Episode 1
by @zulaihat
KUSKURAN FARKO
KASHI NA DAYA
Da sunan Allah Mai Rahma Mai kin Kai.
Zubo Mata idanuwa yayi Kamar abin na son ya ba shi dariya, ganin yadda take kallon fuskarta a madubi kamar wacce aka Yi wa gorin kyau. Hada ido suka Yi lokacin da tamaida kallonta gare shi."Walahi Gwaggo da gaske ne yanzu Kam na yarda" kasa magana Gwaggo ta yi domin wannan karon sakarcin Nur ya soma fusata ta.yayin da shi murmushi ya kwace masa. Jikin Gwaggon ta dawo ta manne kafin ta dan sunkuyar da Kai tace"Yaya Nura Ina wuni?" Bai daina murmushinsa ba ya amsa mata "Au Ashe ma kin gane shi?" Haha Gwaggo kowa fa cewa yake yaya Nuran mama sa'a Kamar mu daya da shi. Ga shiKuma zahiri na gani"Gwaggo ta wangame baki"Dama shi yasa Kika dauko madubi kina wani dube dube Kamar wacce ta warke makanta?" Shima tsananta kallonsa yayi gare ta, tabbas yarinyar tayi Kama da shi matuka, wani Dan rausaya kai yayi cike da al'ajabi"To yanzu kin amince fuskar maza gare ki?" Gwaggo ta tambaya. Ta Dan turo baki tare da fadin"To ya na iya da samarin kakata"wannan karon Kam Saida ta sa shi ya dara."Je ki kawo Masa ruwan sanyi sarkin magana!" Ta Mike da hanzari ta fice ya raka ta da kallo"Wacce ita Gwaggo?" "Nuriyyah ce fa yar wajen kawu karami. Ba zaka gane ta ba ai tunda rabon ka ita tun ranar sunan ta. Ga ta Nan har ta kare kwaleji,Amma kan ba onga"Dariya sosai yayi "Kai Gwaggo! Gaskiya na dade rabona da Katsina.lallai jini ba Karya bane dubi yarinyar Kamar ciki daya muka fito?""Ai ka ga yanzu ta yarda Amma da da anyi magana Sai tayi tsalle gefe tace yama za'yi tayi Kama da maza.sakarci kalakala ta iya ai zaka Sha kallo" Suna dariya ta shigo dauke tire komi na bukata ta jero su tsaf ta dire a gabansa sannan ta tashi ta fice.
Yana Kora ruwa suna tambayar juna bayan rabuwa har kawu Iliya ya dawo.Kawu malam suke kiransa.kamar a mafarki ya ke ganin Alh.Nura.Basu Gama gaisawa ba aka kwala Kiran sallar magariba don haka su ka Yi alwala suka give masallaci.
Bayan sallar ishai su na tare da kawun a dakinsa"Ba karamin farin ciki na Yi ba da ganin ka Nura." Ya gyara Zama ya sassauta murya" Ku Yi hakuri kawu Nima ba a son Raina na daina zumunci ba Amma insha Allah daga yanzu komi zai gyaru kullum Umma Tana min maganar dangin mahaifiyata Kuma wallahi ba mantawa nayi da ki ba kawai lalurori me suka jagule min." Na sani Nura, ai Rashin Mata uku a jere ba karamin Rashin hankali bane.muna rausaya maka ga maraici ga wannan kadddara da sauko maka." Zufa sosai ke kwarara cikin jikinsa saboda kalaman kawu sine kalamai mafiya Muni a gare shi Sam baya son tuna su Sai dole shi yasa ma ya kasa furta komi,numfashi kawai yake maidawa da kyar.
Ma su karatu yanzu fa aka Fara don haka a loda data!