BANI DA LAIFI!

Part 3

by @shatuuu095

*BANI DA LAIFI!*


_Top_Notch_


03. Free page


✍️Ayshatuuu



Kawun shi ya matsa kusa da maaikacin yace


" Idan da wani matsala yaro, ka fada kada ka bari a cutar da yarinyar mutane!"


Shi Yasan irin wannan information din is highly confidential, leaking information din marar lafiya ko client a asibiti is a punishable offence under court of law, dukkan wani Abu da ya shafi marar lafiya to sirri ne da Bai kamata a fada aji ba, to Amma Kuma kilan sunyi zargin hakan shiyasa suka dawo yin gwajin at the very last minute. Hashir yayi shiru, ya rasa a wanne yanayi yake ciki, yanayi ne na tsoro, firgici da Kuma tashin hankali, gumi se karyo masa yake, he's drenched in his own sweat! Idanun shi sunyi jawur, wayace Masa karya ana cin riba, waye ya fada Masa karya tana 'ya'ya? Sede tayi fure. Sanin Babu wani abu da zai CeCe shi face ya fadi gaskiya da bakin shi yasa ya zube kasa, dukkan gwiwoyin shi a kasa, sanye yake da farar shadda wadda A'isha da kanta ta fada Masa ita take so yasa a irin wannan ranar, ya Manta a laboratory yake, inda dukkan wasu kwayoyin cuta zasu iya samun matsuguni, dukda Babu alamar jini, ko wani abu makamancin sample a flooring din, Amma dai munsan kasan nan bazaiyi rabo da microbes ba. Dadaa ya kalle shi, shima Dadaa take kallo da kowa dake gurin a tsorace yace,


" Kuyi hakuri! Dadaa ka yafe min"


Dadaa ya runtse idanun shi Yana tsoron abinda kunnuwan shi zasu iya jiyo masa, kawun shi ya daka Masa tsawa tare da fadin


" Mu zaka mayar mutanen banza, me kake boyewa?"


Ya fada tare da wartar paper dake hannun Lab scientist din, ya bude, a take idanunshi sukai Ido hudu da HIV SEROPOSITIVE a rubuce, yayi shiru, Yana Kara blinking idanun shi, Dan tabbatar da abinda ke rubuce a jiki, Dadaa ya amsa takardar Yana dubawa kowacce kalma da yake furtawa bugun zuciyar shi na daduwa, ya dago idanun shi jawur Yana kallon Hashir, hannun Dadaa rawa kawai yake Yi saboda kasuwa, dakin yayi shiru dukkan su suna saurarar Hashir da Kuma Dadaa, Hashir bakin shi na Bari yace


" Nasan ni me laifi ne, kuyi hakuri ku yafe min. Dan Allah Dadaa!"


Dadaa ya riko hannun Hashir yasa Masa paper a ciki, cikeda bacin Rai Wanda zakaji a Amon muryar shi dukda ba ihu yake ba, yace



" Hashir ka sani tuntuni ka boye Mana? Me yasa Kai Haka?"


Idanun shi sun Kara yin ja yace


" Ban sani ba wallahi Dadaa, ban sani ba, ban sani ba se ranar da naje yin gwaji kafin lokacin da zamuje da A'isha, kawai aka fada min cewar I'm infected da virus din, bansan ya zanyi na fada muku ba, bansan yadda zanyi ba idan na janye..."


Kowa Banda nanata Inna lillahi wa inna ilaihil rajiun! Babu abinda suke, Baffa Muhammadu yace


" Me yasa baka fada ba, na tabbatar lokacin zaa iya gyara wani abun"


Ya Dan lumshe idanunshi, shi kadai yasan yadda zuciyar shi take, ji yake kamar duniya zata kife dashi, kamar an kwashe Masa dukkan kayan jikin shi, tamkar tsirara yake Kuma kowa na duniya na kallon shi, 


" A'isha Ina son ta, bana son na sata Kuka, lokacin da na fahimci I was HIV positive already an saka rana, kiris ya rage ayi aure, Ina yawan tambayar ta zata iya aurena a kowanne Hali nake se tace eh, ni Kuma tausayi take bani bana son nayi breaking zuciyar ta, Dan Ina ganin idan ta rasa ni ba zata Kara trusting wani ba Kuma, shiyasa nayi Haka Dan Allah ka yafe min"


Dadaa ya gyada Kai yace


" You're mistaken Hashir...ko Dan zamuyi magana daga baya, Amma ka sani bazan iya aura maka A'isha ba, wannan abin da kayi baka kyauta ba, Ina ma ka fada tuntuni da tuni ta warke da rashin ka, Amma se yau Hashir, da banzo na kawo ka ba Haka zaka cuce ta ka cuce ni?"


Se kawai ya juya ya fice, Bai Jira kowa ba, wani iri yake gani shi ba jiri ba shi ba hajijiya ba, tafiya kawai yake Yana saka kafafuwan shi duk inda ya samu, can ya zauna saman wasu gossip chairs Dake farfajiyar asibitin ya zauna, hannun shi yasa ya dafe Kan shi, yayi shiru ya rasa me zaiyi, fuskata kawai yake hangowa Murmushin da nake Masa kafin ya fito, ya tuna rabuwa ta da Zayyad yau Kuma yafi kowanne seda ya Tara mutane? Seda na gama saka rai? Na saka Rai sannan ace an fasa, shi ya zaiyi? Shi me zaiyi? Wa zai samu ya aura min Dan ya wanke min zuciya ta? Ya rasa, Dan shi ya sani shi ne uwata, ubana Haka Kuma aboki na, duk duniya Dadaa kadai na yadda dashi, komai nawa Dadaa ne ke fara sani, komai da kuka sani hatta ranar Dana fara period seda na Jira ya dawo daga office na fada Masa, so Babu wata shakuwa da zakuyi tunanin bamuyi dashi ba. 


Baffa Muhammadu ya zauna gefen shi Yana duba agogon hannun shi yace


" Lokaci na tafiya Ismail, na tabbatar mutane na can na jiran mu. Gashi Yaya Halilu tuntuni Kira na yake"


Dadaa ya dubi kanin mahaifin shi, ya Kuma dubi Uncle Auwal da ya kasa magana saboda kaduwa, idanun shi sunyi ja, tashin hankali boldly written a fuskar shi yace


" Ya zanyi Baba? Me zance da mutane? Me Zan fadawa A'isha above all! Na tabbatar abin zai Mata yawa wannan karan, inaga ka fadawa mutane su watse kawai"


Baffa ya Kara kallon shi a tsanake yace a hankali


" Ka aure ta!"


Da sauri Dadaa ya kalle shi da wani irin fuska me cikeda Amma Wasa kake ko? Ya kalli Uncle Auwal da fuskar shi ta Dan haska alamun yayi welcoming idea din also with a glimpse of hope, Baffa Muhammadu ya dafa kafadar shi yace


" Ba Wasa nake ba, ka aure ta shi ne kadai mafita"


Dadaa ya girgiza Kai da sauri Yana fadin


" A'a Baba kayi hakuri nace maka a'a, Amma duka rayuwar A'isha matsayin uba take daukana mahaifi, Haka Kuma 'ya nake ganin ta, bazan iya ba, bazan iya juya matsayin ta ta koma Mata ba, Dan Allah kada muyi haka"


Baffa Muhammadu ya dafa shi yace


" To ya zakai da ita? Ya zakai da mutanen da suke jiranka?"


Dadaa yayi shiru, idanun shi kadai ka kalla zaka fahimci halin da yake ciki, ya Dan dago ya kalla kanin mahaifin shi yace


" Zan bawa Mubarak ita, ko Faisal ko hanif"


Baffa yayi murmushi yace


" Ismail baka taba min musu ba, baka taba ketare magana ta ba, nasan dasu Faisal nace ka aure ta, Kai ka yadda damka amanar ta a wajen wannan yaran? Ka yadda?"


Se yayi shiru, da farko A'isha Basu shiri da Faisal, Mubarak jinin shi bazai yiwu suyi aure da ni ba, Hanif Kuma Sa'a na ne, beside ba zai ma iya yimin auren dole ba, wannan Abu ne da ba zai taba bari ba, not A'isha, not his beloved. Ya dubi Baffa yace


" Tausayin ta nake ji, bansan yadda zatai ba idan taji na aure ta, Amma let's carry on da auren!"


Uncle Auwal ya dafa shi tare da fadin


" Ni, Hajiya, Mamaa da Kuma Yaya mukan zauna muce inama Kai zaka aura A'isha, saboda a ganin mu Kai kafi cancanta da wannan mukamin. Ka yadda ka dauka hakan daga Allah ne!"


Kamar Wasa kamar a mafarki aka daura min aure da Dadaa! Tun kafin su karasa Baffa Muhammadu ya Kira Baffa Halilu yayi Masa bayanin abinda yake faruwa Kuma dukka Suka ce Babu Wanda yafi cancanta ya aure ni se Dadaa na, tuntuni suke son hakan ya kasance Amma ganin dukkan mu babu Wanda yake wannan tunanin se suka zuba Mana idanu, plus darajar Ammi da suke gani. Babu wani karsashi, Babu wani karfi Dadaa ya zauna aka daura Masa aure, shi dai yayi shiru Yana bin kowa da idanu, ya rasa me zaiyi yaji sanyi cikin zuciyar shi. Abokan shi, Yan uwan mu, yan uwan Ammi dukka son tambayar abinda ya faru suke Yi bayan an gama daurin auren, Amma Dadaa ana gama daurin aure ya fito, ko friends dinsa Bai saurara ba ya shiga mota, yayi reverse ya bar harabar masallacin, seda ya danyi nisa sannan ya Kira Yaya Habib yace ya tabbatar ya kula da Baki sunje reception, shi Yana bukatar kadaicewa. Parking yayi ya fara kokarin Kiran Ammi Amma Bata shiga ba se kawai ya Kira sister ya fada Mata halin da ake ciki, maimakon ta jira shi kamar yadda yace Mata se taga gwara ta tafi da ni inda Bata sani ba. Bayan ya Gama ya nufi gida Yana ta kokarin reaching Ammi, a ganin shi shi ya kamata ta fara jin a bakin shi. Cikin sa'a se ta shiga, tana cikin mutane saboda kannen ta da yayun ta sun karaso, ta nufi dakin da nake tana Kara wayar a kunne tare da fadin


" Baban Amarya! An daura?"


Tasan mijin ta ya fita da dukkan murna, Amma muryar shi da ya amsa Mata da eh yasa tace


" Me ya faru? Kamar baka murna?"


Ya danyi shiru kafin yace


" Maryam ki saurari abinda Zan fada Miki, Kar kiji zancen da Zan Miki da zuciyar ki, ki jini da hankalin ki"


Ta samu guri ta zauna gaban ta na faduwa tace 


" Me ya faru? Fasa auren akai?'


Ta fada tana barin dakin a tsorace zuwa nashi, Dan nan ne take da tabbacin Babu me shigowa


"Eh abubuwa Suka faru da yasa auren ba zai yiwu b...."


Tayi saurin katse shi da salati lokacin da take karasawa cikin dakin shi Tana tura kofar, hannun ta da dukkanin jikin ta rawa yake, cikin kidemawa tace


" Ya Allah! Wannan wacce irin kaddara ce? Dear me ya faru? Ya zamuyi facing A'isha kuwa wannan karon?"


Ya Dan saki ajiyar zuciya yace


" Ki saurare ni, nasan na Miki laifi Amma hannaye na are tied bansan yadda zanyi ba ko kadan..."


" Me kayi? Kada kace min aure ka hadata da wanu? A'isha nawa take, suitor zai zo Mata"


Kan shi ya Sara Jin amsar da ta bashi, Anya kuwa Bai cutar da Maryam ba? Anya yayi Mata adalci yayi aure ba tare da sanin ta ba, Kuma ma yarinyar da ta rike, tayi Mata rikon 'yar da ta Haifa. Da duk tunanin shi yadda Zan dauki maganar ne Amma kuma yanzun se yaji tsoron fada Mata yake, to Amma yanzun ne ko Kuma ya Bari wasu su fada mata ta fahimta a baibai, gwara taji daga bakin shi zaifi sauki! Ya tattaro dukkan wani courage din sa yace


" Maryam kiyi hakuri Amma na auri A'isha, Dani aka daura auren!"


Bai kawo zata ce Masa ya kyauta ba, kamar yadda yasan zata dauka yaci amanar ta ne, Amma Kuma zai daure zai Kuma jure ya karba duk abinda zatayi saboda yasan he wronged her, Amma Kuma Bai taba ko kawowa hakan ba, saboda a zuciyar shi matsayin 'yar shi kawai ya bani, nothing out of it!


" Me kace? Kayi aure? Haba dai Ismail Wasa kake"


Bai taba Jin sunan nan a bakinta ba, shekara Sha hudu suna a aure, Bata taba furta Ismail ba se yau, cikin shi ya kulle kamar knot aka daura, Ya daure yace


" Hakane Maryam, bansan yadda Zan ce Mata an samu matsala da auren ba, shi yasa..."


" Ni zakai ma Haka? Karka Fara fada min Haka!..."


Se Kuma tayi shiru kilan har lokacin kokarin digesting abinda ya fada take, se Kuma ta saki wata Kara tana fadin


" Aure kayi? Ka aure A'isha? Yarinyar da na rike?"


Yayi shiru Bai ce komai ba, Dan da gaske he saw this coming, wannan kadai rehearsal ne baa shiga cikin show din ba. Da kanta ta kashe wayar ya dafe Kan shi, kafin minti goma yayi wani abu Kiran Anty Fati ya shigo, ya dauka Yana gaishe ta Amma Bata amsa ba tace


" Me yake faruwa ne? Gida ya rikice Maryam se throwing tantrum takeyi Wai ka auri A'isha, Haka ne?"


Ya runtse idanun shi Yana Jin wani irin zafi a kirjin shi yace


" Haka ne Anty! Ina A'isha take?"


" Ban gansu ba na duba Babu ita Babu Nasiba, ance anga fitar Nasiba!"


Ya saki ajiyar zuciya dama tsoro yake kada Ammi tayi min wani abu, Amma Kuma Ina mukaje da Nasiba? ya ayyana a ranshi


                ***


" Nasan ke me biyayya ce, nasan Zaki min biyayya, ba Ni da haufi akan ki, Auren ki da Hashir Bai yiwu ba, Ina baki hakuri a Karo na Babu adadi, Baban ki zai Miki bayanin dalilin hakan, that is not important right now, Abu me muhimmanci shi ne auren ki da Ismail aka daura dazun"


" Ismail! Ismail!! Ismail!!!"


Haka sunan ya dinga ringing cikin kunne na, waye Ismail? A'a ba Haka zance ba, wanne Ismail din? Dan dangin mu kowanne gida akwai Ismail saboda sunan kakan mu kenan da ya haifi mahaifina, shi ma mahaifina Ismail yake, to Wanne a ciki?"


Na juya idanuna sun kafe, tunda Baffa yace Dadaa zai min bayanin fasa aure na da akai naji idanuna sun kafe, to Amma waye aka aura min babu consent Dina? na dubi Dadaa da yaki Bari mu hada idanu, Amma dukda haka wa nake dashi Wanda yafi shi? Babu duk duniya inyi ta mahaukaci, na karasa gaban shi na Kama hannayen shi nace


" Dadaa Kai min bayani, ka min alkawarin baza ka taba hadani da wani ba, se yanzun? why now?"


Ya dago ya kalle ni, seda na tsorata da idanun shi, yayi ja jawur kamar ana zagaga wuta a ciki, Amma yanzun ba lokacin tsoron idanun Dadaa bane ba, ko lokacin lisaffin me yasa idon shi kadawa har haka, lokacin a bani amsa ne! 


" Dadaa!"


Na Kira da karfi wannan Karan, tamkar bani ba, Ashe inada murya me karfi har Haka? Anty Fati tazo ta rike ni tace


" A'isha ki dawo hankalin ki, Baki ganin yanayin da yake ciki?"


Na rike hannun ta se Kuma hawaye ya fara sakko min nace


" To ki fada min wanne Ismail din? Anwar? Grandpa?'


Se lokacin Suka fahimci ban ma gane Ismail din da ake magana akai ba, cikin lallashi Hajiyan Lagos tace


" Dadaan ki, Dadaa ne ya aure ki?"


A take na saki hannayen Anty, na koma na zauna dabas, zuciyata wani irin bugawa take har na fara tsoron over extension, hawayen Suka kafe Babu ko diso dake zubowa, I was dumbfounded for a while!!!



BA NI DA LAIFI! Is not free, da N1000 zaka mallaki Ba Ni Da Laifi, Sahla A Paris da Kuma ABINDA YA BAKA TSORO. Da N750 zaka mallaki biyu da N350 zaka mallaki daya! Tafiyar sabuwa ce Kuma salon ma sabo ne. Kasance da Top-notch ta hanyar biyan kudi zuwa ga 3091721807 A'isha kwalam Hassan First Bank of Nigeria, send evidence of payment to *** or *** or ***.