12. . . .13
No.12🟦13
.....Lanta da Yanyala harma da Mama suka saki salati,ganina a k'asa kamar matacciya gaba d'aya suka d'aukeni suka kwantar dani a kujera 3seater,yanyala ta sheka ta d'ebo ruwan gora ta watsamin wata irin ajiyar zuciya nayi sannan na mik'e na tashi ina rarraba idanu.
A take abubuwan da suka faru suka fara dawomin kuka na fashe dashi su Mamana na tambayata me ya faru?cikin kuka na sanar musu duk abinda ya faru,sika saki salati suna fadin albarkacin bakinsu,amman ganin da yadda nake yasa suka yi ta bani baki,har Allah yasa zuciyata ta fara sauka a hankali.
Kwana 2 da faruwar al'amarin mun fito compound din gidanmu nida Layla aminiyata don kwana biyu bamu had'u ba,wani guri naga Layla na kallo kamar ta samu tivi,ina ta magana bata san maganar da na ke yi ba,kallon inda ta ke kallo na yi abinda ta ke kallon ne ya tsorata ni sosai,Doctor Saif ne tsaye a jikin motarsa ya sha wata d'anyar shaddarsa Blue colour,ta hadu da choco d'in skin dinsa sai ya yi wani kyau.ko kallonshi banyi ba nayi wucewa ta amman abin mamaki Layla kallon Saif kawai ta ke yi.
Da sauri ya taho inda nake yana smiling dinsa mai k'ayatarwa,ni kuwa nayi saurin juyarda fuskata don gudun had'a ido dashi,don ayanzu babu wata sauran alak'ar ni da shi,don ma haryanzu iyayena basu san me ke faruwa ba.
Bayan sun gaisa da Layla ne ya kalleni don in kulashi ni kuwa na yi mai banza na shiga gidanmu,bayan Layla ta tafi ne,Doctor Saif ya shigo gidanmu suks gaisa da Lanta har ta ke tambayarsa iyayensa,alokacin ina d'akin Lanta ta kwalamin kira nazo ta tashi ta shiga k'uryar d'akinta,guri na samu na zauna ko kallonshi banyi ba.
"Don Allah Nawwara ki yi hak'uri wallahi ba laifina bane laifin Hajiya ta ne,kuma ayanzu komai insha Allah zai dai_daita insha Allah,na yi hakanne don bin umarnin mahaifiyata,kuma nayi hakanne don in manta dake amman hakan bai yiyu ba,don bazan iya mantawa da ke ba Nawwara kiyi hakuri da abinda ya faru...saurin d'agamai hannu nayi sannan na tashi zan tafi,fuzgoni yayi na fad'a kan k'irjinsa,na tashi ina kokarin tashi kwayar idanunsa nake kallo yayinda nake ganin tsabar soyayyata acikinsa bansan sanda na kwanta k'irjinsa ba ina sheshek'ar kuka don soyayyar Saif har cikin zuciyata na ke jinta.
Tunda daga wannan rana muka shirya nida Saif abin har yafi nada.
****
Da sassafe Saif ya shirya ya tafi Rano garin kakanninsa na Uba da wuri ya gama shirinsa tsaf sannan ya fito ya hau motarsa har tayar da motar sannan ya tuno baiyi sallama da Mahaifiyarsa,sashinta ya shiga ya sameta tana breakfast da k'anwarsa Rabi'atu,yana shiga Rabiatu ta gaishesa cikin girmamawa dob Hajiyarsa bata da wasa wajen bada tarbiyya,shiyyasa suke matuk'ar shakkarta.gaishe da Hajiyarsa ya yi sannan ya shaida mata tafiyarsa,a take ranta ya b'aci ta hau bala'i wai zaije k'auye alhalin yana da aiki.
Da k'er ya lallab'ata sannan ya samu ya tafi don yasan Hajiyarsa basa shiri da kakarsa Hajjo kakarsa,don Hajjo mutunce mai fad'in gaskiya komai d'acinta,ga ta da masifa matuk'ar ka tab'ota don bata barin ta kwana.
A tsakar gida ya sameta tana ta to ne_to ne ita da jikanta k'anin Mahaifin Saif wai bai iya komai ba sai cinye mata abinci da kayan shayi,har ya shiga gidan tana ta sababi bata san ma ya shigo gidan ba.
"Wallahi Sale bazan k'ara bari ka shigar min d'aki ba tunda ba Khabiru ne ya ginamin gidanba Bashir ne ya gina min ba ubanka ba,kuma suma kayan shayin ai naga Bashir ne ya ke kawomin,ka shiga idona in rufe wallahi.....
Dariya ta saki ganin Saif a gabanta tan cewa" sannu da zuwa likita bokan turai,ai na zata ma ka manta dani don ni nasan wannan mai tallan nonon ba barinka za ta yi kazo ba"Mace sai shegen shisshigi oh"oh rabani da wannan uwar taka.
Canza fuska Saif ya yi sannan ya zauna yana cewa"oh Hajjo gaskiya ki daina zagin Uwata me ta yi miki da zaki dinga zaginta haka kawai?".
"Inye sannu mai uwa ita Aishar ce ta ce kazo ka yi min tijara irin ta y'ay'an yanzu to wallahi yau k'afata k'afar ka agidannan saina bika har cen kano d'in inji abinda yasa ta aiko ka kazo kacimin mutunci Allah yau sai dai Bashir ya zab'a koni ko mai tallan Nono,tana kaiwa nan ta fara kuka.
Sale ne ya fara dariya yana cewa" ai indai Hajjo ce sai ta yi wa mutun abinda zaisa su b'ata,watan nan fa albashi na duk haka na d'auka na suyo mata hijabai harda ta kalma ko uwata ban siyawa ba,amman kaga Hajjo abinci na ci agidannan yanzu sai ta yi yimin gori".Tsintsiya Hajjo ta d'auko ta cillowa Sale ya fita da sauri yana dariya,sukayi Sallama da Saif akan cewa Zaije kasuwa in kuma lokacin bai dawo ba to ya gaida gida.
Abin ma dariya ya bawa Saif don daman yasan matuk'ar yazo to fa sai anyi fad'a don ita mutunce mai saurin juya zance,kuma idan tasan da zancen da yazo yaya kenan?amman ya zama dole ya fad'a mata don yasan ita ce zata kawo k'arshen komai don bazai tab'a iya rayuwa babu Nawwara ba.
Sai da ya gama shawararsa sannan ya gayawa Kakartasa duk abinda ya ke faruwa,ai kuwa yana gama maganar ta fara sirfa masifa kuma ta ce yau ba za ta yi kwanan Rano ba,Kwanan Kano za tayi yau sai allura ta tono garma.
Ai kuwa hakan ce ta faru don sai da ta yi sallama y'ay'an ta mata masu Aure harma da mazan sannan ta yi Sallama da mak'otanta,suka d'au hanya sai Kano acikin mota ma Hajjo Masifar ta ke yi.
Suna shigowa lokacin Hajiyarsu Saif ta dawo daga Aiki,ko kallonta Hajjo ba ta yi ba ta yi shigewarta tana masifa,tunda Hajiya taga haka cikinta ya d'uru ruwa don tasan yau kashinta ya bushe.
" yanzu Aisha saboda rashin kirkinki shine zaki hana d'anki Auren sunnah yarinyar da ya keso yake k'auna waidon tana amatsayin buzuwa,Sai me don ya Aureta?"ke kin manta sanda aka auroki kina tallan nono ko?to idan kin manta bari in tuna miki,d'ana yaje Bautar k'asa ki ka lik'emai sai da ya Aureki, ina ji ina gani aka Auroki kika zo kika yi tashan ruwan shadda saboda babu a House,to wallahi yanzu kema wallahi baki isa ba,idanma Bashir d'inne ya ke d'aure miki gaba,yazo in gani,tana fad'in hakan ta d'ora k'afa 1 kan d'aya.
Ranar Saif yasha fad'a wajen Hajiyarsa kamar zata cinyesa,shi dai haka ya d'auki laifinsa don yasan shid'in me laifi ne,sai dai ba zai iya hak'ura da Nawwara ba.
Mahaifinsu Saif yana dawowa Hajjo ta d'ora akan masifarta,Alhaji ya yi mamaki sosai don ya d'auka matar tasa ta hak'ura,abin ya bashi matuk'ar haushi don saida ya nunawa Hajiya matuk'ar ta hana wannan Auren to ta saka ran nata ma zai lalace.
Hajiya fa duniya ta yi mata zafi sosai kuma tasha alwashin matuk'ar tana numfashi sai tasan yadda za ta yi ta raba wannan Auren ko da kuwa zata rasa ranta ne.
Don haka ta kirawo k'awarta Hajiya Hadiza don su shawarta yadda zasu b'ullowa abin,dariya Hajiya Hadiza ta yi sannan ta ce"Hajiya Aisha ki kwantar da hankalinki,wannan Auren koda ma anyi shi sai ta kwammace bata Aureshi ba don sai ta gwammace kid'a da makad'i,dariya suka saka a tare sai alokacin zuciyar Hajiya Aisha ta d'anyi sanyi amman ta tabbatarwa kanta ba zata tab'a barin Nawwara ta ji dad'i ba.
***
Alhmdh a yanzu saura sati 1 bikin Doctor Nawwara da Doctor Saif don an kammala komai jiran lokaci kawai a ke yi,amarya ta yi kyau sosai don masu gyaran jiki tun daga meduguri wato Borno aka d'aukosu.
Don ayanzu in kaga Nawwara ba zaka kagane ta ba,ga uwa ubansu y'an Niger masu magani kala kaka,don Yanyala da kanta ta fara gyara Nawwara.
Don Allah kuyi hak'uri rasuwa akayi mana ne shiyyasa nayi tyiping kad'an,amman next insha Allah zanyi da yawa.
Ummu Maher ce.