ta kan tafi sashen Bayi ne ta zauna cikinsu ayi ta hira da raha musamman tsofaffin ciki, tana ƙaruwa sosai ta fannoni da dama idan tana hira da su.
Wani zubin idan tana wajen da ba a san ta ba idan ba ta faɗi cewa ga daga inda ta fito ba babu wanda zai fahimta, wasu idan suka gano daga baya sai su yi ta mamakin kasancewarta mai sauƙin kai haka.
Amma a wannan rana da ta kasance da Jiddah sai ta ji daban ba kamar yadda ta ke zama tayi hira da wasu mutanen da bata taɓa haɗuwa da su, ga shi kuma yarinyar ta tsaya mata a rai, so take ta tuna inda ta taɓa ganin fuska makamanciyar ta ta amma ta manta, daga ƙarshe dai ta nisa ta kalli dattijon da ke tuƙa motar ta ce, "Baba Labaran dan Allah wannan yarinyar da muka rabo ɗazu a tasha ba ka ganin kamar ta maka kama da wani da ka taɓa sani?"
"Wacce yarinya kenan ranki ya dade?". Ya tambaya.
Wayarta ta ciro daga cikin jaka sannan ta fito da hotonan da tayi wa Jiddah tana nuna mai ta ce, "wannan".
Shiru ya yi na tsawon lokaci suna ci gaba da tafiya har ta cire ran samun amsa daga gare shi, kamar daga sama kuma taji yace, "Kamar a cikin Masarautar Boddo ko?" Ya faɗa yana waigawa yana kallonta don jin amsar da za ta bayar.
Jin ya ambaci sunan Masarautarsu yasa cike da zumuɗi tace, "wallahi kuwa ina ta so na tuna da wanda take yi min kama amma na kasa, ka tuna ko?"
"Nima dai abin ya kwanta min gaskiya, amma idan na tuna zan faɗa miki". Ya amsa mata hankalinshi na kan tuƙin da yake yi.
"Yauwa Allah yasa ka tuna din, dan yarinyar ta tsaya min a rai sosai na rasa dalili".
"Ranki ya daɗe ai zuciyarki kyakkyawa ce kullum kina cike da tausayin mutane na ƙasa da ke". Baba Labaran ya faɗa.
A haka suka ci gaba da tafiyar suna hira jefi-jefi, lokacin da suka shiga garin Jigawa lokacin an jima da yin sallar La'asar, dan haka suka nemi waje suka yi sallah suka nemi abinci sannan suka ɗauki hanyar garin Bauchi.
Ƙarfe takwas na dare da ƴan mintuna suka isa garin Bauchi, Masarautar Boddo suka nufa kai tsaye, babban gini ne na al'ada da aka zamanantar da shi, faɗin tsari da kyawun zubin Masarautar ya wuce misali, haske ya wadata ko'ina mutane na ta kai kawo kamar ba dare ba. Har ƙofar sashinsu Baba Labaran ya isa da motar, wasu daga cikin Bayin dake farfajiyar wajen suka iso suna mata sannu da zuwa. Da fara'a take amsawa, da yawa daga cikinsu suna murna da nuna jindaɗinsu a fili da dawowarta.
Sallama tayi da Baba Labaran ta shige sashin na su da cike da farin cikin dawowarta lafiya cikin danginta.
***Tun daga ƙofar gida nake jiyo sautin muryar Baba yana magana cikin faɗa da hargagi, rass! Ƙirjina ya ba da sauti, na san babu shakka wannan faɗan zai yi wuya ace ba da Umma Baba ke yi ba, dama idan kaji yana irin wannan faɗan to da ni ko Umma yake yi. Ko meye dalilin faɗar na yau oho, don babu shakka idan aka bincika ba wani abu bane da ya kamata a dinga ɗaga jijiyar wuya haka ba. Cikin sanyin jiki na shiga da sallama a bakina.
Da sallama na shiga, Kabir ƙanina da ke zaune kusa da ƙofar soron ne ya amsa sallamar tare da faɗin, "Lahh Baba ga Adda Jiddah ta dawo ma".
Bai kai ga rufe baki ba uwarsa da ke zaune a ƙofar ɗaki ta lailayo masa ashariya tace, " Ɗan banzan yaro, ga nan ɗan'uwanka baka kirashi da Yaya ba amma kana kiran wata bare da Adda".
Baki ya turo yana ƙunƙuni, Kabir shi ne auta a gidanmu kuma daga Baba har ina suna nuna tsantsar soyayyarsa a fili, duk da cewa daga Kabir ɗin har Ɗan'uwansa Nazir iyayen na matuƙar nuna musu soyayya sai dai duk wanda zai zauna ko na mintuna kaɗan ne a cikin gidanmu zai fahimci ƙaunar da ake ma Kabir ɗin daban ce. Sai dai duk da haka yaron sam halin yaron ya banbanta da na Iyayensa, don yaro ne me sanyin hali gami da tausayi ba, wasu lokutan shi ke sato hanya ya kawo mana abincin da suka dafa ni da Inna musamman idan ya fahimci ba mu da abin da za mu ci. Sau da dama uwar ta kan kama shi da laifin hakan sai dai ba ta iya zartar mai da wani hukunci sai dai idan Baba ya dawo ta haɗa ƙarya da gaskiya ta faɗa mai shi kuma ya tasammana da faɗa. Saɓanin ɗan'uwansa Nazir da duk wasu halayen mahaifiyarsa ya ɗauko.
"Kin tsaya kina tsare mutane da ido ne?". Baba ya katse tunanin da nake yi yana kallona, da sauri na ɗan durƙusa na ce, "Barka da yamma Baba". Tsaki yaja mai sauti ya maida kallonshi ga Umma dake tsaye a ƙofar ɗaki yace, "Na faɗa miki ba zaki dinga yi min iko da ƴa ba don kuwa ba ƴarki bace ke kaɗai, don haka ki haɗa mata kaya mako mai zuwa Hajiya Laure za ta tafi da ita, ba zai yiwu ace na haifa amma ba na moruwa da abin da na haifa ba".
Murmushin da na kasa tantance ma'anarsa Umma tayi kafin ta ce, "Ba zan taɓa hana ka iko da Jiddah ba Malam, amma ka da ka kasance cikin mutanen da basa cika alƙawari har tsakaninsu da Ubangiji, kaji tsoron Allah". Daga haka ta juya ta shige ɗaki, shi kuma yaja tsaki ya zo ya wuce ta gefena ya fice daga gidan.
Kamar wacce aka dasa haka na tsaya ina tunanin maganganun da Baba ya yi da kuma amsar da Umma ta ba shi, Hajiya Laure da naji ya ambata shi ne abin da ya ƙara ɗaure min kai.
"Zaki kawo min kuɗina ne ko ya ya?". Inna dake zaune ƙofar ɗakinta ta faɗa.
Jiki a saluɓe na isa inda take na miƙa mata cinikin ƙwan sannan na ajiye robar, ba sannu bare madallah haka ta amshe kuɗin tana ƙirgawa, sai da ta gama ƙirgawa kafin ta kalleni tace, "Allah Ya so ki sun cika, zaki iya tafiya ki bani guri".
Jiki ba laka na nufi ɗakinmu na shiga da sallama, ga mamakina sai na iske Umma ta kifa kai a kan katifarmu tana kuka sosai, abin da ban taɓa gani ba tsawon rayuwata, duk abin da Baba ke mata ban taɓa ganin ko da ruwan hawaye ba a idonta amma sai ga shi yau ita ke wannan kukan. Hankalina ya tashi sosai don haka na ƙarasa kusa da ita ina tambayar abin da ya faru, ba ta tanka ba sai ma jawo ni da tayi jikinta ta ƙanƙameni tana ci gaba da yin kukan, take nima naji kukan ya taho min don a duniya bana ƙaunar na ga abin da zai ɓata ran Ummana sai dai idan ya gagareni kamar matsalar da ke tsakaninta da Baba.
Mun jima cikin wannan yanayin kafin ta sake ni ta ɗago fuskata tana share min hawaye, wasu hawayen naji sun ƙara tarowa cikin idona ganin yadda fuskar Umma ta ɗan kumbura ga idanunta kuma da suka yi jazir.
"Umma meya faru?". Na tambaya cikin shessheƙa.
"Jiddah wannan karon ma mahaifinki ya sake zuwa da wani batun da ba zan iya ja da shi ba."
"Umma Baba ya ce na daina zuwa makaranta ko?" Na fada wasu siraran hawaye na sake sauka a kuncina.
Hannu tasa ta share min hawayen kafin tace, "Kusan hakan ne amma ba hakan bane, Jiddah mahaifinki aikatau yake son kai ki wani gari".
Ganin yadda ta cije leɓe ne yasa na fahimci lallai har yanzu akwai sauran kukan da ke cin ran Umma kawai dauriya take yi.
"Umma aikatau kuma? Laifin me na sake yi masa?"
"Baki aikata masa laifin komai ba Jiddah, Hajiya Laure ce ta zo da batun cewa akwai gidan da suka saka ta nemo ƴar aiki, kuma gidan na masu hannu da shuni ne za a samu alheri, shi ne ta zo don mahaifinki ya bata ke ta kaiki".
Shiru na yi ina tunanin kafin nace, "Umma mu gudu kawai mu tafi gurin danginki mana, dama kince idan na girma sosai za mu je".
Ita ma dai shiru tayi tana kallona kafin daga bisani tace, "Kiyi haƙuri Jiddah zaki je aikatau ɗin amma na ƙanƙanin lokaci, zan shirya tafiyarmu gurin dangina kinji".
Kai kawai na gyaɗa mata, na rasa dalilin da yasa duk sanda zan yi ma Umma maganar danginta sai ta kawo min wani uzuri daban wanda zai sa dole na bar zancen, gaskiya ina kwaɗayin naje na ga dangin Ummata na san za su kula da mu sosai.
Haka muka zauna shiru har zuwa lokacin da a ka fara kiraye-kirayen sallar Magriba, tare muka miƙe zuwa tsakar gida don yi alwala..
******* Tun bayan dawowarta hutu daga makaranta, a kowane yammaci tana zuwa sashen Bayi ta zauna cikinsu su yi ta hira kamar yadda ta saba lokuta da dama. Yau ma tun da tayi sallar La'asar ta nufi sashen don ta zauna cikin tsofaffin su yi hira, ta kuwa yi gami da katar don ta samu ana ta hada-hadar haɗa dambun shinkafa a kicin din sashen, nan ta zauna tana faɗin, "Lallai yau a nan zan ci abincin dare tun abincina kuke dafawa".
Wata dattijuwa daga cikinsu tayi dariya ta ce, "Ranki ya daɗe sai dai a ware a miki na ki daban".
Ɗaure fuska Falmata tayi kafin tace, "Me yasa ba za a dafa duka a dibar min a cikin wanda kowa zai ci ba?".
Tsohuwar ta ɗan rusuna tace, "Allah ya huci ran gimbiya, yadda kike so haka za a yi".
Sai a sannan ta ɗan saki fuska tace, "Ba na jin dadin yadda kuke yi min ɗin nan, dukkanmu ƴan'adam ne kuma matsayi ɗaya gare mu a gurin Ubangiji, sai dai wadanda suka fi mu Bautarsa ne matsayinmu ya banbanta."
Nan ta shantake suka ci gaba da hira wani zubin har wasu ayyuka take taya su, duk yadda suka so hana ta amma abin ya ci tura, a haka har aka sauke dambun.
Tana tsaka da cin Dambun da aka saka mata wani akushi wayarta da ke gefe ta fara ruri, gabanta ne ya faɗi ganin mahaifiyarta ce mai kiran amma duk da haka ta dake ta ɗauki wayar ta kara a kunne ga mi da yin sallama.
Daga ɗaya ɓangaren ba a amsa sallamar ta ta ba, "Ki zo yanzu ki same ni". Abin da kaɗai mahaifiyarta ta faɗa kenan ta kashe wayar.
"Ko me ya ɓata mata rai haka?". Falmata ta tambayi kanta.
Dole ta miƙe sannan tayi sallama da su ta wuce cikin gida tare da hadimarta.
Tun daga ƙofa take amsar gaisuwar masu hidima sashen, har zuwa sanda ta isa babban falon.
Ganin ba ta tare da masu yi mata hidima ne yasa ta tambayi ina take, nan suka faɗa mata tana cikin ɗaki, kai tsaye ɗakin ta nufa ta shiga da sallama.
Tana tsaye a ɗakin tana kaiwa da komowa, jin shigowar Falmatan yasa ya juyo gare ta, wani gigitaccen Mari ta wanke fuskar Falmata da shi tana huci tamkar wacce ta fito daga filin dambe.
Cike da masifa tace, "Ni zaki tozarta saboda ke bakya kishin kanki da na mahaifiyarki? Kin sani sarai a cikinku ake son Yarimah Ajmal ya zaɓi matar aure amma kike zuwa kina ƙasƙantar da kanki a cikin Bayi. A haka ne zan saka ran idan ya zo zai zaɓi ƴa ta? Da wannan mugun halin da kike gwada, ko kina tunanin idan ya zo ba zai yi bincike a kan kowaccenku bane ehe?. Ya samu labarin cewa baki da maraba da Bayin gidanku ko me? Toh wallahi ki kiyayeni, banason wannan ƙasƙantar da kan da kike yi. Wuce ki fita ki bani guri". Ta ƙarashe maganar tana nuna mata ƙofa da hannu.
Falmata da tunda mahaifiyarta ta fara magana kan ta ke ƙasa, sai wannan lokacin ta ɗago tace, "Kiyi haƙuri". Sannan ta juya ta fita a ɗakin da sanyin jiki.
Kai tsaye ɗakinta ta nufa zuciyarta na ƙuna a kan abin da mahaifiyarta ta mata, yanzu kawai dan ta zauna da Bayi shi ne ƙasƙantar da kai? Su ɗin ba mutane ba ne ko kuwa don ana ganin ba su da wani muƙami ne yasa ba a martaba su. Ita kam har abada ba za ta wulaƙanta duk wani wanda ke ƙasanta ba, su ma da suke hakan tana musu fatan shiriya.
Batun auren wani Yarimah kuwa har ga Allah ba so take ba, ita tafi so ta auri wanda ba shi da wani muƙami, wanda zai dinga kasancewa da ita a kowane lokaci ba wanda sai bayan wani lokaci za ta dinga ganinshi ba.
Yarimah Ajmal shi ne babban Ɗa ga Sarkin Gombe kuma shi ne wanda zai gaji Sarkin, gaskiya ba za ta iya auren wanda ba zai dinga kasancewa da ita da yaransu ba. Sannan aure take so tayi na tsantsar soyayya ba auren haɗi irin na Masarautu ba.
Gaba ɗaya sai taji dama ba ta dawo gida hutu ba, to ina zaki zauna da baki dawo ba? Wata zuciyar ta tambayeta. Tsaki tayi mara sauti, gaskiya dole ta nemi dalilin tafiya wani guri tun kafin a saka ranar zuwan Yariman don gaskiya ba ta ko so ta haɗu da shi duk da ta san zai yi wuya ya zaɓe ta a matsayin matar da zai aura kamar yadda mahaifiyarta tace sannan akwai ƴan'uwanta mata wadanda ba ciki ɗaya suka fito ba kuma yawancinsu sun fita kyau sosai dole a cikinsu zai zaɓa. Amma duk da haka taji tana son taje wani guri daban tayi hutu a can musamman da hutun na su na wannan karon ke da tsayi sosai, ba za su koma makaranta ba har sai an saka ranar da za su fara jarabawar kammala jami'ar.
Juyi take da tunanin inda za ta tafi don gaskiya ba zata iya zama cikin gidansu ba tare da taje sashen Bayi ba, gefe guda kuma ba zata iya zama tana ɓata ran mahaifiyarta ba.
Ta sake a kan tanfatsetsen gadonta tana tunanin inda za ta tafi hutu, duk ƴan'uwan mahaifinta suna cikin Masarautar bare tace za ta tafi gurin dangin mahaifinta, ita ma mahaifiyarta ƴar cikin garin Bauchi ce don haka ba za ta iya zuwa nan ba, saboda ita gabaɗaya zaman garin Bauchin ne taji ba ta so, sai yanzu ta fara da na sani ƙin tafiya karatu wata ƙasar, da yanzu tana can hankalinta kwance ko kuma can za ta koma. Ita kaɗai ce cikin ƴaƴan mahaifinsu take karatu a Najeriya amma duka sauran wadanda suka gama da ma wadanda suke kan karatun ba a ƙasar nan suka yi karatun ba. Ita ma an so ta tafi wata ƙasar amma ta tubure sam ita a ƙasarta za ta yi karatu, duk masifa da hargowar da mahaifiyarta tayi a lokacin amma sam ta tubure hakan yasa mahaifinta yace a barta tayi karatun a inda take so, shi da kanshi ya sa aka bincika Jami'a mai zaman kanta a faɗin ƙasar nan don taje can tayi karatunta. Hakan kuwa a ka yi, wata babbar jami'a mai zaman kanta dake garin Kano a ka nema mata, Jami'ar da duk wanda ka gani a ciki toh cikin biyu ɗaya, ko dai ya fito ne daga gidan wani hamshaƙin mai kuɗi ko wani mai muƙami, ko kuma dai ya samu scholarship ne na damar karatu kyauta.
A yanzu haka ta na shekararta ta ƙarshe a jami'ar, kuma wannan hutun da ta dawo ne ƙarshe don daga shi sai dai ta dawo gida da shaidar kammala makarantarta.
Daga ƙarshe dai dole ta yanke shawarar za ta tafi gidansu mahaifiyarta da ke cikin garin Bauchin ta zauna a can har zuwa lokacin da hutunta zai ƙare. Ganin ta samu matsaya ne yasa ta miƙe ta shige toilet ɗin ta don yin alwalar sallar Isha'i da ake kira yanzu.
Tana zaune a inda ta idar da Sallar aka ƙwanƙwansa ƙofar ɗakin, umarni ta bayar a shigo. Hadimarta ce ta shigo ta ɗan rusuna ta gaida ta, da kai kawai ta amsa saboda har yanzu ranta a jagule yake.
"Ranki Gimbiya ya daɗe, me za a shirya miki na abincin dare?"
Fuska ta yamutsa tace"Bana buƙatar komai".
Hadimar za ta sake yin magana ta dakatar da ita ta hanyar faɗin, "Jeki kawai".
Da hanzari ta miƙe ta fita a ɗakin.
Ita ma miƙewa ta yi ta ninke sallaya da hijabin sallarta ta ajiyesu a mazauninsu, durowa ta nufa ta ciro Lafaya mai kyau ta naɗa a kan kayan jikinta. Sashin mahaifinta take son taje don tun dawowarta ba su wani samu sararin zantawa sosai ba, ga shi gobe take son tafiya gidan Kakanninta na gefen uwa.
Sai da ta jira aka yi mata iso kafin ta shiga babban falon na sa da sallama, tun kafin ta ƙara sa gurinshi yake tarbarta da ƙayataccen murmushi a fuskarsa, shi dai duk cikin ƴaƴansa babu ya Falmata shiyasa yake jinta sosai a ranshi, wani lokacin ya kanji Ina ma ace Falmata ɗa namiji ce da babu shakka idan ya sauka a karagar mulki ita zai naɗa a matsayin magajinshi.
Har ƙasa ta rusuna ta gaida shi kafin ta koma gefen ƙafarsa ta zauna, cike da farin ciki ya amsa gaisuwar yana shafa kanta.
"Allah Ya miki Albarka Faɗimatu".
"Amin Ya Allah Abiey". Ta amsa cikin jindadi.
Hira kadan suka yi kafin ta sako mi shi maganar tafiyarta, ya amsa tare da yi mata fatan alkhairi tare da bayar da sakon gaisuwa zuwa ga surukan na shi.
Daga haka ta yi mai sallama ta shige cikin gidan.
Washegari tun da wuri ta shirya ta nemi Baba Labaran ya kaita gidan Kakanninta da ke GRA, sai da ta isa kafin ta kira mahaifiyarta ta shaida mata cewa tana gidansu, aikuwa kamar ta sani masifa ta rufe ta da shi tare da faɗin ta tattaro ta dawo gida su fara shirye-shiryen tarbar Yarimah Ajmal, da Toh kawai ta amsa a ranta sannan ta kashe wayar. Amma a ranta tana fadin babu inda za ta koma har sai hutunta ya kusa ƙarewa.
********* Ni kam a ɓangarena al'amura sam babu sauƙi, Baba ya kafe da batun tafiya ta aikatau sannan da kan shi ya saka ranar tafiyar.
Kullum Umma cikin tausata take yi da daɗaɗan kalamai tare da yi min nasihar tsare mutuncin kaina a duk inda zan kasance, tare da kasancew mai gaskiya da riƙon amana, hakan yasa na rungumi kaddarata tare da fawwala dukkan lamurana ga Allah.
Ba tafiya aikatau ɗin ne ke damuna ba, karatuna da zai tsaya shi yafi komai baƙanta raina. Da ace Baba zai yarda da ya bari na sai na zana jarabawar ƙaramar Sakandire amma na san hakan ba abu bane mai yiwuwa.
Wata ranar Asabar tun da sassafe Hajiya Laure ta iso gidanmu don ɗaukata, ba ta jima da zuwa ba Baba ya ƙwalla min kira tare da faɗin na fito mu tafi, ina kuka ina komai tare da ba a Baba hakuri amma ya murtuke fuska yana daka min tsawar na wuce mu tafi.
Haka na rabu da Umma cike da alhini da tunanin ya za ta kasance babu Ni.
Tafiyar da ke tsakanin garin Gaya da Birnin Kano ba mai nisa ba ce, don haka ba mu jima ba muka isa. Kai tsaye kuma adaidaita Hajiya Laure ta tare mana ta faɗa mai sunan wata anguwa suka yi ciniki muka shiga ya ja muka tafi.
A cikin adaidaitar Hajiya Laure ke ƙara shaida min cewa nayi taka tsantsan da duk wasu dokoki da masu gidan za su shimfiɗa min idan ba haka ba kuma korata za su yi, idan suka kore ni kuma na janyo wa kaina asara da mahaifina asara don kuwa duk cikin gidajen da take kai ƴan aiki ba ta taɓa kai wata irin gidan da za ta kaini ba.
Ni dai da toh kawai na amsa, amma a raina addu'a nake da fatan tun yanzu su ce ba za su ɗauke ni ba ma ba sai an kai wani lokaci ba.
Da kwatancen da take yi wa matuƙin adaidaitar muka iso gaban wani tanfatsetsen gida na alfarma, duk da yanayin da nake ciki na ƙunci amma sai da na kasa ɗauke kai daga ƙare wa gidan da Anguwar kallo sosai. Lallai akwai kuɗi a ƙasar nan sai dai suna hannun masu hanyar samunsu.
Da alama Mai gadin ya shaida Hajiya Laure, ganin yadda suka gaisa faran-faran sannan ba tare da ya tambaye mu daga inda muke ba ya buɗe mana ƙofar muka shiga.
Ashe banga komai a waje ba, don kuwa faɗar tsaruwar cikin gidan ɓata baki ne.
Sai da muka yi tafiya mai ɗan nisa kafin muka iso wata ƙofa, da kanta ta sa hannu ta buɗe muka shiga, wani dogon lungu muka bi har muka ƙara zuwa jikin wata ƙofar, wannan karon wani abu ta matsa, ba mu jima ba ƙofar ta buɗe, wata matashiyar yarinya ce ta buɗe ƙofar tare da yi mana sannu da zuwa. Ita tayi mana iso har wani babban falon da zan iya kira da Aljannar duniya.
Bayan mun zauna ne ta ce bari ta kira mana Hajiyar gidan, da to kawai Hajiya Laure ta amsa.
Tun ina saka ran zuwan Hajiyar har na sadaƙar cewa ba za ta fito nan kusa ba, haka muka ci gaba da zama har zuwa wani lokaci.
A cikin barcin da ya fara ɗaukata na ji wani sassanyan ƙamshi ya gauraye da numfashin da nake shaƙa, ba shiri na buɗe ido don ganin daga inda wannan ƙamshi ke tahowa.
Wata hamshaƙiyar mata ce ta sauko daga benen dake cikin falon, ba yabo ba fallasa ta ƙaraso ta zauna a daya daga cikin manyan kujerun falon ita ma. Hajiya Laure ce ta fara gaisheta, ta amsa a yatsine kafin nima na ɗan matsa tare da ɗaga murya yadda za ta ji Ni na gaisheta, sai da ta kalleni sosai kafin ta amsa sannan ta maida dubanta ga Hajiya Laure ta ce, "wannan ce ƴar aikin?"
Cike da girmamawa Hajiya Laure amsa da, "I, ita ce Hajiya''.
Fuska ta yatsina kafin tace, "Amma gaskiya tayi ƙarama sosai. Bana jin Hajiya Kaka za ta karɓeta".
Wani sanyi naji a raina ina fadin ashe addu'ata ta karɓo, sai dai murnata ta koma ciki da naji Hajiya Laure ta amsa da faɗin, "Ai da yardar Allah ma za ta amsheta saboda yarinyar tana da kwazon yin aiki".
"Ba na ce ba, amma gaskiya zai yi wuya don an kai mata wadanda suka ɗare wannan a komai ma amma ta kaɗo su. Ki barta dai ki je duk yadda ake ciki zan miki waya". Hajiyar ta faɗa tana buɗe wata jaka dake gefenta, rafar kuɗi ƴan dubu-dubu ta ciro ta miƙa wa Hajiya Laure.
Jiki na rawa ta karɓa tana zuba godiya.
A raina nace lallai dole Hajiya Laure ta takura Baba ashe riba mai tsoka za ta samu, duk da bansan nawa bane amma babu shakka wadannan kudin sun ɗara dubu hamsin. Wanda za a ba wa dubu Hamsin a irin wannan lokaci haka siddan ai dole ya hanzarta yin abin da aka umarce shi da yi.
Hajiya Laure ta miƙe ta yi wa Hajiyar sallama ta fita ba tare da ta sake waiwayo inda nake ba, wasu hawaye suka sauka a kuncina, ko wace irin rayuwa zan yi a nan? Dan tun daga yanayin Hajiyar sai na fuskanci kamar ba ta son talakawa.
Ba a jima ba ita ma Hajiyar ta mike ta haura saman benen. Nan na ci gaba da zama Ni kaɗai, TV din dake kunne ne yake dan ɗebe min kewa amma a raina tunanin Ummata kawai nake yi.
Na jima a zaune a wajen kafin wannan budurwar da ta fara yi mana iso ta shigo cikin falon, inda nake ta kalla tace, "Ance ki zo mu tafi, direba zai kai mu na raka ki inda zaki fara aiki".
Da to kawai na amsa sannan na miƙe na bi bayanta kamar raƙumi ta akala, har muka fito farfajiyar gidan.
A nan muka iske direban na jiranmu, ba ɓata lokaci muka shiga motar ya ja muka fita daga gidan. Mu ɗan yi doguwar tafiya kafin muka shigo wata anguwa da babu yawaitar manyan gidaje a ciki ba kamar Anguwar da muka baro ba. A gaban wani madaidaicin gida direban ya yi horn, sai da Mai gadin ya fara leƙowa ya kalle motar kafin ya koma ya buɗe babbar ƙofar don direban ya shiga da motar ciki.
A farfajiyar gidan muka bar direban suna gaisawa da Mai gadin, mu kuma muka shige cikin gidan. Da sallama muka shiga ƙayataccen falon da bai cika girma ba amma an ƙawata shi sosai, tsohuwar matar da hutu da jindadi ya ɓoye kaso hamsin na tsofanta muka tarar a falon kwance a kan doguwar kujera, shigowarmu yasa ta miƙe zaune tana kallonmu. Har ƙasa ta durƙusa ina gaida ta saɓanin wacce muka zo tare da ta zauna a kan kujera tana gaishe ta, da fara'a ta amsa gaisuwar ba kamar Hajiyar da muka rabo ba. Nan ta umarce Ni da na zauna a kan kujeran amma sai na noƙe.
Budurwar nan ta kalleta ta ce, "Hajiya Kaka ance na rakota ki ganta idan tayi miki sai a barta a nan".
Da murmushi a fuskarta ta ce, "Hansatu tashi maza ki bi direba ku koma, ki faɗa wa Uwargidan ta ku wannan karon tayi abin kirki. Don kuwa Ni na ga abokiyar zama".
"To" shi ne kawai abin da Hansatu ta faɗa sannan ta mike tana fadin, "Sai anjima Hajiya Kaka".
"Ko baki fada ba ai zan jima, wato zama da maɗaukakin kanwa yasa duk kun samu farin kai, Gara dai ku yi wa kanku karatun ta nutsu ku daina kwaikwayon mugun halin Uwar ɗakin ta ku. Shi da ke direban isasshe ne kin ga ai ko arzikin gaisuwa ban samu ba". Hajiya Kaka, kamar yadda naji Hansatu ta ambata ta faɗa cike da masifa.
Ita dai ta fice da sauri ta barta tana ci gaba da faɗa. Sai da tayi ta gaji kafin ta waigo gare ni tayi murmushi tace, "Ƴan nan kinji Ina ta faɗa ko? Sam wadannan yara ba su da kirki zama da Zara'u yasa suke koyon ɗabi'unta".
Ni dai murmushi kawai nayi ba tare da nace uffan ba.
"Ƴar nan mene ne sunanki?" Ta tambayeni.
"Suna na Hauwa Jiddah". Na fada kaina a ƙasa.
"Allahu Akbar, sunan wata ƙawata tun ta ƙuruciya amma ta jima da rasuwa. Ki saki jikinki da Ni kinji ki ɗauke ni tamkar Kakarki, ba Ni da damuwa idan kika fahimce ni. Fatana dai ki kasance mai gaskiya da riƙon amana tare da girmama na gaba da ke, sannan ki zama mai tsabta don bana son ƙazanta ko kaɗan, shiyasa har yau aka kasa samu ƴar aikin da zan iya zama da ita. Amma ke kam tun daga sanda kuka shigo naji kin kwanta min a rai shiyasa ma ban wani damu ba nace a barki a nan. Kina fahimta ko?".
Kai na gyaɗa cike da gamsuwa da bayananta.
Sannan ta ci gaba da cewa, "Ba wani aiki ba ne zaki dinga yi a gidan nan, tsabtace gida ne kaɗai shi ma iya cikin nan ne babu ruwanki da farfajiya don akwai masu gyara maza. Sai girki idan kin iya shi ma idan baki iya ba zan koya miki har zuwa lokacin da zaki kware. Kin ji ko, ki sake tamkar kina cikin gidanku ne, idan kika kiyaye abin da na fada miki zaki ji dadin zama da Ni sosai, sannan duk abin da baki fahimta ba ki tambayeni".
"Toh Hajiya" Na amsa cike da girmamawa.
Zan iya cewa na samu kwanciyar hankali sosai a sabuwar rayuwar da na fara a gidan Hajiya Kaka.
Mun shaƙu sosai sannan tana sakewa da Ni mu yi hira, tana bani labarai irin na rayuwar mutanan da.
A wajenta na samu labarin cewa gidan da aka fara kai Ni gidan ɗanta ne wanda shi kaɗai Ni gudan jininta a duniya, Hajiya Zara'u kuma ita ce Uwargidansa, akwai Amaryar wanda a can ƙasar waje inda yake aiki ya ajiyeta sai dai duk sanda zai zo hutu ya kan taho da ita da yaranta biyu don su za ga dangi.
Hajiya Zara'u ita ta zaɓi zaman Nijeriya, a cewarta ba za ta zauna cikin turawa da ba su da daɗin sha'ani ba, sai dai ta kanje hutu wani lokacin tayi kwanaki ta dawo. Yaranta na haihuwa uku ne, Abdallah wanda ke tare da Babansa a ƙasar waje yana karatu, sai Hamida da tayi aure da ƴaƴa biyu sannan Najwa da yanzu haka take aji biyar a Sakandire.
Sai dai a cewar Hajiya Kaka duk cikin ƴaƴan Hajiya Zara'u Abdallah ne kawai na ƙwarai, amma Hamida da Najwa halin uwarsu suka yi, wato girman kai da ƙyamar talaka.
Ni ma na bata labarina a takaice, ta nuna tausayinta matuƙa sannan ta sha alwashin taimakamin. Ba mu yi sati da yin maganar ba ta sa aka nema min gurbin karatu a wata makarantar ƴaƴan manya, na yi murna sosai har na rasa kalmomin da zan yi amfani da su wajen yi mata godiya.
Kasancewata mai ƙwazo ya sa ranar da aka yi min jarabawar gwaji aka mayar da ni ajin da na baro wato aji uku na ƙaramar sakandire. Ni ma na sake shiga cikin ɗalibai a karo na biyu.
A yanzu ba Ni da sauran wata damuwa sai tunanin Ummana wanda kullum da ita nake kwana na tashi a raina, sannan duk abin da zan yi tana nan maƙale a raina. Sai dai na yanke a raina idan an kwana biyu zan tambayi Hajiya Kaka ta barni na je na gano ta ko da ba zan kwana ba.
Lallai dole na godewa Babana da ya yanke shawarar kawo Ni Birni duk da a na shi ɓangaren ba da wata kyakkyawar manufa ya yi hakan ba.
A kullum idan na yi sallar Asubahi bana komawa bacci, da na kammala azkar ɗin safiya zan fara gyare-gyaren gida. Idan na gama sai na dafa mana abin kari, duk da yawancin lokuta sauran abincin da muka ci da dare muke ɗumamawa da safe mu ci, don ita Hajiya Kaka babu ruwanta.
Idan na kammala hada kalaci kuma sai na je nayi wanka na yi shirin makaranta, bakwai da rabi zan yi mata sallama na tafi. Sai kuma ƙarfe hudu kafin na dawo, ƙarfe biyu muke tashi a makarantar boko, sai masu islamiyya su shiga kuma Ni ma ina cikin masu tsaya karatun Islamiyyar shiyasa bana dawowa gida da wuri.
Idan na dawo na huta kuma sai na kara gyara gida na shiga Kicin.
Haka rayuwar ta zo min da sauyi kuma ina jin dadin wannan sauyin rayuwar sosai tare da yi wa Allah godiya..
Allah kenan mai sauya al'amura cikin ƙanƙanin lokaci da mutum bai taɓa tsammani ba, ban yi zaton cewa zan yi rayuwar jindadi nan kusa a rayuwata ba sai ga shi ya zo min a lokaci ƙanƙani.
Na maida hankali sosai wajen karatuna musamman da muke shirye-shirye zana jarabawar kammala ƙaramar sakandire, ina so na fito da kyakkyawan sakamakon da zan iya amfani da shi na samu gurbin karatu a babbar sakandare, kamar yadda Hajiya Kaka ke faɗa min lokuta da dama idan mun zauna. Ta kan ce a yanzu ilimi shi ne gatan kowane Ɗan'adam don kuwa rayuwa babu ilimi ma ba za ta yi kayan gani ba.
Don haka na jajirce ko don na ƙara ƙarfafa mata gwiwar ci gaba da ɗaukar nauyin karatuna kamar yadda ta ɗauki alƙawari, gefe guda kuma Ina son cika burin Ummana na ganin na yi karatu.
****** Sai da hutunta ya rage saura kwanaki kaɗan kafin ta shirya ta koma cikin Masarautar, a ranar da ta koma ko gaisuwarta Mahaifiyarta ba ta amsa ba saboda rashin dawowarta gida har Yarimah Ajmal ya zo ya tafi duk da har zuwa wannan lokacin bai faɗi wacce ya zaɓa ba daga cikin ƴaƴan Sarkin.
Ita dai haƙuri kawai ta ba ta tare da tausarta da cewa kila Allah Ya tanadar mata wanda yafi Yarimah Ajmal din ne shiyasa ba su haɗu ba, da haka ta shawo kanta suka shirya.
Da haka ta gama sauran kwanakin da suka rage mata ta shirya komawa makaranta.
Cike da alhini ta rabu da ahalin gidansu, kamar koyaushe Baba Labaran ne zai mai da ita duk da cewa jirgi aka so ta bi amma sam ta noƙe shiyasa tun da wuri suka ɗauki hanyar Kano don gudun ka da Baba Labaran din ya yi dawowar dare saboda shi a ranar zai juyo.
Wannan karon a baya ta zauna idan ta gaji da zaman sai ta kishingiɗa, jefi-jefi suna hira da Baba Labaran a haka har tafiyar ta su tayi nisa.
Sanda suka shigo garin Gaya tana kishingiɗe ba ta lura da sun shigo ba sai da Baba Labaran ya yi magana ta mike da sauri.
"Ranki ya daɗe, kin ko yi tambaya a kan yarinyar nan"
"Wace yarinya Baba Labaran?". Ta tambaya tana gyara zama.
"Yarinyar da kwanakin baya muka hadu da ita a wata tasha da ke nan gaba, wacce kika ce tana miki kama da wanda kika sani a cikin Masarauta".
Ya yi mata bayani.
Kai ta dafe ta ce, "Wallahi na sha'afa, kuma ka ga ban zauna a gida sosai ba wannan karon shiyasa. Ai ina ga ka biya ta wurin da mu ma na san yanzu haka ta fito tallar".
Kai ya gyaɗa yace, ''To ranki ya dade, ai na lura kin damu da lamarin yarinyar sosai ne shiyasa na ce bari na tuna miki dan na lura kamar baki san mun shigo gaya ba ma".
"Ban lura ba sam". Ta faɗa.
Lokacin da suka iso tashar da kanta ta fito a motar bayan Baba Labaran din ya nema wa motar ma'ajiya. Tun da nesa ta hango gurin zaman Jiddah babu kowa amma duk da haka ba ta karaya ba ta nufi wajen Baba Labaran na biye da ita a baya.
Dube-dube ta fara yi amma ba ta ga ko me kamar Jiddah ba sai ƴan talle da ke zuwa suna zagayeta da abubuwan da suke saidawa ko za ta siya.
Shiru tayi kafin ta yafito wata yarinya ta ba za ta wuce sa'ar Jiddah ba, da zuwan yarinyar ta sauke robar cin-cin din dake kanta don a zatonta Falmata siya za ta yi.
"A'a ba siya zan yi ba, tambayarki nake so na yi don Allah". Falmata ta faɗa tana taya ta rufe murfin robar da ta buɗe.
Robar ta maida kanta kafin tace, "To Allah yasa na sani".
"Yauwa. Dan Allah akwai wata yarinya da ke zama a nan, tana sai da dafaffen ƙwan zabi kin san ta?"
Shiru yarinyar tayi alamar tunani kafin lokaci guda kuma tayi dariya tace, "Jiddah ce ko? Don ita kaɗai ta ke zama a nan duk sanda ta zo talla".
Da murmushi mai kamar dariya Falmata ta amsa da "E. Ita ce ashe kin gane ta, yau ba ta zo bane".
"Woo! Ai Jiddah ta kusa wata uku bata kawo tallah yanzu, mun ji labarin ance wai ta tafi aikatau Birni." Yarinyar ta faɗa tana riƙe haɓa.
"Aikatau kuma?". Falmata ta maimaita tana ware ido.
"E ta tafi Birni aka ce mana".. Yarinyar ta ba ta amsa tana juya wa da sauri saboda kiranta da wani mutum ya yi.
Shiru tayi tsaye a gurin tana nanata kalmar aikatau a ranta, gaskiya Wannan labarin bai yi mata daɗi ba ko kaɗan, tana son yarinyar har ranta kuma ta fahimci yarinyar kamar tana cikin wata damuwa. A waccan ranar rashin isasshen lokaci ne yasa ba ta samu damar tattaunawa da ita sosai, sai yanzu take da na sani rashin rubutawa Jiddah numbarta ta san duk rintsi ai watarana Jiddah za ta kirata.
Jiki ba laka ta juya ta nufi gurin da suka ajiye Mota ta shige, wasu hawaye taji sun sauko a kumatunta da ba za ta iya tantance dalilin saukarsu ba amma ta alaƙanta hakan da rashin samun Jiddahn.
"Kiyi hakuri ranki ya daɗe, idan da rabo watarana za ku haɗu. Allah Ya sada fuskokinku da alkhairi". Cewar Baba Labaran.
"Amin Ya Allah" ta amsa cikin sanyin murya.
A haka suka ci gaba da tafiyar babu wanda ke magana a cikinsu ba kamar yadda suka faro na, har suka iso cikin garin Kano.
Kai tsaye gidan wata ƙawar mahaifiyarta da take zama Baba Labaran ya nufa da ita, don a tsarin Falmata ba za ta iya zaman cikin makaranta ba ko kuma ta zauna a wani gida daban ita kaɗai, shiyasa ta zaɓi zama tare da ƙawar Mamanta.
A gaban wani babban gida Baba Labaran ya danna horn, mintuna kaɗan Mai gadin ya bude ƙaramar ƙofa ya leƙo, ganin motar yasa ya washe baki tare da komawa ya buɗe ƙofar da hanzari, suka shigar da motar ciki.
Duk wanda ya ganta zai fahimci cewa lallai akwai abin da ke damunta, a haka ta fito daga cikin motar tana amsa gaisuwar da Mai gadin ya iso yana yi mata, ɗan risinawa kaɗan tayi saboda ya manyanta kamar Baba Labaran don za su iya zuwa sa'anni ma.
Ta baya taji an rungumeta tare da faɗin, "Oyoyo Anty Falmata".
Murmushi tayi mai sauti kafin tace, "Najwa wannan cakumar ai sai ki karyamin ƙasusuwa".
Wacce aka kira da Najwa ne ta zagayo gaban Falmata tana dariya tace, "Haba Anty Falmata sai kace wata Babyn roba. Tun ɗazu Mummy ta kasa zama tana jiran isowarki, ga shi kin kulle waya ba a samunki duk ta kasa sukuni".
Dariya ta ɗan yi ta rike hannunta tana faɗin, "Mu je Mummy ta ganni hankalinta ya kwanta".
Tare suka nufi ƙofar Babban Falon gidan suka shiga, falo ne na alfarma da aka ƙawata shi da kayan ado na zamani.
Hajiya Zara'u na zaune a kan doguwar kujera tana danna waya suka yi sallama suka shigo.
Da kanta ta miƙe ta taro Falmata tare da rungumeta tana faɗin, "Haba ɗiyata ya zaki kashe waya gabaɗaya kinsan hankalinmu ba zai kwanta ba".
Murmushi kawai tayi tana sadda kai ƙasa.
"Na ga alamun gajiya sosai tattare da ke, ki je kiyi wanka ki huta sai ki sauko ki ci abinci". Hajiya Zara'u ta faɗa.
"Toh Mummy" ta amsa tana nufar hanyar da za ta sadata da sashe guda da aka ware mata kamar wata matar gida, har ta ɗan yi gaba kuma sai ta tsaya ta waigo ta kalli Najwa ta ce, "Najwa dan Allah ki saka ƴar aiki ta kai wa Baba Labaran abinci daga nan sai ta shigo min da kayayyakina, zuwa anjima kaɗan zai koma gida".
Yanayin fuskar Najwa ya canja amma sai tace, "Toh" kawai.
Ita dai Falmata ta wuce abin ta, don wannan na ɗaya daga cikin halayen ƴan gidan da ba ta ƙauna wato nuna ƙasƙanci ga wadanda ke ƙasansu.
Ita dai ba za ta iya hakan ba ko a wane mataki ta tsinci kanta. Amma dai tunda zama ya kama ta da mutane dole za ta koyi haƙuri da halayensu.
***** A yau ne muka kammala jarabawar gama ƙaramar sakandire, ina cikin farin ciki sosai mara misaltuwa. Babu abin da nake yi sai godiyar Allah a cikin zuciyata, tare da gode wa matar da Allah Ya hadani zama da ita.
Ina cike da farin ciki matuƙa musamman idan na tuna cewa Hajiya Kaka tayi min alkawarin idan na gama jarabawa za ta sa direba ya kai Ni na gano Ummata.
Yau ko Islamiyya ban tsaya ba na nufi gidan cike da farin ciki da ya kasa ɓoyuwa a fuskata.
A farfajiyar gidan na ci karo da wasu manyan-manyan motoci na alfarma da ban taɓa ganin sun zo ba duk zamana a gidan. Da alama baƙi Hajiya Kaka ta yi yau, na fada a raina sannan na tunkari ƙofar shiga Na shiga falon da sallama a bakina, Hajiya Kaka na tarar da wani magidancin mutum, tana zaune a kan kujera shi kuma yana zaune a ƙasa gefenta. Tsananin kamarsu da na gani ne yasa na gaskata cewa lallai wannan shi ne ɗan ta da take bani labari.
Cike da ladabi na ƙarasa na durƙusa har ƙasa na gaida shi, da fara'a ya amsa yana saka min albarka. Ƙwalla na ji ta taro a idona, ina ma ace mahaifina ne haka ke samun Albarka da fatan nasara a rayuwa.
"Meyasa yau baki tsaya a Islamiyya ba". Hajiya Kaka ta tambaya tana tsare Ni da ido.
Dariya na ɗan yi kafin na ce" Babu komai. Kawai ina murna ne yau mun kammala jarabawar".
Ita ma dariyar tayi kafin ta ce, "To Allah yasa a fito da sakamako mai kyau. Wannan Ɗa na ne da nake baki labarinsa, ki ɗauke shi tamkar mahaifi kinji ɗiya Albarka".
Kallona ya sake yi kafin ya ce, "Ai Hajiya jikar ta ki na da hankali sosai".
Jin abin da ya faɗa ya sa ta washe baki ta ce, "Ai sai ma ka zauna da ita tukun".
"Hajiya Kaka bari na shiga". Na faɗa ina miƙewe.
"Kin ga ɗebo masa dambun naman nan da kika yi shekaran jiya, kuma kaɗan zaki ɗebo ba da yawa ba".
Da to na amsa na nufi hanyar kicin, ina jinta tana daɗa jaddada min cewa kadan zan ɗebo, Ni kuwa wata ƙaramar roba madaidaiciya na samu na zuba dambun a ciki sosai kafin na fito.
Haba ta riƙe tana kallona lokacin da na durƙusa ina mika mai robar, kafin ta harare ni ta ce, "Au da nace ki debo kaɗan shi ne kika ɗebo da yawa haka".
Dariya ya yi kafin yace, "Hajiya rabo na ne".
"Saboda kai ne kayi min ko, ko kuma matarka da bata da kirki ka turo tayi min. Saboda rashin kirki wai ace mace ta san da dawowar mijinta amma ta kama hanya ta fita". Hajiyar ta faɗa cikin faɗa.
Sai yanzu na fahimci dalilin maganarta ya farko, Hajiya Kaka ba dama, Ni dai dariya kawai na yi na wuce ciki.
Bayan nayi sallah ne na yi tunanin shirya kayana a cikin wata madaidaiciyar jaka cikin wadanda Hajiya Kaka ta siya min.
Kasancewar gobe Juma'a yasa nake son tafiya wajen Ummata sai na dawo ranar Lahadi da yamma tunda a Islamiyya ba mu yi hutu ba.
Duk da na so shiga kasuwa na yi wa Ummata siyayya sosai da kuɗaɗen da nake da su wanda na tara. Don kullum idan zan tafi makaranta Hajiya Kaka ɗari biyar take bani wai ko zan ga wani abin siya tunda ba da wuri nake dawowa ba, da fari bana karɓa amma da ta nuna ɓacin ranta sai na fara karɓar musamman da tace min ko da ba zan yi amfani da shi a makaranta ba na dinga ajiyewa watarana kila na bukaci yin amfani da su.
Dalilin da yasa kenan na ke tara kuɗin kullum. Sannan akwai ƴan'uwa da abokan arziki dake kawowa Hajiya Kaka ziyara, duk wanda ya zo idan zai tafi sai ya bani wani abin.
Ga uwa uba tarin kayan da ta siya min kuma take kan siyamin, tare muke zuwa duk inda za ta je matsalar ba ina gida, lokuta da dama ma ko za ta fita tana hakura ne sai na dawo da yamma mu tafi. Sannan idan muka gama uzurin da za mu yi mu kan biya kanti ta yi ta zabar min abubuwan ƴanmata, dama Ni Ko tace na zaba bana iya zabar wasu abin kirki.
Duk kayan ƙyale-ƙyale na mata wanda ake yayi tana siya min, ba Ni da wani abu da zan iya saka ma wannan Baiwar Allah da shi sai dai na mata fatan gamawa da duniya lafiya kuma lahirarta tayi kyau.
Ina tsaka da shirya kayan a jaka Hajiya Kaka ta ƙwala min kira dan haka na miƙe don zuwa na amsa kiran na ta.
"Hajiya ga Ni".
"Na ji ki shiru ne, ki zo nan ki zauna mu yi hirar tare, don na san warhaka gobe kina can kin barni da kewa".
"A'a Hajiya ba tare za ku tafi ba?".
"Da direba za su tafi idan zai koma ɗaukota sai na bi shi mu dawo tare".
"Allah Ya kai mu goben".
"Amin. Ya kamata ka isa gida ka huta, nima zan dan kwanta kafin La'asar". Hajiya Kaka ta faɗa tana miƙewa.
"To Hajiya, a huta lafiya". Ya faɗa yana miƙewa shi ma.
Sallama ya mana ya tafi.
Washegari tun da wuri na gama dukkan ayyukan da zan yi, Hajiya Kaka na tsokana ta da faɗin wannan zumuɗin kar na tafi na ƙi dawowa fa, Ni dai dariya kawai nayi.
Ƙarfe goma sai ga Daddy, kamar yadda Hajiya Kaka tace na dinga kiransa da haka.
Bai wani jima ba ya ce na fito direbansa ne zai kai ni, duk da Hajiya Kaka tayi ƙorafin cewa ta riga ta yi magana direbanta ne zai kai ni amma haka ya ba ta hakuri, dubu ashirin Hajiya Kaka ta bani ta ce na kai wa Ummata kafin ta zo, shi ma Daddy da muka fito rafar kuɗin da bansan nawa bane ya bani. Tsabar farin ciki kuka na fashe da shi sosai da kyar Hajiya Kaka ta rarrashe Ni tare da jaddada min cewa tana tafe ranar Lahadi.
Tsananin farin cikin da na ke ciki na ganin Ummata da zan yi yasa nake ganin kamar direban baya sauri da motar, amma dai na gimtse na yi shiru muka ci gaba da tafiya.
Sanda muka iso garin haka na dinga kwatanta masa har muka iso ƙofar gidanmu. Gidan yana nan yadda yake sai dai wasu ƴan gyare-gyare da aka yi a gaban gida.
Da hanzari na yi shirin buɗe ƙofar sai dai na gagara, direban ya yi dariya ya ce, "Zumuɗinki ya yi yawa".
Dariyar kawai nima nayi kafin ya danna wani guri a gaban motar sannan yace na buɗe.
"Ga shi garin na ku babu yara, ko zaki nemo wadanda za su taya ki kwashe kayan da ke boot". Ya faɗa shi ma yana buɗe tasa ƙofar.
Zagayawa ya yi ya buɗe Boot ɗin motar ya kira Ni.
Kayan abinci ne maƙil a ciki da wasu kayayyakin amfani na yau da kullum.
"Alhaji ne yace a sauke miki wadannan kayan idan mun iso". Ya faɗa yana ƙoƙarin fara fitowa da kayan.
Shiru nayi, don har ga Allah na rasa maganar da zan yi saboda yadda nake ji a raina.
Ina kallonshi yana sauke kayan na kasa komai bare nayi ƙoƙarin shiga gida kamar yadda nayi niyya tun farko.
Ana haka sai ga Babana ya fito daga cikin gida, sai ya tsaya ya kalleni sosai har na tsargu da cewa ko masifar ta sa zai yi min sai na ga ya ƙaraso kusa yace, "Wannan kamar Jiddah ko?"
Da hanzari na durƙusa nace, "E. Baba ina wuni".
Ga mamakina sai na ga ya amsa fuska ba yabo ba fallasa ya ƙarasa kusa da direban suna gaisawa, ganin haka yasa na nufi cikin gida da sauri da zumuɗin ganin Ummata.
Da sallama na shiga, Kabir na gani zaune a ƙofar ɗakin Inna yana cin gyaɗa dafaffiya.
"Laahh! Adda Jiddah kin dawo ne? Kin ga yadda kika koma kuwa?". Yana faɗa yana dariya tare da miƙewa yana ƙarasowa inda nake.
"Kabir kenan, ina Nazir yake?". Na tambaya ina shafa kanshi.
"Nazir suna gidan Baba Kaltume shi da Innarmu yau ana bikin Adda Bara'atu. Nima ban jima da dawowa ba".
"Toh Sannu da gida". Na faɗa ina nufar ɗakinmu..
"Adda Jiddah ai Ummanki ba ta dawo ba". Ya faɗa yana biyo bayana daidai lokacin da na ɗaga labulen ɗakin.
Da mamaki na kalle shi na ce, "Ina ta tafi Kabir?".
Zama ya yi a ƙofar ɗakin kafin ya fara magana, "Ai baki sani ba Adda Jiddah da kika tafi Innarmu tace wai bata samun kuɗi yanzu shi ne tace wai kawai a dinga dafawa Ummanki Abinci tana kai wa makarantarku. Shi ne Baba ya yi ta wa Ummanki faɗa yana cewa wai zai korata idan tace ba za ta kai tallen ba. Yanzu sai can anjima za ta dawo idan abincin ya ƙare".
Juwa na ji na neman kada Ni, kalmar Tallah kawai ƙwaƙwalwata ke ambata, da ƙyar na kalle shi na ce, "Kabir yanzu Umma na wajen tallar kenan.?"
"E. Ai anjima zan koma na taya ta ɗauko kaya idan abincin ya ƙare. Kullum Ni nake rakata na dawo idan lokacin ya yi sai na koma na taya ta kwaso kayan, kuma kinsan me Adda Jiddah kullum Ummanki sai tayi kuka"..
"Ke Jiddah!". Na jiyo murya Baba yana ƙwala min kira tun daga zaure.
Shiru nayi ban amsa ba har ya shigo cikin gidan da kaya niƙi-niƙi a hannunsa ya ajiye, dakuwa ya min kafin ya ƙara faɗin, "Kin bar mutum a tsaye ba zaki kawo masa ruwa ba ehee! Kai Kabir zo ka taya Ni shigo da kaya. Kiyi maza ki kawo masa ruwa duk da yace tafiya zai yi amma bai kamata ya zo da abin alheri haka ya tafi ko ruwa bai sha ba". Yana gama faɗin ya sake yin waje da sauri.
Ba ni da ikon yi masa turjiya tunda har yanzu a matsayin mahaifina yake, jiki babu laka na isa madafin Inna na ɗauko kofin silba mai murfi na ɗebi ruwa a randa na nufi waje da shi, suna ta ƙoƙarin shigo da kaya shi da Kabir, a jikin motar na tarar da direban na miƙa mai ruwan ya karɓa. Ba laifi ya ɗan sha sosai kafin ya miƙo min kofin ya ce, "Bari na wuce, sai zuwa jibin idan na kawo Hajiya".
"To na gode sosai, ka gaishe su, Allah Ya tsare hanya Ya sauke ka lafiya?" Na faɗa cike da dauriya.
Daga haka ya yi min sallama ya ja motar ya tafi, Baba na ɗaga mai hannu fuska a washe.
Juyawa nayi cikin gidan hawaye na sauka a kuncina, jakar kayana kawai na ɗauka na shiga ɗakinmu da shi. Ɗakin yana nan kamar yadda na san shi, ko ina tsab babu alamar ƙazanta. Allah Sarki Umma.
Ina jin Baba yana ta maganganu yana kara gode wa direban kamar shi ne wanda ya yi kyautan, Kabir kuwa na taya shi da murnar sun zama ƴan gayu.
Ni dai ina jinshi ban fito ba har sai da naji shiru alamun ya shige ɗaki kafin na miƙe na fito, Kabir da ke ƙofar ɗakin na yafito da hannuna. Da sauri ya taso ya iso inda nake, ba tare da nayi magana ba na ja hannunshi muka fita, sai da muka fito a gidan kafin na kalle shi na ce, "Kabir mu je ka raka ni wurin tallar Umma".
"Toh". Ya amsa min da shi kafin muka fara tafiya.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"... Abin da kaɗai nake ambata kenan sanda muka iso, da gaske Ummata ke Tallah, tana zaune a ƙasan wata bishiya da ke cikin tsohuwar makarantar da nake, ga kular abinci nan a gabanta da robobin da ake zubawa.
Wasu daga cikin ɗaliban da suka siya abincin suna zaune a gefe suna ci.
Kuka mai ciwo ya kwace min, daidai lokacin da Kabir ya sake hannuna ya nufi gurinta da gudu yana ƙwala mata kira. Da sauri ta ɗago tana kallonshi lokacin da ya ƙarasa inda take, da hannu ya mata nuni da inda nake tsaye.
Ai kuwa ta tashi a zabure tana ware ido cike da son tabbatarwa.
Da gudu na ƙarasa inda take na rungumeta tare da sake fashewa da wani kukan mai tsuma rai.
*"Jiddatulrahman!"* Ta faɗa muryarta na rawa.
..."Ummana". Na amsa ina sake fashewa da wani kukan mai tsuma zuciya, a hankali ta dinga shafa bayana har na sassauta kukan da nake yi, na ɗago daga jikinta ina ƙara kallonta sosai. Murmushi tayi tare da jan hannuna zuwa kan bencin da ta tashi, sai a lokacin na kula da yadda wasu daga cikin ɗaliban suka zagaye mu suna kallonmu.
"Umma mu tafi gida". Na faɗa ina kara damƙe hannunta sosai kamar wanda aka ce za a kwaceta.
"Ai abincin bai ƙare ba Jiddah". Ta faɗa tana kauda kai daga gareni da alama hawayen da ke son zubowa daga fuskarta ne ba ya son na gani.
Hannunta na saki na mike na isa wajen kular abincin. Sauran abincin babu yawa, don haka na shiga rabawa wasu daga cikin ɗaliban da har yanzu suke tsaye a wajen, sai na raba musu duka Umma na zaune tana kallona.
Bayan na gama na ce Kabir ya nemo almajirin da zai ɗauki kayan zuwa gida.
Da gudu ya tafi ba jimawa ya dawo da wani saurayin yaro.
Kayan na hada wa yaron suka fara yin gaba shi da Kabir. Kana daga baya na koma wajen Umma na ce ta taso mu tafi, ba musu ta miƙe sai dai na ga kamar jikinta ya yi sanyi, bansan dalili ba Ni dai na riƙe hannunta muka fito muka nufi gida.
"Gaba ɗaya kin canja Jiddah kamar ba ke ba, ina tunanin da addu'ar Allah Yasa ba wahala kike sha a inda aka kai ki ba". Umma ta faɗa da sanyin murya.
"Umma addu'arki ta riskeni har inda nake".
Nan na shiga ba ta labarin tun daga zuwana Birni har zamana da Hajiya Kaka da ɗumbin alkhairinta a gareni.
Farin ciki ya bayyana sosai a fuskarta, addu'a ta shiga kwararowa Hajiya Kaka Ni kuwa ina taya ta da amsawa da Amin.
Har muka iso gida hirar su Hajiya Kaka muke yi ko kadan Umma ba ta sako min hirar Baba ba da dalilin da ya sa ta aminta da zuwa wannan tallar.
Sanda muka isa gidan Baba na zaune a kan tabarma yana shan kayan marmari, duk cikin kayan da Daddy ya sako a motar ne. Ko da muka yi sallama ma bai amsa ba, Kabiru dake zaune gefenshi ne ya amsa tare da miƙewa ya nufo mu.
"Kai Kabiru karɓo min kuɗin cinikin na ajiye wa Innarku". Cewar Baba yana kauda kai kamar ba shi ya yi maganar ba.
Ita dai Umma ba ta ce komai ba ta shige ɗaki, nima bayanta na bi.
"Umma nawa ne kudin abincin ne?". Na tambaya ina bude jakata
"Dubu biyu ne da ɗari biyar duka". Ta amsa min tana zuba tagumi
Sabbin ɗari biyar na ciro daga cikin jakata na mike na nufi ƙofa ina kiran Kabiru, kudin na miƙa mai sanda ya zo nace ya kaiwa Baban Ni kuma na juyo daki.
Kusa da Umma na dawo na dafa ta, firgit! tayi alamar ta fara wani tunanin.
Tausayin mahaifiyar ta wa ya ƙara yin na so a cikin zuciyata, na san duk wannan abin tana yi ne don ni saboda kar Baba ya sake ta kamar yadda ya sha fada lokuta da dama a gabana.
"Umma!" Na faɗa a hankali.
Juyowa tayi ta kalleni tana murmushin da na tabbatar na yake ne.
"Jiddatuna". Ta faɗa tana kama Kumatuna.
Dariya ta bani sosai har sai da na ƙyalkyala.
"Umma meyasa kika da Baba yace ki dinga kai talla?". Na tambaya ina kallonta sosai.
Shiru tayi, har na cire ran za ta yi magana sai kuma na ga ta gyara zama ta fara magana, don haka na nutsu ina saurarenta.
"Har yanzu ke yarinyace Jiddatuna, ba zaki fahimci wasu manyan dalilan da yasa lokuta da dama bana iya ja da wasu abubuwa da mahaifinki zai gindaya mana ni da ke ba. Ba don ba zan iya tankawa ba a'a sai don wani dalili da har yanzu baki yi girman da zan faɗa miki ba".
Numfasawa tayi kafin ta cigaba da cewa, "Magana ɗaya tak mahaifinki ya faɗa min a lokacin da na so ƙin amincewa da batun yi wa matarsa talla, kinsan mene ne?".
Kai na girgiza alamar a'a, murmushi tayi kafin tace, "Cewa ya yi idan ba zan iya ba sai dai na tattara na bar masa gidanshi. Na so yin hakan da fara sai kuma wata zuciyar ta gargaɗeni musamman da na tuna a halin da muka rabu kuma bansan wane hannu zaki fada ba. Na san idan na tafi zan jima ban dawo ba kila ke kuma a lokacin zaki dawo nemana, a yanzu da nake nan ma ya rayuwarki take bare ace kuma kin dawo kin tarar babu Ni. Wannan shi kaɗai ne dalilin da yasa na kasa bijire Umarnin mahaifinki".
Ajiyar zuciya a karo na ba adadi, lokaci guda kuma hawaye suka shiga zirya a kuncina. Jikinta ta jawo ni tana lallashina tare da share hawayen fuskata.
Mun jima a haka kafin daga bisani muka ware muna hira cikin annushuwa, kuɗin da Daddy ya bani na ciro muka kirga, Naira dubu hamsin ne. Ga kuma wanda Hajiya Kaka ta bani da wanda nake tarawa, daga ƙarshe da muka gama kirga kudin kusan dubu casa'in da ƴan kai.
Nan muka fara shawarar abin da za ayi da kuɗin. Daga karshe dai mun yanke shawarar Umma za ta fara sana'a sannan za mu siya wasu kayayyakin da ba mu da su na aiki.
"Umma kin ga yanzu tunda mun samu kudi sai kawai mu tafi wajen danginki, dama har da rashin kudin mota ma ko?". Na faɗa cike da zumuɗi, don har ga Allah ina son naje wajen dangin Ummata.
Ba ta amsamin ba har sai da na sake maimaita maganar, sannan tace, "Ke da zaki koma ranar Lahadi Jiddah".
"Umma ai idan na fada ma Hajiya Kaka za ta yarda, kin ji Umma za mu je ko". Na faɗa ina marairaicewa.
"Za mu yi maganar anjima". Abin da ya faɗa kenan kafin ta kishingida ta kwanta.
Nima kwanciyar nayi kafin daga bisani na mike na fita zuwa tsakar gida don na dafa mana abin da za mu ci, sai yanzu na fara jin yunwa ma dama safiyar ranar ban wani ci abincin kirki ba saboda zumuɗin zuwa gida.
Da taimakon Kabiru da ya yo min cefane na dafa mana shinkafa da miya har da kifi, dadina ɗaya tun da na fara girkin har na gama Baba bai fito ba dama Kabiru ya ce min bacci yake yi. Ita ma Umma nayi mamakin yadda har na gama bata tashi a baccin ba, koda yake akwai alamun gajiya sosai tattare da ita, ga kuma rashin kwanciyar hankali.
Sai da aka kira sallar azahar kafin na tashi Umma, ita ma tayi mamakin yadda ta yi bacci haka har tana tsokanata anya ba wani abin na bata ba.
Ni dai dariya kawai nayi cike da farin cikin yadda na ga Mahaifiyata cikin walwalwa.
Haka na wuni ina farin cikin kasancewata da mahaifiyata.
Ko da Inna ta dawo da yamma ta tarar da ni ba ta wani nuna maraba ba, har sai da Baba ya nuna mata kayan da Daddy ya bayar kafin ta fara fara'a da yashe baki. Surutai ta dinga yi barkatai ita a dole ta ba wa Baba shawara mai kyau na kai Ni aikatau, har tana fadin cewa idan ma na dawo da niyyar zama ne to kada Baba ya yarda dole zan koma idan ba haka ba shida abin arziki irin wannan har abada.
Kamar kowane lokaci babu wanda ya tanka a cikin Ni da Umma har suka gama maganganunsu. Ni dai kullum addu'ata Allah Ya ganar da Mahaifina ya fahimci cewa abin da yake yi ba daidai bane, tun kafin lokaci ya ƙure masa.
****Kwanaki biyun da nayi da mahaifiyata shaƙuwa mai ƙarfi ce ta sake shiga tsakaninmu har na fara tunanin anya ba zan hakura na cigaba da zama da mahaifiyata ba, ko da yake ba daga Ni bane yanzu koda Ina son zama Baba ba zai bari ba sannan a daya ɓangaren kuma ba zan iya yiwa Hajiya Kaka butulci ba. Sai dai na kuduri niyyar cewa daga yanzu duk wata zan dinga zuwa ina duba halin da mahaifiyata ke ciki kuma nasan ita ma Hajiya Kaka ba za ta ƙi bari ba.
Ranar Lahadi tun da safe na gama harhada kayana, duk da cewa bana son tafiya amma haka nan naji zaƙuwar zuwan Hajiya Kaka, lokaci bayan lokaci nake fita ƙofar gida na duba, abin har ya fara ba wa Umma dariya.
Shi kuwa Baba dake gefen ɗakin Inna a kishingide a kan tabarma da ya ga shige da ficen nawa ya yi yawa sai ya fara masifa.
"Baba Wanda nake aiki a gidansu ne za su zo ɗaukata na koma". Na faɗa sanda ya kirani yana tambayar ba'asin zirga-zirgar da nake yi.
Jin haka sai ya washe baki ya ce, "Ja'irar yarinya wato da ban tambayeki ba ba zaki fadamin ba, saboda kina so baƙin su zo mu ci kunya ko? Tashi ki bani guri".
Ni dai na mike na koma ɗaki na zauna, ina ji ya kira Inna yana faɗa mata tare da cewa wai ta shirya wa bakin abinci na musamman.
Tun ina zaman jira har bacci ya fara ɗaukata, don haka Umma tace na kishingida kafin su iso ƙila wani abin ne ya tsaresu a hanya.
Ban jima da kwanciya ba naji dirin mota, aikuwa na mike da hanzari na fita. Su Baba basa tsakar gida don haka kai tsaye na fice ƙofar gida.
Kamar yadda na tsammata kuwa, Hajiya Kaka ce da direban da ya kawoni.
Hannu Hajiya Kaka ta bude min, aikuwa da gudu na ƙarasa na shige jikinta ina dariya.
"Hajiya tun ɗazu nake ta jiran isowarku fa". Na faɗa ina karɓar jakar hannunta.
"Ke dai bari Jiddah, ai tun safe na so tahowa na cin da wannan yaron (Daddy take nufi) ke yi min ne yasa na fasa tahowa da wuri, tun safe ya aiko direba wai ya zo mu tafi, da yaji ba mu tafi ba shi ne ya zo da kansa. Ni kuma nace bani tahowa kuma kar ya yadda naji labarin ya zo". Ta faɗa cikin mita.
Dariya nayi nace, "Hajiya Daddyn".
"I mana".
Gaba na yi ita kuma ya biyoni a baya, da sallama muka shiga daidai lokacin da Baba da Inna suka fito daga ɗaki.
Umma ma tana tsaye a bakin ƙofa, sai dai mai shigowa dakin Inna zai fara gani.
"Wa'alaiki Salam, Maraba da zuwa". Inna ta faɗa tana nufo inda muke.
Ido Hajiya Kaka ta ware tana kallon Baba da shi ma na lura tun shigowarmu ita yake kallo.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Hasbunallahu wa ni'imal wakil! Wa na ke gani kamar Murtala?". Hajiya Kaka ta faɗa tana dora hannu a ka.
Umma dake ƙofar daki ita ma ta nufo gurinmu, ganin Hajiya Kaka yasa ta tsaya turus. Salati Hajiya Kaka ta ƙara saki tana kallon Umma.
"Fathiya!". Hajiya Kaka ta ambaci sunan Umma da ƙarfi.
Umma ta juya kanta da sauri daga kallon inda Hajiya Kaka take, ita kuwa salati ta cigaba da yi tana nanatawa. Shi ma Baba sai na ga ya koma ɗakin Inna da sauri.
"Ke Jiddah! Wadannan su ne iyayenki?". Ta tambaya tana nuna Umma da ƙofar da ɗakin Inna da Baba ya shige.
Kai kawai na gyaɗa don na kasa fahimtar komai.
Hannu ta sake tafawa tana gyada kai kafin tace, "E lallai dole rayuwarki ta zama wani iri Jiddah. Maza tattaro kayanki mu tafi ba zan barki a nan ba su lalata miki rayuwa".
Umma ta waigo da sauri tana kallonta.
Tsawa Hajiya Kaka ta dakawa Umma tace, "Zaki hana ni tafiya da ita kike zaremin ido?"
"Kaka!" Umma ta faɗa hawaye na sauka a kuncinta.
Tsaki Hajiya Kaka taja tare da kama hannuna muka fita waje, ƙoƙarin turani cikin mota take yi amma na turje.
"Shiga mana". Ta faɗa da muryar da ban taɓa sanin ta da ita ba duk zamanmu tare.
"Hajiya Ummata!". Na faɗa da rawar murya.
Hannu ta ɗaga kamar za ta mareni sai kuma na ga ta fasa, ɓacin rai ya bayyana sosai a kan fuskarta.
"Ummanki ta taɓa kai ki wajen wani daga cikin danginta?".
Kai na girgiza alamar a'a, murmushi tayi kafin tace, "To Ni ce mahaifiyarta".
Ido na zaro sosai ina kallon Hajiya Kaka na kasa magana, daidai lokacin da Umma ta fito daga cikin gida.
"Hajiya". Umma ta faɗa murya na rawa ga hawaye kwance a kuncinta.
Mota Hajiya Kaka ta bude ta turani ciki, wannan karon ba zan iya gardama ba saboda babu sauran laka a jikina. Ita ma motar ta shigo tare da ƙwalawa Direba da ke zaune a gefe kira.
"Shigo mu tafi". Ta faɗa tana rufe ƙofar.
Ina kallon yadda Umma ke kuka sosai, nima sai kukan ya taso min.
"Wannan ita ce mahaifiyarki da kika ba ni labarinta?". Hajiya Kaka ta waiwayo tana tambayata.
Kai na gyaɗa mata.
"Tsaya Direba". Ta faɗa cike da fada.
Da kanta ta sauke gilas ɗin motar ta kalli Umma dake tsaye tace, "Za ki iya zuwa mu tafi ko kuma har yanzu Murtala ya fiye miki alhalinki?".
Da sauri Umma ta nufo motar ta buɗe ta shiga gidan baya.
Babu bata lokaci direba yaja motar muka fara tafiya.
Shiru motar babu wanda ke magana sai shessheƙan kukan da Umma take yi a hankali.
"Kin dame ni". Hajiya Kaka ta faɗi.
Shiru Umma tayi, Ni dai na zama mutum-mutumi, da ido kawai nake kallon kowa.
Can Hajiya Kaka ta ciro waya a jaka ta fara kira, daga yadda take maganar na fahimci da Daddy take yin wayar.
"Ka nema mana jirgin da zai je Katsina yanzun nan, kai ma ka shirya don tare za mu tafi".
Shiru tayi da alama Daddyn magana yake yi, "Bansan ka da gardama ba Ɗan Albarka, kayi yadda na ce ɗin kawai. Mu hadu a filin jirgin".
"Yauwa to sai mun ƙaraso".
Daga haka ta kashe wayar.
Tunani kala-kala nake yi a ƙwaƙwalwata, musamman maganar da Hajiya Kaka tayi na cewa ita ce Mahaifiyar Umma. A ɓangare guda kuma yanayin da Umma ta shiga ya sa na gaskata hakan musamman da na ga ba ta yi wa Hajiya Kaka gardama ba. Ko wannan shine dalilin da yasa duk sanda na yi wa Umma maganar danginta take ƙoƙarin kaucewa? Ni dai ina cikin duhu amma zan yi hakuri har zuwa lokacin da za a warware min abin da yake ɓoye.
Har muka isa tunanin da nake yi kenan a raina, kai tsaye filin jirgi direba ya nufa da mu kamar yadda Hajiya ta umarta.
Na kasa haƙuri har sai da na rankwafa nayi wa Umma magana a kunne, nace, "Umma da gaske Hajiya Kaka ita ce Mahaifiyarki".
Kai kawai Umma ta gyada min alamar hakane, sai yanzu na ɗan samu nutsuwa kadan. Gefe guda kuma naji farin ciki ya kamani, Allah Sarki ko shiyasa Allah Ya saka mana ƙaunar juna Ni da Hajiyar.
Da kwatance muka isa inda Daddy yake lokacin da muka iso filin jirgin, da kanshi ya ƙaraso jikin motar ya bude wa Hajiya Kaka ƙofa ta fita.
"Umma muje kar ta sake miki fada". Na faɗa ina bude ƙofar ɓangarena na fita ita ma ta biyo bayana.
Daidai lokacin da Daddy ke fadin, "Jiddah fito mana, ko hada baki kuka yi da Kakar taki".
Karaf! Idonsa ya sauka a kan Umma da fuskarta tayi ca sosai saboda kukan da tayi.
Ido ya ware sosai yana matsowa inda take.
"Manga!" Ya faɗa cikin rawar murya.
"Kai!". Hajiya Kaka ta daka mai tsawa, lokaci guda ya nutsu ya waiga yana kallonta.
"Ban baka umarnin yi mata magana ba". Hajiya Kaka ta faɗa fuska a hade.
"Hajiya.." Ya faɗa a hankali.
"Haka nace idan har na isa da kai". Ta faɗa tana yin gaba.
Babu musu shi ma ya juya ya bi bayanta tare da yafito mu da hannu alamar mu taho. Duk da haka yana tafe yana waigowa yana kallon Umma.
Ba mu wani jima ba lokacin tafiya ya yi don haka muka nufi shiga jirgin, tsoro ne ya kamani sosai don haka Hajiya Kaka ta riƙe Ni muka shige.
Ko da jirgin ya zo tashi ma sai da na ƙanƙameta sosai saboda tsoro, sai daga baya na ware amma har wannan lokacin ban tashi daga jikinta ba. Oh! Lallai dare daya Allah kan yi bature, ban taɓa kawowa a raina cewa watarana zan shiga jirgi ba, sai ga shi na shiga a lokacin da ban taɓa tsammani ba.
Wasu manyan motoci ne guda biyu suka zo daukarmua a filin jirgin sanda muka isa garin Katsina, mota daya muka shiga da Hajiya Kaka da Umma shi kuma Daddy ya shiga ɗayar motar duk da na fahimci bai so hakan ba.
Mun ɗan yi tafiya sosai kafin mu iso gaban wani babban gida, masu gadi biyu ne suka bude babban gate din gidan, girman gidan ya zarce na Daddy Wanda ke Kano sai dai wannan bai kai waccan ƙayatuwa ba.
Yara da manya ne suka fito suna murnar zuwan Hajiya Kaka da Daddy, kowa yana ƙoƙarin ya ga shi ne a kusa da ita. Kallon baƙunta yaran ke mana ni da Umma sai dai na lura wasu daga cikin manyan matan da suka fito sun yi matukar mamakin ganin Umman sai dai babu wanda ya furta har muka isa wani babban falon.
Wasu dattijai biyu muka tarar suna zaune a kujera mai zaman mutum biyu, kamar sauran mutane su ma da mamaki suke kallon Umma da wannan lokacin kukan da take yi ya karu sosai, ɗaya daga cikinsu ya mike a fusace yace, "Me kika zo yi mana a gida? Ki fice tun kafin na sanya a tozartaki".
Wanda ke zaune ne ya riƙo gefen rigarsa tare da zaunar da shi yana fadin, "Da izinina ta zo, Hajiya Kaka ta shaida min sun haɗu Ni na bata umarnin su taho tare".
Shiru ya yi yana huci ɓacin rai ya bayyana sosai a fuskarsa.
Wanda ya yi maganar ne ya sake kallonmu yace, "Ku shiga ciki ku huta, bari mu je sallah".
Ya karasa maganar yana miƙewa, "kai ku wuce masallaci lokacin sallah ya yi, kuma na gidan ku shiga ku yi". Gabaɗaya yara da manya duk suka mike.
Wata daga cikin matan ce taja hannun Umma suka bi wata ƙofa, Ni kuwa dama tunda Hajiya Kaka ta riƙe hannuna ba ta sake ba, don haka tare muka miƙe muka bi wata ƙofar daban.
Sallah muka fara yi, kafin daga bisani aka kawo mana abinci, ita kam Hajiya Kaka ta zake sosai ta ci abincin Ni kuwa ɗan tsakura kawai nayi na ture nace na ƙoshi.
Murmushi Hajiya Kaka tayi ta kalleni tace, "Ki ci abincin kawai, duk wasu tarin tambayoyi da kike da su zan amsa miki".
Jin abin da ta faɗa yasa na matsa kusa da ita nace, "Yauwa Hajiya, wallahi duk na damu ina so na san asalin abin da ya faru Umma ta bar ku da har babu wanda ke ɗokin ganinta yanzu''.
"Labari ne mai tsayi Jiddah, ki bari sai mun huta sosai".
Marairaice fuska nayi nace, "Dan Allah Hajiya Kin ji?".
"Kulle min ƙofar can da makulli sai ki zo". Ta faɗa tana gyara zama.
Da sauri na miƙe na je na kulle ƙofar na dawo na zauna, na nutsu sosai ina jira ta fara magana.
"Kamar yadda na fada miki ɗazu, duk da cewa cikin fushi na faɗa. To Ummanki ƴa ta ce, Ni na raini cikinta wata tara kuma na haifeta na raineta har zuwa munzalin girma, sai dai daga baya cire ni daga wannan matsayin inda ta zaɓi wani daban a maimakon Ni da ya dace ta sadaukar da komai saboda Ni. Ki saurara".
Zama na ƙara gyarawa sosai ina kallonta, inda ta fara magana da cewa:
*Ahalin Muhammad Lamiɗo*
Babu shakka Kakanmu ya yi ƙoƙari wajen gina tarbiyyar iyayenmu akan soyayya da ƙaunar juna.
Tun kafin rasuwar mahaifinmu ya haramta mana aurar da ƴaƴanmu ga bare, duk da kasancewar mu uku kacal iyayenmu suka haifa amma Allah Ya azurta mu da hayayyafa, Ni kaɗai ce arzikin hakan bai riska ba saboda ƴaƴana biyu ne kacal a duniya. Saɓanin Yayye na biyu da babu wanda ƴaƴan da ya haifa ba su haura biyar ba.
Kamar yadda na fada miki da farko cewar mu uku ne a wajen iyayenmu, babban Yayanmu Hashim wanda ƴaƴa ke kira Abiey a yanzu, sai wanda ke bin sa Jamilu wanda ƴaƴa ke kira Abbu sai Ni kuma Jamila da ƴaƴa ke kira Hajiya Kaka.
Mahaifinmu yana da dukiya daidai gwargwado, bafulatani ne daya mallaki shanu sosai sannan kuma ya yi harkar noma a waccan lokacin, shiyasa yake da rufin asiri. Da kuɗinshi ya sayi fili ya gina wannan babban gidan saboda ahalinshi kamar yadda ya faɗa.
Ni ce wacce mahaifinmu ya fara aurarwa, kuma ba wani ya aura min ba face Ɗan amininsa. Sannan ya ba shi fili a cikin gidan nan yace ya gina mu zauna a waccan lokacin.
Haka sauran Yayye na da suka tashi aure duk yace su yanki fili su gina su zauna da iyalansu.
Dan haka ne zumunci mai ƙarfi ya sake ƙulluwa a tsakaninmu. Lafiya lau muke zaune da Matan Yaya tunda dama tun asali mun saba da juna, kamar yadda na fada miki cewa mahaifinmu bai yarda a auro bare ba shiyasa Yayye na su ma a cikin dangi suka nemo matansu.
Matar Yaya Hashimu ce ta fara samar da jika a gidanmu, don Ni kam dama tunda nayi wasu shekaru da aure ban yi ko ɓatan wata ba yasa na cire rai da samun haihuwar duk da har wannan lokacin ban daina addu'a da neman zabin Allah ba.
Tun daga wannan lokacin kuma sai haihuwar tayi sallama a danginmu, matar wannan na yaye wa matar wannan na haifowa. Tamkar mu, haka yaran suka taso da soyayyar juna sosai.
Kwatsam watarana Matar Yaya Jamilu ta tashi da wani matsanancin ciwo, ko da aka bincika sai aka fahimci ta sake samun shigar ciki ne. Sai dai a wannan lokacin laulayin cikin ya sha bam-bam da yadda ya ke mata a haihuwa biyar da tayi a baya. Tun da ta samu cikin kullum cikin ciwo take, hakan yasa a kullum idan na gama aiki na kan tafi sashinta na yi mata ayyuka tare da kula da ita dama yara sun jima da komawa sashin Yaya Hashimu.
Kullum zance daya take yi min, "Jamila idan Allah yasa na sauka lafiya na baki kyautar abin da zan haifa duniya da lahira, tun ranar za ki tafi da abin ki gida ki fara jego".
Na kan yi dariya ne kawai, amma har raina naji dadin hakan musamman watarana da ta faɗa a gaban Yaya Jamilu shi ma ya yi na'am da batun tare da faɗin sun so tuni su yi min kyauta da wani daga ƴaƴansu halak malak Allah ne bai nufi lokacin ba sai yanzu.
A haka dai muka ci gaba da rainon cikin har ya girma, tun ana saka ran haihuwarta har lokacin ya wuce.
Wataranar Laraba da asuba Yaya Jamilu ya zo sashin mu ya tada mu tare da faɗin cewa matarshi ta fara naƙuda, ba shiri na ɗauki mayafi na nufi sashin. Tun ana saka ranar za ta haihu har aka fara yanke ƙauna dama kuma lokacin ba a wani damu da zuwa asibiti ba, sai da ta sha wuta sosai kafin ta haifo Ɗa namiji, yaron da kaf haihuwar da ake yi a danginmu ba'a taba haifo kyakkyawa kamarsa ba duk da cewa dama muna da kyau sosai irin na fulanin asali, amma kyawun yaron ya zarce yadda zan misalta miki.
Mahaifiyarmu Inno ce ta kimtsata ita da jaririn, Ni da matar Yaya Hashimu kuwa muka fara ƙoƙarin gyara gidan.
Mai jego kuwa tun da yaron ya fito daga jikinta ba kara cewa uffan ba, har zuwa lokacin da muka gama kimtsa gidan muka koma ɗakin Mai jegon.
Zamana ke da wuya ta riƙo hannuna, da sauri na waiga ina kallonta don a tunaninmu bacci take yi, "Jamila ki kira min duk wani wanda ke cikin gidan nan dan Allah, kiyi sauri Jamila". Yanayin yadda take maganar ne yasa muka tsorata don haka na miƙe da sauri na fita.
Tare da mahaifanmu da Yayyena muka sake dawowa dakin, a lokacin ta zauna sai shaƙuwa take yi sosai.
Bayan na zauna a gefen gadonta da kanta ta sa hannu ta dauko jaririn ta miko min, babu musu na sa hannu na karbe shi. Murmushi tayi sannan ta kalli sauran mutanen da ke dakin tace, "Ku zama shaidu, ba wa Jamila kyautar wannan jaririn duniya da lahira. Ko da Ni Ko babu Ni Jamila ita ce mahaifiyarsa. Ina roƙonki da kiyi wa yaron nan tarbiyya kamar yadda zaki yi wa ɗan da kika haifa Jamila, ki ƙaddara a ranki cewa ke ce kika raini cikinsa kuma kika haife. ".
Tari mai ƙarfi ya sarƙafeta har sai da ta kai ga kishingida kafin ta cigaba da cewa, "Ina ji a raina watarana zaki haifi yara Jamila, ina roƙonki idan wannan yaron ya girma har ya kai munzalin aure, kada ki aura masa kowa face ƴar da kika haifa a cikinki. Ki riƙe min amana ki cika min alƙawari Jamila"..
Daga haka ta sake hannuna ta koma ta kwanta a hankali bakinta na ci gaba da motsawa, lokaci guda kuma jikinta ya saki rai ya yi halinsa, wanda ya ba mu aronta ya karɓi abar sa.
Ba zan iya misalta miki tashin hankalin da muka shiga ba na rashin wannan baiwar Allah, mai haƙuri, kawaici da iya zama da kowa gwargwadon halinsa.
Sai dai ba mu da wani tsumi ko dabarar da zai dawo mana da ita tunda dama wannan rubutaccen abu ne a kan kowa.
Dan haka da gari ya waye aka suturceta a bisa tsarin addini aka sada ta da makwancinta na gaskiya.
Haƙiƙa ta tafi ta bar mu da kewa sosai, amma hakuri shi ne kaɗai abin da za mu sai kuma mi bita da addu'ar dacewa.
Tun daga wannan rana riƙon jaririn ya dawo hannuna kamar yadda aka ba Ni kyautarsa. Ranar da aka cika sati, Yaya Jamilu ya ce na zabar wa yaro suna tunda dai ɗana ne, na kuwa zaba masa sunan mahaifinmu wato Muhammad duk da cewa Yaya Hashimu shi ma yana da yaron da ya yi wa mahaifinmu takwara da sunanshi.
Muhammad ya taso cikin gata da soyayya sai dai hakan bai hana shi zama mai cikakkiyar tarbiyya kamar sauran ƴan'uwansa ba, a lokuta da dama hatta mahaifanmu sukan kasa ɓoye soyayyar da suke masa a zuci har sai sun bayyana.
Ina son Muhammad sosai fiye da yadda zan kwatanta miki, ko da ace yaron da ana haifa ne iyakar soyayyar da zan masa kenan. Musamman da ya kasance mai nagartattun halaye da kowa ke sha'awa, zai yi wuya mutum ya zauna da shi bai ji ya kwanta masa a rai ba.
Tun yana shekara sha ɗaya ya yi saukar Alkur'ani Mai Girma da wasu muhimman littafai, a ɓangaren boko ma yana da hazaƙa sosai.
Sai da ya shekara goma sha biyar a duniya kafin Allah ya azurta Ni da samun juna biyu, murna a wajen dangi ba a magana, a zahiri na cire rai da samun haihuwa sai ga shi Allah ya azurta Ni a lokacin da ban yi tsammani ba.
Tun lokacin da cikina ya fara girma Muhammad ya dauke min aikin komai, duk yadda na so hanawa amma abin ya gagara, daga ƙarshe dole na bar shi. Tun safe yake tashi ya yi aikace-aikacen cikin kamar yadda duk wata mace za ta yi har ma fiye da hakan, idan ya gama ya wuce makaranta. Ana tashi kuwa zai nufo gida, duk abin da nake yi komai ƙanƙantarsa da zarar Muhammad ya shigo to na gama aikin kenan, wani lokacin har tsiya Kakanninsa ke yi idan mun shiga sashinsu cewar shi ya zama ɗan daudu.
A haka har lokacin haihuwa ya riskeni, wata ranar juma'a da safe na haifo santaleliyar yarinya fara tas!.
Duk wanda ya zo barka abu ɗaya yake fara furtawa shi ne Yarinyar tana kama da Muhammad.
Ranar suna anyi shagali sosai, Muhammad da kanshi ya zabi sunan da aka sakawa yarinyar wato *Fathiya* (Mai samar da farin ciki).
Tare da Muhammad muka ci gaba da rainon Fathiya, har ya fi Ni zaƙewa wajen kula da ita sosai, a taƙaice zan iya cewa ta shaƙu da shi fiye da kowa na gidan.
Shekararta uku na sake samun wani cikin, inda na haifi Ɗa namiji yaci suna Al'amin. Sai dai bai jima ba shekaru biyu da haihuwarsa ya rasu.
Muhammad yana da ƙashin arziki sosai, a lokacin da ya fara kasuwanci bayan kammala karatun sakandare sai ya fara samun alheri sosai. Don haka da kudinshi ya biya wa kanshi karatun jami'a ba kamar sauran yaran gidan.
Kullum so da shaƙuwa ke ƙara wanzuwa a ahalinmu musamman d aya kasance Mahaifinmu Lamiɗo Jajirtaccen ne sosai.
***
Zamani ya sauya, cudanya da mutane daban-daban da yaran mu na yanzu ke yi yasa ba akan komai bane suke iya yiwa iyayensu biyayya, sai wadanda suka samu cikakkiyar tarbiyya.
A lokacin da yaranmu suka kai munzalin aure, wasu daga ciki a dangi suka fitar da abokan zamansu yayin da wasu daga waje. Da fari Lamiɗo ya so hana yaran auren bare sai dai tuburewa da suka yi yasa dole ya aminta sai dai ya kafa sharuɗɗa sosai a kan hakan.
Na shiga damuwa sosai a lokacin da Muhammad ya zo min da batun cewa ya samu yarinyar da yake so har sun daidaita kuma iyayenta sun buƙaci ya turo. A lokacin Fathiya ba ta wuce shekara 13 ba.
Kai tsaye sai na umarce shi da ya samu Lamiɗo da maganar saboda ban manta da alƙawari mai girman da ke kaina ba.
Bayan wasu kwanaki Lamiɗo ya tara mu ya shaida mana batun aure da Muhammad ya zo da shi, sannan ya kara mana tuni da alfarmar da mahaifiyarsa ta nema a lokacin da take gargarar mutuwa. Nan dai aka shiga muhawara sosai saboda an sako malamai a ciki.
Daga ƙarshe dai aka yanke hukuncin aura masa wadda yake so sai dai batun alƙawarin da aka wa mahaifiyarsa za a sanar da shi idan yaji ya aminta yana son Fathiya sai a aura masa ita daga baya tunda a yanzu ita ba ta kai munzalin da za a aurar da ita ba.
Ba a dauki lokaci sosai ba aka yi bikin Muhammad da matar da ya zaɓo wa kansa suka tare.
A hankali kasuwancinsa ya haɓaka har ta kai ga ya fara fita kasashen waje, cikin ƙankanin lokaci ya tara kadarori da yawa, kasancewarsa mutum mai yawan kyauta da sadaka, ga kyautatawa iyaye.
Hatta wannan gidan da muke ciki shi ya bada umarnin a rushe a sake yi mai sabon zubi.
A lokacin da Fathiya ta cika shekara 18 ne Lamiɗo ya kira Ni da Yayye na sai matar Yaya Hashimu sai Muhammad da Fathiya.
Bayan an bude taro da addu'a ne Lamiɗo ya yi bayanin abin da ya tara mu, wato batun auren Fathiya da Muhammad kamar yadda ta nemi alfarmar hakan. A tsawon rayuwarmu ban taɓa nunawa ko a fuska ga Muhammad cewar ba Ni ce wacce na haifeshi ba, don haka a ranar ya yi kuka sosai kamar ransa zai fita tare da ƙalubalantar rashin fadamai hakan da wuri har sai da aka bari ya yi wani auren. Ba ja ba gurin amsa cewar zai auri Fathiya kamar yadda ita ma tayi na'am da zaɓin iyaye.
Don haka Lamiɗo ya yanke shawarar da zarar ta kammala sakandare za a hada aurensu ayi da na sauran ƴan'uwanta da ake shirin yi. A wannan ranar anyi lissafin shekara daya da wasu watanni.
Dama can Fathiya da Muhammad suna ƙaunar juna a matsayinsu na ƴan'uwa, da batun aure ya shiga tsakaninsu kuma sai ya kasance suna kula da juna fiye da da. Basa iya ɓoye soyayyar su ga juna ko a gaban waye, har ya kasance Muhammad ya daina yawan tafiye-tafiye da yake yi zuwa wani garin ko ƙasar saboda kawai ya kasance da Fathiya.
Ashe ƙaddara za ta hana auren na su.
Ba mu sani ba ashe a ɓoye Fathiya tana soyayya da wani yaro da ake kira da Murtala, Ɗan cirani ne da ya zo daga garin da babu wanda ya sani, baya ga haka mutum ne mai matukar hassada da son abin duniya.
Ba mu san ya aka yi suka fara soyayya da Fathiya ba sai wayar gari muka yi da baƙuncinsa shi da wasu daga cikin abokansa Ƴan cirani da sunan sun zo neman auren Fathiya, zancen nan da nake miki a lokacin saura wata daya da kwanaki ya rage auren Fathiya, kai tsaye Lamiɗo ya fada musu ya ba da auren jikarsa kuma koda ace bai ba da aurenta ba Murtala ba irin nagartattun mutanen da zai iya ba shi aure bane.
Ba zan manta ba, a lokacin da bikin Muhammad da Fathiya ya gabato na fahimci wasu sabbin halaye daga gareta. Tana yawan zama a daki ita kadai sannan ta fara ɗabi'ar da bansanta da shi ba ko a da, kuɗi sosai take karba daga hannunmu da fari na dauka saboda hidiman bikin ne sai dai daga baya na fahimci abin ya yi yawa don haka ne daina ba ta, sai ta koma wajen Muhammad wanda dama shi tun can mai kyauta ne bare ace kuma ka tambayeshi kuma wanda ta tambayar ma Fathiya da yake shirin aure, sai daga baya muka ji labarin cewa kuɗin da ya bata gabanin aurensu ya zarce miliyan guda.
Ashe Fathiya da Murtala sun shirya guduwa ne su yi aure a wani waje ba tare da sanin mu ba, sai dai a tsawon lokacin ko a fuska ba ta taɓa nuna bata son Muhammad ko aurenshi ba.
A ranar ɗaurin auren da asuba ta fice daga gida, sai dai rabon ganinta yasa a ranar Lamiɗo ya fita zuwa Masallaci tun kafin a kai ga kiran Sallah.
A lokacin tana tsaye a bayan wata bishiya tana jiran zuwan Murtala, ko da Lamiɗo ya fahimce cewa lallai ita ce sai ya tsaya daga gefe yana kallonta, sai da Murtala ya iso suna ƙoƙarin tafiya kafin Lamiɗo ya karasa kusa da su ya riƙe Murtala ta yadda ba zai taba iya kwacewa ba.
Gida ya dawo da su ya sa aka tsare mai Murtala ita kuma Fathiya ta shigo cikin gida.
Sai da gari ya yi haske Lamiɗo ya kira taro zuwa babban Falonshi gaba-daya ahalin gidan sun hallara yara da manya, har da bakin da suka zo biki.
A tsakiyar Falon kuwa Murtala ne da Fathiya a zaune, nan Lamiɗo ya sanar da mutane a inda ya gansu. Ko da aka tambayi Murtala kai tsaye ya faɗa cewa guduwa garinsu za su yi shi da Fathiya a daura n
Musu aure a can tunda Lamiɗo baya so. Da aka tambayi Fathiya ita ma ba ta musa ba sannan ta kara da faɗin sun jima suna son juna ita da Murtalan.
Murmushi kawai Lamiɗo ya yi sannan ya ba ta zabi biyu: Na farko shi ne idan tana son ta cigaba da rayuwa cikin danginta dole ta hakura da auren Murtala, na biyu kuwa idan Murtala ta ke so to dole za ta hakura da danginta hakura kuma ta har abada, don koda wasa kar ta waiwayemu da sunan ita din jininmu ce. Koda ya bukaci jin amsarta kai tsaye ta faɗa mai ta zabi Murtala don shi take so. Lamiɗo bai ba wa kowa damar magana ba, ya nemi alfarmar wani daga cikin abokansa da suka zo daurin auren da ya zama waliyyin Murtala, shi kuma ya zama waliyyin Fathiya. A nan cikin falon aka daura musu auren da Murtala ya biya dubu biyar kudin sadaki.
Bayan an daura auren Lamiɗo ya umarci da su tashi su tafi sannan ya sake jaddada wa Fathiya cewa ta manta tana da dangi ma a rayuwarta don duk ranar da ta zo inda suke sai ya wulakanta ta.
Ba zan iya misalta miki bakin cikin da muka shiga ba, musamman Ni da nake mahaifiyarta dama shi Muhammad tun da aka fara maganar ya ke kuka, lokacin da Fathiya suka fita da Murtala kuma sai da ya suma. Duk da haka Lamiɗo ya ce a cigaba da hidiman biki kamar yadda aka fara. Sannan yace bai yafe wa duk wanda ko a bayan idonshi ne ya yi zancen abin da Fathiya tayi ba.
Ko da lokacin daurin auren ya yi, sai aka daura auren Muhammad da ɗiyar wani abokin Yaya Hashimu.
A takaice dai wannan shi ne sanadin rabuwarmu da mahaifiyarki kuma tun daga lokacin babu wanda ya sake tada maganarta, sai lokacin da Lamiɗo ke wata jinya da ta zame masa ajali ya umarci da mu bibiyeta musan halin da take ciki ko da ba za mu je inda take ba, sannan daga baya idan tayi nadama mu yafe mata. Sati guda da yin maganar ya ce ga garinku nan, rasuwar Lamiɗo ta girgiza mu matuka ba iya mu kadai ba hatta mutanen gari, ya samu kyakkyawar shaida kwarai.
Ita ma mahaiciyarmu wata guda da rasuwar Lamiɗo ta rasu sanadiyyar jininta da ya hau sosai saboda damuwar da ta shiga.
"Kin ji fa tarihin ahalin na mu Jiddah". Hajiya Kaka ta faɗa tana share hawayen fuskarta da gefen zani, nima a nawa ɓangaren kukan nake yi sosai. Mun jima a haka kafin na tsagaita nace, " Hajiya to ya aka yi kika koma Kano da zama?".
Murmushi tayi kafin tace, "Tun bayan rasuwar Mai gidana Muhammad ko kuma nace Daddy ya dauke ya maida Ni Kano, da fari tare da Matarsa muka fara zama gida daya sai dai yanayin yadda halayyarmu bai zo ɗaya bane yasa ya saya min waccen gidan na koma, dama shi ya jima a can tun bayan tafiyar Fathiya. Da al'amuransa suka yawaita a ƙasar waje shi ne ya dauki matarsa ta biyu da aka aura masa a maimakon Fathiya suka koma can. Hutu kawai ke kawo su Nijeriya".
Shiru nayi ina ci gaba da sharar kwallah.
Ƙwanƙwansa ƙofar ɗakin aka yi dan haka Hajiya ta bude murya tana tambayar waye, daga can aka masa cewa wai Abiey ke nemanmu a babban falon.
Da to ta amsa sannan ta umarce Ni da na taso mu tafi.
Mutane ne sosai a falon da alama gaba daya ahalin gidan aka tara, guri muka nema muka zauna.
Sai da ya bude taro da addu'a kafin ya fara magana a takaice, kamar yadda Hajiya Kaka ta faɗa min shi ma haka ya sake nanata sanadin da Ummata ta bar gida. Bayan ya gama ya kalli Umma dake rakube a gefe yace, "Fathiya ba mu san abin da ke tafe da ke ba, shin kin dawo a matsayin wacce ta yi laifi ta zo neman afuwa tare da fatan sulhuntawa da danginta, ko akasin haka?".
Umma cikin shessheƙa ta fara magana, "Abiey ku yafemin, wallahi na jima da yin nadamar abin da na aikata, sai dai tsoro ya hana ni waiwayowa gida. Na fahimci nayi kuskure mai girma kuma a shirye nake da na gyara, dan Allah ku yafe min". Ta ƙarasa zancen tana sake fashewa da kuka.
Shiru ya yi kafin ya fara magana, "Ba za mu ƙi bin umarnin mahaifinmu dake kwance a kabari ba kamar yadda ya yi wasiyyar duk sanda kika dawo mu amsheki. Dan haka za mu yafe miki sannan mu cigaba da rike ki a matsayinki na ƴar mu, sai dai a wannan karon ma zan saka miki sharaɗi. Matukar kina son cigaba da zama da danginki to zaki mai da wa Murtala da ƴar sa, abin nufi a nan shi ne ba zamu rike ƴar Murtala da kika taho da ita ba, idan ma akwai wasu bayan ita to babu wanda za mu riƙe a ciki".
Ya ƙarashe maganar yana nuno inda nake zaune a jikin kafar Hajiya Kaka.
Da sauri na daga ido ina kallonsa kamar yadda ita ma Umma ta ɗago a firgice.
Fuska a murtuke yace, "Kin amince?".
Shiru Umma tayi na wani lokaci kafin cikin shessheƙa ta ce, "Abiey wallahi *Jiddatulrahman* ba diyar Murtala ba ce, hasalima bansan su waye iyayenta ba....
Tirƙashi!!!