CHAPTER 1
by @ashtar
DAN MAFIYA 🧛
#CHAPTER_1
By ✍️ Malik al-Ashtar
Alhamdulillahi ina godiya ga Allah maɗaukakin sarki da ya bani ikon fara rubutun wannan labari, ina fatan yadda na ɗora alƙalamina lafiya na saukeshi lafiya, Allah ka bani ikon rubuta abinda zai amfani wannan al'umma taAnnabi (S.A.W)
بسم الله الرحمن الرحيم
“Abinda ƴan mata suke nema waje ne ban sani ba. Kullum a cikin jaridu ana faɗa, koda yaushe har ma bisa yanakun gizo, maganar ake yi... Ta yaya har yanzu suke faɗawa a irin wannan tarkon?”
“Ai koda manya ana faɗa, ƴaƴanmu na yanzu ba zasu sauya ba ! Kawai sai dai mu roƙi Allah ya shirya mana su.”
“Ni fa a cikin daren nan na ji motsi a bayan gida amma sai nayi tunanin ko maguna ne..”
Cewar ɗaya daga cikin mutanen unguwar, wanda ya kasance shi ne gidansa yafi kusanci da inda aka tsinci gawa da safen nan..
“Koma dai meye a samu a sanar da danginta. Wa ya san ina ne gidansu?”
“Kai ni ban taɓa ganin yarinyar nan a wannan unguwar ba?” Cewar wani magidanci.
“Zai iya yiyuwa daga wani wajen aka kawo gawar aka jefar a nan.”
“Eh lallai hakan zai iya kasancewa.. baiwar Allah ƙaramar yarinya da ita.”
A takaice dai ina tsaye ne a cikin yan kallon wata gawa da aka jefar a cikin unguwa. Na je wucewa na ga cincirindon mutane, da son ganin me yake faruwa na kutsa kaina ciki.. nan take na bi sahun sauran ƴan unguwa, wato na tsinci kaina cikin firgici..
Abinda idanuwana suka gane min, gawar wata matashiyar budurwa da ba zata wuce shekaru ashirin ba, yashe a bayan gida cikin shara. Abin da yafi firgirtarwa a wannan lamarin ba ganin yarinyar da bamu sani ba ne babu rai, saidai halin da gangar jikinta yake ciki.
Babu wanda zai iya kallon wannan gawar ba tare da ya toshe hancinsa ko kuma ya toshe bakinsa da hannayen sa tsabar mamaki, firgici da kuma tsoro domin mutanen unguwar basu taɓa cin karo da irin wannan abin tsoratarwar ba.
Amma ina son na faɗa muku wani abu kafin na cigaba, na yi muku wasu tambayoyi kafin ku ƙara tsunduma cikin labarin da nake shirin baku.
Kuna tunanin duniya tana a yanda kuke ganin ta ne? Kuna tunanin wannan duniyar, iya mutane irin mu ne kaɗai ke rayuwa a cikinta? Wannan duniyar ɗauke take da mutane iri daban-daban, cunkushe take da mutane marasa imani wanda suka zaɓi wata hanya daban. Kuma idan nace wata hanya, zan bar ku kuyi tunanin ɗaya daga cikin tsananin tashin hankalin da zaku iya tunanowa. Ɗaya daga cikin abubuwa mafi ban tsoro da zaku iya tunani kuma zai iya kasantuwa da gaske. Ku je cen kololuwar tsoronku sannan ku yi tunanin wannan abun da kuke ganin ba zai yiwu ba, zai iya yiyuwa idan har kuka yi tunaninsa...
Wasu shekaru baya wani matashi da ke ƙoƙarin rasa kakarsa. Wacce ita ce ta rage masa a duniya, wacce ta tarbiyantar da shi ta kuma rene shi.
Lokacin da ta kwanta rashin lafiya, kuma ta tabbatar rashin lafiyar ba ta warkewa ba ce, bata ɓata lokaci ba wajen sanar da matashin sauyarin wato jikan nata domin kar ya yi mamaki idan ya wayi gari babu ita.
“Na san wannan ciwon ba na tashi ba ne Adamu. Na sha faɗa maka, ni ba madauwamiya ba ce. Ina tunanin lokaci ya yi da zan tafi, tafiya ta har abada.”
Matashin yaron a lokacin bai ɗauki maganar kakar tashi da wani muhimmanci ba. Shi da yake ganin ta a kullum tamkar wacce zata rayu har abada...
Hankalinsa bai fara tashi ba har sai da ya ga ciwon kakarsa kullum ƙara tsananta yake yi.
... Ta yaya zai cigaba da rayuwa kenan? Ta yaya zai samu abinda zai ci idan ya ji yunwa? Ina zai je ya cigaba da rayuwa? Domin ya sani bayan mutuwarta ya tabbatar za a kore shi daga cikin gidan da suke haya shi da kakarsa, wanda suke faɗi tashin haɗa dubu takwas na kuɗin haya kowanne ƙarshen wata.
Yana ƙoƙarin taimakawa kakarsa a kullum ganin ta samu lafiya amma duk da ƙoƙarinsa kullum jikin nata ba sauƙi ciwon arne.
Kwanaki uku kafin mutuwar kakarsa, shi da bai san ma kwanakin kakar tashi suna dab da ƙarewa ba, yana cikin tafiya babu nisa da gida... Ya fito ne domin siyawa Kaka ɗan kokon da zata sha. Saidai koda ya isa kusa da mai siyar da koko, ya duba ya ga ashe ya zubar da kuɗin da ke aljihunsa kuma bai san ina ba.
Babu halin da zai mayar da koko dan tuni an zuba masa. Bai yi taku biyar ba mai koko ta kira shi, tare da yi masa barazana ita da ƴan uwanta maza.
Kalma ɗaya ita ce “Ka biya kuɗin koko, ko kuwa yanzu ka yi nadama.”
Ku sani irin hakan ba sauƙi ne da shi ba... A cikin ɓoyayyar duniya gaban madubi ko kuma ƙwarya cike da ruwa ko ɗiyan wuri, bayan tautaruwarsa ta haska gaban uban sheɗanu. Tun daga yammacin ranar nan sheɗanu suka sanyawa Adamu idanu, aiki ya fara domin mayar da shi ɗaya daga cikin bayun baƙaƙen sheɗanu...
“Mintuna biyar ke gare ka a nan ka biya kuɗin kokon nan ! Idan ba haka ba zan yi maka jina-jina.”
Cewar ɗan uwan mai siyar da kokon, da ya yi ƙaurin suna wajen tantiranci a unguwar, tuni har ya bayar da wayarsa riƙo. Adamu a ɓangarensa, yasan tashi ta ƙare.
Me zai aikata? Wa zai ƙwace shi a hannun wannan ƙaton?
Kai ka ce babu mutane a gurin, basu ganin abinda ke faruwa alhali duk sun yi cincirindo abinci kawai suke son ba wa idanunsu.
“Shikenan!"
Cewar babban wan mai kokon da ya miƙe tsaye tare da cire rigarsa domin cika alƙawarinsa. Ya ɗaga hannu da niyyar sumar da Adamu, ya ji wani hannun ya tare nasa, tare da wata murya da ta ce :
“Nawa ne kuɗin kokon?”
Wani mutum ne. Babu wanda ya san daga ina ya fito, ko tun yaushe ya zo gurin.
Kowa kallon sa yake, zan iya cewa ma kamar ya ɗauke hankalinsu... Kuma ku yarda da ni, abinda ya aikata kenan.
“Hamsin ne !” Cewar mai koko.
Saka hannu ya yi aljihu ya fiddo galleliyar dubu biyar ya miƙawa mai kokon, kallon Adamu ya yi yace
“Zaka iya ƙara ɗauka idan kana so!”
Adamu saboda tsoro ya ƙi karɓar kyautar da mutumin ya yi masa, sannan ya tilasta yayyun mai kokon suka sake Adamu.
Adamu ya kama hanyar komawa gida lokacin wata mota ta shiga bin sa a baya. Tsayawa ya yi, ita ma motar ta faka. Wannan mutumin ne da ya ƙwace shi yanzu yake tambayar sa sunansa.
Adamu ya bashi amsa da “Sunana Adamu."
“...Adamu ka shirya mutuwa saboda naira 50? Ta yaya zaka zo shan abin mutane baka da kuɗi?”
“Da kuɗi na je amma na yar da su.”
“Hum.. wannan mutanen har kashe ka sun yi idan da ban zo ba..”
“Nagode malam.”
Lokacin da mutumin ya tambayi Adamu sauran bayani game da shi, ina mahaifansa suke, mutumin bai yi wannan tambayar ba kamar irin sauran mutanen kirki masu taimako, ya san abinda yake yi kuma ya san inda yake son amsar da Adamu zai bashi ta kai shi.
Dan haka Adamu ya bashi labarin ƴar ƙaramar rayuwar ƙuncinsa da ke ƙoƙarin sake taɓarɓarewa kuma daga wannan lokacin komai ya fara.
“Kana ji na Adamu, kana son kakarka?”
“Fiye da komai a duniyar nan?”
“Kuma na tabbatar ita ma tana sonka ko?”
“Fiye da komai !! Na san da kaka tana iya taimaka min yanzu, toh zata taimaka min, kuma da ban samu matsala na biyan kokon naira hamsin ba.”
“Abinda nake son ji kenan Adamu. Ni zan iya warkar da kakarka.”
Tuni fuskar Adamu ta kwashi annuri da jin wannan maganar kuma a shirye yake ya aikata komai domin ceto kakarsa. Cikin ƙaguwa ya matsu ya ji ta wacce hanya wannan baƙon mutumin zai taimaka masa.
“Zan iya warkar da kakarka amma ba zata sake rayuwa wannan duniyar ba. Ba zaka sake ganin ta ba, amma zata baka abinda kake so a lokacin da kake so!!”
“Toh amma ina zata cigaba rayuwa?”
“Inda zan tura ta a warkar da ita!! Zai kare ka daga shiga ƙunci da kuma damuwa!! Faɗa mini Adamu, ka tambayi kanka idan ta mutu yanzu yaya makomarka zata kasance? Ka tambayi kanka ya gobenka zata kasance? Na tabbatar ka yiwa kanka wannan tambayoyin kuma ka samu amsar su.”
Ƙwarai kuwa ɗan matashi Adamu yanada amsoshin wannan tambayoyin. Wanda duka amsoshinsu ke tattarewa su koma ga kalmar Wahala... Saidai lokacin da ya shiga tunani kafin ya bai wa mutumin amsa, mutumin yace masa
“Ina ganin ɓatawa kaina lokaci kawai nake, ni ka ga tafiyata.”
Baƙon mutumin nan ya shiga motarsa, yana ƙoƙarin rufo ƙofa, Adamu yace
“Malam me zan yi domin kakata ta samu lafiya sannan ta cigaba da taimaka min?”
Baƙon mutumin nan ya fiddo kansa daga cikin motar sannan yace wa Adamu.
“Kafin ta mutu, zaka rufe ta da ranta a wani ɓoyayyen guri wanda kai kaɗai ka san shi daga nan zata rayu kuma ta haskaka tauraruwarka...”
A bayyane yake, da fari Adamu bai fahimci abinda wannan baƙon mutumin yake son faɗa masa ba, amma abinda ya kamata ku sani shi ne wannan ƙaramin yaron mai suna Adamu, Ni ne...
TO BE CONTINUED...
Ku biyo ni domin jin ko Adamu zai amince da tayin wannan mutumin? Ko kuwa zai bar kakarsa ta mutu mutuwar ajali, ya tsinci kansa cikin ƙuncin rayuwa?
#Al_ashtar_novels