BANI DA LAIFI!

Part one

by @shatuuu095


Ammi ta Kara shigowa dakin Dadaa a Karo na biyu, se a lokacin ta same shi ya fito daga wankan, Dan duk zuwan ta wanka yake, tayi kyau saboda dama ita din me kyau ce, kallon farko bana tunanin zakai saurin saka ta cikin wani yare da sauri, idan ka zauna da ita zaka fahimci ta fito ne daga yankin da ake ma lakabi da "home of beauty" wato Adamawar Yola! Tana sanye da wani lace mustard yellow da aka Masa ado da bakin zare, fuskar ta Babu kwalliya Amma Bata manta ta zizara kwalli a idanun ba, lebenta se kyalli yake saboda balm din da ta saka, tayi kyau sede duk wannan abun Babu wani annuri a fuskar tata! Ya dubeta lokacin da take kokarin Taya shi saka links yace


" Ya fuskar taki Haka Babu annuri a cikin ta!"


Ta Dan dube shi wani Abu na Dan tsikar zuciyar ta tace


" Kayi kyau da yawa Dear! Se kace Kai ne angon ba Baban amarya ba'


Dukda maganar ta tasa gaban Dadaa ya Fadi Amma se ya saki murmushi Wanda yasa tsakiyar jaw dinsa lotsawa yace


" Idan Kuma Haka ne fa?"


Se tayi dariya Wanda ya Kara fito da kyanta tace


" Da duniya ta zage ka! Beside waye yake auren Yar sa?!"


Yayi Dan murmushi Dan yau din dai nishadi yake ji, Yana cikin farin ciki yace


" Ki daina kawo hakan, Dole nayi ado, Dole nayi farin ciki yau zanga auren 'ya ta kwaya daya Tak"


Ta Kara fadada Murmushin ta lokacin da take Kara hular shi Dake hannun ta tace


" Tabbas wannan ranar na Dade Ina jiranta, gashi Allah ya nuna Mana! Ina fata A'isha zata kasance cikin farin ciki me daurewa!"


Ya Dan rankwafa yadda zata saka Masa hular duba da yafi ta tsawo yace


" Amin Amin! Nagode sosae da karamcin ki, nagode da dukkan abinda kikai min, Ina fata mu dawamma tare har a aljanna"


Ta danyi juyi me nuni da farin ciki, kafin Kuma ta rungume shi a jikin ta, ya Dan buga bayan ta Yana murmushi, yasan yau din ranar babba ce Amma wannan yafi karfin excitement sede mu Kira shi euphoria, he's euphoric, moment din Dadi yake Masa. Tare Suka fito, Banda kamshi Babu abinda ke fita daga jikin Dadaa, Haka Kuma fuskar shi madaukakin murmushi ne a kwance, tana gefen shi tana Taya shi jin Dadi, yau ranar farin ciki ce, yau din ranar da Suka Jima suna son gani ce, gashi Allah ya kawo ta bayan dogon jira da sukai, ance Wai me Rai Kar ya cire tsamannin samu, Haka Kuma me nema kada ya fitar da rai daga samu, gashi finally A'isha zatayi aure!


Ina zaune gaban kujerar dressing mirror din dakin Ammi, an Gama shirya ni tsaf cikin wani lace me rose pattern sea green, se wani glittering zare Baki da akai ado dashi, kaina an daura min head baki, dukda na kasance ba fara bace Amma ban kawo bakin head zaiyi min kyau ba, fuskata an kawata ta da bridal make up, da daya daga cikin amintattun masu kwalliya ta yimin, idan na tsaya fada muku irin kyan da nayi Bata lokacin ne, nasan dai wannan ita ce "One day" da ake ta fada. Na dubi hannuna da yasha kunshi na Kara kawata su da jewelry da na siya daga wajen Ta_kwalam jewelry! Fuskata madaukakin murmushi ne a kanta. Wayata Dake gefe ta danyi haske Wanda ya tabbatar min shigowar message ne, nayi saurin janyowa dan dubawa


_My girl! How I wish ni ne a matsayin Hashir, how I wish zamu iya canja fate din mu, da Zan so ki zamo Mata ta. Anyways, Allah ya Sanya alkhairi girl ya Baku zaman lafiya me daurewa!_


Bayan na gama karantawa se nayi murmushi dukda can kasan Raina naji Babu dadi, bawai rashin Jin dadin auren shi da banyi ba, a'a se tunawa nayi da yadda na so shi, yadda nayi kukan rashin shi, Amma yanzun banji wani Abu na inama ace shi bane, na Kan Yi tunanin yadda zuciya take, nakan Yi tunanin yadda take iya son wani ta cire son ta saka wani, I believe the heart is magical sannan na yadda Allah is wonderful! Akwai lokacin da muke ganin ba zamu taba iya son wani Abu ba bayan mutum daya Amma se kaga lokaci kalilan mutum ya Zama tarihi a rayuwar ka! It's really pains yadda mutane suke canjawa, it pains Naga Wanda ka damu dashi ya Zama ba kowa ba a gurin ka.


_Thank you_ 


Shi ne kadai amsar da na turawa Zayyad, na cigaba da kallon Kai na deep in thought! Jin an bude kofar yasa na juyo na dubi Dadaa da Ammi da suka shigo, Babu shiri na mike tsaye a hankali fuskata na Kara haskawa da Murmushin da nake, Dadaa ya dubi Ammi yace


" Wannan 'ya ta ce kuwa?"


Nayi dariya Ina matsawa gefen shi, a tausashe nace


" Ni ce Dadaa na! Baa canja ni ba"


Ammi ta rike hannuna tana murmushi tace


" A'isha alhamdulillah! Nagode Allah da Naga wannan ranar! Kinyi kyau wannan make up artist din deserves a double pay!"


Dadaa ya gyada Kai Yana fadin


" Amin ya rabbul alamin! Zan wuce wajen daurin aure, I'll miss you daughter!"


A take idanuna Suka ciko da kwalla, I was so engrossed da son nayi aure na manta cewar zanyi nesa da Dadaa da Ammi, ko kafin Ammi tayi magana tuni hawaye sun fara sakkowa saman kunci na. Dadaa yayi saurin juyawa ya fita, yayinda Ammi ta fara lallashi na, sede banyi kukan soae ba aka Kira make up artist me suna lubna ta Kara gyara min fuskar tare da zolaya ta Wai wayace min amare suna kuka yanzun? Ai kauyanci ne yin kuka. Ni Kam Ina ruwa na, magana ake ta aure, magana ake ta rabuwa da Dadaa, ya kuwa bazan Yi kuka ba.


Seda na shirya tsaf sannan Ammi ta fita Dani zuwa main parlor, kowa sede yace "Mashaaa Allah" saboda yadda nayi kyau, sister ta zauna gefena, su Anty Mamaa da kowa se santin kyan da nayi suke, hajiyan Lagos tana fadin Wai dama Zan dan murmure, nayi dariya kawai bance komai ba. Sister bakin ta dauke da murmushi, na kalle ta Ina riko hannun ta cikin nawa, dukda batai magana ba Amma Kuma idanun ta kawai na kalla nasan abinda take nufi. Haka aka ta zuwa kallona, ance me yafi komai farin jini amarya da madubi, tabbas yau na yadda da hakan. Bani da kawaye se ya zamana cousins Dina sune kawaye na,saboda yawan jinyar da nake yasa bana sake wa da mutane, Kuma dama Haka din Hali na ne, idan kana son ganin surutu na to ni da Dadaa ne Amma wani lokacin Ammi ma bana sakewa sosae da ita. Bayan secondary, course din da nayi a Jami' a ni daya ce mace a cikin maza, Kuma a Haka muka gama.


Ammi tazo ta dubi sister tare da fadin


" Nasiba A'isha taje ta je a Kara gyara fuskar ta, nasan by now an daura auren!"


Ta gyada Kai tana duba wayar ta, se ta Kara rike hannuna muka nufi cikin dakin Ammi, ta Taya ni na zauna gefen gado da Kuma su Anty hafsa na gefe, Lubna ta gyara min zaman head dina ta Kara touching fuskar a bit, sister tana ta kallona tace


" Kinyi kyau yarinyar Dadaa! Allah ya Sanya alkhairi ke da Hashir"


Na saki murmushi nace


" Yau kin fada sunan shi"


Tayi dariya tace


" How I wish suna nan suga wannan ranar, inama suna nan"


Na Dan Bata fuska, dukda bawai na San su bane, Amma yadda sister ke fadar su yasa nake jin Ina kewar su, to bature yace baka kewar abinda baka sani ba.


" Allah ya musu rahma, ni Banga ummu ba"


Ta Dan daidaita yanayin ta, tace


" Nana ce ta fita da ita karbo kayan da zasu saka anjima"


Na gyada Kai, ta Kara kallon wayar ta tare da fadin


" Ya kamata ace sun dawo yanzun fa, Yaya ya kusan awa uku da fita"


Nima se na kalla agogon hannuna Naga har daya tayi, muna Dan nesa da masallaci shi yasa Kiran sallar bamu hi ba, plus hayaniyar da ake a gidan saboda mutane da Suka taru da yawa! 


" Aikuwa dai sister ni ban ma lura ba!"


Se ta Ciro wayatta tana fada min zata Kira Baban Amna taji me ya faru, Haka kurum se naji jikina yayi sanyi, kada fa a maimaita, kada fa ya fasa? Kada shima jinin shi yazo is not compatible da nawa jinin, kada fa a samu matsala irin wadan can sauran samarin nawa. Na dunkule hannuna Ina jin wani irin zufa da suke Yi, sun jike da gumi, fuskar ma dan ta saka min wannan paste din dake Hana gumi, I'm sure da se nayi.


" Babes! Naji shiru Baku dawo ba"


Se tayi shiru, a lokacin ji nake kamar na zura a guje saboda bana son naji wani Abu kuma, at this rate indai har shima Hashir ya fasa ko an samu matsala haukacewa zanyi, nayi hakuri, nayi juriya ni kaina na sani, Amma wani lokacin na Kan ji kaddarar tawa me zafi ce!


" Oooh! To ai shikenan, Allah ya dawo daku lafiya!"


Se ta sauke wayar tana duba na tare da fadin


" An Dan samu tsaiko ne wai akwai test din da baiyi ba Dadaa ki ya kaishi ayi, Amma yanzun zaa daura"


Unconsciously na saki murmushi tare da sakin ajiyar zuciya Ina jin wani farin ciki Yana mamaye ni, na saki hamdala ga Allah sannan kuma Ammi ta shigo da Anty Fati. Dukka se fadin wannan kayan yafi wancan kyau a jikina, ni Kam Ina ganin daga wannan ranar to murmushi na ya Kare Dan kuwa nayi na Kara, na Kara karawa! 


Tun Ina zaune cikin cousins Dina har na kosa na koma daki, kawai jikina na fada min something is absolutely not right, to me ya faru? auren aka fasa ko Kuma me? Wajen mintina talatin se ga sister ta shigo cikin sauri, idanun ta sun kada sun yi ja, Kuma Allah ya taimake ta ni daya ce cikin dakin, ita ba kuka take ba Amma dai hankalin ta a mugun tashe yake. Na dube ta a tsanake Naga ko magana ba tayi min ba, ta wuce wardrobe dina ta bude, ko ta manta an Gama kwashe kayana kaf daga gidan, ganin tana kallon dakin yasa na Dan matsa daga inda nake zaune nace


" Sister Abu kike nema?"


Ta dube ni muryar ta na Dan rawa tace.


" Ina hijab din da kikai sallah dashi dazun?"


Na Dan kalla dakin na hango shi can saman chest nut a ninke, na karasa na dakko na damka Mata sannan nace


" Me ya faru? Menene sister?"


Maimakon ta bani amsa se kawai Naga ta tuje min daurin da aka kusan mintina talatin ana yin shi, ta zura min hijab ko wayata Bata Bari na dauka ba taja hannuna kamar zata tsinka min wrist di na , tun daga shigowar ta da yanayin da take ciki ya tabbatar min Babu lafiya, sede bansan a Ina aka samu matsalar ba. Kai a lokacin banyi tunanin an samu matsala bane a auren na dauka wani abune da bani da idea ko menene. Har mukaje bakin kofar dakin se ta tsaya ta dube ni da jajayen idanun ta tace


" Fita zamuyi, ko da wani zai gane ki kada ki amsa, Dole ki bar gidannan!"


Na dube ta gaba na na wani irin faduwar nace


" Sister Dan Allah me ya faru? Dan Allah ki fada min Dan Allah!"


Ta kalleni se Naga idanun ta sun ciko da kwalla tace


" Mike!"


Daga Haka nabi Bayan ta muka fita, bansan ya akai ba'a lura damu ba, mutane nata Kai kawo ana hidima, kowa hankalin shi na kan abinda take, ta samu ta kaini can nesa da tayi parking motar, har ta bude mota Zan shiga na tsaya nace a hankali 


" Sister Dadaa! Ban fada Masa Zan fita ba, I can't just leave without informing him"


Hannun ta tasa ta janyo ni na zauna seat din dake gefenta tace


"Just follow me!"


Daga Haka ta danna central lock ta figi motar se waje, lokaci daya hawayen da nake rikewa ya wanke min fuska, itama Kuma tana tukin tana kuka!


BA NI DA LAIFI! Is not free, da N1000 zaka mallaki Ba Ni Da Laifi, Sahla A Paris da Kuma ABINDA YA BAKA TSORO. Da N750 zaka mallaki biyu da N350 zaka mallaki daya! Tafiyar sabuwa ce Kuma salon ma sabo ne. Kasance da Top-notch ta hanyar biyan kudi zuwa ga 3091721807 A'isha kwalam Hassan First Bank of Nigeria, send evidence of payment to *** or *** or ***.