BANI DA LAIFI!

Part 5

by @shatuuu095

*BANI DA LAIFI!*


_Top_Notch_


05. Free page


✍️Ayshatuuu





A hankali Kuma se ya fahimci kunyar shi take ji, Kuma gashi ya saba da yadda take on and off akan shi, da gaske ya fahimci komai da take Amma Bai San commiting kanshi a kanta ko ya bata false hope. Amma yanzun Yana zaune se yaji kewar ta yake, ya mike daidai shigowar uncle Auwal yace


" Wai ni Kam Ina A'isha ne? Kwana biyu bana ganin ta"


Ya yadda takaddun hannun shi da ya shigo dasu, tare da Zama gefen katifa yace


" Tana can karatu take, ta fara exams!"


Babana yace


" Da gaske? Wait wai me take karantawa ne?"


" Pharmacy ne, shit irin naka course dinne"


Se yayi murmushi yace


" Allah ya bada saa"


Ya amsa da Amin, da yamma ta fito ta shimfida abin sallah ta hada littatafai a gaban ta tana ta karatu kamar yadda ta saba, ya Jima Yana kallon ta daga daki kafin Kuma ya fito ya nufo inda take, turaren shi yasa ta Dan tsaya kamar me tunani se Kuma taji footsteps din sa, ta Dan waigo se karaf idanun su Suka hade, tayi saurin dauke Kai tana tunanin ta tashi ta koma ciki Amma Kuma ai tana son ganin shi itama, kafin ta gama tsara yadda zatayi se taga ya zauna kujera tare da daukar daya daga cikin books din gaban ta yace


" Ban taba sanin abinda kike karanta ba kenan"


Ta dube shi tace


" Kaima pharmacy kayi?"


Ya gyada Kai Yana ce Mata wanne course zasuyi gobe, ba tare da ta dube shi ba ta fada Masa, kokari take sosae wajen ganin tayi controlling bugun zuciyar ta, waye yace Mata heartbeat voluntary activity ne? Ita kanta zuciya nada intrinsic factors dake sata bugawa ita daya. A hankali ya fara Mata tambayoyin tana bashi amsa, se ya koma Yana tambayar ta inda Bata gane ba, Suka zauna har aka Kira sallar maghrib kafin ya wuce masallaci ita Kuma ta tattare gurin tayi ciki, alwala tayi ta dawo daki ta kalla madubi, a take murmushi ya kubce Mata Wanda tayi yafi a irga! Kamar Wasa kullum se sunyi karatu, wannan karatun da suke ba karamin faranta musu zukatan su yake ba, kafin wani lokacin sun fara shakuwa ta ban mamaki, kowa a gidan kallon su kawai yake, idan suna Abu ko baa fada maka ba kasan ba karamin son juna suke ba, Amma sun kasa furtawa . A Haka kwanaki Suka shude har ta bar ajin da take ta koma level 3 shi Kuma a lokacin ya kammalla service dinsa da yake Yi a wani babban pharmaceutical company cikin Lagos din. Ranar da yayi POP washegari da zai tafi kowa yayi tunanin aljanu ne da ita yadda ta dinga kuka kamar ranta zai fita, shi Kan shi baiyi kuka ba Amma ji yake kamar numfashin shi zaa yanke Masa. Tafiyar shi tasa ta koma kamar wata marar lafiya, Hajiya tun tana lallashin ta had ta fara Mata masifa


" To ki hada kayan ki ki koma can Gwaram din Mana, ni Naga jaraba tukunna meye tsakanin ku dashi da har kike neman zaucewa akan shi"


Tana kuka akan gado tace


" Hajiya son shi nake"


Hajiya ta dafe kirjin ta, idanu a waje, a wañnan lokacin mace tace tana son namiji ai babban abu ne, Hajiya ta Gama sallallami kafin Kuma ta zauna tace


" Kina da hankali kuwa? Kinsan me kike fada?"


Mamana ta share hawayen ta tace


" Ni dai na fada Miki Allah son shi nake, ji nake kamar kaina zai tabu"


Wasa Wasa karamar magana se ta Zama babba tun kakana Bai San abinda ke faruwa ba har Hajiya ta fada masa, to shima Abba na abinda ke faruwa dashi kenan, bansan waye yace musu shakuwa, soyayya abun Wasa bace. Shima ya sauke abinda yake ji ya samu mahaifin shi ya fada Masa. To cut the long story short, Mama ta auri Abba. Ya samu aiki anan pharmaceutical company da yayi service dasu, su sukai retaining din shi. Dan Haka cikin aminci ya koma Lagos ya zauna da Mamana. Tana karatun ta Yana aikin shi, bana tunanin se na fada muku yadda suke kaunar junan su, fada ma batawa. Shekara biyu tayi kafin ta Haifa sister, sunan ta Nasiba Bayan haihuwar ta da shekara bakwai sannan aka samu ciki na, tunda Mama ta samu ciki take rashin lafiya, so far rashin lafiyar da tayi ajalin ta kenan. Hakan yasa Hajiya ta dauki sister daga gidan ta take zuwa makaranta komai da komai, ita Kuma Mamana tana gida tana fama. A hankali tana turawa takai wata biyar, Abba aka tura shi wani aiki ikeja zaiyi kwanaki hudu, tunda Mama taji zancen Tafiyar take kuka, dukda bawai shi ne karon farko da yayi tafiya ba a shekara kusan bakwai da sukai aure, dukka hankalin shi ya tashi, kamar Kar yaje Amma Hajiya ta nuna mishi jinyar da take ne, ba wani Abu. A Haka ya tafi suna communicating, ranar da zai dawo taji karfin jikin ta sosae Dan har girki tayi da kanta, ta shirya tayi kyau dukda rama da Kuma rashin kuzari. Sede suna tafiya mota ta lalace cikin daji, tamkar wani setup Sega bandits daga only God knows where Suka kashe su. Shiru shiru Babu Abba Babu labari har washegari nan hankalin Mama da kowa ma ya tashi, pharmaceutical company din kanshi kokarin ganin sun samo masaniya akan hakan suke se a kwana na biyu zuwa uku sannan aka tsinci gawar wasu daga ciki a can cikin dajin, Haka aka zo aka fadawa kowa wannan mummunan bakin labari, ance daga nan Mamana ta daina magana, kullum kuka take, Babu mhmmm Babu uhm uhmm! Har aka fara tunanin ko shafan aljanu ne, da Baban Abba yaji hakan Suka tafi da ita rukiya kala kala Amma shiru, se da Baffa Muhammadu ya ganta sannan yace ba aljanu bane Post traumatic stress disorder, wadda muka fi kira da PTSD. A hankali ya hada Mata session da psychotherapist shi ne ma ta fara kokarin yin magana. A hankali cikin ya dinga girma har ya Isa haihuwa, daf da zata haihu Uncle Auwal ya samu aiki a embassy na Nigeria Dake UK, da zai tafi da matar shi Ummaah se ya dauki sister ya tafi da ita.


Ranar da Mamana ta fara labor a ranar Dadaa ya dawo daga Portugal ya Gama Msc din shi a QLS. Bai ma tsaya gidan su ba Dake cikin Kano ya nufi Tasha dan zuwa Gwaram, kafin motar ta tashi yaga wani distant relative din su Wanda ke fada Masa ai hajja Muna ta taho Kano saboda Mamana na labor Kuma yazo da gardama, Dole ya bar tashar ya nufi Aminu Kano Dan yasan nan zaa kawo ta. Yana shiga ta wajen labor room ya hango har mahaifiyar shi, ya karasa ko gaisawa baayi ba balle yayi gaisuwar Abba na da ya rasu, to wa ma zaiyiwa gaisuwa a wañnan tashin hankalin Suma da suke ciki, 


"Inna ya me jiki"


Jikin ta a sanyaye tace


" Se ta Allah kawai, yanzun ma aiki zasuyi mata Wai abinda ke cikin ta Yana cikin wahala"


Ya Dan runtse idanun shi Yana Jin wani irin ciwo a zuciyar shi, mahaifina kawun shi ne, Yama girme shi Amma Kuma su din kamar abokai Haka suke a dangi, musamman da take jikokin farkon Mata ne shi ne babba namiji a jikoki, shi Kuma Abba na bashi da kani ko saa se suke good time dashi, to ko rasuwar shi tazo ma Dadaa a mugun bazata Bai taba kawowa ba, Kuma Baba wato Baffa Muhammadu ya fada Masa halin da Mamana ke ciki, se hankalin shi ya Kara tashi, to gashi yanzun Kuma abin Babu dadi. Kan couch akai wheeling dinta anyi Mata shigar surgery, idanun ta a lumshe Amma ba bacci take ba, gefen hagun dinta Anty Mamaa ce da tazo daga Port Harcourt inda take aure, se hajja Muna a gefen Daman ta, ta Dan bude idanun ta anan idanun ta da Suka rine sukai ja jawur ya sauka Kan Dadaa dake tsaye Yana kallon ta in shock, ta rame ta lalace tayi Baki , se ya tuna farkon haduwar su Wanda shi yaje Lagos din kammalla degree dinsa daga Miami, yadda ta tarbe shi kamar ta San shi Kuma Basu taba haduwa ba kawai dai kamannin Abba ta gani, Abba ma baya nan se dare da ya dawo sannan ta fahimci waye ma yazo, she have the respect of almost every body in the family, kowa ya budi Baki A'ishan Lagos mutuniyar arziki ce, tana da kirki Haka ake fada.


Ta Dan kalle shi tare da Masa alamar yazo, a hankali ya karaso ta kalle shi se ta fara hawaye, a hankali tace


" Naji dadi dana ganka, nasan ba lallai na Kuma tashi ba, nasan kilan nabi bayan shi..."


Dadaa ya girgiza Mata Kai yace


" Ki daina fada Antin Uncle, Zaki tashi Inshaaa Allah"


Ta danyi murmushi tace


" Ko me na Haifa a yau na baka har abada, na baka ka zame Masa uwa da uba, aboki da komai na rayuwa, kada ka Bari ya fahimci shi maraya ne. Dan Allah Kai min haka..."


Bleeding tamkar ta Baki take, se karuwa yake ba tare da ta Gama magana ba aka tura ta tafi, suna shiga kafin a fara surgery dinma, an daura ta Kan table anyi komai, yankawa kawai zaayi se ta rasu, gaba daya team din sukai shiru, kowa se kallon ta yake, abin duniya yayi musu yawa, Babu abinda yafi tashin hankali irin a mutu akan table! Consulant din ya dakko fetal scope yasa a cikin ta se ga heart beat dina ana ji, cikin sauri yace musu ayi salvaging a fito da yaron ciki, aikuwa Haka akai shi ne aka fito Dani, Allah yace Yana fitar da rayayye daga cikin matacce!


Haka aka fito dani hade da corpse din Mamana, duniya kenan! A ranar da wani yazo a ranar wani yake tafiya! Mama ta mutu ni Kuma an haife ni, Babu Wanda yayi farin cikin zuwana kowa alhini da kukan rasuwar Mamana yake, Dadaa ya karbe ni ya rungume ni a jikin shi tun daga jariran taka kowa ya kalle ni yaga uwata, Kama muke sosae da sosae. Ana Gama sutura Yan Lagos Suka karaso da Kuma dangin Mama na kusa Dana nesa. Har lokacin Ina hannun Dadaa, ba Wanda yayi kokarin karba ta ma, se da aka kammalla Yi Mata sutura kafin ya kai wa mahaifiyar shi ni, ta hada ruwa tayi min wanka aka dakko sabon Kaya aka saka min sannan aka sama Madara aka fara bani na Dan karba kadan na bari, a bayan ta ta Goya ni saboda da tayi kokarin kaiwa hajja Muna da Kuma Hajiya ni kuka sukai tayi me ciwo Dole yasa ta goya ni. Washegari yayi min huduba da A'isha ba tare da ya bi takan kowa ba. Seda akai sadakar uku sannan hankalin mutane ya fara dawowa jikin su sannan hankalin su ya koma kaina aka fara tausaya min.


Washegari sadakar bakwai gidan ya dauka haramar watsewa, kowa Yana kokarin Kama gaban shi, Hajiya zata koma Lagos, Hajja zata koma Gwaram se kowanne yace zai dauke ni ya tafi dani, shiru Baffa Halilu da Kuma Uncle Aliyu shi ne babban yayan su Mama na, Yana zaune a sokoto da family din shi, idan so samu ne zai so shima ya dauke ni saboda kallo na kawai idan kayi zakaji tausayina ya ratsa zuciyar ka, gani Yar mitsitsiya tana da ciki Bata da lafiya bata ci adequate diet ba shiyasa aka samu restricted growth! Anty Mamaa tace


" Gaskiya kafin Yaya shatuu ta rasu Yaya ta bawa A'isha"


Hajja tace


" Eh dukka mun sani Amma har yanzun karamin Me gida baiyi aure ba, Ina zai aje jaririyar kwanaki?"


Se lokacin yayi magana yace


" Inna zata rike ta kafin nayi aure, Amma idan Bata Saba Dani ba tun yanzun idan tayi nisa rikon zaiyi wahala"


Baba na Lagos yace


" Tunda dai shi tace, to mu bar Masa a hannun shi, na tabbatar A'isha baza tayi maraici ba"


Abinda Baban Lagos yace yasa aka amince Dadaa ya zauna Dani. It wasn't easy at first dukda kusan duk wahalar Inna ke mini mahaifiyar shi, kannen shi na kula Dani sosae da sosae. A hankali ya fara aiki course din da yayi ana neman su a take ya samu aiki da albashi me tsokar gaske, degree din shi na farko yayi architecture da yazo Msc se yayi QLS. Riba biyu kenan!






BA NI DA LAIFI! Is not free, da N1000 zaka mallaki Ba Ni Da Laifi, Sahla A Paris da Kuma ABINDA YA BAKA TSORO. Da N750 zaka mallaki biyu da N350 zaka mallaki daya! Tafiyar sabuwa ce Kuma salon ma sabo ne. Kasance da Top-notch ta hanyar biyan kudi zuwa ga 3091721807 A'isha kwalam Hassan First Bank of Nigeria, send evidence of payment to *** or *** or ***.