ABIN DA YA BAKA TSORO

1️⃣1️⃣

by @maidambu41

1️⃣1️⃣

*TOP-NOTCH*

Lallausar Murmushi ya sake musu, yana me durkusawa ya bude musu hannu, da gudu suka nufe shi. Duk shi mutum ne ba mazaunin gida ba, amma yana mugun bawa Iyalin shi lokacin sa, matukar yana gari toh makaranta shi yake kai su, kome shi yake musu domin yana girmama ahalin shi.


A shekara kuwa yana kwashe su ne, su tafi Umrah shi dasu. Sai abu daya da yake nakasa duk wannan gatan yaran rayuwar su ta Turai ce babu ilimin addinin musulunci ko daya, wai a haka idan yana gari ne zai zauna yana tambayar su me suka iya me suka karanta.


Hajiya Mama wato Mahaifiyar shi taso kwarai yaran su dawo Nijar da zama baki daya har uwar su, domin ta fahimci jikokin ta babu wani ilimin addini a tare da su, sai a hankali ta fahimci akwai rata me yawa a tsakanin D'anta da Surukarta, koda ta fuskar rayuwa da dabi'u. Tasan rabo da ƙaddara ya kashe Inna Isa, amma da a ce ita ce take tare da Maina ba makawa da Yaran shi zasu taso kamar yadda shi yake mafarkin. Wannan yasa baki daya ta takura lallai yana kawo su gida duk karshen shekara domin su koyi addinin su da Al'adar su ta asali.

Ita kan Meryam mahaifayar su Nadiah mace ce me ra'ayin rayuwa wato (social life) wayayya ce na bala'i. Kuma sai aka yi dace mijin da take aure ba mazaunin nijar bane, duk da rabin rayuwar shi a France suka yi sakamakon mahaifin shi ya rike matsayin Ambassador.

Wato marigayi Alhaji Junaid. Yasa baki daya rayuwar su a Faransa Faransa suka yi shi.

Wannan yanayin ya haifar mishi da son rayuwar turai ga shi dan kasuwa, ita kuma Meryam tayi amfani da haka wurin nunawa dangin ta da mutanen da suke fadar cewa taci amanar Aminci da kauna, take rayuwar ta. Duk da a haka kallon wacce tayi sa'ar rayuwa ake mata, amma da zasu bincika shafin rayuwarta sai sun zubda kwallar tausayi da bakin ciki.


Sumbatar goshin Eman yayi ya sumbaci kuncin Junaid, sannan ya zubawa hasken rayuwar shi idanu. Kaunar Nadiah wani abu ne me girma, yarinya ce da take taya shi kuka a duk lokacin da ya kebe shi dayan shi, zata zo ta zauna kusa da shi tana bashi labarin da Mahaifiyar ta, ta bata akan Innah Isa. Haka yasa yake kaunar yarinyar domin tasha cewa.

"Daada! Ina jin ciwon ka ina jin tausayin ka kai da Mammy. Daada ka daina zama kana shiru kaji Allah yana sane da masu hakuri kuma ladar su daban ne ita kuma Inna Isa Allah ya gafarta mata"

Mika mata hannu yayi, duk tayi zuru-zuru, da sassafar ta isa gare shi.

"Daada!" Ta kira sunan shi tana sauke ajiyar zuciya.

Tausayi ta bashi, ya riko hannunta suka nufi cikin asibitin, sai kallon cikin asibitin Junaid yake yana gyara zaman Medical glass din shi, kamar yadda Mahaifinsa yake sanye da na shi.

"Daada! Kaga Baby" Eman ta fada daidai wata Baturiya ta turo babyn a keken jarirai.

"Baby girl ne, ni bana son Baby girl Daada Baby Boy nake so kaji" Junaid ya fada yana bangaje Eman.

Murmusa musu yayi yana girmama rigimar Junaid da Eman, har suka isa dakin Maman su rigimar.

"Mammy!!!" Suka fada da ƙarfi, iya haka ma wallahi ta gode domin ta ajiyewa Mehd abin da ba zai manta da ita.

Bude musu hannu tayi, suka nufe ta. Nadiah ce ta koma bayan tana me fashewa da kuka. Cikin tsananin tsoro da tashin hankali take kallon Maman su da tayi wani irin duhu.

"Fadimatu!" D'ago kai tayi a durkushe. Ya bude mata hannu, da sauri ta mike ta fada jikin shi tana kuka.

Ita kanta kallon Nadiah take cikin tausayi da soyayyar, ita ɗaya tasan meye a tsakanin su. Ita daya tasan fushin da Mehd yake da ita.

Eman da Junaid kuwa tunda suka haura gadon suke bata labarin kewar ta da suka yi, jin su take amma Hankalinta baki daya yana ga Nadiah da Uban ke rarrashinta,sannan ya janye ta a jikin shi ya ce mata.

"Kije wurinta"

★★

Birnin Bayero.

Tun rasuwar Malam baki daya rayuwar ta sauya musu, walwala da hiran da suke ana farin ciki ya ragu, dan haka daga daki sai tsakar gidan anan rayuwar ta juya musu baya, idan kaga Meriama zaka iya rantsewa ta shekara tana jinya ne, domin tun kwana bakwai mutane suka watse. Sai Baaba Jumalo da tazo daga Maradi, ita ce a tare da Baaba me kosai.


Wata biyu da rasuwar Malam, Alhaji Hamza Mansa shima da iyalin shi suka bar ƙasar Nijar zuwa kasar su ta haihuwa Mali, wanda sanadin haka karatun meriama ya tsaya cak, babu yadda ta iya dole tasa Rabe da Baaba me kosai suka tattara yar abin da yake hannun su, suka nima mata wata makarantar gwamnati, inda zata karasa aji ukun ta. Makatantar tana dan gaba da su. Ita kuma Baaba Jumalo da Rabe suka koma kasuwa sayar da kosai da kunun da waina. Alhamdulillah babu laifi akwai nasara da cigaba, bayan hutu su meriama ya kare ta fara zuwa makarantar, dake ta samu kyakkyawar ilimi daga tushe sai gashi babu wani abin da yake bata tsoro. Karatun kuwa sai gashi yazo mata da sauki.

Sai dai duk kokarin tan nan, sai da aka samu wanda ya bada labarin ta, ai Uwarta mahaukaciya ce. Bata shiga harkan kowa karatu take, sai gashi watanta biyu da fara karatun ta fara gajiya da iskancin yan ajin su.

Yau ta kama Talata, idanun ta cike da kwalla take shirin ta. Kafin ta saka farin hijab din ta da jakar makarantar.

Ta fito tsaya tana kallon Mamma da take ta wasa da kunu,.kaunar Mahaifiyar ta take bata tab'a jin wani abu ya ragu a ranta akan Mahaifiyar ta ba.

Dan durkusawa tayi a gaban ta, kafin ta ce mata.

"Mamma!" Shiru tayi tana kallon yadda mahaifiyar take kallon ta.

"Mamma don Allah yaushe zaki warke?" Hawaye ya zubo mata.

"Mamma ki samu lafiya kin ji, kullum tsokanata suke wai yar Mahaukaciya"

"Meroh wannan wani irin hauka ne zaki saka baiwar Allah a gaba da shirme?"

Mikewa tayi tana share kwalla da yake bin fuskar ta, tana fitowa Baaba me kosai ta mata fada sannan ta bata kudin tara, ta fita baki daya tana jin wani irin damuwa ne, da tsoron shi cikin al'umma, gani take kamar kowani lokaci zasu iya cutar da ita.


A hanya ta hadu da wasu yan ajin su, suna ganin ta daya tace.

"Ke ga yar Mahaukaciya!" Juyawa suka yi suna mata dariya, ita kan kanta a sunkuye yake har suka isa makarantar yara sai tsokanarta suke, ji take kamar ta koma gida, amma babu yadda ta iya ta nufi ajin su, a cikin kofar ajin aka rubuta.

*Yar Mahaukaciya*

Bata iya wani abu ba, ta shiga mazan ajin suka kwashe da dariya.

"Faisal kasan kuwa mahaukaciyar nan uwar wata yarinya a a kasuwa aka samu wanda ya danne ta aka haifi wancan kyakyawar budurwa" aikuwa aka kuma kwashewa da dariya.

"Kace ko yau zan iya zuwa na danne uwar wata"

"Haba Jazuli, na zata zaka danne uwar ka danne yar ne, abin zai bada citta"

Duk ajin aka kwashe da dariya.

"Kasan ance Mahaukaciya akwai dad'i a jikin su, dan haka zan fara gwada Uwar ne idan ta min dadi na bar yar idan kuma uwar kofar...."

"Tasss" ta wanke shi da mari, sai da ajin ya dauki wani irin kara.

"Idan kai baka san darajar Uwa ba, ni nasan darajar tawa, Alhamdulillahi ni shegiya ce, sai aka yi Yayya? Uwata kome tayi ta samar dani ina mika mata godiyar daukar nauyina da tayi, duk da haukarta bata daura ni akan turban zama gurbatacciya cikin al'umma ba, idan ku kun rasa tarbiyya ni ban rasa tawa, karatun da makarantar Alhamdulillahi, tunda ina da haddar Alqur'ani ya ishe ni, ku kwadanta bokon ku cinye, ba sai kun bada labari ba ni na baku labarin jahilai"


Daga haka ta gyara zaman jakarta, ta bar ajin baki daya tayi alkawarin ko bata yi boko ba, zata rayu. Ta bar boko domin matsalar ta dana Mahaifiyar ta yana kokarin hanata farin cikin rayuwa.


Tana fita kuwa ajin ya dauki wani irin shiru.

"Jazuli kyale ta kayi?"

Shafa fuskar shi yayi. Tare da da fita fuuu ya bita bayan ta, tana fita wajen makarantar, shi da abokan shi su hudu suka bi bayan ta. Ba tare da wata wata ba, suka rufeta da mugun duka kamar sun samu jaka, dakyar masu wucewa suka kwace ta.

Tsabar ta daku, kasa tashi tayi abin da yasa aka kira malaman makarantar aka wuce da ita asibiti.

Su kuma yaran aka Kore su ranar su kira iyayen su.


Tunda aka kaita asibiti take aman jini, sabida dukar cikin ta da suka yi, wanda ya hadu da damuwa da rashin walwala. Daga makatantar aka tura malamai suka je har gidan su, aka gayawa Baaba me kosai, tashin hankali da ba a saka mishi tana sun gan shi. A rikice ta nufi kasuwa inda Rabe yake ta gaya mishi, Mudansiru da Ghali suka tafi asibitin, ganin mawuyacin halin da take ciki.


Ai basu yi kasa a gwiwa ba, suka nufi makarantar, anan suka tadda hankali domin kuwa sun sako hukuma cikin al'amarin, tashin hankali babu dad'i. Iyayen yaran suna zaune aka yi ta musu sallama.

Domin da farko shi Yaron Jazuli ya xata Meriama bata da galihu ne, yasa yayi mata dukar haka, amma ganin yadda al'amarin ya zafaffa hatta shugaban kasuwa da sauran al'ummar kasuwan sun tsaya sai an mata adalci yasa tsoro ya kama su, ashe ita din yar gata ne.

Haka aka yi ta tuka rigima dakyar aka sassanta tsakanin bangare biyu, a cikin sati daya, taji sauki dan ta samu kulawa, sai dai baki daya ta tsani boko da masu yin ta, burin ta na zama ma'aikaciyar jinya ya raunana, gashi ta saka damuwa sosai a ranta. Koda aka sallomata. Suka dawo Baaba da Baaba Jumalo suka ce karatun bokon ya isa ta maida hankali ta kara yawan karatunta na islamiyya shekara me zuwa tayi saukar ta.


Wannan dalilin da yasa baki daya ta ajiye bokon, zaman gidan babu dad'i haka yasa ta fara bin su Baaba Jumalo kasuwa, Alhamdulillahi zaa ce ta wannan fuskar, domin zuwan ya zame mata alkhairi da su baki daya, sai gashi da a filin kasuwa suke saka yar lema suna soyar su, zuwan Meriama yasa Chairman din kasuwa ya basu rumfa.


Allah da ikon shi rayuwar ta mike cikin Amincin Allah da buwayar shi, sai ga shi kowa son Meriama yake, dake bata da rawan kai, ga nutsuwa da kamala. Sannan tana da wani irin yanayi da ba kowa yake iya mata magana ba, domin Allah ya saka mata kamun kai da nutsuwa. Haka kuma dabi'a ce ta nagartattun mutane, dan haka yasa ake mata kallon wata irin mace me daraja.


★★

WATA RAYUWA


Matasa ne a wani gidan gona da aka kawata shi na musamman, kid'a ke tashi kamar zasu ɓalle gidan gonar kasancewar yayi wajen gari.


Yan mata biyu ne a gefen shi, sanye da wasu shaidanun kaya, ban da rawan Iskanci babu abinda ake. Kwance daya cikin Yan matan take a jikin shi.

Fari ne kyakyawar gaske, domin idan ka duba yanayin sho zaka fahimci ruwa biyu ne gauraye a jikin shi.

Zukar shisha yake, idanun shi lumshe cikin black puma glass, daga shi sai gajeren wando iya gwiwar shi,

"FAM"

Ta kira sunan shi hannun ta tana shafa kirjin shi.

"Muje ciki mana"

"Ko?"

"Dalla can Yusriyah kin cika son kai last party da aka yi dake aka fara wannan kuma ai sai ki bari ayi da ni "

Ta fada tana kai hannun ta saman wandon shi.


"Guys!" Ya d'aga musu hannu kashe kidar aka yi.

Daya daga cikin matasan da suke wurin ya ce.

"Yau zamu cigaba da gasar mu dan haka yau da Zaheen zamu fara kin shirya?"

Fu'ad Ahmed Marwan, shine tare da abokan shi masu shaidancin bala'i. Hamraz Turad, sai Anwar Kabir, sai Amaan Nuhu, yara ne ya'yan attajirai masu gata da galihu.


Kallon shi Yusriyah tayi tana tura baki ta ce.

"Kar ka manta FAM da Condom din ka"

Murmushi yayi yana nuna mata can table din kwalin Condom ne aka ajiye. Murmushi Zaheen tayi tana jin a ranta itama zata samu damar zama Babban Yarinyar.

A hankali ya juya yana kallon Zaheen yana janyo fuskar ta yana matsa boons din ta.

"Ku bata ruwan korama" a kofi aka kawo mata juice ta sha, sannan Hamraz Turad ya zo da allura ya tsikara mata, kafin ya finciko ta, ya cillata cikin ruwan swimming pool da yake wurin ta fashe da dariya. A hankali ya janyo Yusriyah ya rungume ta.

"Ba zan jima ba Yan mata yau kawai shagali ni dake"

"Ina jiranka" ta fada a shagwab'e, domin Allah yana ganin tana masifar kishin Fu'ad. Cire rigar shi yayi sannan ya fada cikin ruwan inda Zaheen take wanka. Suka shiga wasan ruwa shi da ita, tare da wasan banza irin na shu'uman Yara. Sai da ya ga ta haura yadda yake so sannan ya juya a hankali ya janyo ta, tare da ɗaukar ta ya fito waje da ita.

"Kin shirya?"

"Ina tare da kai"

Haka sauran maza ukun da Yusriyah suka rufa akan ta. Yadda kuka san blue Film haka abin suke yin shi...

Sex Game kenan.....


_Books din da zasu zo kamar haka_

1- Sahla A Paris

2-Bani Da Laifi

3-Abin Da Ya baka tsoro.

Dukkan su Uku 1k

_Guda daya_ 350₦

_Guda Biyu_700₦

_Guda Uku_ 1k


_Zaku iya payment ta to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria_


_and send evidence to does number_

*****

Or

**** or ****

_Dukka zaku iya tura shaidar biya_


_Ga masu turo katin MTN zasu iya turawa Zahrahn Addah Ramlat da kuma Yan Nijar zasu turawa Nana A'ishah_


**** a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah

*+22784506476*


_Welcome ta Top-notch Team_