Chapter 15
MAIDUGURI:
Safinat cikinta sai kukan yunwa yake, ta dubi abincin da ke gabanta ta kai loma ɗaya ta ji kamar za ta amayar, Ummanta na zaune tana sauraran Radiyo an sanya wakar Barmanu coge tana ta bibiya.
Safinat ta dubi mahaifiyarta ta ce, “Umma na fa gagara cin wannan abinci.”
Rage sautin Rediyon ta yi ta ce, “Lallai to me zai ki ci bayan shi babu komai a gidan, ki rufe ina ga zuwa an jima za ki iya ci, don wannan abinci da kike gani har rana shi za ki ci.”
Zazzaro ido ta yi ta ce, “ Umma!"
Ta nuna mata wata masara a buhu ta ce, “Ga can masara an tsurfo shi ki gyare ki kai nika a yi tuwo da daddare, akwai kuka da magi a kitchen sai a kaɗa ki ɗan yi tuwon har da na ɗumamen gobe, ni kuma bari na shiga na yi wanka na nufi ƙauye wurin boka tun da lafiya ta samu.”
Ta miƙe tana gyara ɗaurin kwalinta ta ce, “Sai ki hanzarta ki yi abubuwan da ke gabanki, don lokaci ba jiran ki zai yi ba.”
Safinat ba ta ba ta amsa ba, kawai ta rafka tagumi a zuciyarta ta ce, “Lallai fa yau fa a ke yinta, duk ni na jawo wa kaina.”
Ta ture abincin ta turo baki fuska a yamutse ta kwanta.
“Kwanciya ma kika yi ko. Ga ayyuka a gabanki ga shara ga kuma wanke-wanke ga aikin masara.”
Fuskarta a murtuke ta ce, “Umma duk zan yi idan kin tafi.”
“Wannan kuma ke kika sani.”
Ta yi gaba ta bar ta.
Cikin Feenah ne ke wani kurrr na yunwa, ta ce, “Cikina dole ka yi kurr tun da na zo na kasa cin abincin da zai kosar da ni, na saba cin mai ɗaɗi nan shiru kake ji. Allah dai ya kawo yaya cikin gaggawa a sulhunta.”
Su Umma Laure an shirya tsaf an fito, tana ƙoƙarin sa takalmarta ta ga Safinat na kwance kamar ruwa, “Kina nan dai a kwancen ko. Ko motsa wa ba ki yi ba.”
Ta sosa ƙeyarta, “Wuyan shi ki fita ne fa Umma kina fita zan motsa. Allah ya ba mu sa'a Allah ya sa a dace.”
“Sa'a da dace duk an samu ai tun da wurin bokan nan aikinsa kamar yankan wuka ne ya na yi buƙata ke biya.”
Rufaida na gidan tana jin duk tattaunawa da suke wasu daga cikin ta fahimta wasu ta gagara fahimta.
Ta sha gaban mahaifiyarta, "Don Allah Mama ki ba ni wasu mintuna mu tattauna."
"Ina sauraronki faɗi abin da za ki ce. Ni wallahi ban san me ya kawo ki a duku-dukun safiyar nan ba."
Ta share hawayen da ke ƙoƙarin gangarowa, "Ina ga alherin da ke tafe da ni ne gare ki Allah ya jeho da ni don na tsiratarku da ku daga halakar da kuke son afkawa ke da ƙanwata."
Safinat ta miƙe, "Umma, don Allah kar ki saurare ta za ta iya kashe miki guiwa da kalamanta ta rusa mana ƙudirinmu."
Dariya ta yi, "Ba ta isa ba, bar ta ta yi asarar yawun bakinta." Ta nuna kunnenta, "Kin ga idan ya shiga ta nan zai fita ta nan, ni da shaitan da rundunarsa suka yi mini fitsari aka wanne wa'azi ƙwaƙwalwata zai ɗauka. Ƙwaƙwalwata dai ta ɗauki innallaha gafururrahim. Shi Allah mai rahama ne mai jin ƙan bayinsa. Idan na cimma buri zan nemi gafararsa ina da tabbacin zai gafarta don shi ba irin mu ba ne bayi idan an saɓa mana ba ma yafiya, shi rahamarsa da jinƙansa sun yalwata ko'ina."
Ta yi shiru ta kalli 'yar ta, "Zantukana sun tsuma ki ko? A tunanininki mahaifiyarki jahila ce."
Tana kuka ta ce, "Tabbas Umma Allah gafururrahim ne amma kuma kin san kuma shadidul iƙab ne? Umma kina magana kamar kin san lokacin da za ki mutu, haka kina lissafi kamar kina sane da adadin rayuwarki, ba ki fa da tabbacin za ki ƙara second yanzu haka, amma kina lissafin shekaru Umma muddin mutum ya riƙi boka a matsayin mai biya masa buƙata, to tabbas rayuwarsa za ta ƙare a tsiya ce, domin ɓeran masallaci sai ya fi shi arziki. Ba zai taɓa tsinana ma kansa komai ba, duk abin da aka samu boka ne zai gaje, tun ba ka mutu ba ka samu magajinka Boka. Bayan haka asara babba shi ne ka rusa tauhidinka, duk wanda ba shi da tauhidi zai dauwama a wuta."
Safinat ta katse ta, "Muna salla muna azumi za ki ce ba mu da tauhidi."
Ta dubi Safinat, "Shika-shikan musulunci biyu kika lissafo ba ki ambato sauran ba, to ki sani muddin kina zuwa wurin boka kuma kina amfani da abin da ya ce kin rusa Shika-shikan musuluncinki gabaɗaya don Allah subhanahu wata'ala ya ce, la'in ashrakta la yahbaɗanna amaluka."
Ta kyalkyale da dariya, "Mama, wannan alarammiyar wasting time naki take fa."
Ta juya cikin fushi, "Safinat ni ba sa'arki ba ce ban son rai ni."
Umma Laure ta ce da Safinat ta shiga ciki, Safinat na tafiya take magana ƙasa-ƙasa, "Kin shiga gonata ta yaya ba zan tanka miki ba."
Rufaida ta ci gaba cewa, "Umma, ki sani Allah wanda ya yi ki, ya yi ni, ya yi bokan, shi ne madogara kuma wanda ya cancanci mu miƙa buƙatunmu wurinsa ba wurin katon banza mushiriki ba. Shi Allah za ki je masa da buƙatunki ya biya miki ba tare da kin kashe ko sisi ba. Boka kuwa ga asarar kuɗi ga dauwama a wutar jahannama idan ba ka tuba har ka mutu. Ya Allah ka raba mu da toshewar ƙwaƙwalwar da har zai kai mu wurin bokaye, kuma ki sani duk abin da za ku ƙulla bai isa aikinsa ya yi tasiri ba face da izinin Allah. Umma, Mus'ab na kokari wajen ba ki kayan abinci da ɗan abin kashewa, duk karshen wata, amma duk sai ki karkata ki sayar ki kai wa boka sai isa a kullum kike kukan babu wasu faƙirai mai sun fi ki rufin asiri. Ina addu'a Allah ya shirye ku da duk ma su bin bokaye zuwa tafarkin Allah."
Umma Laure ko gigau a tunatarwa da aka yi mata, ta ja dogon tsaki, ta buɗe randa ta sha ruwa ta yi gaba.
Rufaida jugum ta yi ta tsaya na tsawon minti ɗaya, cike da takaici ta sa takalmarta ta yi gaba.
TAKAI (Tsintar.)
Mama ta ce, “Haba ba za a yi haka ba, a dai sa rana amma ba mai yawa ba.”
Baffa ya ce, “Hajiya, a yi a gama kawai mu mun ba ku yarinya wasu lokutan ma jinkirta abu kan haifar da matsala a yi ta ƙare limami ya ɗaura ku ɗauki matarku.”
Yagwalgwalar ce ta ce, “Ku yi haƙuri, gaggawa aikin shaitan ne komai a yi shi da sannu.”
Ma'u hawaye ne suka fara sauka a fuskarta ta ce, “Iyayena me ya sa kuke zubar da ƙimarku da martabarku haka? Da ma haka kuka gaji da zamana a tare da ku?"
Baffa ne ya miƙe ya nuna Mama ya ce, “Hajiya idan har ba za ki damu ba ina so mu ƙeɓe.”
Ta miƙe tana biye da shi bayan sun samu waje sun tsaya ya ce, “Hajiya na san kina ganinmu kin san mu ba masu ƙarfi ba ne. To ki janye batunki na sa rana da yin biki, saboda ni ba ni da karfin da zan tara jama’a na ciyar da su, ba zan yi taro ba ki amince a ɗaura auren nan ku tafi da amaryarku asiri rufe.”
“Baba, idan don hidimar jama'a ce zan ɗauki nauyin.”
Ya ɗan ja gemunsa ya sunkuyar da kai, “Hajiya bayan wannan akwai wata matsalar fa.”
“Mene ne?”
Wayarta ce ta fara ringing da ta duba ta ga wanda ya ƙira ta ta miƙe, "Baba, yi haƙuri don Allah zan je na amsa waya."
Ta miƙe ta tafi can wani wuri daban ta bar shi a zaune dirshan.
UMMA LAURE A WURIN BOKA
Boka mai aiki da cika wa, gawurtaccen boka ne da ya shahara wajen saɓawa Allah, idan kai matsoraci ne ba za kaso ka yi ido biyu da shi ba saboda yadda kamanninsa ya juye tamkar ba na mutane ba, fasalta shi kai tsaye zai yi wahala sai dai wanda ya gan shi. Shi dai boka mai aiki da cika wa mutum ne, aljan ne, ba za ka iya rarrabewa ba.
Su Umma Laure an iso kauye wurin boka, cikin murya ta kuwwa ta ji an ce da ita,
“Dakata Hajiya!” Cak ta tsaya,
“Me ya sa ki kike ƙoƙarin taka mana ɗan autan aljaninmu. Da kin taka shi a yanzu sai na sa aljani ya tsotse mana jinin ki ko kuma na makantar da ganinki na kurmartar da jin ki na har abada.”
Cikin rawar jiki ta ce, “Allah ya ba wa boka haƙuri, ku kuke kallon mu ai mu ba mu kallonku. Tuba nake.”
Boka ya daka mata tsawa cikin ɗaga murya ya ce, "Ba a ambata mana sunan Allah a nan ki kiyaye ko kuma fushinmu ya tabbata a kanki."
Tamƙar za ta yi wa boka sujjada ta durƙusa jiki na kyarma ta ce, "Tuba nake abin ka da baki ya saba, amma zan kiyaye ba zan kuma ambata ba."
"Zauna a inda kike." Jiki na rawa ta zauna, ta zurawa boka idanu ta saki baki da hanci.
Wata 'yar ƙaramar ƙwarya da ke gaban shi ya ɗauka yana juya shi yana kyakkyacewa da dariya bayan ya yi shiru da ba zai wuce second biyar ba ya ce, “Mus’ab, Hafsy, Safinat." Sai ga su sun bayyana cikin kwarya ya nuna mata su ta dafe kirji. Ta zaro ido tare da cewa "Boka!
Ya ce, "Game da waɗannan kika zo ko ba haka ba?"
"Haka ne boka."
Ya nuna Hafsy, da ke cikin ƙwarya, "Ke ba ki son kishiya ko? To Safinatu sai ta shigo gidan da mijin da kike taƙama da shi, kuma ita ce abokiyar haihuwarsa. Sai na ƙasƙantar da ke kin zama tamkar mujiya a gidan mijinki kai da duk wani jininsa ma."
Umma Laure guntuwar dariya ta yi a zuciyarta ta ce, "Boka tun kafin na feɗe masa biri har wutsiya ya riga ya sani kuma har da manufofina."
TAKAI (Tsintar)
Baffan Ma'u ya ce, “Hajiya ba zan ɓoye miki ba yarinyar nan akwai wani da yake hure mata kunne don a kunnena na ji take ba shi labarin za a aurar da ita da su gudu, kin ga tun kafin hakan ya kai ga wakana gwamma a yi wa tufka hanci. To idan aka tsaya sa rana za ta gudu yaran yau ko na hana ta fita za ta shammace ni ta gudu.”
Ta ce,“Idan ko haka ne ai da matsala yarinya ta auri wanda ba ta so. Anya auren zai ƙarko."
"Hajiya ƙarƙo kai, ai tana ganin kanta cikin daula za ta manta komai wuyar ta a yi auren ne kawai."
Murmushi ta yi, "Wannan kuma ka faɗi gaskiya don naira babu abin da ba ta yi musamman wanda yake cikin ƙanngin talauci ya same shi cikin sauki take sauya shi. Shi kenan, ba damuwa a ɗaura auren na amince, kuma kar ku yi tunanin yi wa ɗiyarku kayan ɗaki, ɗakin da a ka tanadar mata babu abin da babu.”
Yana washe baki ya ce, “To muna godiya Hajiya. Kuma kin san yaron da ta makale wa shallali ne ga shaye-shaye daɗin da ɗawa babu sana'a takamaima sai zaman kashe wando, kin ga duk wani uba na gari ba zai bayar da ɗiyarsa ga irin sa ba. Da Allah ya kawo na gari sai isa na ce ba zan yi ƙasa a guiwa ba.”
"Wannan gaskiyarka, haka suke fa yaran yanzu sai dai Allah ya gyara, shi ma wannan ɗin ai hatsabibiyar mata ya samu sai da na tashi tsaye na farraƙa."
"Subhanallahi! Hajiya yanzu kam ɗan ki da yardar Allah ya samu mata."
"Ni ma na ga alamar hakan, yanzu abin da nake so da kai ka yi wa Ma'u magana ni ma zan yi wa Aliyu su fahimci juna.”
BOKA DA UMMA LAURE
Boka ya sheke da dariya ya buga ƙasa ya ce, “Kwantar da hankalinki Hajiya, Safinat za ta auri Mus'ab, ita ce ma nan abokiyar haihuwarsa domin ƙasa ya nuna mini yana da rabon haihuwa kuma da ɗiyarki, matarsa juya ce har ta mutu ba za ta haihu ba.”
Murmushi ta yi saboda ta ji daɗin kalamansa.
"Sai dai Hajiya ki sani aikinki babban aiki ne don Mus'ab ɗin da matarsa tsayayyu ne ba shagalallu ba, aiki a kansu sai an zage dantse idan ba bokan da ya amsa sunansa ba irin mu da wuya a yi nasara a kansu. Mutanen naki ba su zauna ba."
Ta ce, “Boka, kenan su ma suna shige-shege?"
Ya kyakyata dariya, "Kwarai kuwa na fitar hankali don kin ga makirar matarsa ɗin nan, lungu da sako na garuruwan Inyamurai da Yaruba ba inda ba ta sa kanta ba. Kai har su Nijer akwai masu zuwa mata a kawo mata saƙo har gida."
Ta taɓe baki, "Irin wannan mallaka na san dama ba ta zauna ba, to sai mun karya. Boka na yi mamakin yadda ka san abin da ke tafe da ni kafin na faɗa.”
“Hahhhha daina mamaki Hajiya, sanin wannan abu ba komai ba ne a wurin mu yanzu me kike so a yi miki a kan dukkaninsu?”
“Boka ina buƙatar a karkato mini da hankalin Mus'ab mu juya shi yadda muke so, sannan ya amince da auren 'ya ta, sannan a yi abin da duk cikin dangi su so abin da muke so, kar a samu mai suka, ita kuma matarsa muna so mu ƙuntata mata ta yi bakin jini a wurin mijinta kai dama kowa a dangi, boka ina so ta kasance a rayuwarta ta kasa fahimtar ina ne gabas ina kudu ta ƙasa banbance dare ko rana, amma fa ba wai ina nufin ka haukatata ba, akwai lokacin da zan buƙaci hakan ta kasance, amma a yanzu so nake ta shiga taskun rayuwa a gidan mijinta, idan muka gama ƙuntata mata ta jeme wannan kyawun da take ji da shi ya dishashe sai a yi mai gabaɗaya wato sai a yi mata kurciya fatan ka gamsu da bayanai na.”
Boka ya kuma shekewa da dariya ya ce, “Za a yi yadda kika ce. Saboda haka sai kin shirya.”
“Boka, a shirye nake zanyi duk abin da ka ce.”
Ya tura mata wata kwarya ya ce, “Duba cikin me kika gani?”
Tana lekawa ta ga MUS'AB da iyayensa da Hafsat ta ce, “Ai boka waɗannan sune mutanen da nake buƙata a yi aiki tukuru a kan su.”
Ya saki wata irin ƙara ya fara gurnani can kuma ya dinga huci kamar kumurcin maciji ya dubi Umma Laure, "Hajiya aikinki har ƙasar Sin aljanu za su je su yi za su taka inda nata bokayen aljanunsu ba su taka ba, kin ga kuwa aiki ne ba na wasa ba.”
Murmushi ta yi, "Wannan haka yake boka,ba damuwa duk buƙatun da ka zo da shi za mu yi shi. Ku yi nisan kwana ku daɗe kuna yi boka, mu ma mu ci gaba kawo buƙatu kuna biya mana.”
Ya kyakyata dariya yana girgiza kai ya fara kuwwa.
TAKAI (Tsintar):
Baffa na ƙarasowa ya dubi matarsa ya ce da ita, “Ki je ki yi wa Ma’u magana ta shirya za su zanta da mijinta.”
Mama, ita ma ta dubi Aliyu, “Aliyu kana ji na bayan sallar juma’a za a ɗaura maka aure da Ma’u la’asar na yi zamu ɗauki hanyar Kano gobe mu hau jirgi sai Maiduguri. Yanzu abin da nake so da kai ka ku je ku fahimci juna da amaryarka.”
Yagwalgwalar Turai ta ce, “Amma Hajiya……..”
Ba ta ƙarasa abin da za ta ce ba Mama ta dakatar da ita da cewa, “Ki yi haƙuri Adda na san abin da kuke son faɗa ki adana su mu zanta su idan mun koma gidanki.”
Ta juya ta kalli Saif ta ce, “Ka same ni zan aike ka.”
Ta juya ta yi gaba Saif ya miƙe domin ya bi ta.
Miƙa masa ATM card nata ta yi ta ce, “Na san a wannan ƙauyen da wuya a samu POS but idan ka je Takai za ka iya samu ka cire mini 200k pin number na 1,2,3,4 ne.”
Ya karɓa ya amsa da to Mama ya fice.
Tana shiga ɗakin ta fara ƙwalla kira tana cewa, “Ma’u! Ma'u! Ma'u!” Tana ji ta yi shiru ba ta amsa ba, da ta ƙaraso ta ce, “Kina ji na kika yi shiru ko.”
Kugu ta riƙe tana faɗin, "Wane kalar sabon rashin mutunci ne zan gani haka Ma'u? Wato kina ciki kina ji na ina kwala miki tamkar maroƙiya amma kika yi burus da ni ko, rainin naki yanzu ya kai maƙura."
Ma'u ta tsuke fuska ta ce, "Irin wannan ƙwala mini ƙira da kike ai sai dodon kunne ya samu matsala.”
“Sai ki duke ni idan kin isa, saƙo daga Baffanki ki shirya za ku gana da Aliyu.”
Tana gama faɗa ta juya, ita kuma ta ja dogon tsaki tana cewa, “Wanne shiri zan yi, ado da kwalliya ai ma Ahmadi kaɗai a ke yi ma. Kai ba ka taka matsayin da daidai da jagira nasa dominka ba.”
Tana koma wa ta ce da Maigidanta, “Na faɗa mata, idan ya shirya sai a yi masa jagora.”
Aliyu tun da ya ji kalaman da mahaifiyarsa ta furta ya fita hayyacinsa.
Cikin tsawa ta ce da shi, “Aliyu ya ban ga alamar kana motsa wa ba.”
Runtsa idanuwansa ya yi ya ɗago wanda a take sun sauya sun yi ja ya ce, “Mama, ba sai na gan ta ba, tun da ta amince kuma kun amince hakan ya wadatar.”
Mutanen da ke zaune a wajen suka fara kallon juna wasu na taɓe baƙi.
Mama zumbur ta miƙe kana ganin fuskarta kasan ran maza ya ɓaci ta dunkaro Aliyu cikin ɓacin rai ta sauke masa tagwayen mari a kuncinsa wanda sai da Aliyu ya gigice.
Fuskarta ta tsuke ta kalle shi a tsiya ce, “Aliyu wuyanka ya isa yanka, ni za ka watsa wa ƙasa a bainar jama’a ka je ka yi duk abin da za ka yi, amma ka sani ba ni ba kai.”
Yatsun hannunta ta ɗaga ta kaɗa suka ba da sautin ɗas ɗas ta ciji laɓɓanta ta nuna Aliyu da yatsarta ta manuniya ta girgiza kai, jama'ar da ke wurin na ta ba ta haƙuri ba ta saurare su ba ta fice ta bar gidan.