Episode 3
by @zulaihat
KUSKURAN FARKO
BABI NA UKU
NA
ZULAIHAT SANI KAGARA
Tsawon dakika biyu suna kame kafin kawu ya dawo hayyacinsa," Kina da hankali kuwa Nur?" "Ina fa! Kai ma dai ka San mai hankali ba zai Yi wannan furincin ba! To kin ga fito daga motar Nan don ba za ki tafi ki na masa Shashanci irin na ki ba. Maza maza ki yo waje!" Gwaggo ta Karasa zancen ta cikin tsawa tare da bude murfin motar. Nan da nan idanuwan Nur suka raina fata, da ka dube ta zaka gane ta amsa laifin ta," Don Allah Gwaggo ku yi hakuri,wallahi ba da wata manufa na fadi maganar ba wasa ne kawai" Kawu ya kara fusata" Wasa? Shi abokin wasan ki ne don...." Alh.Nura yayi saurin kase shi,"A'a kawu magana ta gaskiya mu abokan wasa ne..." Shima ya katse shi" Don ku na abokan wasa sai ta Yi maka irin wannan?" "Ni dai malam ta fito kawai Kai ka je ka raka shi."Fuska sake yake magana" Ni dai da ita na shirya tafiya Gwaggo,don Allah ki bar mu wuce Kar rana ta Yi" Gaba dayan su hararar ta su ke Yi yayinda idanuwan Nur suka cika dam da ruwan hawaye."Rufe mu wuce Nur " A kasale ta jawo murfin ta rufe.Ya tada mota su ka wuce su ka bar su kawu be tsaye cike da takaici.
Bakin Nur gum kamar ruwa ya ci ta a cikin motar babu mai magana har ya gama cika but dinsa da kayan tsaraba sannan ya ci gaba da murza sitiyari. Kamar daga sama ya ji muryar ta a raunane"Don Allah Yaya Nura ka Yi hakuri." Bai kalle ta ba y a soma magana"Hakuri? Kika ce na Yi hakuri? Ki Yi min kazafi kuma ki ce na Yi hakuri? To bari na gaya mi ki ji, Ina yafe kowanne irin laifi Amma ban da kaz afi!" Idanuwa waje take dubansa kuma tuni tsoro ya mamaye fuskar ta" Don..." Da sauri ya daga Mata hannu" A kul Kika kuma hada ni da Allah! Me na Yi miki? Jiya jiya jiya fa kika fara gani na amma kika jefe ni da mummunan kalami. mene ma Gwaggo tace kina da shi? Sakarci ko? A,a wannan ba sakarci ba ne Iskanci ne!" Ya dafa tare dukan sitiyari, har cikin zuciyarta tafirgita cikinta ya duri ruwa hawaye kawai ke ambaliya."A karo na farko da na shiga masauki na na gan shi tsaf kamar da injin aka gyara shi, take na Yi zaton ke mai hankali ce ashe cikin be kan ki ba kwakwalwa ba ce dashen dankali ne! To bari ki ji idan ma sakarcin kike takama da shi ni Nura na dama ki na shanye shekaru ne suka sa na adana ma Yaya! "
Uhmm! Lallai Nur ta Kira ruwa! Da fatan zaa Yi hakuri da abinda ya samu. Mu Tara gaba