OMAR KO FAROOQ?

140-141

by @nuceeyluv

® *OMAR KO FAROOQ* ❓ 


     140_141


  

 "Tana shiga ta wuce parlon gidan, anan ta tarad d 'yan uwan Anty Ameera da su mummy, nan ta gaishe su tunda dama can tasan su ko alkcin da akayi bikin su sun shaku sosai da imaan kamar wadda sukayi shekaru, "saida suka gama gaisawa sannan ta haura sama dan zuwa dakin Anty ameera, "tana shiga ta tarad itama ta sanya material din data dinka masu tana dauri a gaban mirror, bayan tayi sallama imaan ta zauna bakin gado, "Anty ameera tace ke yanzu daga ganin bby sau daya sai muji Ku shiru gsky muna fushi dake, imaan tayi dariya tace afuwan Anty ameera, Allah kwana biyun ne duk banajin dadi, Anty ameera tayi saurin juyowa tana kallon imaan tace a haba kodai mun samu bby ne? Imaan tayi murmushi a karo na biyu a zuciyar tace eyya bazaki gane bane Anty ameera ni nasan halin Dana shiga,.. Anty ameera tace wannan shirun fah? Imaan tayi saurin cewa ehmm..kinga wlhy maleria ke damuna, "Anty ameera tayi dariya tace zakiyi bayani bby kina dauke d ajiyar omar dai. "Imaan itama dariyar tayi tace Allah dgske ba komai. "Anty ameera tace kinsan Allah kawai ki daina rantsewa dan ba yadda zanyi ba, imaan tace heheh toh ai shikenan nikam ina bbyn? Anty ameera tace tana wajen su mummy, imaan tace laa kinsan Allah ni ko lura da ita banyi ba shaf2 na gaishe su dukdan naga bby. "Anty ameera tace bari na kira a kawo maki ita, imaan ta mike da Sauri tace bari dai naje da kaina. Lkcin data isa parlon sai guda ake ana fadin Allah Ya raya zainab, imaan ta isa gaban mummy ta amshi bby dake bcci tana murmushi tace mummy kinji anyi maki takwara, mummy tayi dariya tace eh dan haka ki kulamin da takwara ta, "imaan tana murmushi tace sosai kuwa zan kula maki da ita, daga nan ta haura sama da murnar ta, tana shiga ta shiga fadawa anty ameera sunan bbyn, anty ameera dukda daman tasan sunan Amman tayi murmushi tace Allah ya raya mana ita. Imaan tace ameen, buh anty ameera yanxu wanne suna zamu dinga kiranta dashi? Anty ameera tayi dariya tace duk Wanda kika sa mata mun baki zabi, habawa take farinciki ya lullube imaan tace kai Amman naji dadi, bari mugani.. Ta tsaya tunani.. Can tace asa mata *AIMAN*, Anty ameera har cikin ranta taji dadin sunan, dan haka ta fadada murmushin ta tace gsky kin iya zaben suna mekyau, imaan tayi dariya tace tnx u,.. Nan suka fara hirar su. Suna cikin hirar frnds din anty ameera suka shigo dakin, nan hayaniya ta kaure ana fira, daga nan suka fara daukar pic, su cire wannan Susa wannan qarshe ma waje suka fito sukaci gaba da selfie, imaan dai na makale da bby dakyar ma ta iya bada ita, haka suka sha budiri da buradada. 

  "Komai anyi shi cikin kwanciyar hankali, har bayan la'asar sosai sannan mutane suka fara watsewa. "Imaan na dauke da bby a dakin anty ameera, anty ameera ta shigo dakin, tace imaan dan Allah mikawa muhsin wannan ledar yana waje, imaan tace waye kuma wannan? Anty ameera tace abokin farooq ne yazo da Matar sa wannan saliman? Imaan tace eh me rawan kan nan da ana pic, anty ameera tayi dariya har tana rike ciki sannan dakyar ta iya saita kanta tace kinga ta manta kayan ta dan shiririta har sanda suka isa gida ta tuna kuma ta sake maido mijin ya dauka mata, imaan ta tabe baki tace shima din mijin tace ne, hhhh wlhy imaan yaji ki baruwa na, kinga dan Allah kai masa sauri yake bari na shiga wanka. "Imaan tace Allah badan keba bzan kaiba. Anty ameera tana dariya tace wai me tamiki ne? Imaan ta yatsina fuska tace ba komai kawai bansan mutum me shishshigin banza ne, anty ameera ta rike haba tace nidai dan Allah tashi yana jira. Imaan tace toh, tana fita anty ameera ta fada toilet.  


  "A bakin gate ta tarad dashi yana tsaye, imaan ta karasa wajen da sallamar ta, sannan tace gashi inji anty ameera, muhsin yyi murmushi yace tnx u, imaan tazo zata juya yace am.. Dan Allah ba, imaan ta juyo tace lpy? Yyi dariya yace sorry dan Allah ki cire wannan fuskar shanun da kika sa nidai ba sace mutane nake ba, imaan batasan lkcin da tayi dariya ba tace ba haka bane, muhsin yace yauwa ki fadawa ameera na gode, imaan tace toh, sannan ta juya da niyyar tafiya.. Karaffffff suka hada ido da omar dake tsaye jikin mota ya harde hannayen sa, fuskar nan babu alamun annuri kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa. "Tsananin tsorata da imaan tayi kafafun ta ma sun kasa daukar ta dan zata iya tuna tunda take a rayuwa bata taba ganin omar a irin halin da yake ciki ba yanzu, da kyar ta iya daga kafar ta taka har gaban sa, "har yanzu ya kafe ta da ido wannan fararen idanun sun fara canja kala zuwa jaa. "Kirjin imaan ne ya bada darararam cikin dauriya ta kwakulo murmushi tace swt...l..u..v sa..n..n.u..da..zu..wa. Tayi mgnr bakinta na rawa, ko ba'a fada ba tasan ma lefin ta.

  "Omar ya watsa mata wani mugun kallo Wanda yyi saura kadan imaan ta saki fitsari a wando, batare da yace mata komai ba ya koma cikin mota. "Imaan ma da sauri ta bude motar ta shiga, d niyyar masa mgn taga yana kokarin tada mota batare daya kalle side din da take ba, imaan d sauri tace ya omar banyi sallama dasu bafa? Sai alkcin omar ya juyo da red eyes dinsa cikin wata murya data sake firgita imaan yace.. Dani nace ki shigo? Me ya hana kibi wancan katon?? Imaan tayi saurin sadda kanta hankalin ta atashe sosai ta hango tsantsar kishi a idanun omar, dan haka tayi kokarin rufe murfin motar, ko karasa rufewa batayi ba ya fisgi motar da wani mahaukacin gudu.

 "Imaan dake zaune sai addu'a take tana Allah dai ya saukesu lpy dan wannan gudun fitar hankalin da omar yake ikon Allah ne kawai zai kaisu gida. "Geefe guda kuma tana tunanin wanne hukunci ya Omar zai yanke mata kai harma fargaba take yanda taga tsantsar kishi ke masa yawo a ido.


Nuceey luv😘