142-143
by @nuceeyluv
® *OMAR KO FAROOQ* ❓
142_143
"Cikin lkci kadan suka isa gidan, yana gama parking batare daya kalleta ba ya fice a motar yyi gaba abinsa. "Imaan duk ta tsorata da wannan fushin na ya omar, "itama fitowa tayi domin tabi bayan sa, kafin ta karasa wayar ta tahau ringing, kamar bazata daga ba sai kuma ta duba, ganin anty ameera ce yasa tayi saurin daukan call din, hello. Anty ameera daga dayan bangaren tace kee imaan me kike a waje ne tun dazu? Imaan ta shiga yiwa ameera bayanin abinda ya faru.. Anty ameera salati tayi sannan tace kinga kinsan me zakiyi yanzu? Imaan ta girgiza kai kamar tana gaban ta, anty ameera tace yauwa, bude kunnen ki, ki saurari abinda zance, imaan tace toh, anan anty ameera tahau fada mata abubuwan daya kamata tayi.....
"Bayan sun gama wayar imaan ta shiga parlon, ganin baya wajen tasa aranta yana dakinta, dan haka ta haura sama da sauri, ga mamakin ta sai taga dakin wayam baya ciki, jiki a sanyaye ta koma nasa dakin, adan tsorace ta bude kofar, saidai data duba yana toilet ga alama ma wanka yake, zuciyar ba dadi ta jawo masa kofar ta koma dakinta danyin wanka itama, saidai koda ta fara wankan sai taji babu dadi dan tayi sabo dayin wanka da ya omar, haka tayi ta shafa jikin ta kamar me koyon wanka.
"Shima ta wajen omar din kuwa hakan ta kasance, yafi 5mins a toilet yana zaune ya kasa yin wankan, gaba1 jikinsa yyi sabo da wanka d bbynsa, gefe guda kuma yana hango fuskar matar shi tanama wani kato dariya, mwtss yaja tsaki yyinda zuciyar sa take ta azalzala dan takaici. Shima dai haka yake goga jikin kamar dan koyo.
"Imaan sanda ta shirya tsaff, lkcin harma tayi sallar isha, sannan tasa wasu kayan Wanda dasu da babu duk daya suke, sannan tabi jikin ta da turaren data San suna haukatar d tunanin hubbyn ta. " yanzun ma dakinsa ta duba, saidai kuma baya nan, hakan ya tabbatar mata d kasa ya sauka. "Itama kasan ta sauko tana tafiya kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki, har ta iso gaban ya omar, omar kuwa tunda ya hango ta ya kasa dauke idon sa dan irin wannan tafiyar nata yana matukar daukar hankalin sa, Amman tana isowa Gaban shi yyi saurin dauke kai yana bata rai, "imaan ta zauna a gaban shi tayi kalar tausayi sannan tace ya omar, shiru be amsa ba, imaan ta kirashi kusan 4tyms Amman yayi banza da ita tamkar ma besan d wata halitta a wajen ba, imaan dukda haka bata hakura ba tace dan Allah ya omar ka saurare ni, wlhy abinda kke zargi ba haka bane, ni aika ma na bashi fah shine kurum abinda ya faru Amman wlhy banma taba ganin sa ba, omar a zuciyar sa yace eh lalle wato iya aika ta bashi? Bayan kuma ta gama washewa wani kato hakwara tana dariya Amman dan rainin hankali zatace aika ta bashi., Mtwsss yaja tsaki da karfi sannan ya tashi daga zaman da yakeyi ya haura sama. "Imaan kamar zatayi kuka ita burinta ma ko mgn yyi mata, ya salam wai haka ya omar yake da zafi? Itama tashin tayi tabi bayan sa da sauri
"Kan Gadon sa ta sameshi ya jawo system yana dubawa, "imaan ta sunkuya a gefen gadon tace ya omar, swt luv, hubbynah duk sunan data kirashi omar kokadan be dago ido ya kalleta ba, "imaan fa hankalin ta sosai ya sake tashi, qarshe tace ya omar Indai raina zai kasance fansa ga fushin ka a shirye nake da in sadaukar maka dashi... Ta karasa mgnr a sanyaye, omar dake kallon system zahiri zaka dauka wani important Abu yakeyi yanda ya bada dukkanin hankalin sa a wajen, Amman abin ba haka yake ba, sosai yake sauraron imaan saidai har yanzu zuciyar sa bata daina zugin abinda ya gani da idon sa ba shi haka yake Allah yyi sa da kishi sannan yana da zuciya, ta wani bangaren kuwa ji yake kamar ya rungumo imaan Amman daya tuno abinda tayi saiya share, ganin 'yan tunane2 bazasu kaishi ko'ina ba, ya rufe system din sannan ya ajiyeta daga nan yyi kwanciyar sa batare daya kalli imaan dake tsugunne a wajen ba.
"Abun tausayi imaan a zaton ta zai hakura ne Amman sai taga sabanin hakan, "cike da tsoro da fargaba ta haura kan gadon, ta baya ta rungumo shi..
"Ya salam abinda omar ya iya furtawa a zuciyar sa kenan.
"Imaan ta matsa jikin kunnen sa tace kayimin afuwa ka yarda dani, wlhy kai kadai ne a zuciyata dan Allah ka dubeni.
"Har cikin ransa yakejin wutar son imaan na ruruwa cikin zuciyar sa, Saidai a yanzu ya yanke shawarar gwara ya koya mata hankali sbd next tym. Banza yyi da ita batare d yyi koda motsi ba. "Imaan na kwance ta bayan shi tun tana bashi hakuri har bacci barawo ya sace ta. "Jin nauyin ta ya karu, shiya tabbatr wa da omar tayi bcci, dan haka ya juyo a hankali, sannan ya rungume ta tsam a jikin sa.
"Da asuba shiya fara tashi dan haka yyi saurin janye jikin sa daga nata, bayan yyo alwala guntun ruwan dake hannun sa ya yarfa mata a fuska. Tana motsawa shikuma ya tada salla. "Imaan tana bude ido taga ya omar yana sallah, sai kawai taji ba dadi, mutumin da saiya jirata sunyi salla tare Amman jibi yanda ya shareta koya tasheta, haka ta tashi itama tayo nata alwalan. "Koda suka idar d sallah, wannan karon omar can gefe ya matsa, imaan ta taho zata matsa jikin sa, yyi saurin daga mata hannu batare d yyi mgn ba. "Jiki a sabule ta rakube gefe guda itama ta kwanta, sanda tayi 'yan juye juyen ta sannan bcci ya dauke ta domin omar ya gama yi mata sabo da jikin sa.
"Shima dai hakan takasance ta wajen sa.
"Da safe dake babu aiki sunsha bccin su sosai. "Sai wajen 9 imaan ta tashi, kitchen ta wuce tayi masu abinci, sannan ta wuce dakinta tayi wanka, cikin kayan ta ta zabo wasu riga da wando, wandon ko Rabin cinya bekai ba, sai rigar dududu iyakar ta cibiya, gashin ta ta kama shi bayan ta gyara shi. Sannan ta fito a dakin bayan ta gama bude jikinta da turare masu kamshi.
"Dakin omar taje, shima lkcin harya shirya cikin Riga d ¾ wando, shima yyi kyau sosai. "Imaan nayin sallama furkar ta dauke da murmushi ta tafi inda yake, sannan tace morning hubbynah. "Omar dukda kwalliyar ta, ta tafi da imanin sa, Amman saiya daure fuska ko gaisuwar be amsa ba."imaan ta marairace fuska sannan tadan kamo hannun ya omar tace hubbynah shin har akwai ranar d bbynka zatayi maka magana ka shareta? Haba hubbynah taya zan amince da fushin mafi tsadar mutane a wajen nah? Dan Allah ka fahimceni.. Ta karasa mgnr a sanyaye.
"Omar dake tsaye sai ji yyi kafafun sa suna Neman yin rawa, ko kadan bayason bbynsa ta shiga damuwa, kamar dai ya fasa Fushin da yake da ita, sai kuma idanunsa suka sake hango ta da wannan mutumin, take ransa ya kara zafi, hannun sa ya fincike a hannun ta sannan yabar mata dakin.
"Inna lillahi wa'inna ilahin raji'un abinda imaan take furtawa kenan, kanta tahau yamutsawa tace shin wai wanne irin zuciyace da ya omar? Ya salam. "Fitowa tayi d sauri ta bishi kasan, yana zaune kan kujera.
"Gefen sa ta zauna a kasa, sannan ta kifa kanta cikin wata irin murya tace, inada masoyin da bana walwala batare dashi ba,bani da wani sauran karfi a yanzu matukar yana fushi dani... Sannan ta dago idanun ta da suka gama cikowa da kwalla, taci gaba da fadin, ka tausaya kayi min afuwa zuciyata tana radadi kaji tausayi na Dan Allah..😰👏🏻
"Wannan karon gaba1 sai yaji ta bashi tausayi, riko hannun ta yyi yace kinga tashi komai ya wuce, habwa wani irin farinciki ne ya ziyarci zuciyar imaan, sannan tace, Ya omar zuciyata zata kasance cikin zulumi da kunci har saina ga fuskar ka tana fitar da Annurin yarda A gareni.....
Nuceey luv😘