BANI DA LAIFI!

Part 2

by @shatuuu095





Ta kusa awa daya tana tafiya, Kuma gudu take akan titi, ban ma fahimci tana gudun ba seda naga uban kilometers din da muka rufa a awa daya, ta samu gefen titi tayi parking tare da hade kanta da steerer wheel tana Kara sakin kuka, na lumshe idanuna Ina jin wani irin Tsoro cikin zuciyata, na dubeta a tsanake nace


"Sister dan Allah ki fada min abinda yake faruwa, me ya faru? Abu ya samu Dadaa ne? Kinki magana se kuka kike Kuma na tambaye ki kinki kice komai, haba mana sister!"


Ta Dan dago ta dubeni sannan ta maida kanta ga window tare da fadin


" Bazan taba son ace daga Baki na Zaki ji ba, Amma Kuma ni daya kike da a duk duniya Dole ni Zan fada Miki!"


Na dubeta cikeda kosawa nace


" Whatever may be duk yadda abin yake Dan Allah ki fada min, ji nake zuciyata kamar zata buga sister"


Ta rike hannuna cikin nata tana kallon fuskta me cikeda rauni da Kuma tashin hankali tace


" Auren ki da Hashir Bai yiwu ba..."


Tamkar saukar aradu Haka naji, tamkar an tsula min bulala Haka naji, nayi shiru dumbfounded, naji komai ya tsaya ko Kara bana ji, tamkar zuciyata ta daina aiki, se Kuma can naji kamar an tsikare ni, nayi saurin kallon sister Dake girgiza ni tana fadin


" A'isha! Talk to me! Ki na jina?"


Na Yi saurin kallon ta Ina kyafta idanu nace


" Menene?"


Se ta Kara kallona ganin na dauke kaina with a blank emotion a fuskata tace


" Nace Miki an fasa auren ki da Hashir, kiyi kuka kinji?"


Na girgiza Kai nace


" Sister! Ina son nayi magana da Dadaa ki maida ni gida'


Ko kafin ta bani amsa se ga Kira ya shigo cikin wayar ta, kusan lokaci daya muka Kai hannun mu saboda idanuna sun gane min Dadaa ne me kiran, sede ta rigani dauka, maimakon tayi swiping ta Kara a kunnen ta kawai se ta katse kiran, nayi shiru Ina kallon ta, na rasa tunanin me zanyi, Bai hakura ba ya sake Kira wannan Karan nayi saurin dauka na Kara kunne na


" Nasiba!"


" Dadaa!"


Na fada a take hawaye ya balle min daga fuskata, 


" A'isha! Are you the one? Kuna ina? Kuna tare da Nasiba?"


Na Kara sakin kuka Ina kallon ta, cikin muryar kuka nace


" Dadaa ta tafi Dani, bansan inda muke ba Kuma, Taki ta fada min"


Muryar shi a tausashe kamar ko da yaushe yace


" Kiyi shiru, bawa Nasiba wayar! Lemme talk to her"


Se na Mika Mata Babu musu, Dan bana tunanin a iya rayuwa ta na taba yiwa Dadaa musu, ni din nasan ko Bai fada ba ni 'yar albarka ce, yaran da ake alfahari dasu. Na cigaba da goge hawayen dake min zarya, Ina jin wani irin tukukin bakin ciki Yana zagaye min ilahirin zuciya ta, bakina daci yake, idanuna har yaji suke saboda ni kadai nasan abinda nake ji. Babu Wanda zai San menene azo daurin aure a fasa, wanne irin tozarci ne wannan? Wanne bakin ciki yafi wannan a duniya. 


" Ina Kika kaita? Ina kuka je? Are you in your right senses Nasiba!"


Shi ne abinda ya fara fada Mata tana karbar wayar, tayi saurin bude motar ta fita ta barni zaune tamkar mutum mutumi. 


" Yaya...!"


" Nasiba! Ki dawo min da 'yata, I caused this, so ni Zan warware shi"


Hawaye ya Kara sakko Mata tace


" Dan Allah Yaya! A'isha is innocent, a matsayin Baba Kuma mahaifi kawai ta dauke ka, bana tunanin A'isha ta taba furta cewar Kai ba mahaifin ta bane, ya kake tunanin zata ji ka Zama mijin ta! Yaya zata ji?"


" Nasiba! Ki dawo da ita, Da Kika dauke ta Ina zaki kaita? Me Zaki fada Mata? Do you have solution? Ki dawo da ita ni Zan kula da komai"


Ta kashe wayar tana Kara kifa kanta, Ina hango duk abinda takeyi Amma bana Jin abinda take cewa, sede ni Kuma bazan iya tambayar ta me yake faruwa ba, tsoro nake ji, tsoron abinda kunnuwa na zasu ji nake, a yanzun na tabbatar ba iya auren kawai aka fasa ba, nasan akwai abinda yake faruwa, na tuna aure na da aka fasa da Hammad sister ta fara sanin ya janye, Dan Babar shi ita ta Kira ta fadawa sun janye ba zasu aura lalura ba, ai ni din liability ce, ni din parasite ce, Ina namiji zai iya auren mace kullum ciwo.... Ko lokacin sister Dadaa ta fadawa, he talked to me yadda yasan zan fahimta dan yasan tsakanina dashi bond din mu is on another level! 


To me ya faru? Menene yake faruwa? Na dubi gefena, Ina neman waya ta, Amma se na tuna Bata gurin, na tuna sister Bata bani damar dakkowa ba, da ace wayar na wajen da tabbas Zan Kira Hashir naji me ya faru, na gaji da tunanin what possibly happened? Sister ta bude ta shigo ta zauna gefe na, ta aje wayar ta kusa dani sannan tayi shiru tana kallon Hanya, se Kuma ta tada motar tayi reverse Amma wannan karon a hankali take tafiya, lokacin da muka kusa karasawa se ga Kiran Dadaa ya shigo, na kalle ta se ta gyada min Kai alamar na dauka, nasa hannu na dauka, muryar shi a hankali yace


" Nasiba!'


Nayi saurin ce Masa ni ce, se yace na saka shi a speaker, Babu musu na danna speaker a take muryar shi ta cika ko Ina cikin motar, 


" Kada ku zo gida, ku wuce gidan Baffa Halilu, Zan same ku acan"


Cikin dasashiyar murya ta amsa shi wadda Banda tabbacin ko ya jita, na cire shi daga speaker na Kara kunne na nace


" Dadaa! Tsoro nake ji!"


Ya danyi siririn tsaki yace


" Ki saurare ni A'isha kinji, kiyi ta maimaita Inna lillahi wa inna ilaihil rajiun! I'm sure Zaki daina ji, I'll be waiting for you, kinji my beloved?"


Na gyada Kai na, na sauke wayar daga kunne na tare da lumshe idanuna, karar wayar yasa na kalla sister, ta min signal kada na dauka Anty Fati ce, tun dazun ita da Anty Mamaa suke Kira, se Kuma tunani yazo min me yasa Ammi na Bata Kira ba, ko dai Bata lura cewar bana gidan ba, to Amma Kuma hakan ba me yiwuwa bane, Ammi mutum ce me kula, ko Yaya yanayi na ya canja sede idan ba zatai magana ba Amma tana ganewa, na jinginar da kaina Ina jin kaina kamar zai tarwatse, kenan Haka anxiety yake, tsoron me Zan tarar nake. Kamar yadda yace Yana tsaye kofar gidan Baffa Halilu, wannan Karan ya cire babbar rigar se Yar ciki, Kan shi Babu hula, kana kallon shi kaga Wanda ke cikin tashin hankali hade da damuwa, nayi saurin fitowa bayan tayi parking, na nufe shi tare da fadawa jikin shi na saki kuka, yayi shiru Ina jin yadda zuciyar shi ke bugawa tamkar zata balla kirjin shi ta fito, shi Bai ce komai ba se kallon fuskata da hawaye yake ma zarya yake, this is unlike him, ya kamata Dadaa na da na sani ya fara lallashi na, he's my strength, dukkan wani karfi da Kuma kwarin gwiwa da nake dashi daga gurin shi yake zuwa. Kamar kuwa yasan tunanin da nake ya janye ni daga jikin shi Yana fadin


" Ya Isa Haka! Kiyi shiru kinji"


Na kankame hannun shi nace


" Ina da laifi ne? Dadaa kowa Bai son ya aureni? Nayi wani laifin ne? Ni na daurawa kaina cutar nan?..."


Da sauri ya saka hannun shi a bakina Yana fadin


" Baki da laifi, cuta Allah ke daurewa, ki daina kuka zanyi komai in my power naga kinyi farin ciki"


Me Zan kawo? Kuna ganin Zan kawo yayi aure? ko kadan hakan ba zai zo Raina ba. Tare muka shiga ciki, kusan dukkannin Baffanin mu suna zaune a parlor, maimakon Naga kamar ana zaman makoki se Naga akasin Haka, tun daga Kan Baffa Halilu, Baffa Jafaru, Baffa Muhammadu, Baffa Zubairu. Anty Fati da Kuma Anty Amina, ga Kuma dangin Mamana Hajiyan Lagos, Uncle Auwal, Anty Mamaa dukka a zaune. Na Kara rike hannun Dadaa dake cikin nawa har muka karasa cikin parlon, sister na bayan mu tana kallona yadda naki matsawa an inch daga jikin shi, muka zauna. Baffa Zubairu yafi kowa fada Dan Haka kafin sister ta karasa Zama ya fara Mata fadan tafiya dani


" Mu kin Raina mu, Baki maida mu iyayen ki ba ko? Da gidan ubanwa Zaki kaita da Kika tafi da ita, ai da se ki tafi da ita ki nuna Mana mu ba iyayen ki bane, shashasha kawai!"


Ta sunkuyar da kanta ko kadan banji dadin abinda yake faruwa ba, gaba daya idanuna Suka Kara cikowa da kwalla, Amma bazan iya cewa komai ba, Uncle Auwal shima fada yayi tayi Mata, Yana fada Mata ta nuna Masa ita Yar Kan ta ce, Hajiyan Lagos da Baffa Muhammadu Suka dakatar dasu, Baffa ya Dan daga musu hannu yace


" Kuruciya ce Zubairu, gani take idan tayi hakan ta tseratar da ita, abun yazo Mata a bazata itama Auwalu, ku bisu a hankali Dan Allah! Duk ba wannan ba A'isha"


Na Dan dago a hankali na Kai idanuna Kan shi, tare da amsawa a hankali, gaba daya jikina ya Kara sanyi maganar me suke? Nikam ayi ayi a fada min, Baffa yace


" Nasan yau munyi Miki laifi, nasan ban kyauta Miki ba Amma Kuma acan kasan zuciyata Ina jin abinda nayi nayi daidai..."


Na kagu, na kagu naji menene, na dubi Dadaa da Kan shi ke kasa, na dubi sister itama Haka, na lumshe idanuna Ina tunanin zuciyata saura kadan ta buga, wannan Jan ran da ake min har Ina? Ina Zan saka Raina naji Dadi ya rabbul alamin?


               


                ***


Five hours back!


Bayan Dadaa ya Gama zuzuta irin kyan da nayi, da Kuma irin yadda zaiyi missing dina, seda sister ta tsayar dashi tayi Mana hoto, na daura kaina a kafadar shi Ina murmushi, Haka Kuma Ammi ta shigo Suka sakani a tsakiya Muna dariya gaba daya. Muka Kara saka shi tsakiya dukka mu dariya muke, Khadija'yar Uncle Auwal tace


" Yau ga dariyar Yaya A'isha!"


Dadaa Ya duba agogon shi Dake daure a hannu, ya shafa kaina fuskar shi da wannan wide grin din da yake min magana da shi, yace


" I'm gonna miss you daughter! Allah ya albarkace rayuwar auren ki"


Idanuna a take Suka ciko da kwalla, Yana ganin Haka ya Kara tausasa Murmushin shi ya fice, Ina jin ana ta masa Wai yayi kyau kamar ango, kamar jira ake, Yana Shiga mota aka tura Masa message, ya fito da wayar se yaga anonymous message ne, Dan number sender din Babu kwata kwata, wannan kusan sati biyu kenan ana tura Masa irin shi, Kuma sender din is anonymous


_ka tabbatar da yaron da zaka bawa 'yar ka ya cancanci auren ta! Shawara ka Kara duba result din test dinsa_


Dadaa yayi shiru rike da waya a hannun shi, ya gaji da wannan message din. Ya danyi tsaki ya tada motar se Kuma ya kashe ya dakko wayar ya fara tun daga farkon message din har karshe, Abu daya yake hinting akan Lab test, to menene me message din ke son fadawa, ya rasa menene se kawai ya fara Kiran Baffa Muhammadu, Bai Jima ba ya amsa Suka gaisa, Suka tambayi juna taro da Kuma fatan na samu farin ciki da zuri'a dayyiba. Se ya fara Masa bayanin abinda ke faruwa, zuwa lokacin baifi mintina talatin suka rage ba aje daurin aure


" Gaskiya akwai wani Abu a kasa kenan Ismail, ya kamata mu bincika"


Sun Jima suna tunanin yadda za suyi, kafin daga bisani Dadaa ya ciro wayar shi ya Kira waliyyin Hashir, bayan sun gaisa yace Masa Yana son ganin Hashir dashi waliyyin Dan komawa asibiti, da farko waliyyin Hashir Wanda abokin baban shi ne sosae ya nemi dalili, Dadaa yace Masa ya rasa papers din da Hashir ya kawo Masa Kuma Bai San me zaiyi presenting wajen daurin aure ba. Se waliyyin yace da Dadaa wannan ba matsala ba ne, kawai yazo ya dauke su su wuce. Ko Hashir Bai San da maganar ba hasalima Yana wani hotel shi da abokan sa suna shiryawa, Dan anan ya sauke su da suka zo. Yana kokarin saka links Kiran kawun shi ya shigo, kawai se ya fita Yana fada musu su iso wajen da sauri, Koda ya fito kasa ya samu su Dadaa suna jiran shi, bayan sun gaisa Dadaa ya sanar dashi ya yi hakuri papers dinnan sun bata, a take wani gumi ya karyo Masa, Babu wanda ya lura da hakan, duk excuse din da ya kawo se kawun shi da walliyin shi suce Basu San maganar ba, a Haka Suka Isa asibiti, da Uncle Auwal da yayi joining din su not long ago bayan Dadaa ya Kira shi, Bai dauka mintina talatin ba se gashi result ya fito, kawun shi ya Kai hannu Dan karba Amma lab scientist din yace


" Kunce na aure ne gwajin ko?"


Dadaa ya gyada kai, mutumin ya girgiza Kai yayi shiru da takadda a hannun shi..





BA NI DA LAIFI! Is not free, da N1000 zaka mallaki Ba Ni Da Laifi, Sahla A Paris da Kuma ABINDA YA BAKA TSORO. Da N750 zaka mallaki biyu da N350 zaka mallaki daya! Tafiyar sabuwa ce Kuma salon ma sabo ne. Kasance da Top-notch ta hanyar biyan kudi zuwa ga 3091721807 A'isha kwalam Hassan First Bank of Nigeria, send evidence of payment to *** or *** or ***.