ABIN DA YA BAKA TSORO

1️⃣3️⃣

by @maidambu41

1️⃣3️⃣

"Sannan!!!" Yayi ta maimaita sannan², murmushi irin na Manyan Sultan yayi yana kallon shi.

"Sultan Mansa kai da nake maka kallon kakan kakana, ashe ragon maza ne a gaba na"

Idan hankalin Alhaji Hamza Mansa yayi dubu toh ya tashi tsoron yasa ya kalli Ali.

"Ba zaka.."

"Ina jin ka Sayyid"

"Ina da wacce nake so ne!" Ya fada a hankali ya zubawa kasa idanu, yana wasa da lallausar kafet din falon.

"Allah ya huci zuciyar ka, Sultan Sayyid bai da hankalin bai san cewa bai da ikon tafiyar da rayuwar shi sai abin da.."

D'aga mishi hannu Papi yayi yana kallon Ali. Duk da cewa sab'a dokar masarautan ce auren bare amma duk cikin jikokin shi babu kamar Ali, yana son yaran tun daga lokacin da Mahaifiyar shi ta haife shi bata samu zarran kallon shi ba, ta koma ga mahaliccin ta, ya dauki soyayyar duniya ya daura mishi. Da wani jikan ne yayi mishi batun niman wata mace daga waje daga shi har iyayen su sai sunci Kaniyar su, shi kuma yaron a tura shi gidan sauya hali, kai kaf masarautar babu wanda yake da zarran cewa Papi yaga mace ko da a cikin gidan sarautar ne.

"Kun daidaita?" Ya tambaye shi cikin so da kauna, da wani irin kulawa.

"Papi!" Sake d'agawa Alhaji Hamza hannu yayi. Baya son yaji kome daga gare shi.

Cikin tsantsan girmamawa ya sunkuyar da kan shi yana me cure hannun shi wuri guda ya ce.

"Bamu gama daidaitawa ba"

"Allah ya maka albarka, kaje ku daidaita sai ka dawo min da zancen ni kuma zan taka da kafana na nima maka auren ta da yardan Allah Ubana"

"Ya Rabbil Alamina ya kara maka lafiya da nisan kwana, Allah ya albarkaci rayuwar ka Papi Nagode Nagode sosai Allah ya baka nisan kwana"

Murmushi yayi kawai daga jin yadda Sayyid yake wannan godiyar jikin shi ya bashi akwai wani al'amari behind abin da ya fada sai dai ya share domin soyayyar Aliyu a zuciyar shi rubutacciyar al'amari ce. Yayi kukan mutuwar surukar shi yayi kukan maraicin rashin Uwar Aliyu a duk lokacin da yazo sashin Sultanah yaji Aliyu na kuka shima gani ake yana kuka har hawayen yana jika mishi kasumbar shi.

Da wannan ake girmama soyayyar da Papi yake yiwa Aliyu.


Masarautar Mali.

Gida biyu ne akwai Gidan Mansa, Akwai gidan Kaisa.

Sultan Abubakar Mansa shine mafi shaharan attajirin Sarkin da aka a nahiyar Afirka baki daya, Allah ba tuba bayan karuna ba a kuma wani attajirin mai kudi a nahiyar Afirka kamar Abubakar Mansa kimanin shekaru dari duhu da suka gabata bayan wafatin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da shekaru dubu daya da arba'in.

Abubakar Mansa yana da mata hudu da kwakwaran guda dari da ashirin, a yadda tarihi yazo, sannan daga matan shi har kwarkwaran shi suna wanka da adon zinari saboda Allah ya albarkaci kasar Mali da zinari da gishiri. Duk inda gishiri yayi yawa zaka samu akwai zinari a kasar ta.

Hatta Yaran Abubakar Mansa suna rayuwa cikin zinari da gwala-gwalai. Domin kuwa ko bayin masarautan sun shaida haka.

Ya jagoranci mulkin shi bisa adalci da kyautatta al'ummar shi.

Abubakar Mansa yana da Kanin shi wanda a lokacin shine wazirin shi, wato Musa Kaisa. Shine ya amshi rikon kwarya masarautan bayan tafiyar Aboubakar mansa aikin hajji, a lokacin ya haɗa rundunar mayaka da bayi da bororo tare da tarin dukiya me masifar yawa, suka keta sahara.

Masana ilimin tarihi sun tabbatar da cewa Abubakar Mansa yayi alkhairorin a sauran ƙasashen afirka kafin ya shiga saudiya.

Bayan tafiyar shi a hanyar dawowa ajali ta riske shi. Bayan rasuwar shi Kanin shi Musa Keita ya cigaba da rike mulkin har ya koma ga Allah kafin aka bawa Abubakar Mansa.


Har zuwa kan Papi me suna Adam Aliyu Mansa. Shine ya haifi Yara bakwai cur maza da mata mazan hudu matan uku. Alhaji Hamza shine da na biyu a dakin shi,.akwai Ibrahim, Dawood, Usman, Unisu, sai Khadijah da Kharimatu sai Ubadatu.

A cikin familyn bangaren Gidan Kaita akwai ta can mahaifiyar su Aliyu ta fito, akwai maza uku a dakin su Maman Aliyu. Abubakar Kaita, Hashim Kaita, Jamilatu Mahaifiyar su Aliyu kenan, sai Ridwan Kaita.

Akwai kuma wasu ɓangarori gidan akwai yan uwa waɗanda suke jiran sarautar ta dawo gidan su ko hannun su, suma Mansa ne da kuma Keita.

Mahaifiyar Aliyu da Mahaifin su auren zumunta ne aka musu, sai akayi dace suna son juna, sun haifi yara shida(ba sai na kawo muku ba, ku duba can pagen farko) kuma a zahirin gaskiya auren zumunta ake a cikin masarautar ba a auren bare, sai dai ko ƴaƴan attajirai su auri Yan matan gidan, amma da matukar wahala yara mazan gidan su auri mace daga waje.

Haka tsarin masarautar yake dukkan su yan uwan juna ne.

--- Bayan Aliyu ya bar Falon Sultan ya shiga cikin gidan wurin kakanin shi ba karamin rawan jiki Nadrah take ba, shi kuma ya tsane ta tun daga kasar zuciyar shi ne. Dan haka can iyayen su maza suka shiga bangaren Papi anan suka juyo labarin Sayyid yayi rejecting din auren Nadrah, kuma har Papi ya bashi damar kawo wacce yake so. Abin ya basu mamaki da kuma da tsoro lokacin da Yayun shi maza suka ji labarin tsare shi suka yi yaki fada musu wacce yarinya ce, sai yace su taya shi da addu'a kawai idan suna son shi. Yes suna sun kanin nasu amma suna tsoron Amincewar Papi.

Da ya gama cin abinci ya wuce bangaren shi, ya dauki hoton Maram ya zuba masa idanu, jin ana tab'a kofar ya mayar inda yake, Nadrah ce ta shigo fuskar ta Jajjur.

"Sayyid!" Ta kira sunan shi cikin shashekar kuka.

"Ka gaya min me na rasa da zaka gabatar da wata mace bayan Ni?"

Harde hannun shi yayi a kirji yana mata kallon mamaki, yarinyar da bata gama fita a hanji ba ita ce a gaban shi.

"Fita kafin na miki dukar da sai kin kusan mutuwa" ya fada a sanyayye muryan shi mara amo da kwaraniya.

Hawaye ya bin fuskar ta, ta juya tana kuka. Kamar zararriya wacce me sa'a ce ta dauke mata Mafarkin ta. Tun tashin ta, take kwadayin shi, Sabida haka ta roqi yar uwar ta suka tafi nijar, wato matar baban su Aliyu. Duk kulawar da ya dace ta samu a wurin shi sai gashi, wa wata shegiya yar Mahaukaciya yake bawa. Tasan dai sun bar Nijar Amma soyayyar shi bata bar zuciyar ta ba, shi yasa koda aka dawo dasu an hada ta aure da dan wani dan uwanta, amma tayi ta ciwo kamar zata mutu, dole Papi ya kirata shi da ita ya tambaye ta waye take so, domin da zaran an d'aga bikin zata warke. Baya iya gaya mishi ba domin fada mishi wanda take so kamar ZUBDA mutuncin shi ne ya zab'a mata miji amma taki amsa sai wanda ranta yake so.

Dakyar da rarrashi aka samu ta fadi wanda take so, shima din Matar Baban Aliyu aka saka dan tana yawan zuwa wurin ta, koda aka gayawa Papi bai ce kome ba, sai ya haɗa Kamal da Kanwar Shkura me suna Bahijja.

Aka yi bikin ita kuma aka tsayar da maganar da Aliyu, kuma shima Papi ya amshi haka ne domin dan gaban Goshin sa take so, amma bai boye ba idan har Aliyu yace baya son ta ba zai tab'a mishi dole ba. Dan haka bayan fitar Aliyu ya kira yaran shi da na yan uwa ya gaya musu Aliyu yana da wacce yaƙe so.

Wannan kenan

A bangaren Aliyu sam bai ji ko dar ba, sai ma kwarin gwiwar da ya samu dan haka ya shirya Tsaf domin tunkarar kowacce matsalar da zata zo mishi.

---

Washi gari

Yake gaya musu zai tafi niger, domin aikin shi.

"Sayyid da wuri haka?" Yan uwan shi suka tambaye shi, dake a wurin karyawa ne kuma a babban Falon Papi.

"Eh kasancewar aikin ya dace na koma wata sati toh ina son idan na tafi da wuri na nime masauki da apartment din da zan zauna da sauran su. Kafin nan da sati biyu na koma bakin aiki"

Ya fada yana fatan kar wani ya kawo mishi cikas.

Kamar daga sama ya tsinkayi muryan Papi.

"Na baka nan shekara ne zuwa! Yau nawa ga wata?" Ya tambaya, har rige-rige ake a duba agogo da kakansa.

"Sha biyar ga watan Maris" suka fada bakin su a haɗe.

"Ranar sha biyar ga watan Maris ka dawo min da yadda kuka sassanta kan ku da yarinyar da kake so, idan naji wani abu bayan hakan." A hankali ya dogara sandar shi ya mike.

"Allah ya tabbatar da alkhairi" ya fada yana barin Falon, gaban Aliyu ya fara faduwa shi ko ya gaya musu gaskiya? Kai bari ya nimo soyayyar ta ba zasu mishi auren dole ba.

"Hmm da dai ka hakura da ma ko wacece ka rungume Nadrah wallahi da yafi maka"

"Tunda ya amince meye naku a ciki ne don Allah ku bar shiga abin da babu ruwan ku" inji Yayan Abban su ya fada.

Jikin shi ya kara yin sanyi domin ya fahimci baki daya babu me yin ra'ayin shi sai Papi..

GARIN BAYERO

Babu abinda ya sauya a rayuwar ta, sai Alhamdulillahi, a yanzun da ta fara hankali da girma ta fahimci, ƙaddaran ta yana lullube da ita ne kamar hijabinta, sannan bata jin zata iya kalubalantar Mahaifiyar ta, da take cikin lalura, soyayyar gaskiya da take hangowa a cikin kwayar idanun ta, ya ishe ta bata jin zata kuma fushi da zanen ƙaddarar ta. Dan haka ta shiga harkokin rayuwar ta kawai, har Baaba me kosai ta fita takaba, itama ta kuma cigaba da fitowa suna barin yarinye a gida, duk da ba ta fita ko ina domin tun da aka kawo ta gidan bata tab'a fita da kanta ba, sai dai a fitar da ita kamar zuwa asibiti.

Bayan fitar Baaba takaba Baaba Jumalo ta koma Maradi, dan ta gayawa Baaba cewa ai yanzu tana aikin agent ne na kai masu aiki birni a can maradin, shi yasa zata koma kuma cikin yardan Allah zata na zuwa tana ganin su.

Da wannan ta musu sallama ta bar garin Bayero, cike da kewar su. Aka koma Rabe da Baaba me kosai, sai Meriama, idan rana tayi sai ta dawo gida ta zauna wurin Mamanta, kafin su Baaba su dawo.

Wani abun burgewa tana dawowa zata dibi ruwa ta daura akan wuta ta share gidan ta gyara ko'ina tana juye ruwan zata kai Maman ta ban daki ta wanke ta tass, sannan ta dawo da ita daki ta shafa mata mai.

Sannan ta saka mata kaya,idan kuma ta gama ta tsefe mata kai ta kitse, mata shi tass sai kaga uwar kamar ba ita ba. Haka yasa take rage damuwa sosai.

Ana azahar zasu dawo lokacin xata shiga makaranta tana koyar da yara, tun ana mata kallon yar Mahaukaciya shegiya mara uba, tana kuka tana faɗin ba zata shiga cikin su ba, yanzun ta kai idan ka gaya mata sai tayi murmushi, ta koma shanye batancin mutane duk da ba abu me sauki bane, amma a wurin ta tana ganin me sauki ne a wurin Allah.

Hakurin ta da kawaicinta ya kai matakin da zai yi wuya ka ga bacin rai a shimfida a fuskar ta.

Wani irin sanyin hali gare ta, bata tab'a daukar rayuwa da zafi ba, bata taɓa kallon abin wurin wani da wani kyau ba, kullum tana jikin Baaba da Mamma ko Kawu Rabe, gashi Allah ya bata kaifin basirar da matukar zaka zauna da ita idan har wani yare gare ka, sai ta koya koda kuwa ace Jefi-jefi kake yi sai ta dauka, idan ta juya harshen French kuwa, kamar Baturiyar faransa ita kanta har girmama yanayin ta take, su Ghali sunyi sunyi ta koma makaranta ta ce a'a wannan ma da tayi ya isa ba don son su ba, haka suka hakura ya cigaba da rayuwar ta cikin Masoyan ta da suke hanawa tayi kuka, kuma Alhamdulillahi kukan ta ya kare.....


_Books din da zasu zo kamar haka_

1- Sahla A Paris

2-Bani Da Laifi

3-Abin Da Ya baka tsoro.

Dukkan su Uku 1k

_Guda daya_ 350₦

_Guda Biyu_700₦

_Guda Uku_ 1k


_Zaku iya payment ta to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria_

_and send evidence to does number_

*****

Or

**** or ****

_Dukka zaku iya tura shaidar biya_


_Ga masu turo katin MTN zasu iya turawa Zahrahn Addah Ramlat da kuma Yan Nijar zasu turawa Nana A'ishah_


**** a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah

*+22784506476*


_Welcome ta Top-notch Team_