16. . . . .17
*_⚡DOCTOR NAWWARA⚡_*
NA
(UMMU MAHER) MISS GREEN🍀
Na kusa gama free pages start paying 200 ne kacal ta wannan account number 2212328303 RABIATU BASHIR ZENITH Bank.ko katin Aitel ko na Mtn ta wannan number ***.yanzu za'a fara labari.
16🟩17
..hankalin Mahaifina ya tashi sosai,da Saif yasan bazai Aureni ba ai ba zai tara mutane akan aikin banza ba,Mai Martaba ma yaji haushi sosai akan abinda ya faru,matsowa yayi dai dai kunnen Alhaji Auwal ya rad'a masa wata magana ban san ko meye ba ni dai Ummu Maher naga Alhaji Adam ya fara fara'a nan da nan aka sanar cewa akwai d'aurin Auren da za'ayi kowa ya tsaya,abinda kowa yayi mamaki dashi shine Sarki mai Martaba ne ya d'aurawa d'ansa Auren Nawwara.
Nan fa wajen ya kaure da maganganu wad'anda suka San abinda Yarima Jalal ya ke ciki suka dunga tausayawa Nawwara don wasu har kwalla suka yi mata cewa ita ma ta zama gawa kamar yadda sauran matan nasa suka zama gawa,Mai Martaba ya umarce Alhaji Adam bayan d'aurin Aure akwai maganar da za suyi ta sirri,aka d'aura Aure akan sadaki dubu d'ari.
Bayan an gama d'aurin Auren ne Mahaifin Nawwara ya samu Mai Martaba a babban falon gidanshi Amman ba ainahin gidanshi,Gidan da yake hutawa.
Babu abinda Mai Martaba ya b'oyewa Mahaifin Nawwara komai sai da ya sanar dashi har zuwa yanzu,Mahaifin Nawwara ya yi shiru hankalinsa ya yi matuk'ar tashi,cen kuma ya CE"babu Komai Allah ya shige mana gaba,daga haka suka cigaba da zantawarsu akan matsalar da kuma yadda za,ah tun kari matsalar da shi Kansa angon yadda za'a sanar mishi.
Gidanmu ya cika damk'am bayan y'an d'aurin Aure sun dawo kowa fuskarsa babu fa'a sam,kowa kaga fuskarsa kamar anyi mai alk'awarin shiga wuta.
Yayan Mahaifiya ta ne ya sameta ya fad'a mata duk abinda ya ke faruwa sannan ya ce kada a sanar dani da wuri saboda hankalina zai tashi,Umma ta samu Lanta da Yanyala da kuma sauran y'an uwa ta fad'a musu abinda ke faruwa cikin tashin hankali,kowa da abinda ya ke cikin ransa mamaki da kuma tausayin Nawwara,haka suna ji suna gani aka hana kowa sanar da Nawwara abinda ya ke faruwa.
Ni kuwa haka kawai naji gabana yana fad'uwa don rabona da waya da Saif kwana 1 kenan har yanzu ko da na buga wayarsa baya d'auka,ko gaisuwar iyaye ban sunzo sunyi ba tunda al'adarmu CE yin hakan,na yi matuk'ar damuwa ga shi har yamma ta yi wayarshi switch up.
Na kalli Humaira Y'ar k'anwar Mahaifina na CE"wallahi Humaira narasa me ke damuna gaba ki d'aya zuciyata babu dad'i tun jiya nake kiran wayar Saif a rufe"?na fad'i hakan ina ya mutsa fuska kamar zanyi kuka.
Allah ya Sani ina matuk'ar son Saif bazan iya rayuwa babu shi ba,tunda muka fara soyayya bamu tab'a kwana 1 ba muyi waya ba koda text message ne sai gashi yau aranar d'aurin Auren mu wannan matsalar ta faru.
Humaira ta yi dariya ta ce"kai gaskiya Nawwara kina da zumud'i wallahi kin San wasu angwayen sunfi son hakan sai kinje su jiyar dake farin ciki,don haka ki daina damuwa watak'il angwan naki suna cikin irin wad'annan mutanen.
Ban gama shiga damuwa ba sai da dare ya yi naji babu Wanda ya yi min maganar kai ni d'akin miji,gashi ni kuma babu damar in tambaya?ranar har 10 na dare banyi bacci ba ina cikin tashin hankali sosai.
Ko dai Saif ya mutu ne?ake bb'oyemin in dai har ba mutuwa yayi me yasa ba a gaya min ba?babu tambayar da banyi wa kaina ba Amman na nakasa gano amsar don dole na hak'ura na kwanta bacci b'arawo ya sace ni.
Cikin bacci na na yi wani mummunan Mafarki wai gani a wani daji babu kowa ina ta kuka,wata mata tana bina da wuk'a kawai sai na ga wani kyakkyawan matashi yazo ya hankad'eta ta fad'i k'asa.
Nan matar ta fara ihu tana kuka matashin ya ruk'o hannuna muka tafi wani gida mai kyaun gaske,dai dai na farka a gigice ina kiran sunan Allah,y'an matan da ke d'akin suka fara tambayata ko wani Abu ne ya faru?na ce musu a,ah.
*Yarima Jalal*
Yana kwance a babban farlonsa yana kallon wani kabarai a aljazira,kawai sai yaji kiran mai Martaba a wayarsa ya d'auka cikin girmamawa ya gaishe shi Yace yazo yana son ganinsa yanzu,kafin ya amsa kawai sai ganin Saima akansa tana wani had'e fuska.
D'aga mata gira ya yi alamar tambaya?.
"Wai Jalal dawa ka ke waya ne kake wani kashe murya a farlona"?
" ke kin isa ki hanani waye acikin gida na?ki Sani cewa ita dama 1 ce take zuwarwa mutunm arayuwarshi idan damar ta wuce shikken don haka ki yi taka tsan tsan da rayuwa.
Tashi ya yi ya shiga d'akinsa ya fesa wankansa ya yi matuk'ar kyau Yarima irin mazan Nanne masu zubin k'arfafa irin y'an raatilin d'innan,ga kyau ga kud'i ga kuma ilimin addini sai abin ya bada armashi sosai.
Yana sanye da yadinsa ruwan fari mai shara² ya taje sajensa mai yawa ga shi sai k'elli ya ke yi,yana cikin fesa turare Saima ta shigo ta wani rafka salati"ya juyo ya wuce ta kusa da ita yana tsaki.
Binsa ta yi da kallon mamaki wai yau Yarima ne ya ke yi mata wannan shan kashin,lallai ta yi sake a wannan lokacin don yadda ta saka aka d'aure bakin Yarima sai yadda ta ce ya yi,Amman wai yau ne har da wannan shirin kamar me shirin zuwa tad'i,lallai dole ta yi wani Abu don ba zata tab'a had'a miji da wata mace ba yadda take son Yarima tamkar ranta,kuma za ta iyayin komai saboda ta mallakeshi shi kad'ai.
Tuni ta nemo wayarta ta d'auko wata number hannunta har yana kakkarwa,ringing 1aka d'auki wayar kamar zata fashe da kuka ta fara magana.
"Na shiga ukuna ni Saima domin asirina gab ya ke da tonuwa wai
[11/25, 17:51] 🥰Ummu Maher🏕️⛱️: Ni Jalal ya ke wulak'antawa harda yimin tsaki,daga d'aya b'angaren na jiyo muryar wata mata na cewa"to se me idan yayi miki tsaki kedai kawai ki rik'e mana alk'awari kada ki bari kowa yasan halin da muke ciki don tonuwar asirinmu tonuwar asirinki ne don haka kiki yaye.
Saima bata so hakan ba Amman babu yadda ta iya dole ta yi musu biyayya ko don kwad'ayin abin duniya.
"Jalal ba komai ne yasa na kirawo ka ba magana ce mai mahimmaci don haka ka nutsu kaji me zan CE maka ba umartarka ko Neman izininka na ke yi ba,domin kuwa na Riga da na yanke duk wani abinda zanyi don haka ya zamar maka dole ka yi min biyayya.
Shi dai Jalal kanshi a k'asa ya ke yana sauraron fad'an da Mahaifinsa ya ke masa,don zai iya cewa hakan bata tab'a faruwa a tsakaninsu ba don haka koma menene wannan abin yana da matuk'ar mahimmanci.
Nan Mai Martaba ya fad'a mai duk abinda ya faru har zuwa yanzu da ya D'aura mai Aure ba tare da saninsa ba.
Wani irin razana Jalal ya yi idanunsa sunyi jawur jijiyoyin kansa sunyi rud'u² alamar b'acin rai sosai a fuskarsa da zuciyarsa,Me yasa mahaifinsa ya yi masa haka?me yasa be nemi shawararsa lokacin aiwatar da wannan babban laifin ba,azuciyarsa kuwa harya fara tausayawa wannan yarinyar domin Mahaifinsa yafi kowa sanin halin da ya ke ciki duk matar da ya Aura sai haka ya faru da ita ma'ana sai ta mutu, Saima ce kawai Allah yasa da sauran kwananta agaba Amman ita ma mafi yawanci tana gaya masa irin mafarkan da ta ke yi lokaci zuwa lokaci.
Shima Mai Martaba tashin ya yi daga zaunen da ya ke sannan ya CE"Jalal nasan abinda ka ke tunani nima na yi wannan tunanin Amman nasan koma menene ajiki na ina jin wannan Auren naka shine zai kawo k'arshen komai Insha Allah.
[11/25, 18:19] 🥰Ummu Maher🏕️⛱️: Zamu dage da addu'ah insha Allah babu abinda zai faru na saka ayi mana saukar alQur'ani mai girma insha Allah babu abinda zai faru kaima ka dage da addu'ah insha Allah wataran ko bayan raina sai ka yi alfahari da wannan Auren,Domin Allah ya Sani har yanzu akwai wani Abu da ya ke cikin raina kuma na ke zarginsa domin nasha mafarki da fuskar mutumin Amman Allah baya bacci ka dage da addu'ah.
Har yanzu hankalinsa bai kwanta ba gani ya ke yi kamar ma ana sane ake had'a shi da mata yana Aura suna mutuwa,ko dai maganar da Saima ta tab'a gaya mai ne akan cewa Kodai iyayensa suna sane suke had'ashi da Mata suna mutuwa,yana son iya yensa sosai bazai tab'a yiyuwa ace sune suke yimai haka ba,don ranar da Saima ta fad'i wannan maganar ba k'ara min fad'a suka kwasa ba don bazai tab'a bawa wata mace damar yiwa iyayensa wani cin zarafi ba don iyayensa sune gaba da komai a rayuwarsa.
*Nawwara*
Wani irin ihu na saka alokacin da Mahaifina ya ke shaidamin duk abinda ya faru ina kuka Lanta na kuka ta rungumeni tana cemin ai Allah ya musanya min da abinda yafi alkhairi tunda gashi yanzu na Auri d'an Sarki,wannan Kalmar ta kaka ta itace ta ke k'ara yimin k'una acikin Zuciyata ban sanshi ba?ban San daga inda ya ke ba kawai sai ace an d'auramin Aure dashi?.
*Ummu Maher CE*