138-139
by @nuceeyluv
® *OMAR KO FAROOQ* ❓
138_139
Sai karfe 4:15 omar ya dawo gidan, tunda yyi horn, imaan dake falo ta mike da sauri dan tasan jaan dinta ne ya dawo, fitowa tayi ta bude kofar falon, can ta hango shi yana kokarin daidaita parking motar sa, imaan ta fara taku cikin wani irin salo fuskar ta dauke da wani irin murmushi dake qara mata kyau sosai, "omar bayan ya gama parking sannan ya rufe motar bayan ya dauko jakar sa da wata bakar Leda daya taho d ita. "Hango imaan na tahowa yasa shi tsayawa ya zuba mata ido yana kallon ta, sosai ta tafi da dukkannin imanin sa, kallon ta yake sosai yanda tayi kyau cikin Riga da skirt na atamfar da ta saka dinkin ya kama ta sosai ga na fulanin ta sai wlcm suke masa, daurin da tayi kuwa shi ake kira ya kalli gabas maso yamma dan sosai ya dace da ita,...ko kadan besan lkcn data iso ba, haka imaan tana murmushi ta kalleshi na seconds sannan ta hura masa iska a ido, take omar ya fara murmushi sannan ya ware hannun sa da nufin tazo gareshi, ba musu kuwa ta fada kan faffadan kirjin sa tana murmushi tace wlcm back my jaan. "Omar shima murmushin yyi, yyinda yake shinshina kamshin turaren dake jikin ta me fisgar da hankalin sa, yace tnx u bbynah ya gida, imaan tayi kokarin raba jikin ta da nashi, sannan tace alhmdllh, daga nan ta dauki jakar laptop dinsa, sannan ta riko hannun sa, shi kuma omar ya dauko bakar ledar, ahaka suna tmbyr juna har suka isa falo, nan suka yada zango, kamar yanda imaan ta saba haka ta sunkuyo ta fara cire masa takalman sa daga nan ta rage masa kayan jikin sa, sannan ta koma fridge ta dauko masa ruwa me sanyi ta tsiyaya masa a cup yasha sannan ta mayar dashi, bayan ta gama ta haye kan cinyar sa tana matsa masa kafadun sa, omar yace bbynah nayi missing dinki, kinsan Allah gani nayi kamar hours din basa tafiya, dan sosai na qagu dana ganki, imaan tayi masa kiss a kumatun sa, sannan tace mee too my swt berry miss yhu more, Yanzu dai muje na tayaka wanka. "Omar yace ohk, daga nan suka tashi dakin omar suka wuce, nan dai imaan ta wanke mijin ta tsaff, sannan ta shafa masa mai daga nan tasa masa kaya, "bayan ta gama suka dawo falo rungume da junan su kamar yanda suka saba.
"Sanda suka zauna imaan ta rike kafafun omar tana mammatsa masa su, omar sai lumshe ido yake yanajin dadi, can ya bude ido yace aff bby, imaan tace na'am. "Omar yace mikomin ledar can, imaan tace toh. Kawo masa tayi har gaban sa, sannan ya bude ledar, wani material mekyan gske hade da takalmi da jaka da kuma sarka da dan kunne, sai kuma less da atamfa da shadda dukkansu a ciki a dinke yahau fiddowa yana dorasu kan cinyar imaan, "imaan ta balalo ido tana Neman karin bayani wajen omar. "Omar kam sanda ya gama fiddo komai sannan yace bby wannan sakon ki aka bani na kawo maki, imaan da sauri tace inji wa? Omar yyi dan murmushi yace inji antyn ki, dazu farooq yazo har office dina ya kawo min wai ankon kune keda ita na suna. "Wayyo Allah dadi imaan ta furta ta shiga daddaga kayan tana dubawa sosai kuwa sukayi mata kyau gashi cas cas daidai jikin ta, sai washe hakora take dan farinciki ta rungumo kayan tana lumshe ido tace kai Allah dai ya barmin ke Anty ameera sister 'Yar arziki. "Omar ya kafa mata ido yana kallon ta yanda yaga ta shiga nishadi, shima sai ya samu kansa dayin farinciki, rungumo ta yyi yace ameen bbynah. "Imaan ta ware idon ta tace, gsky gobe tun asuba zamu bar gidan nan. "Omar d sauri yace zuwa ina? Imaan tace sunan Anty ameera, omar yyi dariya yace kai bby kina da zumudi da yawa, ai kya bari wajen azahar haka mu tafi, imaan tace taabb. Inaa ai son samu ma ace tun yau ina can. "Omar ya rike haba yace ikon god, kema fah kila akwai little bby a tare dake 😉. Imaan ta zaro ido tace habadai ya omar tun yanzu, omar ya sake yin dariya yace nasan nidin bana wasa bane fatana dai Allah yasa kwallon na ya shiga raga, imaan ta rufe ido tace Allah dai Jaan baka kunyata tayi mgnr tana turo baki, "omar yyi murmushi yace ah ni da matata kuma? Ai fatan Alkhairi nayi mana kedai kawai kice ameen, imaan tace ameen. "Haka sukayi ta hirar su gwanin ban sha'awa.
"Washe gari kam tun 8 imaan ta farka ta shiga shirye2 breakfast tayi masu sannan ta dawo daki, omar dake bcci Sam besan ma ta tashi ba, yatsun kafar sa tahau ja a hankali, tana dan matsa su, Omar ya bude ido har idon ya gama budewa duka, imaan ya gani zaune a Gaban sa, dan haka shima ya tashi daga kwanciyar da yake, imaan ta zuba masa
Ido tana murmushi tace swt luv ka taso muyi wanka. Omar yace tun yaushe kika tashi haka? Imaan tace tun dazu harma na hada mana breakfast, omar ya balalo ido yace oh shine ko kitasheni muyi koh? Kuma dai kinsan yau weekend tare zamuyi tunda ina gida, imaan tace eyya I'm sorry honey banason katsema bccin kane, omar yyi murmushi yadan ja hancin ta yace haka nan nima banaso kina wahalar min da kanki matukar ina gida komai tare zamuyi, imaan tace an gama ur Excellency, omar yyi dariya sannan ya sauko daga kan gadon, daga nan suka fada toilet danyin wanka. "Saida suka gama shirin su, sannan imaan ta shirya 'yan kayan ta cikin 'Yar jaka irin ta tafiyar nan, "omar dai sai kallon ta yake yace wannan shirin fah kamar Wanda zaki bar gari? Imaan tayi murmushi bayan ta dauko jakar d hijab a hannu sannan ta kamo hannun omar tace muje muci abinci tym na tafiya, Omar yace ohk. "Saida suka gama cin abincin sannan imaan ta sanya hijab dinta suka bar gidan.
"Tunda Omar yyi parking bakin gate imaan take shirin fita dan sosai take son ganin bbyn Anty ameera, omar ne ya riko hannun ta yace wannan saurin fa bby? Imaan tace bby nakeson gani, omar yyi murmushi yace kwantar da hankalin ki ai gashi dai mun iso gidan, imaan tace toh, sannan yace kinga gidan taro ne karki soma kula wani katon macen ma ba kowa nakeson ki dinga kulawa ba dan wannan duniyar abar tsoro CE baga mazan ba baga matan ba, "imaan ta kalli omar da mamaki tace toh Amman jaan ai tunda cikin gidane mezai shigo da maza kuma? Omar yyi murmushi yace bby kenan nadai fada maki ne in case. "Imaan itama murmushin tayi tace insha Allah zan kula ma da kaina sosai. Omar yace good, sannan ya manna mata kiss a goshi, itama ta maida masa da martani, sannan ta fito a motar, omar yace take care. Imaan tace ohkk byee. Daga nan ta shige gidan.
Nuceey luv😘