BANI DA LAIFI!

Part 4

by @shatuuu095

*BANI DA LAIFI!*


_Top_Notch_


04. Free page


✍️Ayshatuuu


Ina lokacin da zaka ji tamkar baka duniya, tamkar zuciyar ka zata fashe, tamkar the world will cripple at your feet? Haka naji, na kasa fahimtar a Ina nake, kwalkwalwata se aunawa take, Dadaa na aura? Dadaa a matsayin miji na? Meye Haka ? Meye yake faruwa? Wanne irin mummunan labari ne wannan? Se Kuma na fara tunanin to ko dai mafarki nake? Se na saki ajiyar zuciya with the hope mafarki ne Kuma Zan farka. Amma Kuma se ban farka ba in fact komai dake gabana is so real! A hankali na daura hannuna a idanuna na mirtsika Amma dai Haka dinne kowa da komai yana nan yadda yake, parlon yayi shiru Ina tunanin jiran ta inda Zan fara suke,Jin Shirin yayi yawa Dadaa ya karaso inda nake zaune ya riko hannuna, na dago na kalle shi, wannan dukka rayuwa ta baba na ne, da farko ban taba kawowa ba shi ya hafe ni ba, daga baya Kuma da na gane se na fara daukar shi uncle Dina ne, Amma daga baya se na fahimci we were only cousins!


*THROW BACK*


Sunana A'isha, kowa da kowa Haka yake cemin A'isha, bani da wani suna da ya wuce hakan Kuma na kasance Ina alafahari da sunana har gobe. Asalin mu Yan jigawa ne, da mahaifina da mahaifiya ta. Mahaifina Dan asalin Gwaram ne, family din shi sannanu ne sosae a ciki da wajen Gwaram da Kuma makwabtan jahohi, saboda akwai Wanda zaku ga tamkar sunyi gadon arziki ne, to family din babana kenan. Mahaifin su yayi gadon kasuwan ci da noma a gun iyaye da kakkani, suna safaran fata zuwa jahohi da wajen kasa, idan wajen noma ne Kuma sun shahara a noman auduga. Se ya kasance kamar idan kaje Gwaram ka tambaya Sarkin auduga bana tunanin ko karamin yaro zai gagara raka ka, an San gidan saboda fice da yayi. Wani abun armashi Kuma shi din Dan siyasa ne Wanda ke kokarin ganin ya taimaki talaka! So far they're famous. Matar shi daya Maimuna, ana kiranta hajja Muna, Kaka ta mace ce me karamci da dattako. Baffa Halilu shi ne babban Dan ta Wanda yayi karatu Kuma ya daura da noman auduga Amma ya Kara da wasu ba nan kadai ba. Se Baffa Jafaru Wanda shi ne mahaifin Dadaa na, Me bi Masa shi ne Baffa Muhammadu . Anty Amina ita ke bin Baffa Zubairu Wanda ke bin Baffa Muhammadu. Daga Anty Amina se mahaifi na Ismail, Wanda yaci sunan mahaifin shi, daga shi Kuma se Anty Fati wadda take matsayin auta a gidan. Dukkan su har matan Babu Wanda baiyi karatu ba, na Boko da na addini, sunyi karatu sosae da sosae Kuma arziki sun Tara su.


Mahaifina ban San shi ba na dai San hoton shi Kuma Ina jin labarin shi a wajen Dadaa da Kuma sister! Shi Kan shi Bai San an haife ni ba, Dan ko kafin Mamana ta haife ni Babana Allah yayi Masa rasuwa. Mamana sunan ta A'isha, sunan ta naci saboda tana Haifa ta ko kwana Bata Kara ba Allah yayi Mata rasuwa! I was brought up a complete orphan, Babu uwa Babu uba, uwa uba ga rashin lafiya! Kakana da ya haifi Abba da Kuma kakana da ya haifi Mamana dukkan su abokai ne na kusa, sunyi karatu tare Dan Haka da Abba ya kammalla makaranta, akai posting din shi Lagos nan yayi camping din shi a ikeja, bayan ya fito daga nan se ya fara serving anan Lagos din, da farko a corpers' logde yake na ma'aikatar daga baya da baban Mama yasan da shi se yayi kokarin ganin ya dawo dashi gidan shi, Bai so ko kadan ya koma ba saboda Bai fiye son Shiga mutane ba, Amma baban shi yace ya kamata yaje kada ya ketare tayi. Shi ne yayi parking zuwa can. 


Mamana ita ce 'yar shi ta wajen uku , a lokacin ta gama secondary ana kokarin ganin anyi Mata aure, saboda ita ce mace ta farko a gidan, Amma baban su Mama Yana ganin ya kamata tayi karatu, dukda lokacin gani ake ya bar yarinya katuwa yaki yayi Mata aure, ba lallai sunsan da zuwan zamannin nan ba, da aure ke farawa at the age of 25yrs, da zakaga mace ta Zama spinster batai aure ba. Kakata da ta haifi Mamana batayi karatu ba, so tana da limitations da yawa Wanda yasa take ganin gwara ace an bar Mama tayi karatu. A Haka dai sukai nasara ta samu gurbin karatu a university of Lagos! Dama ta Saba cudanya cikin su, itama ta goge da nacin karatu irin nasu. Sosae take karatu Dan ganin ta fitar da kowa kunya, zuwan Baba Bata ma San da zuwan nashi ba, Se da ya kusan sati daya bai hadu da ita ba, se cikin sati na biyu Yana zaune shi da brother dinta suna Hira, Uncle Auwal kusan sa'an Baba nane Dan shima lokacin Yana service sede stream din su ya banbanta. Suna zaune gaban gidan Hira tayi zafi, a lokacin ita Kuma driver ya sauke ta, ta fito hannun ta rike da handouts da wani katon text book Wanda a ka'ida ya kamata ace a gida yake ba yawo ake dashi ba, a haka nan dai take rike dashi, fuskar ta tayi maiko, idanun ta sunyi zuru zuru kana kallon ta kasan ta sha wahala Kuma a gajiye take, zamu iya cewa yunwa ma take ji. Tana bude kofa Suka dago suna kallon ta, Abba ya dube ta briefly ya dauke Kan shi yayin da Uncle Auwal ya dube ta yace


" A'isha!"


Kiran sunan ta da yayi yasa Abba ya Kara dagowa ya dube ta, sannan ya Kara dauke idanun shi. Ta karaso ciki tana shagwabe fuska kamar zatayi kuka tace


" Yaya wallahi wahala?'


Yayi dariya Yana duban Abba da yayi shiru yace


" Kaji fa Wai da wahala! Ance Miki degree Wasa ne? Better buckle up"


Ta Dan Harare shi kadan sannan ta dubi Abba tace


" Ina wuni?"


Ya dago a hankali ya kalle ta, idanun ta a kanshi yace


" Lafiya Lau! Sannu da zuwa"


Ta danyi murmushi ta Masa godiya sannan ta shige ciki, Uncle Auwal ya dubi Abba yace


" Ita ce take bina, Ina tunanin ita kadai ce baka hadu da ita ba a gidannan! Tana nan unilag tana karantar pharmacy!'


Take fuskar Abba ta Kara haskawa da Murmushin Jin Dadi, a duniyar shi Yana son ganin mace tana karatu, he so much like it, shi ne dadin zaman birni plus Kuma course irin nashi takeyi


" Mashaaa Allah! Amma tayi kokari sosae, wanne level take?"


Yace


" Level 200 take"


Abba yaji Dadi sosae, Karin Jin Dadi course iri daya sukai. Da daddare Uncle Auwal ya Shiga karbo musu dinner, tana zaune ita da Hajiya mahaifiyar ta, Hajiya na kallo ita Kuma ta dukufa tana karatu tun karfin ta, ta dago ta dube shi bayan ya zauna gefen Hajiya, ta bude bakin ta Dan tambayar shi Abba Amma se tayi saurin kallon katon text book din gabanta, Uncle Auwal ya roke ta ta kawo Masa abinci, idan normal ne zata iya ce Masa ita fa karatu take, Amma abun mamaki ta mike ta zubo abinci da komai ta kawo gaban shi ta aje sannan ta koma Kan karatun ta, abin mamaki hayaniyar TV din Bata damun ta.


Daga wannan ranar Basu Kara haduwa ba, duk yadda take kokarin dawowa Akan lokaci ko zata same shi Amma shiru Bata gan shi ba, ita Kuma Babu Wanda zata iya tambaya akan shi kunya take ji. Seda sukai wajen sati biyu, da safe da weekends ta fito da wurwuri ta Shiga kitchen tana cikin aiki Sega Hajiya ta shigo, ta gaishe ta sannan Hajiya tace


" Kiyi sauri ki Gama Ismail zai fita, bana son ya fita Bai karya ba!"


Ta aje cokalin da take kada kwai dashi ta dubi Hajiya tace


" To waye Ismail kuma"?'


Hajiya ta dube ta itama tana Mata nuni da man yayi zafi tayi sauri tasa Kwan tace


"A'a badai Baki San Ismail ba? Dan abokin Alhaji ne da yake bautar kasa a gidannan"


Tayi murmushi cikin basarwa tace


"Oh! Kamar na taba ganin su shi da Yaya, the other day Dana dawo daga school"


Tace


" Shi ne fa, yaron arziki wallahi"


Mamana ta saki murmushi, kawai Dadi take ji da suke hirar shi


" Allah sarki ai na zata abokin Yaya Auwal ne'


Hajiya ta Mata bayanin yadda kakana yake da alaka da kakana, zuwa lokacin ta Gama hada abinci, ta dakko kwanuka ta zuba Masa sannan ta dauka Dan Kai Masa, Hajiya ta tsayar da ita da fadin


" Bar Masa zai zo ya dauka!"


Ta gyada Kai kawai se ta tsiri goge goge a kitchen din, abin mamaki har ta Gama Abba Bai zo ba, tana kokarin fitowa a kitchen din Se gashi sanye da kananan kaya, ta window take hangen shi, yadda taji bugawar zuciyar ta zata iya rantsuwa dalilin ganin shi ne hakan ya faru, seda ya dauka flask din sannan ta fito fuskar ta da murmushi ta gaishe shi, ya Dan kalle ta briefly kafin ya amsa yayi gaba abun shi, ta tsaya tana kallon Bayan shi har ya shige dakin da yake Zama da Uncle Auwal kafin ta Dan saki tsaki tana Jin haushi yadda ya basar da ita. A Haka dai ta Kan gan shi jefi jefi, duk lokacin da ta gan shi zata tsaya ta gaishe shi cikin mutumtawa da bada girma, Amma wani lokacin ma a ciki ciki yake amsawa, se abun ya fara damunta, ta fara shiga damuwa saboda ita dai Bata San dalili ba Amma tana Jin wani irin yanayi a tare dashi, kullum idan ta gan shi so take su zauna suyi Hira, she wants to know more about him ba Wai iyakar sunan shi da garin su ba. Ana Haka ya tafi Gwaram, a Daren da ya tafi Bata sani ba, se can Bayan ishai ta shiga kitchen Dan dafa Masa tea kamar yadda ta Saba Amma bayan ta gama tana juyewa cikin tea flask, autar su Anty Mamaa ta dube ta tace


" Wai Yaya Ismail Kika dafawa? Ya koma jigawa fa jiya"


Tayi saurin juyowa tana kallon Mamaa da har ta dauki gwangwanin Madara tana kokarin ficewa tace


" Yaushe? Ya akai ban sani ba?"


Ta fada muryar ta a raunane kamar zatayi kuka, Mamaa ta dube ta tace


" Oh! Jiya da sassafe Baki tashi bama, to menene Naga idon ki ya kawo ruwa? Dole se kin San movement dinsa? A'a! Naga ko sabawa bakiyi ba"


Tayi saurin juyawa , Anty Mamaa ta tabe bakin ta ta fice, her sister is acting weird. Tayi shiru tana Jin zuciyar ta babu dadi, ya zaayi ya tafi Bata sani ba, bansan me ta dauki kanta a wajen shi ba,Dan shi din dai Bai wani bawa mace muhimmanci ba indai a dangantakar soyayya ne. Akwai set of mutane dake da halin daurawa Kan su abinda Bai kamata ba, to Mamana is one of them, a wañnan Daren har da kukan ta kafin ta samu tayi bacci. A Haka akai sati daya kullum so take ta tambayi wani yaushe zai dawo Amma ta gagara, kullum cikin kasa kunne take ko zataji ya Kira through landline. Ranar da ya cika sati daya ta fito hannun ta dauke da wani handout ta zauna kofar daki tana tsafe kanta, Anty Mamaa tazo ta zauna gefen ta, tana ta Mata Hira ita Kuma tayi Mata banza, se kawai taji tace


" Ban fada Miki ba Yaya Ismail zaiyi aure!"


Tayi saurin kallon Anty Mamaa tace


" Wanne?"


Anty Mamaa ta Kai kwababbiyar madara bakin ta da karamin tea spoon tace


" Corper dinnan Mana!"


Mamana ta dube ta hankali a tashe tace


" Wasa kike?"


Anty Mamaa ta saki dariya tana nuna ta tana fadin


" Son shi kike? Kinga yadda kikai kuwa? Wasa nake Miki"


Mamana ta saki ajiyar zuciya, se Kuma ta fara dukan Anty Mamaa da handout din hannun ta Wanda Babu shiri yasa tana dariya ta bar gurin, Mamana ta dafe kirjin ta tana sakin ajiyar zuciya, da gaske ta tsorata wani Abu taji more of a sword ya caki kirjinta, se tayi shiru, Wai kuwa Anya ba son shi take ba? Cikin sauri ta mike ta daure kanta tasa wata karamar hula ta dauki hijab bayan ta cewa Hajiya zata shiga wajen kawarta Maryam. Tana shiga gidan su Maryam Wanda baifi miles away ba ta samu Basu nan, Haka ta dawo sukuku Babu karfin jiki, ta rasa me takeji game dashi.


Washegari Bayan fitar Yaya Auwal da dukkan Yan gidan dan ranar har Hajiya ma ta fita zuwa gidan abokin baban, dukda Bata fita sosae. Ta kulle gidan ta nufi dakin Uncle Auwal, wata corner ta hango wadda ta tabbatar na Babana ne, ta karasa taga manyan text books na pharmacy, ta dauki daya tana wondering wannan littatafan me suke yi anan? Jin knocking yasa ta aje littafin ta fita, tana budewa sukai kicibis dashi, kana kallon shi kaga Wanda ya gaji saboda Hanya, ya dubeta, gaba daya rigar jikinta hannun singlet ne, iyakar tsayin gwiwa, kanta Babu dankwali manyan kalbar da Anty Mamaa tayi Mata ta zubo wuyan ta, ya Dan kauda Kai Yana kallon yadda take kallon shi admiringly ba lalle tasan kallon da take Masa ba.


" Idan Zaki bude Kofa make sure ki rufe jikin ki"


Se tayi saurin kallon kanta, se ta saki karamar Kara ta ruga a guje ciki, ya saki murmushi Yana ayyana kuruciyar ta. A ranar duk farin cikin ganin shi se ya koma kunya, tun daga nan ta rage shishigge Masa dukda tana son hakan, Amma idan ta tuna yadda ya hanya, se taji kamar ta kurma ihu!



BA NI DA LAIFI! Is not free, da N1000 zaka mallaki Ba Ni Da Laifi, Sahla A Paris da Kuma ABINDA YA BAKA TSORO. Da N750 zaka mallaki biyu da N350 zaka mallaki daya! Tafiyar sabuwa ce Kuma salon ma sabo ne. Kasance da Top-notch ta hanyar biyan kudi zuwa ga 3091721807 A'isha kwalam Hassan First Bank of Nigeria, send evidence of payment to *** or *** or ***.