Chapter 27
by @mamanyusuf
🅿️ 27
Lak'ace masu hanci yayi yace Wai ku haryanzu bazaku girma bane , suna dariya sukace welcome yaya munyi kewarka sosai ,
....Nima nayi kewarku sosai yan k'annena,
"Ni bakuyi kewata ba ,sukaji anfad'a cikin wani irin salo , da sauri suka juya don ganin waye , Habeeb ne abokin Mu'azzam da tunda su Husna suka k'araso ya kafesu da ido Yana kallon tsantsar kyau musamman ma Husna ba k'aramun burgeshi tayi ba sai dai Yana tunanin ko itace Huznan da Abokinshi ke mutuwar so , idan kuwa itace to tabbas baiga laifin Abokinshi ba don ta cancanci asota doli duk Wanda ya sameta a matsayin Mata akirashi da Mai *Sa'a* idan kuwa ba ita ce Huzna ba to tabbas shikam yasamu matar aure sai yaga abunda ya turewa buzu nad'i,
Gayar da Habeeb sukayi suna dariya shima cikin dariyar yake amsa masu ,dai dai Nan suka k'araso wajan su Abee, da gudu Mu'azzam ya karasa wajansu ya rungume Abba yana dariya , cike da farinciki da wata irin K'auna Abba ya rungumeshi shima , yanajin wani sanyi azuciyarshi , shi kanshi Yana mamakin irin son da yakema Ibrahim Mu'azzam , nan suka shiga gaishe gaishe inda Yaya Mu'azzam ya gabatar masu da baban Abokinshi Habeeb Wanda d'a ne ga Goavernor Lagos Alhaji Nasir Bashir (NB ) , kamun suka dunguma suka shiga motocinsu suka dauki hanyar gida ,
Wanda har wannan lokacin Huzna Bata kalli inda Mu'azzam yake ba bare ta gaisheshi , Yana kula da ita Sarai don ba k'aramun k'ona mashi Rai tayi ba , ya rasa da ubanwa take waya tun d'azu dar zata kasa zuwa ta yi mashi sannu da zuwa Yana ganin sai ajiye So a gefe yayi mata dukan tsiya sannan zata dawo hayyacinta don ya kula yanzu ba k'aramun raini tayi Masa ba , k'wafa kawai yayi Yana tunanin abunda zai Mata ya huce ,
Habeeb kuwa gaba Daya yashiga damuwa sai faman addu'a yake allah yasa wannan da yagani ba itace wadda Abokinshi ke so ba , don shi Sam baikula da wata Huzna ba ,
Lokacin da suka Isa gida tarba sosai Mamah tayi masu kasancewar ita bataje ba da ita da Umma ,
Umma ma sosai ta nuna murnar ta duk da taciki na ciki don har yanzu tanajin ciyon yadda yaran Mamah ke samun daukaka ko ta wane fanni musamman Mu'azzam tafijin haushinshi akan kowa kasancewarshi namiji Kuma babba a gidan , gashi ita batada namiji ,matan Kuma har yanzu sun kasa zama wani Abu saima tarin matsaloli ,kowace da matsalar da take fuskanta agidan aurenta Wanda ita Umma tana ganin Kamar asiri akayiwa yaranta shiyasa rayuwarsu ta ta'bar'bare Haka , wannan yasa taci alwashin sai ta Rama abunda aka Mata yazama doli ta dauki fansa cikin ruwan sanyi ta yadda ba Wanda zai zargeta,
Na aka baje a babban falon Abee aka Kara gaisawa kamun Yaya Mu'azzam da Habeeb su Sufi part din shi don hutawa sannan suci abinci. Da yake Habeeb din zai zauna dasu ne na kwana biyu kamun ya wuce Lagos , don baima sanarma da iyayenshi zai dawo ba yanason yamasu bazata ne,
Wanka sukayi suka sake shiri sanna suka zuba abinci sukaci a hankali , dukda kowannensu Yana cikin damuwa Amma suna kokarin dannewa , Habeeb ne ya dubeshi cike da siyasa yace "Kai gaskiya abokina ka iya za'be irin Wannan had'ewa Haka , tsabar soyayya harda zuwa ta rungumeka agaban su Abee ko kunya bakwaji ,yayi maganar cike da tsokana,
Tsaki Mu'azzam yayi yace waya Gaya maka itace wannan yar rainin hankalince zatazo ta rungumeni saikace bakasan irin abubuwan da take mun ba .
Wata k'atuwar ajiyar zuciya Habeeb ya sauke cike da wani irin farinciki ji yayi kamar ya tashi ya taka rawa amma saiya danne yace "oh ai na dauka ko itace , to ita wannan din wacece ne ?
" Abokiyar tagwaicinta ce dayar Kuma Hussaina ce kanwata ,
Jinjina Kai Habeeb yayi yace to ita gimbiyar taka Bata nan ne batazo tarbonka ba?
"Wani huci yayi yace taje Mana kawai dai ban Isa tazo tayimun sannu da zuwa bane shiyasa , " ikon Allah Amma Ni banganta ba ,
"Taya zaka ganta tunda Bata damu damu ganta dinta ba ,
To Amma .........hannu Mu'azzam ya d'aga mashi yace kaga d'an jarida tambayoyin sun isheni Haka ka rabu Dani na sarara in k'arin bayani kakeso kaje ka tambayeta ,daga Haka ya tashi yayi shigewarsa bedroom akan gado ya fad'a yayi ruf da ciki cikin tsananin damuwa , daurewa kawai yakeyi Amma yarinyar nan tanason takaishi mak'ura ya kula dai dagaske Bata sonshi ada Yana daukar yarinta ce Amma yanzu ai ta Isa tasan wa takeso indai ta nuna Bata sonshi.har yanzu to zai hakura da aurenta kawai donshi bazai auri maccen da Bata sonshi ba ko wacece kuwa,
Habeeb kuwa bayan Abokinshi yabi da kallo cike da tausayinshi don yasan Yana cikin jarabawar soyayya ,yau kadai Daya hadu da Husna yaji bazai iya rayuwa in Babu itaba bareshi da yayi shekara da shekaru Yana dakun soyayyar Huzna sai yanzu da aski yazo gaban goshi komai na nema ya lalace. Girgiza Kai yayi Yana nema mashi zabi mafi alkhairi a cikin zuciyarshi,
______________________
Wai Kai kam sai yaushe zakayi hankali , Sam baka ganin irin bambancin da ake nuna maku acikin gidan nan , yanzu shi an daukeshi ankai k'asar waje karatu ku anbarku nan Amma ba Wanda ya dauki wani mataki acikinku , yanzu Kuma ya dawo don sakarci sai wani rawar k'afa kukeyi ku ga masu d'an uwa ko , to wallahi kuyi a hankali don in bakuyi wasaba zuwa gaba gaba Daya zaku nemi dukiyar mahaifinku ku rasa ,don nasan yanzu da yayi aure Alhaji zai iya damk'a mashi komai na dukiyarshi sai yadda yayi da ita Wanda alokacin ne zaku gane bakuda wayo wallahi ,
Duk wannan masifar da takeyi suna zaune a k'asa sun sadda kansu basuce komai ba don inda sabo tuni sun Saba da wannan masifa ta Ammi akan Yayansu Mu'azzam kullum idonta na kanshi , kullum cikin kusheshi take sukuma Sam basuga wani aibunshi ba Yana sonsu Yana k'aunarsu to akan mi zasu sauki kiyayya su Dora mashi,
Katse masu tunani tayi da cewa "Kai Aliyu na yanke shawara nabaka nan da sati biyu ka fito da matar aure inason in za'ayi bikin yayanku a hada da naka ,Kuma banason musu Ni nasan manufata tayin hakan,
Tunda tafara magana sai yanzu ya d'ago kanshi , ga mamakin Ammi murmushi tagani kwance akan fuskarshi ,cikin taushin harshe yace "Ai Ammi tuni na samu matar aure dama kwanan nan nakeson in gayamaki to Kuma sai gashi yanzu kinyi magana,
Cike da murna tace da gaske Aliyu ? Kai Alhamdulillah naji dadi wallahi kajima baka farantamun ba irin yau , 'Ysar gidan waye yarinyar ??
Ina fatan dai 'Yar manyan mutane ce kasan Ni Sam banason harkar k'aranta sannan inason komi za'ayi yazamana naka yafi na yayanku tana magana cike da farinciki,
Dam_dam gaba Aliyu yarinka bugawa jin zancan mahaifiyarshi yasan da wuya in zasu kwashe lafiya ,
"Kai nake saurare, ta katse mashi tunani,
.....cikin karfin hali yace ai Ammi 'yar gida ce Kuma nasan kema zakiyi farinciki da hakan , dama Husna ce ta nan gidan kinga zumuncin.............bai k'arasaba yaji saukar tagwayen maruka fau-fau Ammi ta wankeshi da Mari sai huci take tsabar bakinciki Tama kasa magana,
A razane Jamil ya d'ago ya dubeta cikin jin haushi yace " Wai Ammi miyasa kike hakane , aibune don yace Husna yakeso tasssss shima ta daukeshi da Mari cikin masifa tace " Amma dai bantaba ganin shashashai ba Kamar ku to wallahi ba a gidan nan ba Sam ban yarda ba Kuma ban aminceba musamman Kai Mara kunya wallahi zanyi mummunan Sa'ba maka akan maganar nan tayi magana tan nuna Jamil da yatsa , zaiyi magana Yaya Aliyu ya d'aga mashi Hannu akan yayi shiru nan fa Ammi tadinga zuba masifa Kamar Allah ya aikota tana cewa saidai bayan ranta tunda dukkansu sunfison su tare a gidin 'Ya'yan Hafsatu da Hassan , yaran da har yanzu tana tantama akansu in ba mayu bane a cewarta ,
Afusace Jamil ya Mike yafita daga falon nata yabar part din gaba Daya , dama shi akwai shi da zuciya kuma Sam baya shakkar Ammi duk abunda tasashi in har baimashi ba tofa bazaiyi ba ,wannan yasa Basu shiri Sam ,
Shidai Aliyu hakuri kawai yarinka bawa Ammi kamun yasamu ya fice daga part din , dakinshi ya shiga ya fad'a kan gado yanajin kanshi na wani irin juyawa akan mi Ammi zata shiga tsakaninshi da farincikinshi yaran nan tun suna kanana yake son Huzna ya rayu da burin aurenta kwatsam sai ga Yayanshi yayi mashi shigar sauri , haka ya jure ya yak'iceta a zuciyarshi don ya sadaukar da soyayyar shi ga Dan uwanshi , a hankali Kuma sai soyayyar da yakewa Huzna ta rikide ta koma ga Yar uwarta Husna ,to yanzu Kuma gashi Ammi na nema ta jefa rayuwarshi cikin hatsari don tabbas komai zai iya faruwa dashi muddin aka rabashi da Husna ,
Haka ya wuni ba ci ba Sha cikin tsananin damuwa lokaci Daya ya fad'a Kamar bashiba duk yayi wani zuru-zuru,
Duk halin da yake ciki Jamil na kule dashi , ganin irin damuwar da yake ciki ne yasa shi yanke shawarar nemawa Dan uwanshi mafita ,
Bayan sallar Isha'i ne yaje part din Abee , Yakuwa ci sa'a ba kowa a sashen sai Abee da yake zaune a falo Yana kallon news ,
Zama yayi ya gayar da Abee kamun suka Dan ta'ba fira ,
Zuwa can Abee ya kalleshi yace yadai Jamil Naga alamar akwai magana a bakinka ,
Murmushi yayi yace "hakane Abee,
Gyara zama Abee yayi yace to Ina saurarenka ,
".am..am dama Yaya ne ya aikoni wajanka , yafad'a cike da fargaba,
Dariya Abee yayi yace wane daga cikin Yayyun naka, ?
Yaya Aliyu ne Abee,
,,,,Ok Ina jinka,
Dama cewa yayi na sanar da Kai shifa Husna yakeso Kuma yanason a hada auren Dana Yaya Mu'azzam ne,
Cak ta tsaya jin abunda kunnuwanta suka jiyo Mata , a hankali tafara ja da baya tana girgiza Kai har tabar part din kamun taruga aguje cikin fitar hayyaci ,direct dakinsu ta fada kamun tafad'i a k'asa tasaki wani irin kuka ,
Aguje Huzna da Hussaina dake dakin sukayo kanta suna tambayar ta ko lafiya,..............✍🏼
[9/18, 8:31 PM] Maman Yus