SALMA

Part 5

by @meenatyandoma

👽 *SALMA* 👽

    (HORROR STORY)

  

   _NA MEEN@RT A YANDOMA_



*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

       *M. W. A*


```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ```🤙🏻

***

________________________

*NOTE* Labarin Salma nina kirƙiri abuna, aguji juya mani labari ta kowa ce Siga sai da izinina.



*NA KUƊI NE, KI TURO 300 TA WANNAN ACCOUNT ƊIN AISHA ABUBAKAR 2151366600 UBA BANK, KO KATIN MTN TA WANNAN NUMBER ****



*BANYI ALƘAWARIN YIN FREE PAGE DA YAWA BA, SABODA LABARIN NADA YAWA, HAJIYA KI BIYA KUƊI KISHA LABARI* 🤷🏼‍♀️🤷🏼‍♀



*TALLAH!* *TALLAH!!* *TALLAH!!!*


*MEDICATED SOAP!* *MEDICATED SOUP!!* *MEDICATES SOAP!!!*


*Ina kuke mata ƴan kwalisa uwayen gida amare har ma da ƴan mata, masu gurin ƙayata fatarsu musamman alokacin sanyin nan, da kuɗinki ƙalilan zaki sayi sabulun da zai gyara maki fatarki tayi haske laushi gami da ƙamshi,* *MEDICATED SOAP yana gyara fata yafidda tabo, ya kashe quraje fata tayi subul💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽 price roba 700 only akwai discount ga yan sari💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽 Macen da tasan kanta ita ke gyara jikinta ta fito fes tamkar wata amarya ta yadda mijinki bazai samu damar karo maki wata ba 😜 To mi ma zai kaishi gashi da haɗaɗɗiyar mace wadda tasan kanta take gyara, in kin shirya hajiyata katsina muke da zama muna aikawa ko ina, ki kira wannan number Domin naiman ƙarin bayani ***, sayen na gari maida kuɗi gida sai mun jiku.*




*FREE PAGE*

*PAGE 9️⃣__1️⃣0️⃣*

........Juyin duniya anyi amma Baƙuwa taƙi bada jinjirar.


Kowa ya sadaƙar bazata bayar da jinjirar da keta tsala kuka.


Agaban Mairamu Baƙuwa dake Darzar kukan rashin ɗiyarta Baƙuwa ta tsuguna hawaye nabin fuskarta.


Janjirar ta miƙo mata tana girgiza kanta.


Cike da tsabar tausayi gamisa Tu'ajjabi suke kallon Baƙuwa.


Yinin ranar Baƙuwa bataci komi ba sai kukan da take anyi juyin duniya amma taƙi sauraren kowa.


Ruwan magani Malam Abu ya ɗebo tarr da tsayuwa tsakiyar kanta ya fara zuba matashi.


Yasalam wato da Malam Abu yasan abinda zai biyo baya to bazai fara zuba mata ruwan nan ba.



Ruwan na sauka kanta ta ƙwala wata gigitacciyar kururuwa ta fara harbe_harbe.


Ba almajiran Malam Abu ba hatta maƙotansu sai da suka firgita dajin wannan kuwwa.



Miƙewa tayi ta shiga farfasa tuƙwanen ruwan da almajirai suka ciccika da ruwa.


Ranar sunga tashin hankali wanda basu ta6a ganin irinshi, mutanen unguwar tururuwa suka rikayi zuwa gidan Malam Abu.


Da ƙyar aka yi nasarar rirriƙeta Malam Abu ya shiga tofa mata addu'a.



Wani bacci ne ya ɗauketa idonta na zubda hawaye.


Gida ya cika da mutane tamkar ana wani shagalin biki ko suna.


Abubuwanda ta 6atane aka shiga gyarawa.



Kasancewar da maraice ne lamarin ya faru sai bayan magariba suka gama gyara gida.


Jaje mutane suka riƙa yima Malam Abu tae da fatan Ubangiji ya bata lafiya.


Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun.


Da malam Abu yasan abinda zai faru cikin daren nan da baiyi gigin yimata wannan addu'ar ba

Duhun dare ya tsala bakajin komi sai kukan katunuka da ƙarar busassun bishiyoyi dake zubda ganyayensu a lokacin.



Kururuwa gami da iface_ifacen mabanbantan muryoyi ne Cikin amo mai rikitar da tunanin bil'adama sautin su ya karaɗe gidan Malam Abu.


Dukkan wani mutum dake da makwaftaka da gidan malam Abu ranar bai rintsaba.



Guguwace mai matuƙar ƙarfi ta taso tare da baibaye dukkan gidajen dake cikin unguwar.........

_______________________________________________

.....Tunda DAVID ya taso shaiɗanin yarone kuma hatsabibi.


Son duniya BANESA da DAVID sun ɗora mashi.



Yanada shekaru biyo amma hatsabibanci wurinshi ba'a magana.



Su kansu iyayensi shakkarshi suke domin gani suke anya ma DAVID mutum ne?.



Kamar yadda MAKEL ya saba duk Marece yana ɗaukar BANEAA da DAVID ya kaisu wuraren shakatawa yauma haka ce ta kasance.



Tun cikin mota DAVIN keso a buɗe ya fito amma BANESA ta matseshi tare da hanashi fitowa.



 Bayan sun isa babban wurin shaƙatawa na ENUGU.



Zaune suke suna ƴan ciye_ciye DAVID na gefensu.


Hankalinsu ya kaɗu ga hurar da suke.


Da sauri BANESA ta jujo tare da tambayar mai kula da DAVID cewar yana ina.



Nan fa bodyguard ɗin ya ankare da babu DAVID a wurin.



Naiman duniya sunyi amma basu ganshi ba nan fa MAKEL ya hau masu tsaronshi da masifa.



Basu ƙara daskarewa ba sai da suka hango DAVID da alokacin shekarunshi biyu ya nufo inda suke bakinshi jini na dalala.


Maganar wata mata ce ta ƙara tayar masu hankali dake faɗar.

"Ku riƙeshi Mayene, jama'a nace ku riƙeshi Mayene ya kashe ɗiyar mutane ta hanyar cizonta a wuya ya zuƙe mata jini."


Kafin su an kara tuni wasu ƙarti majiya ƙarfi sun danƙe DAVID.


A guje su MAKEL suka rirriƙe DAVID da jini duk ya 6ata mashi baki......

__________________________________

..."Cuwai ba nace kizo muyi waca."

Salma ta ƙara maimaita mata maganar.



A guje Subi ta dawo ɗaki tare da mai da kyauren falon ta rufe.


Numfashi ta shiga maidawa hankali a tashe.



A firgice ta nuna ta da yatsa la66abta har kyarma suke ta furta.

"Sallmah!"



Zaune take bisa daya daga cikin kujerun falon taNa kyalkyata mata dariya.


Subi yau ta riga da ta yadda mutuwarta ce tazo.


Ace ta baro yarinya waje cikin ruwa amma ta juyo ta ganta cikin falo zaune tana sheka dariya abinta.




Cikin dariyar ta mai tayar da hankali ta furta "Cuwaiba kimatsa daga hanya BUSARI shima zai shigo."


A guje Subi tabar falon tare da shigewa ɗakinta ta maida kyaure ta rufe.



Tunda aka fara tsala ruwan Sahabi ke tsala gudu saman kwalta shidai gurinshi daya shine ya ganshi ya ƙarasa gida.



A hankali ya fara tuno abinda ya faru a baya, cikin irin wannan ruwan ne aka bashi kyautar Salma, yarinyar da yake jinta a zuciyarshi tamkar Ɗiyarshi daya haifa.



Yana isowa gida lokacin ruwan ya dan lafa.



Kofar ɗakin Subi ya hau bugu amma taƙi budewa.



Jin ana bugun ƙofar ɗakinta yasa Subi ƙara shigewa ciki bargo tana ƙara tsinema shugaban ƙungiyarsu da haryau sunƙi maida ta ƙungiya.


Ganin bazata buɗeba yasa shi nufar ɗakin Salma dake buɗe.



Kwance take tsakiyar gadonta an lullu6eta tanata sharar bacci abinta.


Sumar kanta ya shafa tare da kulle mata kashe mata haske ya jawo ƙofar.



Makullanshi ya fiddo tare da buɗe ɗakin ya shige.



Jin an buɗe ɗakin yasa Subi kurma wani uban ihun da sai da Sahabi ya firgita.



"Na bani dan Allah Salma kiyi hakuri, babu abinda nayi maki."



Galala Sahabi ya kalli Subi jin abinda take faɗa.



"Ke lafiyarki kuwa, mi Salma tayi maki."?

Subi jin muryar Sahabi ta yakice rufar da tayi tare da nufoshi da gudu.



"Sahabi ka yarda dani Salma ba mutum bace, na barota cikin ruwa ina shigowa falo na isketa."



Kafeta da ido yayi jin wannan tatsuniyar da Subi ke karanto mashi.



"Bayan Salmar da ke ɗaki tana bacci wace kike nufin kin gani."?



Daskarewa tayi jin wannan furuci na Sahabi.



Ita yanzu tana cikin tsaka mai wuya, ga Sahabi asirin jikinshi ya fara karyewa ga Salma da ta sanyoshi gaba ga ƙungiya ta dakatar da ita.


"Ni ki sakeni bacci nikeji."

Ta tsinto muryar Sahabi



Ranar bacci bai ga idonta ba.



Salma nada shekaru biyar Sahabi ya sanyata wata tsadaddiyar makaranta wadda sai 'ya'yan manya masu hannu da shuni ke yinta.


*BUKAR INTERNATIONAL SCHOOL*


Duk faɗin makarantar Salmar kawarta daya ɗiyar mai makarantar Mina Bukar.



Ita ɗaya ce ƙawar Salma wadda suke hira har take ganin dariyarta.



Zaune suke cikin ƙayataccen ajin nasu mai ɗauke da ababen more rayuwa.


Malamine tsaye gabansu



Yana kiyar dasu darasi.


Lura yayi hankalin Salma yana wani wuri tana kallon wurin tana dariya.



"Keeee!"

 Uncle Ola ya Dana Mata mahaukaciyar tsawa.


"Mikike kallon ina koya maku kina wasa."?

Ƙuri Salma tayi mashi tana murmushi



Iyakar ƙuluwa Uncle Ola ya ƙule.


"Ina maki magana kina dariya, mikika maidani."?


Murmushi taci gaba dayi batare da ta furta koda kalma ɗaya bace.



A ƙa'idar makarantar babu bugu duk laifin da ɗalibi zai yi sai dai in abu yayi tsanani akira mahaifin yaro.


Cike da mugunta Ola ya firgo Salma da hannu ɗaya tare da direta gabanshi.



Cikin tsoro ƙawar Salma Mina Bukar ta fara magana.

"Uncle kayi mata haƙuri dan Allah kada ka bigeta."


Bai saurari magana Mina ba.



"Shege yaron hausawa duk inda kake ɗan iskane kai, yau sai na zaneki."

Yana gana faɗin haka ya dukar da Salma tare da yimata kulli mul_mul kakeji.


Ya hada mata da wata zazzafar ƙwanya tsakiyar kai.


Zafin bugun sai da ta Duƙewa ƙasa.


Sai gani Ola yayi ta miƙe tare da tuntsirewa da mahaukaciyar dariya.


A hankali ta furta "BUSARI."

Lokaci ɗaya ajin ya gauraye da wani matsanancin duhu tare da wata ƙara mai kama da tasowar hadari suka gauraye ajin.





*HAJIYOYINA FREE PAGE YA KUSA KAREWA KU GAGGAUTA BIYA KADA AYI BABU KU.* 💃🏼💃🏼💃🏼





*MEEN@RT...✍🏼*

***