HUSNA KO HUZNA

Chapter 28

by @mamanyusuf

🅿️_28





Da gaske kake Jamil ,? Kai Masha Allah Amma naji dadi sosai nasan ko bayan Ranmu zumuncinku zai dore har abada ,Allah yamaku albarka jeka kace Masa gobe in nafito ya sameni a sashen Inna zamuyi magana ,


Cike da farincikin samun nasara Jamil ya tashi yayiwa Abee sallama yabar part din,



Washe gari Aliyu na zaune yayi tagumi abun duniya duk ya taru yayi mashi yawa ,Jamil yayi sallama ya shigo d'akin , kallon Yayan nashi yayi cike da tausayawa yace yay kaje Abee na kiranka a shashen Inna , gyad'a kanshi kawai yayi alamar amsawa kamun ya tashi ya shiga bayi baijimaba ya fito ya Sanya takalmunshi yanufi sashen na Inna ,


Zaune ya samesu a falon Inna ce da Abba da Abee suna kalaci suna fira don wasu lokuttan a sashen Inna suke karyawa , 

Gaishesu yayi kamun ya nemi waje ya zauna ,


Kallon shi Inna tayi tace " Kai halan bakada lafiya ne lokaci Daya Naga ka zabge Haka Kamar wanda ya kwanta ciyo , murmushin karfin hali yayi yace "Kai tsohuwar nan bar kiramun ciyo Ni lafiyata qalau , ta'be baki Inna tayi tace Kai kajiyo don ma kasamu na kulaka , 


Su Abba dai Basu tankamasu ba sunata cin abincinsu , suna Haka Aslam ya shigo direc wajan Abee ya nufa yace " Abee yau Zan rakaka kasuwa kaji, dariya Abee yayi yace to d'an auta yau rigimar ta tashi kenan , Abba yace ba inda zamuje da Kai tunda ko anje Banda rigima ba abunda kakeyi tsokane tsokane da Dan banzan yawo acikin kasuwa , 

Inna tace yo duk tsokanarshi yayi tsokanar yan biyu, ? Dariya Abba da Abee sukayi' Abba yace bar zancan wadan nan yaran har yanzu sunkasa nutsuwa kullum sai sunyi abunda za'a masu magana , Inna tace " yo ai ku kuke sagartasu mussaman Kai Hussain tayi maganar tana kallon Abee, 

murmushi Abee yayi yace ai Inna yanzu yarana sun girma duk aure Zan masu cikin shekarar nan su huta , dariya Inna tayi tace su huta ko mu huta , ai mune zamu huta wallahi , 


Bayan sungama karyawa ne Abba ya gyara zama a dubi Aliyu yace " Aliyu naji sak'on da ka aiko Jamil dashi , shin da gaske kake kanason Husna ???? 


Da sauri Aliyu ya d'ago da kanshi Yana kallon Abee a razane da mamaki ,maimaita maganar Abee yayi acikin kwakwalwarshi *_naji sak'on da ka aiko Jamil dashi_* kenan Jamil ne ya sanar da Abee Amma miyasa yaron nan .........katse mashi tunani Abee yayi da cewa tambayarka nake kayi shiru , 

Cikin rawar baki ya furta eh hakane Abee , 


Daga Inna har Abba ajiyar zuciya sukayi kamun suka furta Alhamdulillah don wannan shine babban burinsu ganin sun hade zuri'arsu waje Daya, Abee kuwa kallon Aliyu yayi yace to ita yarinyar tana sonka ne ? 

Dam-dam yaji zuciyarshi ta buga , a hankali ya furta "aa Abee 'ban ta'ba gayamata Ina sonta ba , jinjina Kai Abee yayi yace " to kaje ka nemi so a wajanta ,inta amince zamufi kowa farinciki inkuma Bata aminceba to ka hak'ura don bazamuyi Mata tilas ba , 


Ai ko ta yarda ko karta yarda aure anyi angama Hussain , cewar Inna,.

    Aa Inna kubari mubi komai a hankali in ta yarda shikenan in Bata yardaba a hakura banason abunda zai kawo Mana wata matsala a family ,kiduba kigani tunda akayi maganar yaran nan Huzna da Ibarahim Basu Kara samun jituwa ba a tsakaninsu bana tunanin har yanzu a kwai soyayya a tsakanin yaran nan ,shikuma aure tubalinshi soyayya ce inba soyayya to karshenta Azo ana samun matsala don Haka Aliyu kaje ka nemi so a wajan Husna inta amince zamu hada bikinku Dana yan uwanku tashi ka tafi ,


Cikin matsanancin farinciki Aliyu ya tashi bayan yayi masu godiya ya fita, direct dakin Jamil ya nufa , zaune ya sameshi agaban tv Yana buga Game , Yana ganin Aliyu ya zabura da sauri don a tunaninshi fada zai mashi , ga mamakinshi sai ganin yayi Aliyu ya zube akan kujera Banda murmushi ba abunda yake Sam yakasa boye farincikinsa , 


K'arasowa yayi kusa da yayan nashi cike da fara'a yace " Yaya ya kuka Yi da Abee ne ?, 

    Wato Kai Jamil Sam baka tsoron Ammi ko ? Sam baka gudun abunda zaije yazo ,inba haka ba nida naso nabi komai a hankali na lalla'bata har ta amince shine zakaje ka gayawa Abee , yanzu kasan irin matsalar da hakan zai haifar matukar abee ya fitar da maganar nan Ammi ta nuna rashin amincewarta? A gaskiya banji dadi ba duk da ta wani fanni ka taimakeni Amma fa Ina fargaban abunda zai iya faruwa ,


Kai Yaya kacika tsoro wallahi insha Allah ba abunda zai faru ai in taga Abee ya dage doli zata hakura ta kyaleka Amma Inka biye ta Ammi wallahi bazata taba yarda ba , don ta dauki burin aurenka ta Dora akan wannan Mata mazan *Laila* yanzu Kamar tip da Taya Haka suke da mahaifiyar Laila shiyasa Naga gara kawai muyi Mata shigar sauri tun basu kasheka da ranka ba don wallahi da na auri irin Laila gara na mutu gwaro yak'arasa maganar Yana dariyar shak'iyanci ,


"Wai da gaske kake Jamil ? Wai mi yake damun Ammi ne? Sai kace Bata ganin halin rashin tarbiya irin na yarinyar nan ! Bata wannan hotel Bata wannan club wannan har matar aure ce yarinyar da kowane Kare da doki ganinsu kake tare ! to Allah ya kyauta nikam da su hadani da wannan yarinyar ai gara kawai su samun guba a abinci naci na mutu yafiyemun sauki, 

Dariya sosai Jamil ya kwashe da ita yace Kai Yaya Amma wlh ka gama da yarinyar nan hhhhhhh Haka dai suka jima suna tattaunawa akan matsalar mahaifiyarsu




Wai Husna mi yake damunki ne ,? Tun jiya kike kuka anyi tambayar duniya Amma kin kasa gayamana abunda ke damunki , cikin kuka tace 

   " Ina cikin damuwa matuka da tashin hankali Hussaina narasa inda zansa Raina naji sanyi , zuciyata Sam batamun adalci ba na kamu da soyayyar Wanda baisan inayi ba Ina matukar sonsa da kaunarsa Hussaina rasashi ba k'aramar barazana ne ba ga rayuwata da lafiyata sai dai Kuma yazama doli na hakura dashi Koda sonsa zaiyi ajalina don bazan taba samunsa ba ,sannan Kuma yanzu sai........takasa k'arasawa saboda wani mugun tari da yaci karfinta , da sauri Hussaina ta dauko Mata goran ruwa ta Bata Tasha sai sannu take Mata cike da tausayawa Kamar zatayi kuka tace please Husna ki sassautawa kanki Mana Taya Zaki dauki irin Wannan damuwar kisawa ranki , tsayama tukunna ta Ina kika Yi saurayin Wanda mu yan uwanki bamusan dashi ba, yanzu har akwai abunda Zaki iya 'boyemana Husna ?


"Ki fahimceni Hussaina doli ce tasa na boyemaku Ni kaina abun Yana damuna Kuma nayi kokari Naga na cireshi a zuciyata Amma abun ya gagara so yayimun mummunan kamu Wanda hakan yakusa haddasamun tsanar Yar uwata wadda banida kamarta a fadin duniyar nan, 


Kallon mamaki Hussaina ta Mata tace bangane abunda kike nufiba Husna kimun yadda Zan gane,


    " Tun da nafara wayo nafara mallakan hankalin kaina naji a duniya ba Wanda yake burgeni Kamar Yaya Mu'azzam , wannan yasa kullum nake manne dashi duk da shi baya Mana da sauki Amma Sam bana damuwa Koda zai dakeni hakan bazai Hana na koma inda yake ba sannu a hankali bayan tsawon shekarru nan na fahimci son sa nakeyi so bana wasaba Wanda yasa lokaci Daya naji na tsani Yar uwata kishinta nakeji sosai , kullum burina da tunani na shine Taya Zan k'wace Yaya Mu'azzam daga hannun Huzna ya dawo da soyayyarshi gareni duk da dai ita din ba sonshi take ba , nayi iya yina Amma abun ya faskara , 

Wannan dawowar da yayi ita ta k'ara rura wutar kaunarsa a zuciyata naji in ban sameshi ba Zan iya rasa Raina , duk kwanakin nan Ina tunanin hanyar da zanbi don ganin Yaya Mu'azzam ya dawo gareni kwatsam jiya sai na yanke shawarar tunkarar Abee da maganar ,duk da nasan za'a ga nayi rashin kunya Amma ban damuba tunda Zan samu abunda nakeso don nasan Huzna Bata son Yaya Mu'azzam abune Mai sauki a dawo da auren kaina , shine....shine....sai wani sabon kuka ya kwace Mata , 


Huzna dake tsaye a bayansu wadda sam Basu san da zuwanta wajan ba , tunda suka Fara magana take tsaye tana sauraren bayanin Yar uwarta ,murmushi ne kwance akan kyakyawar fuskarta wani irin dadi taji Yana tsinkarar zuciyarta tana ganin ta samu damar da zata yada kwallin mangwaro ta huta da kuda.................✍🏼