MIJIN MACE ƊAYA PART ONE

Chapter 14

by @ummindaddy77

MUS'AB A GIDANSU

Mus'ab ya gama zaiyyanewa Abbansa komai game da saɓanin da suka samu da Safinat da mahaifiyarta ya ciro wayarsa ya nuna masa video na sheƙe ayar da suke yi ita da saurayinta kana ya ce daga mahaifinsa da Umma Laure zai nunawa don su san abin da yake waƙana shi ma don ya zama hujja.

Abban Mus’ab da ya gani ya girgiza matuƙa kuma ran shi ya ɓaci sosai, “Subhanallahi! Me ya sa yarinyar nan take son ɓata rawar ta tsalle. Albasa ba ta yi halin ruwa ba. Ya Allah ka shirye ta da dukkanin waɗanda suka kauce hanya.”

Shiru ya yi da zai kai daƙiƙa guda yana takaicin abin da ya gani. Safinat dangin Babanta dukkaninsu 'yan Maraɗi, shi ma mahaifin nata kasuwanci ne ya kawo shi ya zauna gabaɗaya, jifa-jifa yakan zuwa ƙasar tasu gaishe da 'yan uwa. A haka suka haɗu da Umma Laure har suka kai ga aure.

Yayin da mahaifin Safinat ya rasu, suka ce sun damƙa amanar 'ya'yan duniya da lahira a hannun Abban Mus'ab kasancewar sun yi nesa da su kuma ba za su raba yara da inda suka saba, inda suka taso.

Bayan ya sauke ajiyar zuciya ya ce, " Kana ji na Safinat ta fitar da mijin aure, idan ba ta fitar ba ni zan haɗa ta da wanda na ga dama, ka shaida mata saƙona.”

“To Abba in sha Allah zan sanar da ita.Amma ya batun Umma Laure, da ta ce za ta riƙe Safinat.”

“Bar ni da ita. Ba ta isa ta karɓe Safinat daga hannuka ba, idan ka ga Safinat ta bar hannunka sai mutuwa ko aure. Ba mai iya jure zama da Laure, ina mai tabbatar maka da Safinat da kanta za ta nemi koma wa gidanka. Allah ya kara maka haƙuri da juriya.” Ya amsa masa da “Amin Abba.” Ya ajiye masa kuɗi, "Abba ga wannan kaɗan ne."

Ya miƙe ya ya nufi ɓangaren mahaifiyarsa ya tarar da ita bisa sallaya tana addu'o', ya zauna a gefe bayan ta kammala addu’ar ne cikin rutsunawa ya gaishe ta, ta amsa cike da fara’a, shiru ya yi ita ta katse shirun da “Mus’ab ina dai fatan lafiya.”

Gauron numfashi ya sauke, sannan ya zayyana mata duk abubuwan da ya wakana.

Sai da ta jinjina lamarin sannan ta ce, “Matakin da Abbanka ya ɗauka kuma ya zartas shi ne daidai. Ni ma abin da zan ce da kai ka ƙara haƙuri kuma ka kasance mai juriya saboda 'ya’yan yanzu wanda ka haifa a cikinka ma zama da su sai da haƙuri ballantana 'yar riƙo. Kuma ka sani riƙe maraya yana da ɗimbin lada, saboda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce, ni da mai riƙe maraya ka hataini fil janna yana mai nuni da yatsunsa biyu da ke jere, wannan hadisin yana nuna mana duk wanda ya riƙe maraya bisa gaskiya da amana za su shiga aljanna kafaɗa-da-kafaɗa da Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama. Mutum ya shiga aljanna tare da a fiyayyen halitta akwai falala da ta kai haka kuwa?”

Mus’ab kan shi a sunkuye ya ce, “Babu Umma, ai ko da Sahabbai za ka shiga aljanna abin farin ciki ne ballantana fiyayyen halitta.”

“To ka yi haƙuri ka kasance tare da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.”

Mus'ab ya ji daɗi sosai da tunatarwar da mahaifiyarsa ta yi masa, domin ya ƙara kwarin gwiwa.

Ta yi masa addu'o'i na fata na alheri, yana amsawa da amin da zai fita ya ajeye mata bandir na kuɗi ya fice.

Umman Mus'ab ta juya kuɗin ba ta san lokacin da ƙwalla ya cika idanunta.

"Ya Allah wannan bawa naka ya Allah ya arzurta shi da haihuwa ya Allah ka ba shi 'ya’yan da za su ji ƙansa kamar yadda ya kasance mai jin kan iyayensa." Ta share hawayen da ke zirya saman fuskarta na tausayin ɗan ta.

BAYAN MUS'AB YA KOMA GIDA

Mus’ab na koma wa gida ya tarar da matar shi ta yi shiga mai ɗaukar hankali, tana kwance a gado a rigingine wanda duk baligin da ya ganta sai ya rikice ga ƙamshi mai ɗimautar da wanda ya ji ke tashi a ɗakin yana ƙarasawa inda take ya rungume ta yana sumbatarta, idanunsa ya lumshe daidai lokacin da breast ɗinta suka soki chest ɗinta, haka ma tausasan lips ɗin ta suka gogi shoulder ɗinsa.

Wahalallen numfashinsa da ke ƙoƙarin barin jikinsa ya kwato, wanda hakan ya sa shi sakin wani irin nishi cikin wani irin sexy voice ya ce da ita a kunne, “I love you my wife.”

Ita dai ta gagara ce kanzil ji take yi wani abu na musamman na ratsa ta, daga sama har zuwa tafin ƙafarta. Numfashi kawai take saukewa shi kuwa ya kara matse ta gam bisa ƙirjinsa yana shafar jikinta ya ce, “Tawa, ba zan taɓa gajiya da jin ɗumin jikinki ba, haka kuma ba zan taɓa ƙosawa da shafar wannan tattausar jiki kamar na mage ba. A duk lokacin da na kasance da ke nakan manta a wanne duniyar nake.”

A hankali ya kai fuskarsa saman nata ya fara tsotsan bakinta, a hankali ta samu ta janye ta ce, “Dear ya kamata mu je mu ci abinci.”

Numfashi ya sauke sannan ya ce, "To ai irin shigar da kika yi ai na ɗauka yau babu cin abinci."

Murmushi ta yi kawai ta sauka daga gado.

Ya zuba mata idanuwa ya ce, “Kin yi kyau sosai fa my wife.”

Ta amsa da “Na gode nawa ni kaɗai.”

“Kin ganki kuwa kamar Balarabiya.”

Ya kuma runtsa idonsa ya buɗe, ya ce, “Kin kuma juye wa fa kamar Ba'indiya.”

Ta kyalkyale da dariya, “Kai ba, ba ka gajiya da raha ko, ƙara runtse wa na koma Baturiya.”

Ya runtsa ta kamo hannunsa ta ce, “Mu je a ci abinci kar garin runtse-runtse ido ka ce na koma aljanna ka tsora ta.”

Shi ma kyalkyale wa da dariyar ya yi suka nufi inda abinci yake.

WASHE GARI:

Umma Laure da Feenah a tunanisu Mus’ab tun yamma zai zo gidan don sulhu, sai suka ga saɓanin haka ga shi har gari ya waye babu shi babu ƙirar wayarsa.

Feenah zaune take da shinkafa a gabanta fara da mai ko wake babu, sai ruwa a cup ko black tea babu tana turawa da kyar, ta dubi Ummanta ta ce,

“Umma ki ga yaya shiru babu ɗuriyarsa.”

Wani irin kallo ta jefe ta da shi ta ce, “Ko za ki komar da kan ki ne? Don tun jiya na gama fahimtar inda kika dosa ke kika kawo kanki sai ki mai da kanki.”

Ta sosa ƙeya “ To Umma, bari hantsi idan ya yi sai na yi wanka na koma.”

Dalla mata harara ta yi ta ce, “Lallai ba ki san gatse ba, ki koma idan ba ki da hankali ina ƙoƙarin samar miki da 'yanci, ke kuma kina nuna ƙosawarki da zama a tushenki. Ki koma ki zama a bar gori.”

Ta tura baki, “Umma, ni ba ƙosawa na yi ba, kin san halin Yaya idan ya share ka baya saurin waiwayar mutum, idan zama ya yi zama ‘yan tsegumi za su samu abin faɗa. Ni a ganina ko ina can za ki iya kiran wayarsa ki ja masa kunne sai kuma ki ƙira Baffa ya masa iyaka.”

Miƙe wa ta yi a kufule ta nuna mata hanyar waje ta ce, “Safinat ga hanya kina iya tafiya, amma ki sani idan kin tafi za mu raba gari ba ni ba shiga lamarinki.”

Miƙe wa ta yi ita ma ta kama Umman nata ta ce, “Ki yi haƙuri Umma, ban taɓa tunanin maganganuna zai ɓata miki rai haka ba.”

Tsaki ta yi mata fuuu ta shige ɗakinta ta bar Safinat tsaye.

Wuri ta nema ta zauna ta ture abincin da ke gabanta gefe ta yi ta gumi hawaye suka fara zirara a kuncinta.

KANO (TAKAI)

Bayan su Aliyu sun kammala ƙarin kumallo, da hantsi ya yi a ka yi musu jagora zuwa gidan sirkaninsq.

Kwaraɓaɓen gida ne ginin ƙasa, kana shiga gidan za ka fahimci mazauna gidan gajiyayyu ne.

Yagwalgwalar Turai da Mama ke tafiya a jere yayin da Aliyu da Saif ke mara musu baya.

Yayin da suka shiga cikin suka yi sallama, dukkanin jama'ar gidan suka miƙe suna yi musu sannu da zuwa.

Tabarmar ƙaba a ka shimfiɗa musu, bayan sun zauna a ka gaggaisa.

Ma'u na ɗaki zuciyarta cike yake fal da baƙin ciki.

Yagwalgwalar ce ta yi gyaran murya ta fara bayani kamar haka.

“Baffan Ma'u yau Allah ya nufa sirikinka da mahaifiyar shi sun zo, Allah ya sa mu fahimci juna Allah kuma ya tabbatar mana da alheri.”

Hular da ke kansa ya cire ya sosa sankonsa ya kuma mayar da hular ya ce, “Amin, da yardar Allah za a fahimci juna, ai duk wanda ya nuna yana son naka ya gama maka komai.”

Yagwalgwalar Turai ta nuna Mama ta ce, “Wannan ita ce mahaifiyar wanda zai auri ɗiyarku, mijinta marigayi ƙani ne a gare ni.”

Ta nuna Saif ta ce, “Wannan mahaifin shi shi ne autanmu.”

Ta nuna Aliyu da kansa ke sunkuye ta ce, “Wannan kuma shi ne angon Ma’u da yardar Allah.”

Wata da ke zaune a gefe ne ta sake guɗa “Ayyeriyeee! Su Ma’u an yi goshi Allah ya ba wa 'yan baya.”

Ma’u kasancewar duk tana sauraran hirar da a ke ta ja tsaki “Idan har raba ni da Ahmadina shi zai sa na yi goshi, na shekara dubu ban yi goshin ba.”

Yagwalgwalar Turai ta dubi Mama ta ce, “Hajiya na san ba za ki rasa abin cewa ba, to Bismillah.”

Mama cikin izza da nuna isa ta fara magana tana cewa, “Tabbas yarinyarku ta dace, samun miji irin Aliyu da haɗa zuriya da irin mu babbar nasara ce ga wanda ya samu, za a tara mata dubu da wuya a cire kwara ɗaya wacce za ta taƙi sa'ar samu miji irin Aliyu, a birni ma ba a ƙauye ba. Wannan kaɗai ya isa ku godewa Allah.”

Baffa ya ce, “Wannan gaskiya ne, mun godewa Allah sannan kuma muna yi muku godiya da irin wannan karamci, mata birjik a birni amma kuka tsallake su, a ƙauyen ma don kuna son mu da alheri ba ku je ga kowa ba kuka tunkare mu, ba ni da ishashshiyar kalmar da zan gode muku sai fatan Allah ya saka muku, wannan haɗi da za a yi Allah ya sa idan an ɗaura auren mutu ƙaraba ne.”

Waɗanda ke wajen suka amsa da amin.

Ma'u da ke ɗaki ta ce, “Na fuskanci wannan da ake ikirarin surkuwata ce tana da raini da son nuna izza, to kar ki yi tunanin ni 'yar ƙauye za ki nuna mini isa da izza, to walki ce daidai kugun kowa. Ki sani idan har aurena da ɗan ki ya tabbata sai na tankaɗa miki tankaɗen rashin mutunci. Sai na saita ki za ki ce gwamma ɗan ki ya auro Magajiya 'yar bariki da ni idan na fara surfa miki buhu-buhun rashin mutunci. Kina wani gwaɗa ɗan ki ke ba ki san soyayya gamon jini ba ne, ba zai taɓa samun gurbi a zuciyata ba. Kai kuma Baffa girma ya faɗi. Allah wadarai kwaɗayi ya sa kana ƙasƙantar da kanka.”

Matar mahaifin Ma’u ce ta ce, “Hajiya muna godiya Allah ƙara girma da ɗauka."

Ta ɗan sahirta kaɗan ta ci gaba, "Hajiya mu fa idan son samu nema a ɗaura auren ku tafi da amaryarku. A bari ya huce shi ke kawo rabon wani. Ko ba haka ba Malam” Ta dubi mijinta.

Aliyu ya ɗago ido ya kalli wacce ta furta hakan ya kuma sunkuyar da kansa.

Yana murmushi ya ce, "Kwarai kuwa, abin da nake da niyyar faɗa kin riga ni."

Mama, kanta ya kuma kumbura, a zuciyarta ta ce, "Irin gidan da nake so alamu ya nuna zan yi mulki daga kan 'yar har iyayen."

Ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi ta ce, ".....