OMAR KO FAROOQ?

144-145

by @nuceeyluv

® *OMAR KO FAROOQ* ❓ 





     144_145 




  "Murmushi ne ya bayyana akan fuskar shi sosai harma dimple dinsa saida suka lotsa, sannan ya jawota jikinsa ya matseta tsam cikin rada yace bbynah na yadda dake, kuma har cikin raina na daina fushi dake, imaan ta dago kanta tace Dgske ya Omar? Omar ya gyada kansa yana murmushi, imaan tadan shagwabe fuska tace nidai so nake ka furtamin da bakin ka. "Omar yyi dariya sannan ya bude baki da niyyar yin mgn, sai jin bakin imaan yyi cikin nasa tana aika masa da wani irin kiss me zafi2, a take kuwa omar ya sake rungumo ta yana maida mata da martani, kamar Wanda sukayi sati basuyi kissing juna ba. "Saida suka gama lashe lashen su, sannan suka hakura, dining area suka nufa anan suka ciyar da junan su kamar yanda suka saba kullum.



*****

  "Rayuwa kenan, me cike da dogon buri da jarabawowi kala2 kana naka kuma Allah na nashi, tofah haka rayuwa omar da imaan ta kasance kullum cikin soyayyar junan su, tare d nishadi abinsu.


 "Bayan wata uku, zaune imaan take kan cinyar omar yyinda shikuma yake duba system dinsa kan gado, imaan tasa hannu tana shafo qirjin sa, omar ya dawo fa hankalin sa kan imaan, yana murmushi yace bby naga Alama yau bazaki barni nayi aikin nan ba ko, imaan ta turo baki tace, kuma dai ya omar bcci nakeji ai ya kamata mu kwanta, omar yace uhum fadi gsky dai bayan bcci sai me? Yyi tmbyr yana dage gira, "imaan tayi saurin rufe idon ta tace ba komai. "Omar yyi dariya yace nidai har yanzu ma bbyn naki shiru kamar bama nema. "Imaan tace Ai komai lkci ne ya omar idan Allah yyi d rabon munada haihuwar kaga saimu samu. "Omar yyi murmushi ya shafo fuskar ta yace kumafa hakane beauty, tashi yyi bayan y rufe system din, sannan ya gyara musu kwanciyar bayan ya kashe fitila. "Toh daman hakan imaan takeso, da sauri ta samawa kanta wajen kwanciya kan kirjin ya omar kenan., sannna tasa hannu tana 'yan tabe2 ahaka suka Lula duniyar ma'aurata.

  "Da safe, kamar kullum imaan ta gama masu breakfast, bayan nan ta haura sama sukayi wanka. "Hannun ta rike Dana ya omar suka sauko kasa, kujera taja omar ya zauna, ita kuma ta zauna kan cinyar sa. "Wannan karon omar shiya hada masu tea, daukowa yyi ya bata, imaan tasa baki ta amsa, saidai kafin tayi kurba ta biyu, taji amai ya taso mata, da gudu ta sauka kan cinyar ya omar, ta nufi toilet din dake kasan. "Omar shima a tsorace ya tashi yabi bayan ta yana tmbyr komai ya faru, samun ta yyi sai sheka amai take kamai zata amayar da hanjin cikin ta. "Omar dukya rude famfo ya kunna yahau wanke mata baki sannan ya wanke inda ta bata da aman. "Hannun ta ya kamo yana mata sannu, imaan kuwa sai maida numfashi take kamar wacce tayi aiki. "Komawa sukayi sannan suka zauna. "Omar yace meya sameki? Imaan tayi murmushi tace b komai fah, omar yace Amman kikayi amai? Imaan tace Allah b komai inaga dai tea dinne yasani amai. "Omar yace ohk bari na baki dankalin, shima koda ya bata a tamanin tabar wajen, wannan karon ta wahala sosai wajen yin Aman. "Imaan dukta galabai ta, omar kuwa hankalin sa ya tashi, shi yama manta yanda ake duba maras lpy, ganin imaan ta baje a falo tana maida numfashi a hankali, hankalin sa ya tashi, a guje ya haura sama sannan ya dauko mata hijab dinta. "Imaan na kwance taga omar d hijabi cikin karfin hali tace ya omar bafa abinda ke damuna. "Omar ya zaro ido yace inaaa bby ai bari ma kiga. "Daga ta yyi sannan ya sanya mata hijab din. "Batare da yace mata komai ba ya dauke ta sai cikin mota. "Imaan dai jikin ta yyi laushi b damar yin mgn, "omar kuwa sosai yake gudu a motar tamkar zai tashi sama.

 "Cikin hukuncin ubangiji, suka isa *OMAR FAROOQ SPECIALIST HOSPITAL* , ko karasa parking motar beyi ba ya dauko imaan a hannu tamkar bby. "Direct office dinsa ya wuce dukda kallon da ake binsa dashi Sam bedamu ba. "Yana Shiga ya danna call ga wata nurse, cikin tsawa yace inason ganin ki right now. "Nurse din da sauri ta isa office din jikin ta na mazari, "omar dake safa da marwa, tarad, da sauri tace gani sir, omar ya nuna mata imaan yace ki dubamin ita sosai haraswa take tun dazu.

 "Nurse ta kalli imaan dake lumshe ido, sosai tasha mamakin ganin ta, dan bazata manta yarinyar data kawo mahaifiyar ta ba sanadin kin taimaka mata harta rasu... Ke me kike jira? Nurse ta firgita dan da tsawa yyi mgnr, sorry sir, abinda tace kenan. Saida tadanyi gwaje2 ta sannan tace akawo fitsarin ta. "Omar d kyar ya samu imaan ta kawo, sannan nurse ta shiga bincike, tana mamakin Dr Omar guda sbd rikicewa ya kasa duba Matar shi, kai lalle ikon Allah ya wuce wasa wai tayama ta zama Matar shi????.. Babu amsa, haka ta gama gwajin ta harta gama.

 "Da murmushi ta mikawa omar result din, omar ya karba sannan ya shiga dubawa,.

 "Abinda ya gani shi ya matukar bashi mamaki, fuskar sa dauke da tsantsar farinciki ya maida kallon sa ga imaan data fara bcci, "kallon nurse din yyi data zura masa ido tun dazu..a zuciyar tace daman Dr omar yana murmushi?.. "Katseta yyi da fadin tnx u very much. "Nurse itama murmushi tayi tace u r wlcm. Anan ta bar office din. "Tana fita omar ya yaye rigar imaan, kiss ya kaiwa shafaffan cikin ta, sannan yace so yanzu bby tana dauke da little bby murmushi ya sakar wow Thanks God.