9️⃣
by @maidambu41
*PAID BOOK*
*ABIN DA YA BAKA TSORO*
(Arrow of Destiny)
EWF
9️⃣
*The Royal Victoria Infirmary Newcastle upon Hospital London*
A hankali ya fito shi daya daga cikin VIP ROOM, da aka rubuta a jikin bangon dakin. Cire safar hannun shi yayi da facemask din shi ya koma gefen kujerar da yake jikin dakin ya zauna jagwab. Yana sauke ajiyar zuciya.
D'ago kai yayi yana me kula da alamuran shi.
"Yallabai ya jikin nata?" A hankali ya sauke heaven breath kafin ya gyara zaman shi ya had'e hannun shi wuri guda, yana mamaki da al'ajabin halin Meryam tana dauke da wannan al'amarin ta iya boye mishi na tsawon shekaru goma sha huɗu, how comes?
"Tana lafiya" ya furta a hankali, yana sauke ajiyar zuciya. A karo na biyu,
"Yallabai yaran suna gida tare da Ayyah!"
"Hmm" ya fada, kafin ya mike a hankali yana me zare necktie din shi ya mikawa mutumin, ya fara walking very gentle. Yana mamakin yadda take taking risk a rayuwar ta, bayan ta san ciwon ta Anytime zata iya mutuwa. Lokacin da ya fito waje anan ya sami motar shi ta zirga-zirga, bude mishi motar drive yayi sannan mutumin da suke tare ya bude na shi bangaren ya shiga gaban motar. A hankali ake tuka motar.
Maganar likitan ne ya dawo ƙwaƙwalwar shi tirya-tiryan.
"Mr Mehd a yadda muka fahimci matsalar matar ka, cutar dajin ya gama cin saba'in cikin dari na jinin ta, idan muka ce zamu barta da cikin jikin ta wanda bai wuce satittika ba, zata iya mutuwa daukar kasadar tayi yawa ka saka hannu zamu cire cikin jikin ta"
Lumshe idanun shi yayi yana jin wani irin kwaila yana cika idanun shi, duk abinda ya faru ai laifin shi ne, domin shi ya banzatar da ita. But ai ba laifin shi ba ne, ba kuma ta zuciyar shi ba ne. Hawaye ne ya sauko daga idanun shi,
*Inna Isa! Itace mafarkina*
Ya furta a kasar zuciyar shi, ita ce duniyar shi baki daya. Ita ce mafarkin shi. Sai dai kuma al'amarin qaddara, ya shiga tsakaninsu ya shinga wata irin sirrintacciyar al'amari wanda shi kansa bai san mafarin balle karshen ba.
"Yallabai mun iso"
Hannun shi ya sa ya ɗauke ƙananan kwallar da suka cika idanun shi, har suka yi nasarar saukowa.
A hankali ya zura kafar shi tare da fitowa a motar. Sannan ya nufi cikin, inda ya same wata babbar mace tsaye da yar shi tana kallon shi. Da gudu ta tawo tare da rungume shi tana kuka.
"Daada ya jikin Mammy?"
Dan saukoyawa yayi daidai fuskartar yana share mata hawayen dake kwance a fuskar ta.
"Da sauki Nadia"
"Toh yaushe zata dawo?"ta tambaye fuskar ta a narke.
"Very soon" ya bata amsa yana kallon yadda take matsar kwalla.
Riko hannun ta yayi suka nufi kofar shiga cikin gidan.
"Barka da dawowa Yallabai ya Mammyn Nadia ya jikin na ta?"
"Da sauki" itama ya bata amsa a takaice, sannan ya nufi hanyar dakin shi yana rike da hannun Nadia.
"Ina Eman da Junaid?"
"Sun yi barci"
"Kice Ayyah ta had'a miki Black tea ki kawo min." Ya fada a hankali, sannan ya nufi hanyar dakin shi.
Wurin Ayyah ta nufa tana faɗin.
"Tente Ayyah inji Daada wai ki bani tea din shi!"
"Toh!" Ta furta, sannan ta nufi kitchen din da yarinyar suka hada mishi tea din, ta daura akan tire din ta bata.
A hankali ta nufi dakin shi, ta same shi a zaune yana cire safar kafan shi, amsar tea yayi yana faɗin.
"Thank you, Fatimah! Ki je ki kwanta gobe after school zan turo akai ku wurin ta"
"Toh" sannan ta mishi sai da safe, ta nufi hanyar waje.
Har ta isa bakin kofar dakin, ta juyo a hankali idanun ta cike da kwalla ta ce mishi.
"Daada ka yafewa Mammy?" Rintsa idanun shi yayi yana jin kamar tana huda mishi zuciyar shi da kibiya.
"Yana yafe mata!" Ya furta kwalla na cika idanun shi, wannan shine karo na karshe da ba zai iya ce mata ya wuce ba, sai dai ya furta mata ya yafewa Mahaifiyar ta. Da gudu ta dawo ya bude mata hannu.
"Daada mun gode, Mammy zata yi farin ciki da jin abin da ka faɗa. Daada Allah ya bika, ya baka abinda kake bukata na Alkhairi" matse ta yayi yana shafa bayan ta, cikin kaunar Uba da y'ar shi.
"Jeki kwanta"
Zare jikin ta, tayi ta fita cikin farin ciki.
Mikewa yayi ya nufi jikin wardrob din da aka tara littattafai na addini da na zamani, ya shafa jikin wall din a hankali motsawa wardrob din ya fara sannan ya koma ya zauna.
Yan kananu bow ne suka haska wani katon zanen hoton wata mace sanye cikin kayan makaranta, sai dai daidai fuskartar ta kamar an yaga hoton.
Lumshe idanun shi yayi yana kara hasko kyakyawar Fuskar ta daga zuciyar shi. Sautin dariyar ta, yana yawo lungu da sako na cikin ƙwaƙwalwar shi.
_Ya Mehd kayi min alƙawarin idan ka dawo daga turai sai bikin mu_
Ba zai manta ranar ba, sanye take da uniform na makaranta wanda aka zana hoton da shi.
*Zan miki alkawarin haka amma sai kin tsaya na dauke ki a hoto*
_Me zai hana_
Ta fada tana dariya, shine dalilin daukar hoton,
Har ta juya zata tafi ya ce mata.
*inna Isa*
juyawa tayi ta kalle shi.
Share kwalla yayi, yana kallon kasar hoton
Ba zai manta ranar da Meryam ta yaga hoton ba, sabida tsabar kishi irin nata.
Lokacin tana da cikin Junaid, ya rasa me ya manta ya dawo gidan, yana shigowa dake hoton a babban falon shi yake, yana shigowa yaga yadda take buga karfe a jikin hoton bai wani d'aga kai ya dubi inda take ba, haka ta fasa glass din hoton ta fara kokarin yaga hoton, daidai ya fito daga cikin part din shi. Rike hannun ta yayi tare da zuba mata lafiyayyen idanun shi ya zuba mata.
"Duk laifin da kika yi bai isa ba, sai kin kara raba ni da sauran abin da ya rage min daga gare ta?" Ya tambaye ta yana tsare ta da idanu haka yasa babu shiri ta sake daidai kan hoton da ta yaga ta fashe da kuka.
"Ya Mehd kayi hakuri, nasan nayi laifi amma kaso ni mana kamar yadda nake son ka"
Durkusawa yayi ya shiga kwashe kwalaben, yana jin kamar tana wasa mishi wuta. Kallon tsohon cikin jikinta wani irin bakin ciki ne ya rufe shi ya dauke kai ya tattara wurin ya mike zai koma dakin shi.
"Mehd Junaid!" Cak ya tsaya yana sauraron ta.
"Na san nayi maka laifi, kuma kullum cikin maka laifi nake. Sai dai ina son ka. Nasan Maryamu itace abin da kake so na amince duk ranar da ka ganta ka aure ta zan zauna da kai a haka."
"Shi kuma maganin da kike saka min a cikin abin sha fa?" Ya tambaye ta yana me juyawa suka fuskanci juna. Jikin ta ne ya kama rawa kamar wacce ya gaya mata wani mugun abu.
Zubewa tayi akan gwiwar ta.
"Ko baki san cewa nasan magani kike saka min nake tarayya dake ba? Meryam idan kika bar ni ba zan zuba miki ido ba, ai ni musulmi ne nasan daidai na san ba daidai ba. Nasan ko ban auri Inna Isa ba, haka Allah ya ƙaddara amma ya zaki ji idan aka wayi gari wani ya miki abin da kika mata? Wai na tambaye ki, kin san me ake kira soyayya? Kin san me ake kira sadaukarwa? Haka nayi ba dan ina so ba. Kun kashe ta sannan kuma kiyi tsammanin zan soki har karshen rayuwata? Ban ki dai na kaunaci Yaran da kika haifa min ba, domin su din jinin jikina ne ina son so sama da yadda nake son kome amma duk da haka basu samu soyayyar Inna Isa ba. Dan haka ki ka kuma ce min wani abu zan baki mamaki"
Tashi yayi ya bar ta a wurin, bai kuma sauraron ta,
Lumshe idanun shi yayi bayan dawowa daga duniyar tunani, ya dauki kofin Black tea din yayi sanyi ajiyewa yayi ya cire kayan shi ya nufi ban daki ya sakarwa kan shi ruwa.
Tsannanin soyayyar da yake gwadawa Nadia yasa Meryam take amfani da ita wurin ba shi hakuri. Tun bata kai haka ba, har tayi wayo wani lokaci da kanta take zuwa ta zauna a gaban shi tana mishi hira duk da bai yawan magana amma kuma son nadiah na musamman ne, domin sunan mahaifiyar shi ce.
*Daada ka yafewa Mammy*
Shafa kan ta yake a lokacin ya ce mata ya wuce. Yana gama jin saukar ruwan ya dauki karamin towel ya daura a kugun shi, dogo ne sosai, yana da murdewan jiki irin ta zaranta maza, mutum me yawan gargasa. Yanayin shi yanayin (Prince Saif Ali Khan) yanayin su daya.
Gyara zaman towel din yayi sannan ya nufi closet din shi ta ya Ciro wani cotton pajamas, fari tas irin open chest din nan. Da kan shi ya dauki kofin black tea din ya wuce kitchen. Ya mai da kan wuta. Sai da yayi zafi sannan ya bude wata yar karamar microwave ya ciro cookies, ya nufi waje. Falon shi ya nufa ya zauna sannan ya kunna tv yana shan tea din yana kallo.
Shi kan har yanzu mamaki yake taya Meryam take dauke da blood Cancer bata tab'a gaya masa, laifin shi ne ko nata? Shi dai yasan mutum ne me yawan tafiye-tafiyen kasuwanci. He's always busy, daga shi har Selim, basu zama yaushe ma haka ya faru? Lumshe idanun shi yayi, babu abin da ya bashi mmki kamar cewa da aka yi tana dauke da wani cikin.
Kallon hoton su yayi shi da Yaran shi. Su hudu babu ita a cikin su.
Bayi mantawa a lokacin sallah yayi hoton, shi da yaran shi.
Yana gama shan tea din ya mike ya kashe tv sannan ya nufi dakin shi, restchair ya hau ya fara jijjiga shi a hankali.
Yana nazarin when suka hadu da har ta dauki cikin shi tafiyar shi Beijing. A ranar da safe ba zai manta ba, bayan gama breakfast ta shigo dakin tana gyara mishi. Shi kuma ya fito ban daki. Dafe goshin sa yayi domin yasan a lokacin tabbas shi ya nime ta har take cewa.
"Daadan Nadia, please ka bari nan da sati me zuwa ka dawo, jiya nayi tsarki idan na dauki ciki yanzu zai kassara lafiya ta bani da lafiya" ware idanu shi yayi, ya mike tare da nufar dakin ta. Anan ya shiga bincike a cikin dakin a can ƙasar gadon ta ya samu kwalayen magani kaca-kaca, da takardun asibiti a cikin wani katon kwali. A hankali ya fara bincike anan ya samu abin da ya sa shi zaman durshan tare da dafe goshin sa.
Takardu ne na asibitoci daban daban, ashe shi yasa take daukar yaran zuwa yawo bude ido, dama ciwo ne da ita tun da jimawa. Kwashe kome yayi ya nufi dakin shi dasu ran shi yayi kazamin B'aci domin bai zaci haka ba, amma kuma shi ne mai laifin na watsar da ita kamar bai damu da ita ba. Ya manta tana da hakki akan shi. Ranar barci rabi da rabi yayi. Koda yayi sallah asuba, komawa yayi yana barci yaji motsin Yaran shi, sun zagaye shi domin su dai bakon yanayi ne a gare su ganin yana barci.
Tashi yayi zaune Nadia ta mika mishi brush, ta cigaba da gyara dakin. Ban dakin ya wuce ya samu ta gyara ban dakin tass kamar Uwarta. Yana wanke bakin ya fito.
"Daada! Mammy"
Juyawa yayi ya ɗan duka kadan ya goyi Junaid duk da yaron kato ne, sannan ya dauki Eman, suka fito falon. Ita kuma Nadiah ta cigaba aikin ta. Tana gamawa ta fito lokacin yana basu abin karyawa dukkan su, itama a gurguje ta ci, sannan ta nufi dakin su, ta saka kayan ta na makaranta. Ta fito da gudu, silifas ya saka ya nufi waje da su, da kan shi yake tuka su.
"Daada! Mammy"
"Kayi shiru Daadah ya ce an jima za a zo a kai mu wurin Mammy ko Tente?" Eman ta fada tana tambayar Nadiah.
"Eh" haka ya kai su makarantar, ya juya ya sumbaci goshin Junaid, sannan ya fito ya bude musu motar, Eman itama ya sumbaci goshinta, sannan ya janyo Nadiah.
"Uwata ki kula da kannen ki"
"Insha Allah" ta fada tana me daukar jakar su. Su kuma suka rike lunch box din su.
Sai da yaga shigar su makarantar sannan shima ya wuce gida, yana shiga harabar gidan ya samu Selim yana jiran.
"Barka da safiya "
"Barka "
"Akwai haduwan ka da yan kasuwan Najeriya har mutane uku"
"A soke zaman ina da mara lafiya" ya nufi cikin gidan, a can wanka yayi ya shirya cikin danyen shadda na kasar Australia ruwan makuba,.sannan ya fito kan shi sanye da jar dara, ya dauki wani farin mayafi ya buga rawani mugun kyau, akan hular.
Sannan ya fito dinning table ya zauna. Selim ya zuba mishi abincin. Kafin ya fara karyawa yana nazarin matsalar Meryam.
"Yallabi ya jikin Mammyn Nadia "
"Da sauki" ya fada bayan ya d'aga hannun shi a saman spoon din, sannan ya mike.
Ayyah ta mika mishi jakar shi da kome Selim ya amsa, suka fito har waje.
"Asibitin zamu"
"Hm" ya fada bayan Drive ya bude mishi motar,.ya zauna Selim ya gayawa drive inda zasu.
Fita suka yi daga gidan suka nufi asibitin. Anan suka samu ta tashi da kan ta. Har nurse sun mata wanka ta gyara jikin ta. Lokacin da ya shigo kallon shi tayi cikin farin ciki tana mutuwar son ganin shi cikin kayan kasar hausa musamman da ya kasance Mahaifiyar shi Bororoji ne, daga family wodubbe. Sai dai Mahaifinsa bazabarme ne, ya dauko farin fatar mahaifiyar shi ce. Amsar basket din abincin da Ayyah ta bawa Selim bayan ta bashi Jakar yallabai Mehd.
"Ya jikin ki Mammy?"
"Da sauki Salim ya aiki"
"Alhamdulillahi, Yallabai bari na tafi zuwa an jima zan kawo Yaran "
"Hm" ya fada yana bude basket din, ya fara zuba mata abincin. Ya zauna a bakin gadon ya fara bata. Hawaye ne ya zubo mata, wannan shine mafarkin da tayi zata samu idan ta ture me wurin, yau gashi nan tana girban abun da ta aikata da hannun su. Kyashi da hassada suka kaita tudun wahala. Ta rasa shi har abada. A hankali ta fashe da kuka, tana me kawar da kan ta.
"Kici " ya fada a tausasshe.
"Ka yafe min"
"Na yafe miki "
Ya fada yana bata abincin, tana amsa amma tana kuka.
Sai da ya ga ta koshi, sannan ya kalli agogon hannun shi.
"Sunce ina da cikin wata uku. Kuma idan ina son nayi nisan kwana dole sai an cire cikin idan kuma ina son cikin dole sai dai abin da Allah ya nufa!"
"Wanne kika zab'a?" Ta tsinkayi muryan shi, domin bata zata zai bata amsa ba.
"Na zaɓi cikin! Ina dauke da Yaron Mehd karo na hudu " ta fada hawaye na zuba mata.
Komawa yayi jikin window dakin ya tsaya.
Yayi shiru bai ce kome ba.
"Mehd ka yafe min, don Allah kar bayan raina ka wulakanta min Yarana. Don Allah ka saka idanu akan su. Nasan tunda ina son cikin ba zai dauke ni dogon lokaci ba!"
Haka ta gama maganarta amma bai ce mata cikanki ba.
Kusan minti talatin yana tsaye a wurin kafin taji tambayar da ya ruguza mata duk wani kwarin gwiwar ta.
"Tun Yaushe kike dauke da Blood Cancer?"
......
*TOP-NOTCH WRITERS*
*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*
_Kasancewar bikin kanwata ake ta biyar me suna Zahrah sai kaiwa da komawa nake Hankalina yana kan Babbar kawata Farisah tsaki nayi na wuce can na kuma dawowa na zuba mata ido cikin takaici mahaukaciya ta zare_
_Malama kin zo biki ne ko kin zo karanta chat kin yi shiru kin b'ata shiru_
_Wani banzan dariya ta saka min tana d'age min gira_
_Hmmm Bestie wai ke ko irin karance-karancen social media baki yi irin su Wattpad,Okada, Arewabooks baki yi?_
_Sake baki nayi ina kallon ta. When rabona da Hausa Novel Allah na tuba tun Iyatuh Abba tana karanta a gidan Radion B.R.C tabe baki nayi na ce mata_
_Ke rabani da kayan wahala rabona da Hausa novel tun zamanin Iyatuh Abba_
_Innalillahi!, Tace tana kallona kafin ta ce. Jasmin yanzun don Allah duk cigaban da aka samu baki san da shi ba? Lallai kin wuce yadda nake tunani kin gani wuri na karanta book din da nake fama da shi_
_Cikin mamaki na wuce na dawo na zauna kusa da ita nace mata don Allah daura ni a hanya ina ganin kowa na karance-karancen amma ban dani_
_hmmm lallai zata fashe... Toh saurara da kyau nan da kike gani na karanta books nake na marubuta daban daban amma idan ana dara ana fidda uwa... Kin ga last na ga The Governor's Wife, one to three, after ma gama na karanta Zaytoonah.... Abun dad'i sai na cikaro da Affiyah da Unaisah_
_Allah Aunty Rukayyah kina karanta online hausa novel ne? Lallai toh ai yanzu ina karanta Zayn Malik Jiya na gama karanta Zanen ƙaddarata,_
_Kanwata Amaryan da muke bikin ta ta saka mana baki a she ba banza yarinyar nan ta nace daga gama sakandare tace a direta gidan miji_
_Amarya Zahra toh kuwa nima Zayn Malik nake karantawa musamman rigimar Hajiya da Uncle Bashir, da Zayn da Abul amma kin san zata fashe on October?_
_Don Allah fa_
_Hmmmm gamayyar marubutan nan sun hade wuri guda za ta fashe sun fitar da sunan Team din su_
_Aunty Don Allah ya sunan Team din?_
_TOP-NOTCH.... Za ta fashe a books uku Sahla A Paris, Bani Da Laifi Abin da Ya baka Tsoro_
_Wow da gaske?_
_Zan Miki karya ne?_
_Ina da number Mai_Dambu bari na duba nasan zata daura a status...._
_juyawa tayi ta kalle ni ina bin su sa kallo ke kuma ko garzaya Wattpad ko duba Ribar Uwa, Mutum Mugu, Wadata, Uwargidan Bahaushe, Bororoji,Kallabi does story sun tab'a ni_
_Kut nace sannan na cigaba da cewa don Allah ga Iphone dina daura Wattpad ke kome ma daura min nima ta fashe dani_
_Tabbas za ta fashe amma fashewar alkhairi....._
_Books din da zasu zo kamar haka_
1- Sahla A Paris
2-Bani Da Laifi
3-Abin Da Ya baka tsoro.
Dukkan su Uku 1k
_Guda daya_ 350
_Guda Biyu_700
_Guda Uku_ 1k
_Zaku iya payment ta to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria_
_and send evidence to does number_
*****
Or
**** or ****
_Dukka zaku iya tura shaidar biya_
_Ga masu turo katin MTN zasu iya turawa Zahrahn Addah Ramlat da kuma Yan Nijar zasu turawa Nana A'ishah_
**** a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
*+22784506476*
_Welcome ta Top-notch Team_