Chapter 8
by @nimcyluv
Yalwataccen gashin kanta wanda ya bazu saman fuskarta,runtsa idanunsa yay lkcn da ƙyaƙƙyawar fuskarta ta bayyana garesa,cikin nayanin mamaki da kuma al'ajabi yace.
"Aljanata"ya faɗa yana zuba mata idanunsu wanda suka soma juyawa zuwa jaa,ya kasa kasgatawa cewa ita ya gani hakan yana nufin ita ɗin mutunce ba aljana ba kamar yadda yay tunani a farko,a hankali ya ƙorawa ring ɗin hannunta idanu wanda ya haske masa idanu sbd sheƙin da yake,ƙara durƙushewa yay saman carpert ɗin tare da kamo hannunta ya haɗa da nasa wanda ring ɗin ke manne a jiki,wani ƙyaƙƙyawan haske ne ya haɗu waje guda sbd haɗuwar rings ɗin waje guda,cikin yanayin tsoro ya saki hannunta tare da miƙewa ya shiga takawa zuwa cikin bedroom ɗinsa,saukar daddaɗan muryarta cikin kunnansa ya sashi tsaya,tabbas itace hakan ya tabbatar masa cewa ita ɗin mutunce,mai yasa ta tsaya masa a rai?,mai yasa take zuwar masa cikin baccinsa?,mai yasa suke ɗauke da zobe iri ɗaya kuma a yatsa ɗaya? Jin cool voice ɗinta ba ƙaramin sauya masa tunani yay ba,tayi amfani da muryar tausayi rauni muryar ɗauke take da neman taimako,a ƙaro na biyu yaji ta ƙara faɗin.
"Please help me"ta ƙare maganar muryata na rawa alamar kuka gaf yake da ƙwace mata.
Yadda kansa ke juya masa yasa shi fara ganin wani duhu jiri ya fara ɗibansa,cikin nuni da shiɗin cikakken soja ne maiji da isasshiyar lpa da ƙuzari,ya saka hannunsa ya dafe kansa dake barazanar tarwatse,tsananin sara masa da kansa keyi masa ne ya sashi taune laɓɓansa,jarumtar dake garesa ya sashi soma takawa zuwa bedroom ɗinsa idanunsa rufe,ba tare daya saurareta ba ko kuma ya duba halin da take ciki ya shige bedroom ɗin tare da banko ƙofar da ƙarfi ya murza key.
Zarina najin shigewarsa cikin ɗaki ta fashe da kuka zuciyarta na aiyana girman wulaƙancinsa,bashi da zuciyar imani da kuma tausayi,jikinta na rawa ta miƙewa tsaye a hankali ta soma takawa tare da niyar ficewa a sashin,zafin zazzaɓinta ne ya ƙaro lkcn da sassan jikinta suka fara amsar iskar da take kaɗawa a wajan masarutar,runtsa idanunta tayi tare da taune lips ɗinta,teeth ɗinta na haɗuwa waje guda suna bada wani sauti,a haka taci gaba da jan jikinta dan bata burin ci gaba da zama da mutum irin mara imani bare tausayi,tana fita sashin ta suka haɗu da Kuyanga Kulsum,cikin tashin hankali Kulsum ta kalli Zarina tace.
"Thank God you are fine,Zarina ina kika shige tun asuba muke nemanki shuru hankalinmu duk ya tashi?"zuba mata idanu kawai tayi ba tare data ce ƙala ba,sbd nauyin da zuciyarta tayi mata tamkar ansaka dutse an danne mata zuciya haka ta keji,wasu sabbin hawayene suka ƙara sauka daga cikin idanun Zarina su take tace wani abu amma ta gagara faɗa sbd nauyin da laɓɓanta sukai mata,gane hakan yasa Kulsum saurin kama hannunta wani tausayinta ya kamata,cikin muryar Kuka Kulsum tace.
"Mun shiga uku Zarina,wannan wacce irin rayuwa muke ciki ne haka?muna rayuwa kamar a bariki,muna rayuwa kamar prison wlh na gaji wannan abun yay yawa,ai mulki ba hauka bane,anci *ZARAFI* nmu ana nuna mana za'a iya komai damu da ƙarfin mulki,Zarina rayuwarki aƙwai matsala wlh damu dake duk muna cikin matsifa yanzu haka Mai martaba ne yaywa Zaitun faɗe gaba ɗaya bata gane komai banda sunanki babu abinda take faɗa,shine tun jiya nake bulayin nemanki amma babu ke sai yanzu da aka aikoni wajan Captain Saifu kawo masa breakfast na ganki,mene kike cikin ɗakinsa badai a can kika ƙwana ba?"Kulsum ta ƙarasa maganar cikin kuka da tsoro haɗi da firgici.
Kasa cewa komai Zarina tayi sai jikin Kulsum ta faɗa tana sakin kuka mai tsuma zuciyar dukkan mai saurare dama mai karatu,kukane wanda yake nuni da yankewar jin daɗin rayuwa,kukane wanda yake nuni da fidda rai dajin daɗi,kukane dake nuni inama Allah zai ɗauki raina na huta da wannan rayuwa,kuka ne dake nuni da zallar baƙin ciki damuwa ƙuncin zuciya,tabbas banda yazu a hadisi cewa idan mutum ya kashe kansa wuta ce masaukinsa babu shakka da ita da kanta zata kashe kanta,bata saba ba,bata san mene tashin hankali ba,tana jin kanta kamar wata sabuwar halitta sbd tension ɗin da take ciki,ganin kukan yayi yawa yasa Kulsum tsagaitawa da nata kukan ta shiga rarrashin Zarina,ƙara fashe Zarina tayi da kuka wanda hakan ya ƙara bawa zazzaɓin jikin damar ƙara ta'azzara,cikin Kuka tace.
"Nagaji i need to go back to my hause,ina tsoro ban iya wannan tashin hankali ina son tsira da raina da kuma mutuncina,wlh i'm tried"ta ƙare maganar tare da ƙanƙame Kulsum tana jinta kamar Mom ɗinta,kama hannunta Kulsum tayi suka ƙarasa sashinsu inda Zaitun ke ƙwance,suna shiga Zarina ta ƙwace hannunta tare da nufar inda Zaitun take a ƙwance tana zuwa ta faɗa jikinta ƙara rushewa da kuka,Murmushi Zaitun tayi wanda yafi kuka ciwo kan Zarina ta shafa tace.
"Masha Allah,Allah kaine abin godiya,tana daɗi da Ubangiji ya bani ikon kare mutuncinki naji daɗi da abin ya tsaya iya kaina bai shafi ƙimarki ba,Zarina ke haske ce a cikin wannan Masarautar,Da yardar Ubangiji saikin zama silar kuɓutar da rayukan jama'ar Bilhas,Ubangiji ya baki baiwa wacce ba lallai ke kisan da ita,ki cire tsoro a ranki ki fuskanci dukkan wani ƙalubale da zaki fuskanta,ki zama mai juriya kada ki taɓa bari prince ya fahimci rauninki?"ta ƙare maganar numfashinta na fusga da ƙarfi.
Ƙara ƙanƙameta Zarina tayi tana kuka tare da faɗin "No! Please kibar faɗin hakan mutun cina da naki duk ɗaya suke,mai yasa zaki bada kimarki ki adana ta wani,mai yasa zakimin hakan wlh kinsa zuciyata ciwo bazan taɓa yafewa kaina ba,indan har wani abu ya sameki,bazan daina kuka ba indai har zakici gaba da kuka a cikin idanunki"ta ƙare maganar tana rushewa da wani sabon kuka,murmushi Zaitun tayi tare da guge hawayen idanunta kana ta riƙe hannun Zarina tace "Abu guda zakimin kisa zuciyata farin ciki ina son kiyi amfani da damarki ki ruguza ikon wannan masarautar ina son ya zamana kece kika kawo ƙarshen wannan zalunci,ina son ki ƙwatarwa jama'ar bilhas ƴan cinso da baiwar da ubangiji ya baki,wannan zuben na hannunki ba haka nan yake zaune a hannunki aƙwai ɓoyayyen abu tattare dashi,tabbas zaki nasara a kansu"da faɗa tana sakin wani murmushin kafin tana idanunta ta rufe,da sauri Zarina ta shiga girgizata tare da faɗin "Tashi dan Allah wlh bazan iya komai babu ke ba,na amince da dukkan abinda kikace kuma zan aiwatar amma ina buƙatarki cikin rayuwata"cikin sannan fitar hayyaci da kuma ɗaukewar numfashi Zaitun ta buɗe idanunta tare da kama hannun Zarina ta ruɗa bisa saitin zuciyarta tace "kinji yadda zuciyata ke aiki ko?to kada ki damu ina tare dake koda yaushe ban bari a cuceki,ina son ki ƙulla alaƙa mai ƙarfi tsakaninki dame Babban ɗaki zan rubuta maki wasu bayanan wanda zaki buƙacesu,Kulsum ɗauketa kuje waje domin tayi wanka ta sauya kayan jikinta ki bata abinci taci zanyi kewarku gaba ɗaya"ta ƙare maganar idanunta na fidda ƙwallah,kuka Zarina tasa tare turjewa haka Kulsum taci gaba da janta har suka fice a ɗakin.
Ajjiyar zuciya ta sauke lkcn da taga sunbar ɗakin,wasu hawaye ta fitar daga cikin idanunta,sbd yadda ta kejin ana zuba mata wani abu a jikinta kamar narkakkiyar dalma haka ta keji,rufe idanuta kana ta buɗe da sauri ganin wani jan abu ya gilma ta cikin idanunta,a hankali ɗakin ya shiga girgiza wani ihu ya soma karaɗe cikin ɗakin,wata guguwa ta shiga bayyana kamar ƙiftawar idanu haka wata jibgegiyar halitta ta bayyana a gabanta,tana zalalu halshe gaba tare da fiddo da banyan haƙwaranta masu tsayi da kuma tsini,sbd tsoron da yayi mata yawa kasa motsawa tayi bare tayi tunanin yin wata addu'ar kamar yadda ta saba,ihu da ƙara ta saki lkcn da halittar ta damƙi wuyanta ta shaƙe,cikin ɗaukewar numfashi Zaitun ta shiga faɗin "La'ilah ha'illahu Muhammadul rasulullah S.a.w"tana faɗin hakan numfashi ya tsaya idanunta suka ƙafe sukai fari jikinta ya saki a wannan lkcnne kuma halittar tayi wurgi da Zaitun kana ta fara wani ihu tare da jijjiga wata sabuwar guguwa ta bayyana kafin wani lkc halittar ta ɓace ɓat.
Su Zarina na fita suka nufi wani ƙaramin ɗaki a nan Kulsum ta haɗa mata ruwan wanka mai zai kana ta fice da ɗakin,zuciyarta cike da tsoran halin da suka bar Zaitun,dircet ɗakin da Zaitun take ciki ta nufa tana zuwa ƙofar ɗakin taji kamar an daki kanta,dan haka ta juya da sauri ta nufin inda tabar Zarina tana zuwa ta sameta harta kammala wankan ta fito,kaya da ɗauko mata farare tas kana ta bata aminci,ƙincin amincin tayi sai kuka da take tana kiran Heart dream and Mom,nan Kulsum ta fahimci zazaɓin dake jikinta da ƙyar ta rarrasheta taci abincin kaɗan ta bata magani tasha,ƙwantar da ita tayi bata bar ɗakin ba,sai da taga tayi bacci kana ta rufe ƙofar ɗakin tayi waje.
Bata ƙarabi dakan Zaitun ba,ta koma sashin Kilishi domin yi mata aiki daman acan take ba,tana ƙoƙarin shiga,taji an fisgota ta faɗi ƙasa kafin ta buɗe idanunta taji an wanketa da mari,cikin ƙaraji Lil prince yace.
"Ina Zarina ina kika ɓuyeta?"ya faɗa yana kai mata wani marin,kuka Kulsum ta shiga faɗin "nima rabona da ita tun jiya munyi nemanta mun rasa"ta ƙare maganar tana sakin wani kukan,wani marin Lil prince ya ƙara kai mata kana yace "ohh sannu ni zaki maida ɗan iska ɗazu zanje Fada naganki tare da ita yanzu kice ba haka ba,ok good"ya faɗa yana bawa Fadawa umarnin suka mata sukaita ɗakin duhun,koda wasa bai yarda a gata abinci ba bare ruwa"kuka ta saka tana neman yafiya amma yay burus ya shige sashin Kilishi,haka Fadawan suka janta zuwa ɗakin duhu wanda yake da nesa da cikin gidan sarautar.
Saifu's pov
Tunda ya shige ɗakinsa ya zube kan bed ɗin ɗakinsa ya shiga juye a kansa,tunani ne fal cikin ransa babu abinda ya tsaya masa a rai sai ƙyaƙƙyawar fuskarta da kuma daimond ring ɗinta wanda ya kasance iri ɗaya da nasa babu banbanci,ya daɗe a wajan domin har akai a zahar yana wajan a ƙwance yana tunani,ganin tunanin bashi da wani amfani ya miƙe ya nufi toilet kayan traning ɗinsa ta cire ya saƙale kan hanger,shower ya sakarwa tare lumshe idanunsa ruwan na dukan ƙyaƙƙyawan naked chocolate skin ɗinsa,babu abin ɗaukan hankali jikin Saifu irin muɗaɗɗan faffaɗan jikinsa,saidai ba ko'ina yake a murɗe ba,amma kallo guda zakai masa kasan cewa shiɗin lafiyayyen mutum ne mai ta ƙama da cikakkiya da kuma kuzari,sosai yake da tsarin halitta mai jan hankali da kuma ɗaukan hankalin ƴan mata, six packs on his body shine abu na biyu mai ɗaukan hankali,wani zazzafan huci ya fesar ta cikin bakinsa,kana yasa duka hannayensa ya dafe jikin bango ruwan ya shiga dukan bayansa,ɗan ya tsuna fuska yay sbd mararsa data ɗaure masa,when zai daina ciwon mara sai yanzu zai daina wahala da wannan banzan feelings ɗin,a hankali yasa hannu ya shafa sumar mararsa tare ɗan matsawa da ƙarfi,ƙara runtsa idanunsa yay sbd zafin da yaji ya rasa sassan jikinsa,wajan 30minutes ya ɗauka kana yay brush ya ɗaura alwala,a nan toilet ɗin ya busar da sumar kansa,kana ya fito yana zuwa ya nufi dressing mirrow inda aka shirya masa kayan shafarsa,wani lotion mai ƙamshi ya ɗauka ya shiga shafawa jikinsa,yana kammalawa ya fesa jikinsa da body spray,kana ya taje kanta ya shafa mai a sumar kan,wajan wadrope ya nufa ya ɗauki wani blue black ɗin long jeans ya sakawa jikinsa,sannan ya ɗauki rigarsa ta sojoji ya saka a jikinsa,sosai yay ƙyau cikin shigar da yayi,covet shoe ya ɗauka ya sakawa kansa,kana ya ƙwashe wayoyinsa,ya fice a ɗakin,bai ko kalli inda take ba,dan yasan zuwa yanzu ta gaji ta bar masa ɗakin,yana fitowa ya nufi masjid domin gabatar da sallah,bai daɗe ba ya fito ya nufi hanyar Fada domin amsa kiran Mai martaba,yana gaf da shigewa Fada ya hangi Fadawa na jan wata a ƙasa,ɗan waro idanunsa yay ganin Lil prince biye dasu,ransa ne ya ɓaci idanunsa suka rufe,cikin takunsa na isa sa izza ya fara takawa izuwa garesu,suna ƙoƙarin janta wani ɓangaren ya buɗe baki tare da dataka masu wata uwar tsawa hatta prince saida ya firgita,cikin taƙaicin abinda sukewa matar ya nufusu gadan-gadan.