SAHLA a Paris

Trailer II

by @azizat

TOP-NOTCH!!

SAHLA a Paris

From the writer of Matar Gwamna.

Trailer!!

***

"Allah kawo ruwa mu koma rafi, bama tsoron Likita bare Ɗansanda"

"Allah kawo ruwa mu koma rafi, bama tsoron Likita bare Ɗansanda"

Na yi nisa sosai cikin waƙar da nake yi kawai na ji gyaran murya daga ta bayana. Na ɗan waiwayo da sauri dan Mr Dodo baya son a ɓata masa lokaci.

"Barka da safiya Uncle F..." na faɗa ina saurin riƙe bakina kar na kirashi da sunan da baya so.

"Zan yi tafiya, kwana uku zan yi. Stay out of trouble"

Bai bari na bashi amsa bama ya fice daga kitchen ɗin. Na bi bayanshi da gwalo. Mutum kullum sai dai shi yayi magana ka saurareshi amma kai ba zai saurari maganar ka ba.

Ta Allah ba tashi ba, ba inda zan je Wallahi ina nan daram a wannan gidan sai dai ya mutu da baƙin ciki, Dodo kawai mtsw.

***

Yau ma dai kamar kullum zan kai Karnuka yawon shaƙatawa. Sai da na haɗa kan karnukan na nufi gidan Mrs Julie saboda karenta ne na ƙarshe da zan ɗauko. Kamar kullum na danna doorbell ɗinta na ɗan jira kaɗan, sakan biyar sai gashi an buɗe ƙofa. Titiɓiri na ganina ya fara haushi. Na sa hannu na shafa kansa. Mrs Julie ta yi murmushi tana gaishe ni

"Bonjour Seela"

Nima na ce "Bonjour Mrs Julie". Ni dai an sa min suna Sahla kuma ma'anarsa sauƙi ne amma babu wani sauƙi a tattare da lamarin rayuwata balle kuma har yau ɗaiɗaikun mutane ne kawai suka iya kiran sunan da kyau. Ko yaushe SAHLA ya koma Seela oho. Mtsw.

Na karɓi igiyar karen daga hannunta na wuce kamar yadda na saba.

Ina cikin tafiya da su na ji cikina ya fara ƙurururururu. To kodai gwaten da na sha da safe ne. Ni dama ban yarda da gyaɗan Bature ba abu duk chemical a ciki. Kai inaga lawashin dana yanka a cikima ba ta da kyau. Komai dai a turai da banbanci tsakaninsa da na chan gida.

Da ke ban yi nisa da gidanmu ba na tarkaɗa karnuka na wuce da su gida. Mr Dodo baya nan Amir da Faisal ma suna makaranta. Na bar karnukan a ta baya na shige gida da gudu na faɗa toilet na zauna sai ɓurururururu kake ji.

Ina ta kaina ina nabi ta wasu karnuka. Hegu da na fito ashe sun shigo gidan sun wuce kitchen. Allah ya fishsheni ma komai a rufe yake da yau na shiga uku a wajen Mr Dodo.

Ko yunwa su ke ji oho ni dai na ciro sauran gwaten acca daga microwave na zuba musu a wani roba suka fara ci har da ture-ture. Ikon Allah! Duk gatan da ake wa karnukan nan shine suke wasoso akan gwate?

....

In taƙaice muku labari gani nan a gaban 'yan sanda ina bada bayani amma sun kasa ganewa. Yanzu dai an tafi kiran wanda zai zo ya fassara musu bayanina da faransanci.

Ina ji ana faɗin za a kira F K Ubandoma hanjina suka kaɗa. Dama a bayan idonsa na ke wannan aikin gashi yanzu zai sani.

Na san ba zamu wanye da kyau ba idan ya zo. Babbar matsalar ma shine kar ya maida ni Nigeria.

To wai miye laifina ne a nan. Abinci fa kawai na bawa karnukan nan suka ɓarke da gudawa amma yadda turawan nan ke kururuta lamarin nan sai kace na yi kisan kai. Kai ku tsaya. Cikina yana ƙurururu. Ta ya zan ce ina jin gudawa da faransanci? Ban sani ba amma dai na ɗaga hannuna sama ƙila za su gane.

***

Tsokaci kenan daga labarin SAHLA a Paris. Ko za a bar Sahla ta je banɗaki a police station ko kuma dai abin kunya za ta yi a wajen.

Anya za a bar Sahla ta wanye lafiya bayan ta sakawa karnuka har guda biyar guba a abinci kamar yadda Mrs Julie da sauran masu karnukan ke iƙirari.

Shin ma minene alaƙar Sahla da Mr Dodo? Wacece ma SAHLA miye labarinta.

Kar ku manta a tare dani a Top-Notch akwai Sister na Shatuu marubuciyar Zuma, Unaisa, Afiyya. Na san kun nishaɗantu da ƙayatattun labaranta. To yanzu ta shirya tsaf dan ta zo muku da BANI DA LAIFI.

Ga Antyna ta kaina Ramlat- MaiDambu, jarumar marubuciya da ta jima kuma ta goge wajen kawo muku ƙayatattun labarai. Na san baku manta da Masarautar Jordan ba, Bahaushiya fa?, kun tuna Ruwa biyu?, na san baku jima da karanta ƙayataccen labarin nan na Zayn Malik ba. To Albishirinku. littafinta ABIN DA YA BAKA TSORO na nan tafe.

Da naira N1000 zaka mallaki dukka ukun, da N750 zaka mallaki biyu, daya Kuma N350. Zai zo muku 1st October, 2022 inshallah

Make payment through 3091721807 A'isha kwalam Hassan, First Bank of Nigeria. Send evidence to either *** or *** or ***!