ZAMANI... riga kowa da irin na shi
12 last free page
ZAMANI...
*Riga kowa da irin nashi*
Na
Rahma Kabir mrsMG
Wattpad @rahmakabir
Page 12.
*Last freepage*
Mahmood yana jin cewa umma tana kiransa sai ya yi sallama da abokansa ya hau mashin tare da mubarak suka nufi gida. Sun samu umma tana ta kokarin kwanciya ta zauna a tsakar daki Mahmood ya zauna bisa tabarma, Mubarak kuma ya wuce dakinsa. Umma ta kalli mahmood da kyau, har wata yar rama taga yayi ga duhu da alamun akwai abinda ke damunsa, tace cikin kulawa.
Mamuda meyasa zaka yi dare ne? kasan unguwarku ihun ka banza barinka wofi, ko dai har yanzu baka daidaita da saudat din bane shiyasa kake rage lokaci a waje.
Uhum umma ina shirin tafiya Mubarak ya kira ni, kuma babu komai kawai dai na jima ban gana da Malam auwal bane shine na tsaya a shagonsa mu gaisa, sai kuma na tadda abokanmu shine na tsaya muyi hira.
To madallah, amma Mahmood kuma ko kayi rashin lafiya ne naga ka rame kayi duhu, ni duk ban kula ba sai yanzu dana kare maka kallo.
Laaa umma ba komai kawai dai zirga zirga ne na yau da kullun.
To Allah yasa mu dace sai ka tashi ka tafi, ka gaida iyalin.
Mahmood ya amsa da amin kana yayi sallama da ita ya fito ya kama hanyar gida.
Yana isa ya shiga cikin gidan ya rufe gate sai ya wuce falo yayi sallama, baiga kowa ba sai ya rufe kofa ya wuce dakinsa dan yasan yau Saudat tayi fushi dashi bata tsaya jiransa niman fitina ba, yayi shirin barcinsa ya kwanta.
Da safe shi ya shirya yaransa kamar yadda ta saba barin masa shirinsu ko kafin ta fito ya gama komai har sun karya zai wuce dasu makaranta daga nan ya tsaya wajen aikinsa, bai ajiye mata kudin mota ba ya fice abinsa, saudat tana jin fitarsu ta fito tana murmushi dan dama duk ta kosa ya fice, sai ta zauna a falon ta shiga kiraye kirayen waya, ba jimawa masu decoration suka zo suka fara aikinsu, zuwa karfe goma sun kammala sun wuce sai ga kawayenta suma sunzo tare da cake din birthday din, a takaice zuwa karfe daya gidan ya soma ta ruwa da mutane maza da mata, sun gama hada komai a tsakar gidan duk da filin gidan ya musu kadan amma haka suka yi maneji wasu baki suna falonta sun baje sai cin abinci suke yi, gida ya kacame da wake waken banza dana wofi wasu sai rawa suke tika, gida ya koma kamar bana malam Mahmood ba, kamar yadda suka tsara komai karfe biyu za a soma gudanar da shagalin haka kuwa babu african time suka fara, Saudat tasha doguwar rigar shadda light purpul wanda taji aiki sosai, fuskarta tasha makeup mai matukar daukar hankali, haka suka zaunar da ita wajen da aka yiwa decoration da furenni gami da balam balam, mai gabatarwa ya soma jawabi ana tafi tare da sakin wani sauti mai jan zuciya.
Mahmood yana makaranta lokacin yana kokarin shiga ajin matan aure masu zuwa karfe biyu, sai ga kira ya shigo wayarsa yana dubawa yaga makocinsu ne Alhaji Ibrahim, sai ya dauka suka gaisa kan Alh. Ibrahim ya ce.
Malam Mahmood iyalina ce ta kirani ina kasuwa take sanar dani gidanka ana wani shagali, shine nace bari na kiraka nayi maka korafi, ace muna makotaka kiri kiri ba zaka sanar damu ba.
mamaki ya cika Mahmood amma sai ya shanye yace cikin kulawa.
Alhaji kayi hakuri kasan abubuwan ne da yawa na sha'afa.
To to ba damuwa, iyalin ce ta haihu?
A'a wani dai taro take yi a gidan, ita da yan uwanta amma ba karuwa na samu ba.
Allah sarki to Allah yasa alkhairi.
Sai suka yi sallama Mahmood yana Amin tare da yi masa godiya, suna sauke wayar sai ya tsaya yayi shuru yana nazarin me zaisa Saudat yin wani shagali a gidansa ba tare da ta sanar da shi ba, shi shaf ya manta da cewar birthday dinta yau saboda bai dauke shi abu mai muhimmanci ba, haka ya wuce ya dauki mashin dinsa ya mufi gida babu shiri.
Yana isa ya yi parking a waje, jin kide kide kawai ya tabbatar masa da cewar shaidanci ake zubawa a gidan sai ya wuce ya tura kofa ya shiga, abinda ya gani yayi matukar tayar masa da hankali, saboda mata da maza ne a tsakiyar gidan suna yin rawa ga kuma daga inda Saudat take zaune maza da mata sun tsaya a bayanta ana kashe musu hoto, wannan kadai daya gani ya tabbatar masa da shagalin bikin birthday dinta take yi, ransa in yayi dubu ya baci, sai ya shiga tunanin abinda zaiyi ya koma waje ya hango wata bishi ya je ya hau tare da karyo babban rashe katon sanda sai ya dawo ya shiga gidan tare da sanya key ya rufe ya zare, ya tunkari wanjen DJ, ya daga sandar hannunsa ya sakar masa a gadon baya, wani irin kara ya saki tare da bajewa a kasa yana wash, nan take kallo ya dawo wajensu, sai matan suka shiga ihu da karar sauti duk ya karade gidan, Mahmood ya kara daga sandar ya bugawa abin sautin mai bada wakar nan take ya tsaya cak sai gidan yayi shuru da waka sai karar matan, Mahmood baiyi kasa a guiwa ba ya shiga rafkawa duk wanda ya samu sanda, ciki har kawayen Saudat domin suke tikar rawa, duk suka yi kofar gida amma sai suka ji kofa a rufe, wadanda suke cikin daki suka yi ta fitowa ko wanne yana niman wajen gudu, mahmood ya cigaba da binsu yana rafka, Saudat ta isa wajensa a matukar tsorace tana kwala masa kira amma ina bai saurareta ba sai ma buga mata sandar da yayi a hannu, ta tsandara kara tayi gefe a guje, Mahmood duk ya gama jigatasu saboda kamar hauka yayi musu, da yawansu sunyi zaton mahaukaci ne sabon kamu duk da shigar kamala a tare da shi kamu ba suyi zaton mijin Saudat bane, sai kawayenta ne suka shaida shi wanda yayi matukar basu mamaki, Mahmood sai da ya gaji da kai musu duka kafin ya tsaya yana kallonsu daya bayan daya yana nuna musu dan yatsa tare da cewar cikin kakkausar murya da haki.
Dan ubanku ku kwashe duk wani abu da kuka san na birtday din nan ne ku fita daga gidan nan gaba daya.
Ai bai kasara rufe baki ba kowanne ya dare ya shiga daukar abinda zai diba, Mahmood ya tsaya a bakin kofa ya bude musu haka suka rika fita da kayan daya bayan daya sai da suka kwashe komai sun fice gaba daya, sai Saudat suka bari tsaye rike da hannun damanta tana murzawa saboda dukan da Mahmood yayi mata kamar ma tayi targade, tana tsaye tana kallonsa yaja kofa ya rufe, ya juyo wajenta yana nunata da tsaya.
Maza ki dauki tsintsiya ki share min gida bana son ganin datti ko kwaya daya.
Saudat ta fashe da kuka zata yi magana ya daka mata tsawa.
Ki share nace kafin inyi kutubal dake shashasha kawai mara tunani.
Saudat ta isa cikin falo jikinta na rawa ba arziki ta soma share gidan, Mahmood ya shiga cikin falon ya daura kafa daya kan daya yana kallon gilmawarta, sai da ta share duk inda suka bata kafin yace ta dauko moper ta goge tiles din falon, Saudat tana kuka wiwi haka tayi aikin nan ranta nayi mata matukar suya, sai da ta gama tas ya tabbatar tayi ligis jikinta ya gaya mata sosai, kafin ya kalleta cike da gargadi.
Daga yau ki kuma hada min shashanci a gida, wlh saina yi miki fiye da haka, ai ban taba zaton rashin tunaninki ya kai haka ba sai yau, to ki sani daga yau zamu sanya kafar wando daya ni da ke shege ka fasa. Bace min da gani.
Ya kare maganar a tsawace, Saudat ta fada dakinta ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai, ita yadda ya jizgata gaban mutane yafi kona mata rai fiye da aikin daya sanya ta, sai ta kwanta bisa gado da tunanin wlh sai ta dauki fansan abinda yayi mata ko yaya ne taji dadi a ranta. Mahmood ya mike ya fita kofar gida yaga akwai sauran wanda basu tafi ba, ai ga mugun kallon da yayi musu yasa su barin kofar gidan cikin sauri suna niman abun hawa, gaba dayansu Mahmood ya shayar dasu ruwan mamaki, wasu sai cewa suke ashe duk iyayinta bata fi karfin gidanta ba take cika baki, hatta su Sajida sunyi mamakin Mahmood basu taba zaton zai iya yin haka ba, da tun farko basu bata shawarar tayi shagalin a gidanta ba, haka duk suka nufi gida da sataccen guiwa.
Da daddare, Mahmood ya dawo daga gidan Umma tare da yaransa, can suka ci abincin dare suka koshi, dan haka suna shigowa yace suje su kwanta, shi kuma ya wuce dakinsa ya rage kaya kana ya shiga toilet yayi wanka, yana fitowa ya yi shirin barci daga shi sai singilet da boxis, ya kwanta rigingine yana tunawa da abinda ya yiwa mutanen Saudat yana sakin murmushi, shi sai yanzu abin yake ba shi dariya, ba karamin namijin kokari yayi ba, duk jikinsa ya gaji sosai saboda yayi artabu ba dan kadan ba, sai da ya kwanta yake jin gajiyar sosai.
Saudat tana daga dakinta tunda taji shigowarsa sai ta mike ta zauna gefen gado ta shiga tunanin abinda za tayi masa ta huce, sai da ta tabbatar ya kwanta sai ta bude kofa ta fito ta wuce kitchen ta bude deep freezer dinsu ta ciro bokitin ruwa da take sakawa sai dai kawai in suna son sha su diba, ta fito dashi taga har akwai kananun kankara a ciki ta dauko wasu gorina da suke ciki duk da ruwa a cikinsu sai ta diddile a bokitin, sai da taga ya cika yadda take so sai ta dauka ta nufi dakin Mahmood, tana isa ta bude kofar taji a bude yake Mahmood kuwa ya zubawa kofar ido a tunaninsa Saudat ce kila tazo bashi hakuri akan abinda tayi masa, bai gama tunani ba Saudat ta shigo da sauri ta daga bokitin ta sheka masa ruwan sai ta saki bokitin a dakin ta ruga a guje kamar zata kifa ta isa dakinta ta rufe. Mahmood kuwa lokacin da ya ji saukar ruwan a jikinsa, a gigice ya tashi zaune yana rafka salati babu inda jikinta baya rawa tsabar firgita da yayi.
_________
Hibba.
Yadikko tana juyowa suka hada ido da Hibba nan take ta daburce ta ce cikin rawar murya.
Hibba babu wanda zaiji wannan labarin har sai kin bani izinin na fada.
Hibba ta saki wani shu'umin murmushi bata kuma cewa komai ba, ita kanta mamakin kanta take yi yadda ta sauya lokaci guda kamar wata sabon halitta, Yaddiko kuwa daga haka ta kame bakinta bata kara magana ba, Hibba ta jawo jakar kayanta ta dauko wayarta sai taga misscal din Baba kusan fiye da ashirin sannan taga na mama ya kai bakwai, ga kuma na Hajara ya kai uku, na Habeeb mai napep nashi guda biyar, sai taji gabanta ya fadi saboda ta shiga wani irin fargaba da ganin kiran baba har haka, dan na Inna bai wani dameta ba, ta fara tunanin me zata ce musu ta kare kanta, haka dai ta yi dialing number din baban ta kirashi, wanda yana kwance saman gado ya kasa fita kasuwa ma yau tun wayewar gari, yana ganin kiran Hibba ya daga da sauri bai jira tayi magana ba ya soma magana cikin raunin murya.
Muhibbatu ina kika shiga tun jiya munata kiranki a waya amma ba kya dauka, wai ina kika je ne? saboda naje makarantarku na samu tabbacin babu inda aka turaku, yanzu har ace kinyi wayon da zaki ci amanarmu Hibba, me na rage miki? Duk niman da nake yi saboda ku ne, amma ace ki tafi wani waje ba tare da saninmu ba.
Ya kare maganar ransa a bace, Hibba ta rasa abinda zata ce domin duk wani dabararta ta kubce mata, a zatonta ai asirin zaiyi tasiri zuwa yanzu ta yadda babu wanda zai tuhumeta amma sai taji sabanin haka, tana kokarin yin magana ne Inna ta karbe wayar daga wajen baba ta soma surfa mata zagi tare da masifa.
Allah ya wadaran halinki Hibba, kanki kika cuta ba mu ba, kuma insha Allah zaki ga bacin ran da kika sanya mu a ciki, mara mutunci da hankali, kuma wlh duk inda kika je zaki dawo ki same mu, ina nan na tanadar miki hukuncin da tunda kika zo duniya baki taba ganinsa ba, shashasha mai mugun hali kawai.
Tana kawai nan Baba ya mike zaune ya wafce wayar wanda yasa ta subuce ta fadi kasa, hakan yayi sanadin tsinkewar wayar, Baba ya shiga yiwa inna bata akan furucinta basu dace ba, kamata yayi ta lallasheta su samu ta dawo in yaso sayi mata hukuncin da suka ga dama, Inna ta cigaba da sababi ita ba zata yi mata a hankali ba domin ai ba yarinya bace, haka dai suka yi ta musayar magana daga bisani baba ya fice daga gidan ya barta.
Hibba kuma hankalinta yayi mugun tashi, zuciyarta ta karye ta gama gasgata asirin baiyi tasiri ba, wanda take ganin tayi zuwan Nijer a banza, dan haka cikin sauri cike da tsoro ta mike tana cewa yadikko.
Gaskiya mu koma yau ba zan sake kwana ba, domin innata ta bani tsoro da furucinta.
Haba hibba ki kwantar da hankalinki, saboda malam ya riga ya gama miki aikinki, da kin koma zaki ga biyan bukata.
Wlh ba wani aiki da yayi domin zancen inna ya nuna min babu nasara, dan haka tafiya zanyi.
To ni kam bazan tafi yau ba saboda a gajiya nake, jiya jiyan nan fa muka zo haka muka ci zaman mota tun safe har yamma, ai ko shi driver bazai iya tuki ba, sai dai tunda kin matsa zansa ya kaiki tasha ya dauraki a mota sai ki tafi.
Na yarda, ya kaini kawai na tafi domin hankalina ya koma gida.
Yadikko bata kuma cewa komai ba sai ta dauki wayarta ta kira driver ta sanar dashi tana so akai hibba tasha, sai ta waiga tana cewa Hibba.
Ki dauki kayanki ki same shi a waje, in kunje tasha zai siya miki abincin da zaki ci Allah ya tsare hanya.
Hibba ta amsa da amin kana ta wuce abinta, ta samu driver suka wuce zuwa tasha, suna isa kuwa ya samar mata mota drop kamar yadda ta bukata, suka yi ciniki akan dubu ashirin, Hibba ta ciro ta bayar sai ta shiga mota driver ya jasu bayan an siya mata abinci da drink hade da ruwa. Haka suka fara tafiya baji ba gani tun hibba tana kallon hanya har barci ya dauketa, sai da suka isa katsina kafin ta farka driver ya tsaya a masallacin matafiya ya yi salla, ita dai hibba tana mota burinta kawai su isa kaduna taje ta samu su Inna taga yadda zasu kwashe, bayan driver ya dawo ya shiga mota suka cigaba da tafiya. Sun kawo wani kauyi da zai sadasu da Funtuwa mota ta kwacewa driver ya fada dayan bangaren titin, kafin kiftawar ido wata mota ta rugo a guje suka ci karo da motar su Hibba, wanda suka takfa mummunar hatsari, gaba dayansu jini ya wanke musu fuska suna kwance ba motsi.
*Last freepage*
1. Wani irin mataki Mahmood zai dauka akan Saudat? Ya zamansu zai cigaba? Mahmood yana samun mafita kuwa? Yaushe Saudat zata gyara halinta?
2. Ya rayuwar Hibba zata kaya? Shin wannan hatsarin da suka yi zata rayu? Idan ta koma gida me zai faru? Asirin data yiwa su Inna yana kamasu kuwa? Ya lamarin zai kaya idan asiri ya kama Alhaji Bukar? Wani irin kalubale Hibba zata fuskanta a rayuwarta? Burinta yana cika kuwa?.