SALMA

Part 3

by @meenatyandoma

👽 *SALMA* 👽

    (HORROR STORY)

  

   _NA MEEN@RT A YANDOMA_



*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

       *M. W. A*


```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ```🤙🏻

***

________________________

*NOTE* Labarin Salma nina kirƙiri abuna, aguji juya mani labari ta kowa ce Siga sai da izinina.



*NA KUƊI NE, KI TURO 300 TA WANNAN ACCOUNT ƊIN AISHA ABUBAKAR 2151366600 UBA BANK, KO KATIN MTN TA WANNAN NUMBER ****



*BANYI ALƘAWARIN YIN FREE PAGE DA YAWA BA, SABODA LABARIN NADA YAWA, HAJIYA KI BIYA KUƊI KISHA LABARI* 🤷🏼‍♀️🤷🏼‍♀️🤷🏼‍



*FREE PAGE 5️⃣__6️⃣*

.........Gumin tashin hankali ya shiga wankema Subi fuska.



Ɗif komi na ɗakin ya daina motsi, kukan jariraine ya gauraye ɗakin.


Daga inda take zaune taji an jawo ƙafadunta da mugun ƙarfi ana hajijiya da ita a tsakar falon.


Ihu take tana kururuwar kiran Sahabi, abinda batavsani ba shine babu mai jinta.



Wurgar da ita akayi gefe ta bugu ta kujera.


Hasken falon ya daina fafarniya.


Miƙewa tayi zaune tana rarraba idon.


Gashin attach ɗin dake kanta taji an fizga.


Kururuwa ta ci gaba dayi.


Sakinta akayi, ta zujo a matuƙar firgice.


Ƙofar falon dake kulle tayi an banko da ƙarfin tsiya.


Kuka take jikinta ya jiƙe sharakaf da gumi.


Ƙofar tayima ƙuri jiinta na ciri, luuuuw taga wani dogon hannu batare da gangar jiki ba ya nufota.


Ƙoƙarin tashi take amma ina ta kasa, haka ya iskota ya kama wuyanta ya ɗagata sama ya shaƙe.



Wutsil niya tahauyi ga idanunta da suka firfito tsabar wahalar shaƙar da tasha.


Sakinta akayi ta faɗo ƙasa tim.


Koda yatsanta kasa ɗagawa tayi, domin yau ta Fidda rai da rayuwa, tasan sa'in mutuwar ta ne yayi.


Tsawar da aka daka mata ce ta sanyata sakin gutun fitsarin da ta matse.



Cikin murya irin ta yara marar daɗin amo aka fara magana.

"Kinyi kuskure Suwaiba, a tunaninki ƙullinki nabaya kinci nasara wannan ma kike tunanin zaki yi nasara, bazan kasheki ba a yanzu domin akwai buƙatuwar ki wulaƙanta alokacin da zaki girbi abinda kika shuka, wannan jaririyar da kike gani ita ce ƙaddararki wadda zata zama ajalinki a nan gaba, kina ƙoƙarin cutar da ita bakisan a koda yaushe ina tare da ita, yanzu zaki girbi abinda kikaso shukawa."

Yana gama maganar wasu ƙananun maguna masu kawunan mutane hannuwansu sunkai shida ga wani kwalelen ido a tsakiyar fuskarsu.


Duk bala'inda ta gani a baya baikai wanda ta ci karo dashi a yanzu ba.


Ihu take tana ƙoƙarin Barin wurin amma kafin ta tashi sun kewayeta suna dariya Hayaƙi na fita daga bakunasu.



Saman kanta suka haye suka rika kartar fatar jikinta da faratansu, ihu take tana kururuwa, cizo ta ko ina suke aikamata.


Ranar saida Subi taga bala'i wanda bata ta6a ganiba arayuwarta, ta tsinema ƴan ƙungiyarsu yafi a ƙirga.


Sai da jikinta ya koma babu wani wuri da zaka kalla batare da kaga sawun cizo ba.


Nan suka barta baje ta sume.


Tsakiyar gadon ya bayya Salma ɗauke a hannunshi.


Kwantar da ita yayi gefen Sahabi daketa sharar bacci baisan wainar da ake toyawa ba.



Baccinta take idonta rufe, kallon hannunta yayi inda aka yanka, wurin harya bushe.

"Ina tare dake Salma, duk rintsi bazani barki ba, ke kaɗai na mallaka, kamar yadda kema bakida kowa, kece zaki cika mani gurina na ɗaukar fansa wurin iyayenda suka salwantar dani."

Yau ma kamar kullum iskar asuba na kaɗawa BUSARI ya 6ace 6at.



Yau anci sa'a Sahabi ya farka da asuba domin yin Sallah.


Salma dake bacci gefenshi ya gyarama kwanciya.


Naiman duniya yayima subi amma bata cikin ɗakin.


Cike da mamaki ya fara tunanin inda ta tafi, domin shidai yasan ba sallah zatayi ba a yanzu.


Dama shine mai ƙoƙarin sallah, shima tunda ya auri Subi duk wani roƙon addininshi yaja baya.


Kwance ya hangota ƙasa kamar matatta.


Da sauri ya ƙarasa wurinta, "Subi, Subi, miya fito dake nan."

Shiru bata farka ba


Ruwa ya ɗauko tare da shafa mata a fuska.


Doguwar ajiyar zuciya tayi tare da miƙewa da sauri.



Cike da mamaki ya ƙara jifarta da tambayar ɗazu.


Harta buɗi baki ta furta "Sal..."

Jitayi ta manta duk wani abu daya faru jiya.




"Na fitone in sha ruwa bacci ya ɗauke ni."

Ta ji bakinta ya furta haka batare da ta shirya ba.



"To kije ki shirya yau ake sunan Salma jiya na sanar dasu Hajiya."

Sahabi ya faɗa tare da miƙewa.


Sororo tayi tana mai binshi da kallo.

"Wato Sahabi har yanka zaiyi ma wannan yarinyar, in dai na haihu sai na raba ka da duk wani wanda naga kana da kyakykyawar alaƙa dashi."



Abin mamaki gida ya cika da ƴan uwa da abokan arziƙi, Sahabi ya yanka manya_manyan Raguna guda biyu.


Yinin ranar Salma bata tasgi daga bacci da take ba.


Duk wanda ya ɗauketa saiya tsorata ganin irin kyan jinjirar kamar ɗiyar aljanu, ba shiri mutum zai ajeta.


Anci ansha inda Sahabi ya rada mata ainahin sunan da yaji mahaifiyarta ta kirata wato SALMA.


Sai da kowa ya watse har duhun dare ya fara sannan Salma ta buɗe ido.


Kalle_kalle ta hauyi.


Sahabi dake riƙe da ita cike da mamaki ya fara magana.

"Subi kiga Salma sai da kowa ya tafi sannan ta buɗe ido."

Banza tayi dashi batare da ta bashi amsaba.


Madarar jarirai ya ɗauko da nufin yabata, abin mamaki duk madarar tayi hunhuna ta lalace.


Cike da mamaki ya duba lokacin expire ɗinta amma lokaci baiyi ba.


Basarwa yayi tare da ɗaukar makullin mitarshi ya fice.


Zoben hannun Subi ne ya fara haske.


A hanzarce taje ta sanya jar rigarta tare da Rufe idonta ta murza zoben.



Mugun dajine mai ɗauke da manya_manyan bishiyoyi, tsatstsaye suke jikinsu jajayen riguna ne fuskar nan babu annuri.


Bayyanar wata mata a tsakaiyarsu ta sanyasu zubewa bisa guiwoyinsu.



Cikin matuƙar bacin rai shugabarsu ta fara magana.

"Babu wani gurin ki da ƙungiya bata cika makiba, duk wani abu da kika buƙata anyi maki, amma ace ƴar ƙanƙanuwar jinjira ta gagara ki kashe, suwaiba kinsan bala'in da kika haddasa ma ƙungiyar nan jiya."?


Jikinta har mazari yake ta buɗu baki zatai magana, shugaba ta kwatsa mata tsawar da ta haddasa mata haɗiye sauran maganar.



"Zuwa yanzu ƙungiya fushi take dake, dumin sanadin kasa aikinki yadda ya kamata kinjjaza mana wata asara, dakin tsafinsu ya fara kamawa da wuta, kin ko kasan hukuncin wanda ya yi kuskure wurin aikinshi i ta ce mutuwa."



Mummunar faɗuwar gaba ta ziyarci Subi dake tsugunne kanta ƙasa.


"Sakamakon haka ƙungiya ta dakatar dake, tare dayi maki gargaɗin kada ki kuskura ki sake ƙoƙarin ta6a jaririyar harsai radda muka ubarceki.



Haƙuri Suwaiba tahau badawa amma ina aikin gama yariga ya gama.



Bayan ya sawo uwar madarar jarirai mai tarin yawa yana ciki tuƙi yaji anzo dai dai kunnenshi tare da furta, "Kayi gaggawar komawa gidanka."

Wayam baiga kowa na.


Dan haka ƙara himma yayi ganin ya isa gidan.



 Sallama yaketa ƙwakawa amma shiru babu kowa sai ƴar caras da ta ƙure volume ɗin TV.


Batasan ma ya shigoba sai da tayi yana tambayarta ina Subi.


"Tana daga ciki." ta bashi amsa.


Zaune ya sameta bakin gado kamar bata cikin hayyacinta.


Firgigit tadawo daga duniyar tunanin da ta lula.


"Ina kuma kika aje Salmar, naganki ke ɗaya."


"Tana wurin Lami mai aiki."

Sabuwar ƴar aikin da suka canza


Amsota yayi abin mamaki fur taƙi shan madarar.


Juyin duniya sunyi amma ta ƙiya.


Daga karshema fidar da aka zuba madarar ciki tarwatsewa dayi da kanta.



Jikin Lami ya fara kyarma ganin wannan baƙon al amari.


Tarwatsewar fidar yayi dai_dai da Salma ta wangale baki ta fara dariya.


A firgice Lami ta miƙoma Sahabi.

"Mai gida dan Allah amsarta wannan daga ni aljana ce kuka samo ba mutum ba, ni tunda nike ko a tatsuniya bantaba jin inda jinjiri sabuwar haihuwa yayi dariya ba.


Sahabi bai wani damu ba ya amshi Salma dake kyalkyata dariya tamkar wani babba na dariya.



Babban abinda ke damun Sahabi shine tunda ya tsinci Salma bata ƙara kuka ba tun lokacin da mahaifiyarta ta 6ace mashi, abu kadan zai faru ta cigaba da dariya bazata bariba sai bacci ya ɗauketa............

_____________________

....Tafe yake sanye cikin fararen kaya, babbar riga da ƴar ciki da wando.



Ƙara nausa kai yake cikin jejin batare da zullumi ko tunanin wani abu zai cutar dashi ba.



Cikin takunshi na dattaku bakinshi ɗauke da azkar daya zame mashi jiki indai zai shigo jejin nan.



Malam Abu kenan da kemanin shekaru biyar kenan da 6atan yaron su ɗaya tilo da Allah ya mallaka masu.



Shifa jeji ta zame mashi jiki kullum, bai fidda rai da zai ga yaronshi ba.


Ji yayi zuciyarshi ta bashi daya bi gabas, batare da tunanin komi ba shida almajiranshi guda biyu suka bi wata hanya mai sarƙaƙiya gami da duhuwa.




 Yaron Malam ne yayi saurin ja da baya tare da furta "Subhanallah!"


"Ya Malam kunga abinda nagani kuwa."?



Juyowa sukayi tare da kallon inda Yaron Malam ke nuna masu.


"Kuhumullahu la'ajabun."

Suka furta a tare.


Mace ce ƴar kimanin shekaru ashirin da shida kwace tamkar matacciya.



"Malam ina ga fa yau ma mun fada wani tarkon na jinnu, kada mu ta6ata mubar wurin nan."



"A'a Gardi, da gani wannan baiwar Allah cutar da ita akayi, tana naiman taimakon mu, yanzu abinda za ai kaida yaron malam ku ɗaukota mu koma gida."



Babu musu bare jayayyah haka suka ɗaukota suka nufo gida.


Baza a kirata tsohuwa ba, amma zata fi cancanta akirata babbar mace,domin Ta haura talatin,Zaune take tsakar gidan ta rafka uban tagumi daya zame mata jiki, domin tun bayan 6atan ɗan su ɗaya tilo da Ubangiji ya mallaka masu tayi bankwana da walwala da farin ciki.



Sallamarsu malam ketayi amma sam inna Hassu bata san sunayi ba.


Matsowa yayi gaf da ita tare da dafa kafaɗar ta, 

"Hafsa bazaki cire damuwa da tunane_tunane daga zuciyarki ba, ita ƙaddara mumine ake kwadawa aga ƙarfin imaninka, muɗauki wannan a matsayin jarabawa daga Allah."



Hawayen da suka wanke mata fuska ta share tare dayi ma mijin nata sannu da zuwa.



Mace ta gani su Yaron malam suna ajewa.


Miƙewa tayi tare da karasawa inda aka ajeta.

"Malam wace ce wannan."?  


Nan malam ya sanar da ita abinda ya faru.


"Yanzu zanje in sanarda mai gari abinda ya faru, kafin in dawo kiyi mata wanka."



Kamar yadda malam ya bukata haka Inna Hassu ta ɗora ruwan zafi ta wanke wannan mata tas.



Akwai maganar da take son faɗawa Malam dan haka tazauna zaman jiranshi.



Sallamarshi yajiyo dan haka ta fito waje 


"Ya ya Malam ka sanar da mai garin."?



"Eh ya sani kuma yayi mani izini akan ayimata magani inda bata mutuba."



"Malam Matar nan da ranta, ina mata wanka ta motsa yatsanta, Malam abinda ya bani mamaki Matar nan ta haihu kuma haihuwar ma sabuwa."



Ciki da al ajabi malam ya shiga ɗakin tare da kare mata kallo.



Idanunta rufe suke babu alamun numfashi a tattare da ita sai ka kalli wuyanta daga ƙasa nan zakaga wurin na harbawa.



"Hassatu Ubangiji ne kadai yasan wace ce ita, shi kaɗai kuma yasan boyayyan sirrin dake tattare da ita, zanyi iyakar ƙoƙarina mudage da rokon Allah ayi mata magani, ƙila ta sanadinta muma Ubangiji ya dubemu ya bayyana mana yaronmu."



Sai da suka kwashe sati ɗaya anayi mata magani amma ko motsi batayi ba.



Wata ranar Juma'a kasancewar Malam Abu shine limamin wannan alƙarya, bayan dawowarshi daga masallaci an fitarma al majirai da abinci.


Zaune suke suna cin abinci shida Inna Hassu.



Alamun motsi suka yiyo ɗakin da suka aje marar lafiyar.


A hanzar ce suka yi hanyar ɗakin.


Zaune take ta fidda ɗan kwalin da aka ɗaure mata kai, gashin nan ya tarwatse.


Kallonsu take ɗaya bayan ɗaya.


"Alhamdulillah Malam Abu ya furta."


"Bawar Allah sannu, ina ke maki ciwo, wace ce ke, ina ne garinku."?

Malam Abu ya jero mata tambayoyi.


Kallonsu tayi tare dayin murmushi, lokaci ɗaya kuma ta fashe da kuka.



Hankalinsu ya kara tashi, juyin duniya sunyi amma taƙiyin shiru.


Sai da Malam Abu ya tsaya saman kanta ya fara kwararo mata ruwan addu'o'i bacci ya ɗauketa.



Kullum cikin yimata addu'o'i ake amma ina bata magana sai dai ta kalli mutum hawayer suna zuba a idonta.


Inna Hassu ita ke mata duk wata hidima, kullum sai tasa almajirai sun ɗebo mata bedi domin kullum sai tayi mata wankan Jego.



Wata Addu'a ce Malam Abu ke haɗawa tsawon mako ɗaya ya ɗauka kafin ya ida haɗa ruwan addu'ar.



Ranar da za'a fara yima Baƙuwa kamar yadda suke kiranta aiki da ruwan addu'ar.



Sanar suka wayi gari ruwan ya 6ace naiman duniya sunyi amma babu shi Sama ko ƙasa.....

_____________________________ Subi ta zuba ma sarautar Allah ido, domin yanzu ta kiyayi Sslma.


Yarinya tanada shekara ɗaya ta fara takawa da ƙafarta.


Abinda zai baka mamaki koda abun mugunta kayi mata mai makon tayi kuka sai dai kaji ta tuntsure da dariya.


Ga wani babban abun mamaki Tana da shekara ɗaya Bakinta ya buɗe bata kiran kowa sai wata kalma da ko wasa take sai dai kaji ta Furta BUSARI.



Kamar kullum yau ma Sahabi ya shirya Salma shi kuma ya fice wurin aiki.


Zaune suke su ukku Subi da wata ƙawarta da tazo gidan.


Sai kuma ƴar caras dake gefe tana kallo.


Dugul_dugul Salma ta fara saukowa daga matakalar benan kikinta rigace fara iyakar ta guiwa, gashin kanta ɗaure yake da wani jan ribon.



Dafe ƙirji tayi tare da furta.

"Yaushi Nusaiba nashiga ukku, Subi minike gani haka, amma dai waccan ɗiyar aljanu ce."



Kallonta Subi tayi tare da ta6e baki.

"Ke ƙawata wallahi ki kiyayi yarinyar can ki kauda idonki akanta, dan wallahi ko dukanta ba'ayi a gidan nan."



"Kai ƙarya ne batayi dai abin bugun ba, ke nifa wannan kyawun nata yasa naji na tsaneta."


Kafin ta rufe baki taji saukar sassanyan ruwan lemu a jikinta.


Salma ce gari. Ta ɗauki Kofin da Nucy keshan lemu tsautsayi yasa lemun ya kife jikin Nucy.



Wata uwar ashar Nucy ta ɗura tare da furta.

"Yau zaki ga yadda ake displine cikin gidan nan, kin bar yarinya ta lalace tana yadda taga dama cikin gida yau zanyi maku maganinta."

Rarumo Salma tayi tare da ɗaukets da wasu lafiyayyun maruka kai kace wani babba take bugu.


Duƙar da ita tayi ta shiga ɗima mata wasu mahaukatan ƙulli, jifa tayi da ita can gefe tana huci.


Mai makon suga Salma ta fashe da kuka, sai gani sukayi ta miƙe zaune tare da kyalkyacewa da dariya tana kallon gefe daya cikin magana irin ta yara ta furta "BUSARI."


Ba Nucy kadai ba hatta Subi sai da hantar cikinsu ta kaɗa.


Lokaci ɗaya wani matsanancin duhu ya ziyarci ɗakin ya fara mamayeshi.



Dun ɗum ɗakin yayi baka ganin koda tafin hannunka, su Nucy da Subi wuri ɗaya suka dunƙule jiki na mazari.


Ƴar caras da rabonta da islamiyya tun tana ƙarama tuni ta fara karanto wata addu'a Da tazo mata a yanzu."Allahumma inni azubika ,Minalkubsi walkaba'isi."

Taci gaba da mai matata abunta cike da firgici.


Wata hargowa tamkar hadari ya taso gami da wani ƙarar iska mai firgita ruhin bil'adam ta karaɗe falon...........





*SARƘAƘIYA, CHAKWAKIYA, BAZATA, 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 KI TURO ƘUƊINKI HAJIYATA FREE PAGE YA KUSA ƘAREWA 300 BAZATA GAGAREKI BA*






*MEEN@RT...✍🏼*

***