KUSKURAN FARKO

Episode 4

by @zulaihat

KUSKURAN FARKO

    BABl NA HUDU

         NA

ZULAIHAT SANI KAGARA


  Kara rushewa tayi da kuka Mai tsuma zuciya shi kansa Sai da ya ji kasala ta kama shi, ya runtse ido Jim ya bude "Malama kin fa dame ni da hayaniya hakan Kuma ba Zai taba kubutar da ke ba! Dole ki ban hujjojinki wadanda zasu tabbatar da cewa ni ke cinye Mata na, idan ba haka ba Kuma....." Ki yayi ta katse shi cikin shashahekar kuka,"ka Yi wa girman...."cikin tsawa Shima ya katse ta,"Ba na ce ki daina hada ni da Allah ba! Ji nake tamkar kina watsa min garwashin wuta!Kamar na shake ki na jefar ta taga saboda tsanar da Kika dasa min! Shin wai ma kin ga na Yi kama da kalar auranki? Idan ba ki sani ba to ki sani, banbancin na da ke misalin sama da kasa ne ko kusa ma Kar ki soma tunanin wata alaka za ta iya shiga tsakanin mu! Da sauri ta ja mayafin ta ta rufe kan ta ruf tare da makurewa jikin kujera ta saki wani malalacin kuka tare da fadin" Na shiga UKU!" Ya ja dogon tsaki ya canja giyar mota kafin yace" Aikin banza! Na dai Gaya miki ki tanadi hujjojinki don ba zan saurara miki ba sai na ji dalilin Yi min KAZAFI"

  Motar tayi tsit ba ka jin motsin kowa Sai ajiyar zuciyar Nur. A hankali ya saci kallonta jim kafin ya saki wani bazawarin murmushi ya sauya harshe zuwa fulatanci,"Yarinya kin kuru, lallai ba ki San waye Nuran Umma ba da ba ki tabo ni ba!" Jin ya sauya harshe ya sa ta kara tsurewa fadi take cikin zuciyar," Na shiga uku ni Kam yau ya zan Yi da Raina? Da na sani ban biyo mutimin Nan ba!"

  Bai sake tanka mata ba haka zalika itama ta kasance a kudundune cikin yafi Bata aikin komi face kwararar hawaye.Idanuwanta sun Yi Jajir shi kuwa yana ta kwarara gudu lokaci lokaci ya kan saci kallonta yayi murmushi har suka fara jiyo kamshin Dutsin_ma.Ba zato taji ya taka birki yayi fakin gefen hanya. Duk da haka Bata iya daga Kai ba balle ta yaye fuskarta. Ba ta ma San ya fita daga motar ba sai da ta ki am bude murfin gefen ta"Malama fito waje!" A zaton ta sun kawo me don haka ta dago da kwarin gwuiwar ta ta gudu cikin gida Amma me? Sai ta gan su cikin daji.Tsoro ya Kara rufe ta shi kuwa kallo daya yayi Mata dole ya kauda fuska,tausayinta sosai ya Kama ko wanne sako na zuciyarsa.Goran ruwan da ke hannunsa ya Mika Mata"Ungo Nan maza ki wanke fuskar ki!" A tsorace ta karba har hannunta na karkarwa ta tsugunna ta wanke ba tare da ta nemi wani ba,asi ba don ba ma zata iya ba.A mota ta same shi ya kare mata kallo kafin yace" oya! Maza bude jaka ki kwaso kayan kwalliya"Wannan kalami yasa dole ta dube shi suka hada ido sosai,"Eh!cewa na Yi ki sauya kwalliya!ko kuwa so kike mu je can a gane kin Yi kuka ki sake manna min wani sharrin?"A razane ta kada kai"To maza! Na San jakar Nan cike ta ke da kayan make-up." Akan dole ta fiddo hoda ta shafa.Ta na kokarin rufe jakar ta yace,"Malama saura Jan baki!" A hankali ta Dan cinno baki kafin ta dauko ta goga sai ga ta tsaf kamar da. Ya Dan lumshe ido bude, Ya sa ke sauya harshe," yarinya yau Allah ya hada ki da Nuran Umma, kin ga ko banza Nima na nuna miki nawa kalar sakarcin" A hankali ta sake dubansa wannan karon batai nasarar gani nasa idanuwan ba domin yayi saurin janye su hakan ya ba ta damar antaya Masa harara tare da murguda baki"Don Allah dube shi wai kamar mu daya! Mugu kawai."Ganin Yana shirin juyowa yasa tayi saurin kauda kanta har yanzu bakin ta a tire ya yake.yayi Jim yana kallonta Shima Yana zancen zuci" Da gaske kamar mu daya Sai dai ni ba na turo baki! Ga Kuma ya Kara Mata kyau!" Shima Dan turo bakin yayi daidai Tana waigowa don haka ya janye da sauri ya murza makulli mota ta tashi,"  kwaikwayo na ma yake?" 

  Ba zato ya waigo karaf suka hada ido da hanzari ta dauke na ta, yayi Dan gutun tsaki"Mai fuskar maza kawai!" Bata dube shi ba take zancan zuci" Ji wannan! Har ma Yana da bakin magana, ni ke kama da maza ko shi ke kama da mata?cikin biyu dai dole akwai daya" Ta Kara cinno baki cike da tsiwa.


   Ma su karatu ko akwai Mai amsa tambayoyin Nur? Mu hadu a Kashi na biyar da yarda Allah!