MIJIN MACE ƊAYA PART ONE

Chapter 12

by @ummindaddy77

YAYIN DA ALIYU YA KOMA GIDA

Yana shiga da mahaifiyarsa ta gansa ta yatsina fuska a zafafe ta ce, “Nemi waje ka zauna mu ƙarasa maganar ta mu ta ɗa zu.”

Zama ya yi, ta dube shi ta ce, “Aliyu yagwalgwalarka na kira a waya na faɗa mata halin da ake ciki, kuma na ce mata idan akwai yarinya mai hankali da nutsuwa da kamun kai a inda ta ke don Allah ta sa ma maka. Buɗar bakinta ta ce ga Ma'u 'yar makwabtansu ta yaba da halayyarta. Kuma tana tuntuɓar iyayenta suka yi na'am.”

Shiru Aliyu ya yi kamar bai ji abin da mahaifiyarsa ta ce da shi ba, cikin tsawa ta ce da shi, "Ba da kai nake magana ba."

“Ni Mama don Allah ki ajiye wannan batu, don raha fa na yi miki shi.”

Harara Mama ta watso masa tare da jan dogon tsaki, “Aliyu sai ka yi auren nan fa, kuma 'yar ƙauyen da na zaɓa maka za ka aura, wacce ko a shekara ka ɗinka mata goggo sha'u za ta yi godiya, ba 'yar birni da ko kantin kwari ka dire mata a gabanta ba za ta gode maka ba.”

“Shi ke nan Mama, na amince Allah ya tabbatar mana da alheri.”

Ta ɗan yi murmushi, “Yauwa ɗan albarka, ko kai fa haka nake son ji dama, gobe sai ka shirya mu ɗauki hanyar Kano ka je Takai, ka kuma ga amaryarka a Tsintar don rabonka da garin tun kana shan nono.”

Ya miƙe “Mama ba sai na je ba, ku gama komai a kawo ta.”

Cike da ɓacin “Sai ka je ka ga fuskar amaryarka kun zanta. Idan ka ga ba ka je ba to sai idan mutuwa ka yi”

“Mama biyayya ce ya sa na karɓi batunki, amma ba batun ina so ba don Allah ki yi duk abin da kika ga ya dace a kai.”

Ita ma ta miƙe "Ni fa Aliyu ba na ga biyayyar da kake ikirarin kana yi mini a zahiri kai da komai na zo maka da shi sai ka ƙuntatawa zuciyata na fa sani bisa tilas kake yin duk abin da nasa ka ba a son rai ba. Bari ka ji sai ka je ko kana so ko ba ka so, batun wani abu wai shi so kuma ya rage naka, iyaye da kakannimu dama ba su san wani abu soyayya ba, kawai aure suke kai ma irin haka za ka yi ɓace mini da gani.”

Jiki babu kuzari ya bar wurin.

SAFINAT DA UMMA LAURE

Safinat gyara zama ta yi tana haɗe gashin kitson da a ka yi mata ta bayan kunnenta. Ta fuskanci mahaifiyarta fuskarta a yamutse ta ce, “Umma idan naga soyayyar da ke tsakanin yaya da mayyar matarsan nan sai nake ganin da kamar da wuya wata mace ta samu gurbi a zuciyar yaya, mace ta mallake mijinta ban taɓa ganin shu'umar mace irin ta ba. Wannan wanne irin boka ta samu haka?”

Murmushi ta sake ta kalli ɗiyarta da gefen ido tare da ajiyar zuciya ta ce, “Duk tsubbace-tsubbacen ta sai na karya shi, Mus’ab sai kin mallake shi kin juya shi yadda ranki ke so, ke idan ma kika ce ba kya buƙatarta a matsayin kishiyarki zan mata ƙurciyar da babu wanda zai tuna da ita, idan kuma kina buƙatar ganinta a matsayin baiwarki a gidan Mus’ab, kuma ba ta da maraba da bola a wajensa duk boka gobe da nisa zai iya yin hakan.”

Dariyar mugunta ta yi, “Umma duk biyun nake buƙata su tabbata.”

“Ban fahimce ki ba Safinat.”

Ta kuma kyalkyalewa da dariya sannan ta ce, “Zan yi miki bayaninsu dalla-dalla ko yanzu. Abin da nake so Hafsy ta shaida wa duniya mijinta mijin mace ɗaya ne, to ni zan ƙaryata hakan tana ji tana gani na zama kishiyarta ba yadda ta iya, bayan haka ya tabbata ina so na kasance ni ce mai juya akalar gidan ita da Mus'ab duk su zama bayi gare ni ko tsinke na ce kar su tsallaka su yi biyayya. Idan na sauya mata kamanni na gallaza mata na cuccusa mata bakin ciki bayan ta wulakantu ta ƙasƙantu ta tozartu ta rasa gabas balle yamma. Ba ta banbance tsakanin fari da baƙi, ba ta gane gabanta ballantana bayanta ba ta san a sama take ko a ƙasa ba, sai a haukatata daga nan mu yi mata ƙurciya mu daina jin ta ko kallonta a doron ƙasa. Har abadan abadi kar a ji ɗuriyarta. Shi ma Mus'ab idan na haifi 'ya'ya na samu magada na wawuri dukiya idan na gaji da shi bai cilla lahira ba sai a ƙarasa shi. Daga nan ba abin da ya rage mana sai fantamawa a duniya."

Ita ma kyalkyalewa ta yi da dariyar, “Yarinya kin fi uwarki kaifin tunani. Za a yi hakan. Idan ƙwaƙwalwarki ma ya kuma binciken mugunta da ya fi wannan sanar da ni duk zai yi su."

Umma Laure kana ganin fuskarta za ka fahimci ta ji daɗin tsarin da ‘yar ta ta kawo ta ci gaba da cewa:

“Safinat a ka ce kyan ɗa ya gaji ubansa. Amma ke ina ga alamar za ki wuce ni a mugunta, ni ban taɓa ma tunanin za ki aminta da mugun nufi na ba, sai ma naga kin ɗara ni.”

Dariya ta yi ta ce, “Umma kenan yaushe barewa za ta yi gudu ɗan ta ya yi rarrafe.”

“Yarinya yanzu ke kika koma Barewa ni na koma ɗan.”

Safinat kyalkyale wa da dariya ta yi sai ta ƙishingiɗe a cinyar mahaifiyarta.

KANO STATE.

Takai yana ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi da ke ƙarƙashin Kano. Yayin da ƙauyen Tsintar kuma ya kasance a ƙarƙashin Takan mafi akasarin mutanen garin Fulani ne usul.

ƘAUYEN TSINTAR

Runtse idanunsa ya yi a take ya ji wani abu na tsarga masa tun daga yatsarsa ta kafa har ya zuwa ƙansa.

Ba komai ya haddasa masa hakan ba face labarin da masoyiyarsa ta ba shi na an yi mata miji.

Ahmadi ɗago fuskarsa ya yi lokaci guda fuskarsa ta sauya daga walwala da annashuwa da ya zo da ita ta koma tamƙar duhun dare.

“Ma’u wa ya shirya wannan al’amarin?”

Cikin rarraunar murya kamar mai son yin kuka ta ce, “Baffa da matarsa, ina cikin ɗimuwa, raba ni da kai tamƙar tarwatsa rayuwata ce.”

Amadu ya matso daf da Ma’u ya fuskance ta ya ce, “Ma’u ba zan iya rabuwa da ke ba, muddin na rasa ki rayuwata za ta salwanta.”

Ta kalli cikin kwayar idon sa. “Ba za ka rasa ni ba saboda na nema mana mafita.”

“Wacce irin mafita Ma’u?”

Gauron numfashi ta sauke sannan ta ce,

“Ahmadina iyayena da gaske suke don har suna maganar karɓar kuɗin aure. Mafita da na nema mana shi ne mu gudu.”

Tana gama furta hakan, ta ji wani tartsatsin wuta ya gifta ta idonta, saboda wawakeken mari mai kama da saukar ƙatuwar guduma da ta ji shi a gefen fuskarta, a take ta ji ana ball da ita. Wani sanda da ya hango shi ya ba shi damar ɗauka ya dinga jibgarta da ita.

Ahmadi ya rikice ya shiga tsakani yana mai cewa, "Baffa don Allah ka yi haƙuri."

Ya dalla masa muguwar harara, "Kauce mini da gani zan zo kanka."

Take Ma'u ta yi jina-jina tana haƙi ya ɗago ta.

"Ja'irar yarinya kaɗan kika gani, Ma’u nawa kike da har za ki dinga furta ki gudu da saurayi, Allah na gode maka da ka nufe ni da jin wannan maganar. Ba don Allah ya kawo ni ba na rakaɓe na ji hirar nan da kin jawo mini abin faɗa a ƙarƙarar nan. " Ya sake ta shiga gida."

Ya juya kan Amadu, “Kai kuma idan na sake ganinka bakin kofar gidan nan hukuma ce za ta raba mu. Kana ta hure wa 'ya ta kunne ko, to wahainiyarka ta kiyayi rama ta, yau da daddare ka ƙira manyanka su kwashi tsiyarsu na abubuwan da kuka kawo na na gani ina so. Ma'u an yi mata miji.”

Ma'u na shiga gida ta nufi ɗaki tana ta rusa kuka.

Uwar goyon ta ne tana tuken awaki tana ba su abinci, ta hango Ma’u a ranta take cewa, “Su Ma'u ko me ya faru da ita?”

A kufule ya shiga gidansa yana ta surutai da bam-bami.

Hansai da ke tuken awaki ta fito tana cewa, “Malam lafiya kake ta bam-bami me yake faru wa ne?”

Bai ba ta amsa ba ɗakin da Ma’u ke ciki ya nufa ya hanakaɗe kofar ya shiga ya fara balbale ta da masifa. “Ke Ma'u ki kiyaye ni ki fita a harkar yaron nan, ke ga ki 'yar zamani ko ba za ki yi biyayya da zaɓin iyayenki ba.”

Cikin sheshshekar kuka take cewa, “Baffa, don Allah ku duba lamarin ban son bijire maka a rayuwa, amma wannan al'amari idan an yi shi ba zan yi daraja a wurin wanda za a aura mini ba, don ba ganina ya yi ya ce yana so ba. Kuma ni ma Ahmadi nake so.”

Ya yi mata dankwalo “Ungo naki ke da Amadun, yaran yanzu sai fitsara kina 'yar Fulani jinin alƙunya har kina ce wa ga wanda kike so."

Ya riƙe haɓa, "Lallai idan mutum bai mutu ba zai sha kallo a wagga zamani. Ma’u ki mai da hankalinki zan ci mutuncinki muddin za ki saɓawa zaɓin da na yi miki. Na kuma faɗa ki shiga taitayinki.”

Uwar goyon ce ta tsoma baki ta ce, “Malam tsatssauran mataki ya kamata ka ɗauka. Ni wallahi ban ga wani abin so wurin wannan figaggen yaron ba, ta bi ta ƙallafa ranta a kansa. Idan ta auri Ahmadi ai kamar mun sayar da akuya ce sai ta dawo tana ci mana danga.”

Kwafa ya yi ya gyara afarangiyarsa ya fice.

Tashi Ma'u ta yi ta murguɗa baki tana guna-guni tana cewa, “Dada, duk ina da masaniyar ke kika yi kutungulai kika haɗa wannan abin saboda kwaɗayin abin duniya to ba za ku yi nasara ba.”

Riƙe haɓarta ta yi tana cewa, “Lallai Ma'u ni kike yi wa haka ko, zan yi maganinki.”

Ɗakinta ta nufa fuu tana zuwa wurin ta ta sharara mata mari a kuncinta ta ce:

“Ni kike murguɗa wa baki ko, na fuskanci tun faruwar wannan lamari raini ke shiga tsakanina da ke idan da ni ce mahaifiyar da na tsuguna na haife ki ba za ki yi mini haka ba."

"Mahaifiyata ba za ta fara hakan ba ma, zaɓin ɗiyarta za ta so."

Ta sake baki, "To ki sani aikin gama ya gama idan har kika ga ba a yi wannan auren ba kin zama gawa ne, ko kuma ita Hajiyar ce ta janye. Arziki yana bibiyarki ke kuma kina ƙoƙarin kufce masa.”

Ma'u miƙe wa ta yi ta ce, “Ku ne makwaɗaita kuke hankoron arzikinsa ko shi Ƙaruna ne ba na son sa, Amadu kuwa ko shi ne shugaban matalautar duniya, ko kuma shi ne ɓeran masallaci shi nake so. Soyayya gamon jini ce ba ta duba da arziki ko talauci.”

Ta kuma murguɗa baki ta yi gaba. Uwar goyon ajiyar zuciya ta yi ta bi ta da kallo a zuciyarta ta ce, “Ni keke kawo wa raini ko, za ki yi da na sanin da ba ki yi ba.”

MAIDUGURI

ALIYU DA MAHAIFIYARSA

Ckin hanzari da kuzari take shirya wa tamƙar mai barin Ƙasar.

Ta kure iya wanka, ta kure ba laifi, ta yi kyau masha Allah! Duk da tana da girman shekaru amma tana da kyawun diri idan ta yi shiga suna amsar jikinta.

Ta sanya awarwaraye da sarka, turarurrukan da ke gabanta ta dinga ɗauka ɗaya bayan ɗaya tana fesa shi a jikinta.

Inda takalmanta suke a jere ta nufa ta duba wanda zai shiga da kaya da gyale ta saka shi.

Ta yafa mayafi ta nufi sashin Aliyu.

Tana zuwa ta kwankwasa masa kofa. Aliyu na ji ya yi tsaki ya ce, “Oh My God! Da gaske fa Mama take tafiyar nan kenan za a yi.”

Ya miƙe ya ɗauki key na mota. Ta Dube shi sama da ƙasa.

“Me ye haka Aliyu? Haka kake nufi za mu tafi babu gyara ballantana kwalliya. Ni tsofaifai da ni ma da kwalliyata.”

Fuskarsa a ɗaure ya ce, “Mama, to me zai yi don mun tafi a yadda nake, ni dai ban ga aibin wannan shigar ba.”

Kwafa ta yi ta ce, “Babu abin da zai yi tabbas, don rashin kwalliya ba zai sa a fasa tafiyar ba. Kuma ko a turɓaya ka yi wanka Ma’u ta ganka za ta so ka a hakan.”

“Umma don Allah mu tafi Kano fa ba kusa ba ne.”

Ta kalle shi ta gefen ido, “Ai tun da a jirgi za mu tafi ba matsala.”

Umar ne ya ƙaraso ya ja akwatin Mama, shi ma Aliyu na jan na shi.

Umar ya kai su airport sai da ya ga jirginsu ya tashi sannan ya bar wurin.