124-125
by @nuceeyluv
® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
124_125
"Imaan tace oh ya omar dan Allah kaje side naka, omar yace meyasa? Imaan tace ni..ni..uhum.. Omar yyi murmushi ke me? Uhum ya omar nidai dan Allah aa kunya nakeji, haba tuni omar ya fara dariya yace kunya? Tabb gsky duk yanda za'ayi saidai ayi yau mummy ta bani matata naje na cire mata wannan kunyar kada na cutu, imaan ta saki baki tana kallon omar wai dama yana mgn haka? Omar yadan shafo fuskar ta yace toh sarkin kunya je kiyi wankan ni, nima zuwa zanyi nayi nawa. Imaan ta saki murmushi tace yauwa yanzu naji zance, omar ya girgiza kai yana murmushi yace kedai je kiyi muyi breakfast imaan ta mike tace toh. Tana shigewa toilet shima ya tashi yabar dakin.
"Tunda imaan ta shirya take zaune bakin gado takasa fitowa sbd kunyar mummy da takeji, omar kuwa yana gama shirinsa ya dawo falo ganin bega imaan a wajen b ya wuce dakin ta, anan ya sameta kan gado tana zaune, omar shima zaman yyi yace lpy baki fito ba? Imaan tayi murmushi tace Allah ya omar kunyar mummy nakeji, omar yace kinga tashi ni yunwa nakeji, imaan tace eyya mana ya omar kaje kaci abincin mana, omar yace aa ai tare zamuci, imaan tadan marairaice tace nikam ba yanxu ba. "Omar yace Allah idan baki tashi ba zan dauke ki, imaan najin haka ta tashi d sauri dan taga alamar ya omar dgske yake. "Lkcin da suka isa dining area imaan ce ta zuba masu chips kowa da plate dinsa, omar yana zaune yana kallon ta sannan ta hado masu tea me kauri bayan ta gama ta turawa Omar nasa a gaban sa itama taja kujera dan ta zauna. "Omar yace wannan kuma na waye ya nuna Mata plate din gaban sa. "Imaan ta kalleshi da mamaki tace naka ne mana, omar yyi murmushi yace lallema bbyn nan toh tare zamuci imaan tace haba ya omar gidan mummy ne fah, omar ya daga kafada alamar be damu ba, kujerar da yake kai y matsa kusa da imaan sannan yasa hannu ya fara ci, imaan ganin babu sarki sai Allah itama ta ware tanaci sosai har sauri2 take dan kar mummy ta fito ta gansu a haka, omar ya kalleta duk yana hankalce da ita yace Allah gwara ma kici abincin ki a hankali kinsan dai mummy bawai sa ido zata mana ba. "Imaan dai tayi shiru bayan ta gama cin abincin ta mike ta koma kan kujera, omar shima tashi yyi shima, daidai zai zauna kan kujera kenan mummy ta fito tare d daddy yyi shirin fita. Da sauri imaan ta sadda kanta kasa ta shiga gaishe su a kunyace, omar shima har kasa kamar kullum ya durkusa ya gaishe su, bayan su mummy sun zauna, daddy yyi gyaran murya yace omar, omar yace na'am daddy yace naji duk abinda ke faruwa kai da Matar ka, inaso na kara Jan hankalin ka akan ka rike amana sannan shi dan Adam daraja gareshi duk a halin da mutum ya ke kada ya wulakanta na kasa dashi domin ance 'ya'ya da dukiya Allah ke bayar wa kuma a duk halin daya so, nasan inada kaso 60 cikin 100 a wannan halin naku na Rena marasa shi da kyamar su, Amman cikin ikon Allah da Allah y bani mata ta gari sai gashi a hankali na fahimci manufar ta na nunamin cewa talaka da me kudi Allah ke halittar su, shiyasa ko wanne namiji akeson idan zaiyi aure ya samu mace ta gari wala Allah koda mijin halinsa baida kyau wata rana saika ga Allah ya shirye shi ya gyara halinsa hakanan yaran da zasu Haifa ma. So omar ga dai imaan nan inada tabbacin 100% duk abinda ake nema a mace ta gari za'a samu a wajen ta, bazan gushe da nanata maka cewar ka rike amana ba domin shi aure kulawar namji kan Matar sa shine ginshikin samun farincikin duka family'n gidan, Dan haka ke imaan ki shirya kayan ki kibi mijin ki yau Allah yyi maku Albarka. Ameeeeen gaba1 suka amsa. Omar yace na gode daddy na gode mummy Allah yaja kwana Abinda kuke mana Allah ya saka maku da gidan Aljanna. Nan ma sukace ameen. "Anan daddy ya mike yabar gidan, mummy ma sanda ta sake ja masu kunne sosai sannan tace zuwa dare omar yazo ya tafi d imaan. Omar sosai yyi farinciki sannan ya shiga zuba mata godiya,ita dai imaan kanta a kasa haka nan kuma ta fara jin kunyar mummy, mummy kam data lura da hakan tayi murmushi sannan ta mike tabar masu falon. Ai kuwa omar kamar jira yake d sauri ya jawo imaan jikinsa ya matse ta tsam yana me cike da farinciki, sai da kyar da kyar omar ya iya barin gidan danma sai damunsa da kira ake ana bukatar sa a hospital din.
Nuceey luv😘