Sahla dear
by @azizat
TOP-NOTCH.....the touch of excellence, just for you.
✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈
Litattafan TOP-NOTCH
Abinda ya baka TSORO---Ramlat MaiDambu
Bani da LAIFI--- Shatuu
SAHLA a Paris---Azi_zat
Guda ɗaya 350
Biyu 750
Uku 1000
***
Sahla Dear...
Gidanmu yana da ɓangarori dayawa. Gini ne na da amma Alhaji ya gyara an zamanantar da shi. Matan Alhaji kowacce da ɓangarenta falo, kitchen da ɗakuna biyu, store da kuma banɗaki.
Ita Mama akwai son girma da shegen son nuna kai. Lokacin da aka aurota Kaka tana yawan mata gori da tsohuwar matar Alhaji wato Gimbiya Maryam. Wannan yasa ta ki jinin ka haɗata da duk abinda ya shafi Maryam ɗin 'ya'yanta ma da suke kasar waje ko sun zo gidan ba ta yi da su. To ba ma zuwan su ke ba dan ni dai hana karya tun dana taso sau biyu na taɓa saka Anty Hasina da Anty Sayyidah a ido. Dan ko bikin Anty Hasina da aka yi shekara biyu da suka wuce a fadar Maimartaba akayi komai. Shi kuma Uncle Faruqu a hotunan biki kawai na ganshi.
To kamar yadda na ke baku labari. Mama dai kullum fitinarta mi za ta saka a ɗakinta da zai fi na sauran kishiyoyinta. In kuwa sutura ce ko bashi sai ta ciwo ta siya dan kawai ta saka ta fi sauran matan.
Ummi kuma ga kwaɗayi, roko da kuma rowa. Har wa yau tana zaran abinci a store ɗinta ta siyar ta kashe kuɗin. Kullum cikin rikici ake da ita akan kayan abincinta baya taɓa kaiwa karshen wata. Bayan waɗannan halayen indai wajen gulma ne to sai dai a shafa mata Fatiha. Radiyo ce mai jini. Wallahi duk gulmar Hajiya Kaka ta sallame mata. Tana da kazanta gaskiya dan da zaka duba karkashin gadonta za ka iya samun ruɓaɓɓen Albasa da aka ɓoye tun shekara biyu da suka wuce. Bara da ta haihu ɗan bai zo da rai ba wata Babarta ta zo yi mata wanka ta sharo mushen kyankyasai sun fi hamsin a kasan gado, inaga maganin sauron da ta ke sawa ne ya ke kashe su. Ga su ledar taliya su macaroni su ledar maggi da ta ɓoye ɓeraye sun ci na ci sun bar na bari. Gaskiya ranan girkinta anfi jin jiki. Ba zata taɓa girki tsakani da Allah ba, duk irin cefanen da za a bata ba zata taɓa amfani da shi ba. Gara Mama takan yi girki mai kyau sai dai ba zaku koshi ba, amma yaranta zasu koshi. Ita Ummi har a yaranta mugunta take musu. Duk wannan halayen nata fa tafi kowa zuwa Islamiyya a cikin matan Alhaji. Sai ka rasa mima ta ke koyowa idan taje chan dan sama da shekaru goma tana zuwa Islamiyya amma babu wani abu daya gyaru cikin halayenta. Da lokacin Azumi ma ita ce gaba-gaba wajen zuwa sallar taraweeh da tahajjud.
Umma Bilki. Hmm. Umma Bilki. Allah ya yafemu dai kawai amma ni kam gara Ummi sau dubu akan Umma Bilki. Ita Ummi duk halayenta a fili su ke sai dai kai ka sha maganin zama da ita, amma Umma Bilki hawainiya ce, yau kalarta fari gobe ja jibi kuma shuɗi. Munafuka ce mai lasisi. Tsabar iya munafurcinta har haɗa Alhaji take da Hajiya Kaka faɗa. Tsaf za ta shirya tuggu mai wuyar warwarewa. Kafin ka kamo bakin zaren ta riga ta cire hannunta a ciki. In dai za a yi faɗa biyu uku tsakanin Mama da Ummi to idan ka bi silsilan maganan za ka ga Umma Bilki ce ta haɗa su. Shiyasa sam bana shiga safgarta. Tun sau ɗaya da ta haɗa min wani sharri a wajen Alhaji na ja baya da ita. Gashi idan ka zo gidan ta maka wani tarba mai kyau sai ka ɗauka tafi kowa kirki amma...a bar kaza a gashinta.
Anty Amarya dai babu ruwanta da kowa. Bata shiga sabgar da ba nata ba. Duk da bata taɓa haihuwa ba bata irin nuna son yaran nan kamar yadda masu son haihuwa ke yi. Idan yaro ya shiga sashinta ya mata shirme zane yaro take sosai. Tana da tsabta har dana Allah ya isa. Idan ka shiga falonta ka ɗan jima. Kana fita za ta fata mopping. Duk wacce za ta kawo saurayinta na musamman to sashen Anty Amarya za ta sauke shi dan kuwa ba za ka ji kunya ba.
Ina ta muku gulman matan Alhaji ko. Idan ban muku gulman ba ba zaku gane abubuwan da zasu biyo baya ba. Ni da yake 'yar gaban goshin Hajiya Kaka ce duk wani abinda yake gudana a gidan ina sani. Dan idan aka je aka dawo duk a falonta ake jibgewa.
Hajiya Kaka tana son Anty Amarya amma kullum korafinta wai bata girmamata yadda ya kamata. Wai itama halinsu ɗaya da Gimbiya Maryam wato jiji da kai.
Amma sauran matan 'yan ayi daɗi ayi faɗa ne.
***
Yau ina kwance a cikin ɗaki ina karanta wani littafin hausa na ji muryan Alhaji yana Sallama. Kaka ta shiga wanka dan haka ni kaɗai ne a ɗakin.
Na yi saurin jefar da littafin na jawo bargo na rufe fiskata amma ban gama rufuwa ba na jiyo muryansa a cikin ɗakin yana faɗin "Sahla taso nan"
Na san dubuna ne ya cika dan yadda yai maganar babu wasa a tattare da shi.
Na yaye bargon na sauko daga kan gado na biyo bayanshi. Ina ganin mun nufi zaure na kama salati a cikin raina, kar dai kar dai.
Ina ganin Malam Buba Maitsire na fara rarraba ido.
Alhaji yace " Malam Buba ga ta nan ta biyaka kuɗin tsirenka"
"Alhaji Allah na tuba ba zan sake ba. Wallahi na tuba"
"Miye na tuba a nan Sahla. Ba kin ce karshen wata ya zo gida ya karɓi kuɗinsa ba"
"Ba haka na faɗa masa ba fa. Cewa na yi ya dinga lissafin kuɗin tsirensa idan ya taru dayawa sai ya samu Alhajinmu. Ko ba haka muka yi ba"
Malam Buba yace haka ne.
"To dana ce ka samu Alhajinmu cewa na yi ka karɓi kuɗi ne?"
"Ikon Allah!. Yallaɓai..."
"Dakata Malam Buba, ka ga ni masallaci zan wuce. Ga Sahla nan za ta ba ka kuɗin ka"
"Dan Allah ka yafe mun. Wallahi ba zan sake ba. Tsiren ɗari huɗu da hamsin kawai na ci"
"Ɗari biyar da hamsin dai"
"To ba ranan gyara ka saka min ba"
Alhaji ya tsaya kallonmu muna ta lissafin kwanakin da na yi ina karɓan tsire. Dama rumfarsa a kan layinmu na zuwa Islamiyya yake shine idan na ɗan ji kwaɗayi sai na tsaya na ce ya yanka min tsiren hamsin a-haka-a-haka har ya taru yai yawa.
Da wata ce ba ni ba a gidan nan da kashinta ya bushe a wajen Alhaji. Amma Allah ya so ni Alhaji baya dukana.
Inaga ma gajiya yai da lissafin da mu ke yi da Malam Buba mai tsire kawai dai na ga ya ciro kuɗi ɗari biyu-biyu guda uku ya bawa Malam Buba.
Ina ji yana godiya na yi caraf na ce masa zan zo na amshi tsire da sauran canjin Alhaji.
"Ni kam Uwata anya ba boarding school zan kai ki ba kuwa"
"Dan Allah Alhaji..." na fashe da kuka na shige gida.
Tab! Ina zan iya barin Hajiya Kaka.
su Safiyya da Zuhriyya da aka kai su boarding school ai ba karamin wahala su ke sha a chan ba, idan suka dawo gida ka gansu a rarrame kamar an tsinto su daga gidan marayu...
***
Yau Asabat ina wanke uniform ɗina a bakin kofar ɗakin Kaka aka yi sallama. Kaka na zaune ɗan gefe dani akan tabarma tana cin goro.
"Wa'alaikumussalamu. Laraba sannu da zuwa. Bismillah"
Ban maida hankali kan zancensu ba na cigaba da wankina, sati biyu kenan da shigata JSS 1. Ina ji da kaina nima. Tsabar an tsaneni sai da aka bari na yi aji ɗaya har aji shida. Hanifa dana girmeta da wata biyar ma a Primary 5 ta zana common entrance ta tafi boarding ita da Safiyya aka barni ni kaɗai a Primary 6 kamar wata mayya.
"Dan Muhammadu ki ce maganan nan ba gaskiya bane"
Ina jin Kaka ta faɗi haka na karkata kunnena na fara sauraron zancensu.
"Hajiya shiyasa na ce gara na faɗa muku kafin a zo a yi abin kunya"
"To wani abin kunyan ya wuce wannan Laraba" ta ɓantari goronta sannan ta cigaba. "Ai su ku nema mata magani"
"Iyayen sun ce an nemi magani har an gaji. Wai Aljanunta na gado ne"
"To sai su rasa abin da zasu sata sai ɗauke-ɗauke"
"Kaka waye ke ɗauke-ɗauken?"
"Wai fa sarkuwarta da aka kawo kwanan nan"
"Inna Laraba wai Amaryar Malam Hashiru, miye ma sunanta?"
"Kulu"
"Kulu mai sata kenan" Kaka ta kai min duka da tsintsiyar laushi dake kusa da ita, na yi saurin kaucewa ina dariya.
"Dan bantenki cutar ɗauke-ɗauke aka ce take da shi ba sata ba"
Ni kam mi na samu banda dariya. Inna Laraba na fita Kaka ta mike za ta kai rahoto wa matan gidan. Yau Amarya Kulu ta shiga uku a gidanmu. Inna Laraba makotanmu ne suma babban gida suke mai balbali-balbali da yawa. A gidan 'yangidanmu ke kitso. Idan ana wani hidima kuwa sukan shigo kwansu da kwarkwatansu su tayamu aiki...
***
Ina JSS two aka saka bikin Anty Firdausi dana Anty Amina har ma dana Anty Fatima Munnirah 'yar Baffanmu Abubakar. Daɗin abinma tuwona maina za ayi dan biyu daga ciki na gida zasu aura, Amina ce kawai za ta auri wani ɗan Bauchi. Munnirah da yaya Mustafah sai da suka gama kulla soyayyarsu kafin suka sanar a gida. Nan fa Kaka ta fara masifa da korafe-korafenta marasa dalili.
Alhaji kuwa ya dage sai an kulla zumunci wai shi da Baffa Abubakar ɗaya suke. Dake gar ta san gar, duk ta yadda ta fito masa sai ya toshe, karshe ta hakura ta saka musu albarka.
Ba abinda yake mun daɗi irin yadda ake cika a gidanmu lokacin biki. Ka ci ka sha ka koshi son ranka. Gashi lokacine da gaba ɗaya familynmu ke haɗuwa, babu banbanci tsakanin'ya'yan Hajiya Kaka dana marigayiya Hajiya Sadiyya. Balle wannan bikin zai kara karfafa zumunci.
Abban Egypt zai zo da iyalinshi haka nan su Anty Hasinan kasar turai ma duk zasu zo...
Tun ana saura sati biyu 'yan Egypt suka shigo. Su Amal da Amrah an zama 'yan gayu, suna wani turancinsu da larabcinsu na 'yan gayu. Ni kam banda ta'al- zo, na'am- e, babun- kofa da kuma sarirun- gado ba abinda na sani a larabci.
'Yan gidanmu sai nan nan suke da su wai su 'yan gayu. Mtssw.
Har ma danna taɓawa Amal riganta take cewa wai zan shafa mata datti, sannu madara. Mtsww...
Ina zaune a ɗaki nida Kaka muna cin tuwon shinkafa da miyar ɗanyen kuɓewa aka yi sallama aka shigo. Ni da Kaka rige-rigen kai loma muke ko ta kan sallamar bamu bi ba. Miyan yayi daɗi, ko ban faɗa ba kun san girkin Anty Amarya ne. Ga naman kaza a ciki ga hanta an yanka kanana, ga kuma busashshen kifi irin wanda Inyamurai ke siyarwa ɗin nan.
"My Kaks ki ci a hankali mana kar ki shake"
"Sahla dear eat slowly kin ji" ya faɗa yana shafa kumatuna
Affan ne. Affan yayan Amal. Shine ya kirani da DEAR. Duk da dai ban kai su Amal jin turanci ba ai na san wannan kalmar. Kai ina cin 60/100 fa a darasin english kuma duk english novel da aka samu karantawa a makaranta ina karantawa.
Na ɗan sunkuyar da kai ina murmushi. Sai na dena ɗiban katon loma na fara ɗiban karami.
"Sahla kina wani aji yanzu?"
"JSS 2"
"Wow! Kinga nan da shekara huɗu sai a ɗaura mana aure"
"Dalla bani wuri. Waye zai baka Sahalar, da gashinka kamar dambun mahaukaciya"
"Kaks wannan gashin swagger kenan fa"
"Ina uwarka. Ba za ta shigo ta gaisheni ba"
"Mom tana sashen Anty Rafee'ah. Kaman tace zasu yi maganar event da za ayi a bikin ne"
Ni dai tunda yai maganar za a ɗaura mana aure nan da shekara huɗu sai na sunkuyar da kai ina cin abinci a hankali. Da hakura ma zan yi da abincin sai na tuna idan na hakura dashi Kaka za ta tsame sauran naman ne ta cinye ita kaɗai. Ni da Kakar tawa duk kuraye ne. Son nama kamar jaraba.
Affan yaita tsokanar Kaka tana biyeshi. Duk cikin 'ya'yan Abba shi kaɗai ne ke sakewa da Kaka. Zai zauna a sha hira da shi. Amma su Amal duk halin Mom ɗinsu suka yi.
Sati ɗaya saura biki su Anty Hasina da Anty Sayyida suka dira a gidan. Anty Hasina har da tsohon ciki za a yiwa Faisal kani ko kanwa. Anty Sayyidah kam ta ki aure har yanzu. Ina ji su Mama da Ummi na gulmanta idan na shiga sashensu.
Ni da su Amal, Hanifa da Safiyya muka ɗunguma sashen Alhaji dan muga Uncle Faruku. Ance ya zo amma har yau bamu gan shi ba.
Har muka karashi ziryanmu bamu ga mai kama da shi ba.
Da muka gama jelarmu bamu ganshi ba sai kowa ya watse. Ina zuwa ɗakin Hajiya na hango wani takalmi irin cover shoe ɗin nan na maza. Sai kyalli ya ke, gefensa kuma wata Akuyar Kaka ce ke Sunsune-Sunsunen abinci. Na kori Akuyar na ɗau takalmi ɗaya ina dubawa dan na ga size ɗin, wannan takalmi ba dai kato ba kam. Kafin na ɗau ɗayan mai takalmi ya fito daga ɗakin Kaka. Dogo ne sosai, fiskarsa babu fara'a ko kaɗan. Yana sanye da blue ɗin riga da jeans 'yan kanti ba 'yan gwanjo ba.
Na ajiye masa takalminsa ina murmushi na fara gaisheshi. Ko ba a faɗamun ba na san Uncle Faruku ne dan suna kama sosai da Anty Sayyidah.
"Ina kwana Uncle Faruku". Faruku Kaka ke kiranshi shiyasa sunan ya bi bakina amma tabbas abinda na faɗa ya ɓata masa rai. Dan kuwa sake haɗe rai yayi kamar ya tauna kashi.
"Takalminka ya min kyau"
Ban ankara ba na ji an shako ni.
"How dare you"
Wallahi irin shakar da ya min sai da na hango iyayena suna min maraba da zuwa Barzahu.
"Faruku kashe min ita za ka yi. Saketa, saketa na ce"
"Mustafah"
Ashe tare su ke dama. Yaya Mustafah ne ya kwaceni daga hannun Dodon nan. Daga gaisuwa.
Sai dana yi minti ɗaya da rabi kafin na fara dawowa dai dai. Sai a sannan nake ji wai ashe Kashin Akuya ce ya gani a cikin takalminsa. To ni na saka a ciki ne?.
Ina ji Kaka na korafi akan koma minene dai bai kai ya kashe mata ni ba. Wallahi na shako kam dan har hawayen dole sai da na yi. Ba dan Yaya Mustafah ba kila da yanzu na zama gawa.
Takalmin Yaya Mustafah ya saka ya bar wajen shi kuma Yaya Mustafah ya saka nasa bayan ya karkaɗe kashin Akuyar.
"Allah ya isa, kuma Wallahi sai na rama" na faɗa a fili...