Chapter 25
by @mamanyusuf
🅿️_25
Aguje ya shiga falon Kamar wani k'aramun yaro Yana fad'in yheeeee wooooooooo yau akwai d'an k'aramun shagali a gidan nan wallahi sai zagaye iyayenshi da sauran 'yan uwanshi dake zaune yake ,
"wai Sa'id sai yaushe zakayi hankali ne , ? Kullum kana girma kana cin k'asa yanzu miye Haka kakeyi agaban k'annenka , cewar Ummu ,
"Ai fiye da hakama zanyi Ummu don yau babban Yaya zai Mana babar kyauta a gidan nan ,ke bama shi kad'ai ba ai harke sai kin mana kyauta Ummu , yafad'a Yana k'ara washe baki,
"Yawwa Yaya Sa'id tasamu kenan na k'araso cewar Salma ,
Aikuwa dai 'yar k'anwata don yau na samowa Yaya Farincinshi , yau dai na tak'ark'are na Nemo mashi Noor dinshi da yake ta k'ulafuci akanta ,
Dagaske !! Duk suka fad'a a tare , gyad'amasu Kai yayi yace Allah da gaske nake Ummu ........ Ai baiko k'arasa ba Salma da Zainab suka buga wani irin ihun murna kamun su ruga da gudu waje wajan da *Abdul Hakeem* yake , tun daga nesa ya hangosu sun nufo wajanshi a guje , girgiza kanshi yayi Yana wannan tsadadden murmushin nashi da akullum baya rabo da fuskarshi ,
Cikin tsananin murna da zumud'i suke fad'in "Yaya da gaske ka gano Mana antynmu ? Fad'ad'a murmushinshi yayi sannan ya gyad'a masu Kai alamar Eh , aikuwa nan suk'a fasa ihu tareda rungumeshi sai faman murna suke kamun Kuma su sakeshi sukayi wani 'bangare dake gefen hannun damasu aguje , da kallo ya bisu cike da k'aunar Family shi Yana matuk'ar son k'annenshi sosai Kamar yadda suke kaunarshi da kaunar farincikinshi, a hankali yafara takawa ya nufi cikin gidan ,
Wai da gaske kakeyi Sa'id ? Allah Ummu da gaske nake aikinsan bana irin Wannan wasan , tace " to Ina na sani tunda nasan halinka Sarai ,ka mayar damu wasu kakanninka , suna haka yayi sallama ya shigo ,
Abu ne ya d'ago da kanshi yana murmushi ya amsa mashi , tunda suka Fara magana baice komai ba sai yanzu da yaji sallamar Dan lelenshi ,direc wajan Abu ya nufa har k'asa ya durk'usa cikin sanyinshi Mai tattare da nutsuwa yace "Abu sannu da gida ya k'arfin jikin , ?
"Alhamdulillah Abdul Hakeem ,naji wani daddanan labari abakin wannan Sudan da gaske ne ?
Cike da jin kunya ya d'agawa Abu Kai alamar amsawa, murmushi Abu yayi kamun yace to Alhamdulillah yanzu damuwa ta k'are da fatan ka gano ko Yar gidan waye, sadda kanshi yayi kamun yace Abbu a makarantar mu take karatu zanyi bincike akanta a hankali Zan gano ko Yar waye Amma kamun nan zanyi k'ok'ari Naga mun fahimci juna da ita kamun maganar takai ga iyayenta ,
" To shikenan Allah yasa adace sai a zage dantse aiki ya samu maza duk wanna sanyin naka sai ka ajiyeshi a gefe indai Mata ne ya k'arasa maganar da zolaya ,
Daga Ummu har Abdul Hakeem da Sa'id dariya sukayi kamun nan sukaci gaba da tatauna nawa akan Noor 🙄😹 (Ina ruwan zafi gangamau koda yake aure rabo ne bansani ba ko shine mijin😹😜)
____________________
Aguje ya shigo falon yana kiran Mama Mama!! Mamah Hafsee dake zaune a falonta cikin shiga ta alfarma kallo Daya zaka Mata ka dauka wata matar Governor ce saboda yadda ta goge sosai da iya ca'ba ado abunka ga kyakykyawar bafilatana ,Sam bazakace ta ajiye Kamar su Huzna ba , ta d'ago da kanta ta kalleshi tace " Kai Kuma kaida wa ? Kayo tsokanar ko?
Mama wai anty Huzna ce zata dakeni Kuma banmata komai ba , yayi maganar Yana tunzuro baki gaba *Aslam* kenan autan Mama,
Huzna ce ta shigo a fusace tana sanye da bak'ar dogowar riga wadda ta ditar da shape dinta sosai sai gashin kanta da ya barbazo ya rufe Mata fuska kasancewar ba a d'aure yake ba sannan Sam Huzna batason saka d'ankwali akanta , da sauri ta nufi wajan da Aslam yake zata dakeshi , cikin daka tsawa mama tace " karki kuskura ki dakeshi kinji na gayamaki tunda ke kullum in baki daki yaron nan ba bakyajin dad'i ,
Cike da shagwa'ba tarinka bubbuga kafafunta k'asa tace Wai mama komai zaimun baki gani tsokanata fa yakeyi wallahi wataran sai na 'ballaka a gidan nan ta k'arashe da watsa mashi harara ,
Tsaki mama tayi tacigaba da kallon da takeyi , tarasa irin Wannan fadan na Huzna da Aslam kullum kamar mage da 'bera Sam basashan inuwa d'aya, kusa da mama ya koma ya zauna Yana yi Mata gwalo a fakaice ,
Husna ce ta shigo da sallama , kallon Huzna tayi tace kije Yaya Yana kiranki a waya ,
Wata muguwar harara ta watsawa Husna kamun taja tsaki ta juya tabar falon cike da jin haushi ,
Wani mugun kallo Husna tabi bayanta dashi Wanda Ni kaina nakasa gane ma'anarsa , k'wafa tayi kamun ta juyo da kallonta ga mama , charaf ta kama mama ta k'ureta da ido , nan take ta daburce takama yan kame-kame ,
Zo nan Husna , cewar mama , a hankali Husna ta k'araso kusa da mama ta zauna , kallonta mama tayi da kyau tace " miyasa kikema 'yar uwarki irin Wannan kallon ?? KO kunsamu wani sa'banine ??
A daburce tafara magana tace " aa mama ba komai ba abunda ya had'amu ,
To Amma miyasa kike Mata irin Wannan kallon Mai kama da tsantsar kiyayya ??
Aa mama ba Haka bane kawai inajin haushin abunda takema Yaya Mu'azzam ne , gyad'a Kai mama tayi tace to shikenan Amma duk da hakan ki kiyaye , gyada kawai kamun tace " to mama,
_________________________
Wai Friend mi yake damunka ne duk kabi ka damu kanka akan 'yar cikinka , yo wannan ai da anmaka auren wuri da tuni ka haifi kamarta , ya karashe maganar cike da tsokana , filon dake kusa da Mu'azzam ya d'auka ya jefi Habeeb dashi kamun cikin fushi yace aa ba haihuwarta nayi ba jikanya nayi da ita , banza kawai ai dai na fika tunda Ni har inada wadda nakeso ,
Dariya Habeeb yayi yace to abun harda Gori , to kasha kuruminka Nima zan Nemo tawa cikar wadda tafi taka hadewa nesa ba kusaba ,
Tsaki Mu'azzam yayi yace kaga don Allah banida lokacin shirme ka barni naji da abunda yake damuna,
"To wai yanzu minene damuwar Kuma cewar Habeeb ,
"Yarinyar nan ce take bani ciyon Kai wani lokaci kamar ba itaba zamu zuba soyayya kamar mi Amma wani lokaci haka zata birkice kamar Bata ta'ba sani na ba Haka zatayita shukamun tsiya kala-kala Allah da a gida nake da tuni na ballawa yarinyar kafafu Naga karshen iskanci ,
Dariya sosai Habeeb yayi yace tooo masoyiyar Kuma zaka cirewa kafafu , kaifa wannan zuciyar ita ce matsalarka kacika zafin zuciya ai Haka Zaka dinga lalla'bata sai kaga kamun katashi komawa komai yy normal
Hmmmm bazaka taba ganewa ba Habeeb Ni kadai nasan abunda yarinyar nan kemun , a da nadauka k'urciya ke damunta Amma yanzu na tabbatar da gaske Bata kaunata , abunda kawai nakeson na sani shine miyasa wani lokaci zata nunamun kamar ba Wanda take so da muradi kamar Ni , miyasa wani lokaci take nunamun so kamar zata lasheni miyasa wani lokaci Kuma take fitomun da asalin kiyayyar da takemun Wanda har hakan ke sanyani tunanin Anya itace kuwa !???? Yarinya sai kace aljana yak'ara maganar cike damuwa ,
Abunda Mu'azzam bai sani ba shine a duk lokacin da ya Kira Huzna mafi yawa Husna ce ke daukar wayar a matsayin Huzna haka zasu shafe dogon lokaci suna zubama junansu kalaman soyayya , duk lokacin da akasamu akasi Kuma Huzna ta dauki wayar to a lokacin ne suke tafka tsiya kala-kala .................✍🏼