WANI RABON........

CHAPTER 3

by @deejasmah

WANI RABON...............🦋🦋🦋




Khadeejah Bint Ismail (deejasmah)



Elegant Verified Writers (E.V.W)



In dedication to all single ladies out there.........


CHAPTER 3 (she's so sweet 1)


 _This whole chapter is wholely dedicated to Amaryar Muhammad (Zahara) this girl is actually amazing she's among the people who support me and been there for me she chatted saying she can even pay ko nawa ne for WANI RABON........That actually gat me Allah ya tsare ki a koina i really love you babe ............Enjoy this page and be safe❤🦋_ 


Tunda muka dawo gida bamu wani zauna ba fad'i tashi kawai mukeyi daga wannan zuwa wannan hidima sun taru sunyi min yawa saboda komai ni ce a gaba tun ba'a shiga hidimar sosai ba har na fara gajiya irin haka ina ga in an shiga bikin ai ina ganin bazan ganu ba tun daga lokacin na fara jinjina bestie da irin k'ok'arin a hidindimu na bata tab'a nuna gajiyawarta a lamura ba

Lefe ake shirin kawowa tun safe ta gudo gidanmu wai kunyar 'yan gidansu takeji ganin zuwanta yasa nima na kwanta a kusa da ita dama gidansu nai niyyar zuwa toh tunda ita tazo sai na fasa fira muka duk'ufa yi kamar an dad'e baa had'u ba girki mukayi tareda sake gyara gidan muka sake kwanciya kamar marasa mafad'a


"Bestie wai meye amfanin kwanciyarki a nan ?" ta tambaya tana mai kallo na hararar ta nayi tareda cewa " in ban kwanta ba goyaki zanyi" itama hararar tawa tayi tareda cewa " in ma kika goyani ai ba laifi kikayi ba besides,yanzu ni 'yar lallashi ce " ta k'arashe da zolaya 


Dariya na k'yalk'yale dashi tareda cewa " lallashi indeed, amma ai ba nawa ba ko saidai na Yaya Sahal" na fad'a ina mai kashe mata ido d'aya "dallacan ni ki tashi " ta fad'a cikin son gujewa maganar domin yanzu da an d'auko tad'in auren gocewa takeyi wai ita tana tsoron aure " wai in na tashi me zan miki ?! Toh na tashi menene ya faru?"


Gyara zama tayi tana fuskantata ba tareda tace komai ba sai bakinta da yake motsi ba tareda fitar harafi ko d'aya hakan yasa k'irjina ya fara bugawa jijjigata nayi tareda cewa " what's wrong bibti? " ajiyar zuciya tayi kafin tace " Nothing is wrong babe.........it is just something that is worrying me...........But inaso ki fahimceni please.......kar ki min bahagon fahimta " kallonta nayi da kyau kafin nace "OK inajinki" Ina mai tattara hankalina kaf a kanta


"Ermmm....lemme ask you first...... Hmmmm what do you think of Sahal?" ta tambaya tana mai kallon idanu na shiru nayi don ban ma san me zance ba wannan wani irin tambaya ne kuma daurewa nayi tareda cewa " ban gane me kike magana akai ba......What about him?" 


Ajiyar zuciya ta kuma saukewa a karo na barkatai kafin tace " Ina nufin me zaki iya fad'i akan Sahal when someone ask you about him and how much can you rate him as a husband" kallon tsaf nai mata kafin nace " Sahal is a nice person,yana d'aya daga d'aid'aikun mazan da na sani a rayuwata kuma zan iya bada shaida akanshi a koina.......Shi d'in mutum ne mai tsananin kirki da kulawa ga girmama lamuranki da duk abinda ya shafe ki sannan kuma yana da ibada ilimi da kuma wayewa ..........Muna mai fatan ya kasance miji Nagari domin dukkan hali da d'abiun shi sun nuna hakan"


Murmushi tayi kana tace "kina ganin cewa nayi dace da miji kuma abokin rayuwa?" dafe kaina nayi don tambayoyin ta sun fara yawa "uhmmm....ba ma keba ko wata mace burinta miji irin Sahal domin ya tara duk wasu characteristics na muradin mace ga mijin aure.....so ba abunda za mui miki sai tayaki murna domin Allah ya baki mijin da zakiyi alfahari dashi a matsayin miji uban y'ay'a kuma abokin rayuwa na har abada " na bata amsa Ina fatan hakan ya zama tambayar k'arshe don ban k'aunar su ko kad'an 

"Yawwa........zaki iya auren namiji irin Sahal ?" ta sake tambaya a gajarce na bata amsa da "eh mana " murmushi ta kuma saki kafin tace "then marry him.......... Let him be our husband ......" a firgice na mik'e Ina mai kallonta jikina har wani rawa yakeyi 'kaiiiii........ This girl can't be normal cos lafiyayyen mutum ba zaiyi hakan ba ' tambayar kaina nayi "shin ko dai aljanu gareta ne ?........." 


( ```in ma aljanu takeda kece ta farkon da zaki fara sani AI🙄)``` 


Katsemin tunani tayi ta hanyar takowa gabana tareda rik'e hannuna " are you sick or possessed?" na tambaya ina mai tab'a wuyanta ture hannuna tayi tareda cewa " babu abunda yake damuna lafiyata k'alau ......... Damuwarki ce kawai damuwa ta........" Katse ta nayi a hasale


 ".......Noosrah Maikwanoni kinga alamun ina cikin damuwa ne?,How on earth zakiyi wannan tunanin? Is it because banda miji ko kuma saboda ban samu damar aure bane ?..........shin na tsufa ne har haka shiyasa kika fara jin tausayina ko me ?........kema kina tunanin bazan auru ba ko?!" Hawaye ne suka fara sunturi a kunci na ban tab'a tunanin rana irinta yau zaizo gareni ba 

Saboda Allah baiyi zanyi aure ba shine Noosrah zata b'ullo da wannan maganar lallai kam !!! Dafani tayi itama tana hawaye " dama akwai randa zaki zargeni da miki shagub'e ko gori ?! Kar ki manta cewa ke d'in jinina ce abar alfaharina kenan yi miki gori daidai yake da yima kaina ......" 


Ture hannunta na sakeyi tareda hayayyak'o mata " in ba hakan ba to menene ? Ehhhh nace menene ?...........kallon cewa yanzu banda wani madafa a rayuwata kikeyi koh ?" 

Kuka ta fashe dashi tareda duk'awa a wurin juya mata baya nayi Ina mai k'ok'arin tsaida hawayen da yake zubomin amma na kasa don sai k'ara zuba yakeyi babu alamar zai tsaya juyo dani tayi tana mai cewa " this is actually not what I mean.......taya zakiy wannan tunanin babe...... Babu komai a zuciyata sai alkhairi......burina Inga kema kin samu natsuwa kamar kowacce mace shiyasa nace ki auri Sahal ba dan komai ba......." 


"Me yasa kike tunanin cewa zan iya auren mijinki........ko mutuwa kikayi bana fatan hakan,ko nama haka ba shi Sahal d'in yace miki zai iya auren mace irina ne? Kar ki manta da abunda ya faru a can baya da irin mazan da suka rabu dani ........."

Na fad'a cikin sanyin jiki murmushi tayi itama kafin tace " Sahal is a family zai iya aurenki in har na mai magana what matters is yarjewa da amincewar ki besides mazan da suka rabu dake a baya saboda ke d'in ba ajin auren ki bane,I believe Allah yana miki tanadi mafi alkhairi and I somehow believe that Sahal might be the man for you........."


Dariya na k'yalk'yace dashi tareda cewa " sannu hajiya........but I can't marry him......so you can rest,indai har kin yarda cewa Allah has greater plans for me then believe that Sahal can't be the man for me .........for he's been yours since from the beginning.......if I can't add to your happiness then bazan zama reason da zan rage miki jin dad'in rayuwa ba.........so kar ki sake tada wannan maganar please "


Gyad'a kai kawai tayi ba dan ta amince ba sai dan ba yadda ta iya dani gyalena na yafa tareda cewa "ni na tafi wurin kawo lefe" ban bata damar magana ba nai waje bayan na d'auki wayata ta baki ta sake tana kallona wato avoiding d'inta nakeyi domin tuntuni na gaya mata cewa bazan je wurin kawo lefen ba amma daga wannan maganar har na tashi 


Gidan su na nufa Ina mai sak'e-sak'e a zuciyata na tarar dangin ango har sun tafi masha Allah nake ta fad'i domin kayan sun had'u ba'a magana mutanen dak'in na gaisar kana na nemi wuri kusa da Anty Nafeesah yayar su Noosrah na zauna muna bud'e kayan tare muna yabawa 


"D'auke min kaya kukai min cikin d'aki naga harda masu bak'in jini a wurin kayan " shine maganar da ta katse mana firar da mukeyi k'asa-k'asa MAMA ce ta fad'a tana mai nunawa wasu almajirai kayan duka d'akin suka d'ago suna kallonta tashi Anty Nafeesah tayi tareda cewa " haba Mama wannan wani irin magana ne?"


"Auuuu Allah!? Wato so kike mu zuba ido yanda wasu suka kasa samun miji itama d'in ta kasa samu koh?" Ta fad'i tana mai rik'e baki jikina fara rawa yayi domin ba yau ta saba mun habaici ba ta cigaba da cewa "kuzo ku kwashe kayan nan nace!!" da sauri ko suka taho izuwa kan kayan kwashe su tass sukayi suka nufi ciki dasu 


Kallona Anty Nafeesahr tayi kana tace " Mama dan Allah ki dunga karantawa mana bai kamata ba wallahi ba fa a k'addarar ko wata mace bane aure da wuri ba......" Da sauri ta katse ta d cewa "dallah can rufe min baki sakarya kawai da kike wannan maganar ni na hanata tai aure ina ce bak'in fentin da yake bin gidansu ne yake sa mazan guduwa?, in ma haushi za'aji sai aji na uwarta ba nawa ba......."


Ban tsaya jin me zata k'arashe fad'i ba na nufi k'ofar gidan a guje hawaye nakeyi bana ko ganin gabana gidanmu na nufa ina mai tsiyayar hawaye hakan yasa na nufi d'akin Fav kawai na kwanta ina jin kaina yana wani irin sarawa kamar zai tsage gida biyu.............


.........Mamar nan fa uwar b'ari ce😏



 **_Hey fans I'm sorry for not updating frequently I'm a student kuma exams ne yake gabato mu so I'll only be posting when I get the chance may be sau d'aya a sati please bear with me as it is not easy daga na gama exams zan dinga updating akai-akai 


Thanks for your support and love💞_ 

** 

Deejasmah❤🦋🥀