CHAPTER 2
by @ashtar
DAN MAFIYA 🧛♂️
#CHAPTER_2
By ✍️ Malik al-Ashtar
Labarina nake baku, irin rayuwar da na yi, abubuwan da na aikata da kuma zaɓin da na yi...
A ina nake ko yaya nake bayan na gama baku labari, wannan bai shafe ku ba... Na ɗau alhakin hakan kuma ina ganin lokaci ya yi da zan faɗa muku gaskiyar labari akan wannan duniyar da kuke ganin kyawunta...
Mu cigaba...
Ban san me zai faru ba da a ce nayi wani zaɓi daban, ban sani ba ko na kasance a yau ina baku wannan labarin amma abinda nake son ku sani shine ba kowa ne yake kamar ku, kamar su ko kamar mu ba.
Abinda nake gani, abinda na sani, inda nake zuwa ko inda nake shiga wani lokacin ma abinda nake ci, na tabbatar kai ba zaka taɓa iya yin sa...
Rayuwa ce, duniyar ce a haka take.
Kowa da irin zaɓin da ya yiwa rayuwarsa...
“Na binne ta da ranta? Kamar yaya na binne ta da ranta?” Adamu ya tambayi mutumin cikin kiɗimar jin zancensa.
“Ka san wata hanyar ce daban ta binne mutum da ransa?”
“Bata mutu ba kuma kana son na binne ta tun yanzu haka kake nufi?”
Mutumin bai ce komai ba, amma yanayin fuskarsa ya amsawa Adamu amsarsa.
“A'a! a'a gaskiya ba zan iya aikata hakan ba. Ka yi haƙuri malam! Zan jira har ta mutu sai na bizne ta. Amma da ranta? A'a, ba zai yiwu ba!”
“Ok kai ka sani! Amma bari na faɗa maka wani abu, kanada zaɓi kafin ta mutu ka ceci kakarka ka sama mata lafiya, zata cigaba da taimakon ka amma ba zaka iya ganin ta ba! Amma idan kana ganin zaka iya tsira nan gaba toh ka bar ta ta mutu na har abada sai in ga yanda za'a yi ta cigaba da taimakon ka.”
Ƙara shigewa ya yi cikin motarsa, wannan karon ya tada motar sannan ya tafi.
Yaro kuma matashi Adamu wanda ba kowa ba ne face ni, ya yi tsaye nan yana kallon motar tana yin nisa. Amma ba iya kallon motar nake yi ba, ina tunani ne akan abinda ya faɗa min amma abu ɗaya da nake da tabbacinsa shine ba zan aikata abinda ya nemi na aikata ba.
Zafin kokon da ke hannuna ne ya dawo da ni daga tunani, na tuna da nayi lattin zuwa gida kuma ya kamata na yi sauri na ba wa Kaka kokon ta sha.
Tunani cike fal a raina na isa gida... Saidai koda na isa kusa da gida, na ji kukan kaka da nishinta na raɗaɗin ciwo.
Shiga na yi da sauri na tarar da ita kwance a ƙasa, ta yi ƙoƙarin zuwa banɗaki ne amma bata yi nasara ba, shi ne ta faɗo daga bisa gado.
Dubawa na yi na ga tayi targaɗe a gwiwa..
Kama ta nayi na taimaka mata zuwa ban ɗaki. Yiwa kaka wanka da yi mata tsarki duk lokacin da tayi wata buƙata, shi yafi komai zama tashin hankali a wajena, ban taɓa tunanin wannan ranar zata zo ba. Abun al'ajabin yana gaba
Ban daina yiwa kaka tambayoyi ba, ina mata sannu amma duk da yawan magana irin na kaka ta kasa furta min ko kalma ɗaya tun bayan da na dawo, na kuma taimaka mata gurin wanka. Kallo na kawai take yi tana zubar da ƙwalla.
Dan haka na mayar da hankali akan wannan sabon al'amari na kaka, wajen yi mata tayin kokon da na siyo mata.
“Kaka na zuba miki kokon ne? Zaki sha koko?”
Idanunta kawai masu cike da hawaye ta kafa min amma babu ko kalma ɗaya da ta fito daga bakinta...
Kaka ba zata sake magana ba, domin sun rufe mata baki... A yau zan iya faɗa muku cewa sune sila, domin idan suna son abu, a shirye suke da yin komai ganin sun same shi.
Ana kiran hakan matsi dan ka yi sauƙin shiga ƙungiya, suna mayar da rayuwarka azaba na ɗan lokaci, masu raunin imani sai su shiga saboda basu iya jurewa ba.
Hmm.. wata ƙila nima ina ciki, wata ƙila kuma a'a domin ina yawan cewa kaina, na yi zaɓin ne saboda na rayu...
Daga ƙarshe dai kaka bata ci komai ba yammacin ranar... Saidai wani abu ya faru, lokacin da na so tursasa ta shan kokon, sai naji buƙatan shiga banɗaki ta kama ni lokaci guda. Na ajiye robar kokon bisa table gaban gadon kaka sannan na nufi banɗaki.
Lokacin da na dawo, babu koko a cikin robar, saidai kashi a ciki...
“Kaka me ya faru? Meye wannan?” Na tambayi kaka ina doɗe hanci saboda irin warin da kashin yake da... Ita kuma kaka tana kwance kamar yanda na bar ta... Cikin mintuna biyu waye ya shigo ya juye kokon ya zuba kashi a ciki?
Ita da bata magana ta yaya kenan zan san abinda ya faru?
Ɗaukar robar nayi na fita waje na jefar nesa da gida sannan na dawo... Kaka har yanzu ciwo sai cin ta yake kuma kamar wannan daren shine darenta na ƙarshe a duniya.
Eh na wani ɗan lokaci sai da nayi wannan tunanin, na ce komai ya zo ƙarshe.
Kukanta yana sosa min rai... Ban taɓa ganin ta a cikin irin wannan yanayin ba. Na dinga tuna rayuwata ta baya da ita, ina ganin matar da ta tarbiyantar da ni, ta ilmantar da ni, wacce ke bani shawara kuma ta saka ni makarantar boko na koyi karatu da rubutu daidai gwargwado...
Ba zan iya jurar wannan ba, zuwa nayi na zauna ƙofar gida ni kaɗai ina kallon sama ina tambayan Allah ya koro min mafita saidai ban samu amsa ba.
Lokaci guda wani tunani ya gifta ƙwaƙwalwata. Tunanin da naji kamar wutar lantarki ta ja ƙwaƙwalwata.
Ku tsoraci sharrin shaɗanu.. A daidai lokacin na ce wa kaina..
«Meye ribar barin kaka ta mutu a banza alhali zan iya amfani da mutuwarta na gyara gobena? Koma dai meye mutuwa zata yi wannan a zahiri yake. Zan iya amfani da mutuwarta ni na ceci kaina.»
«In fa na binne ta da ranta kamar yanda wannan mutumin yace min?»
Juyawa nayi na kalli cikin gidan, na gan ta kwance ko motsin kirki bata yi.
Kamar tuni amincewata kawai ake jira, komai ya haɗu, daidai ƙofar shigowa gida ga kwashe nan da felu ajiye... Zaɓi na riga na yi.
Cikin daƙiƙa ɗaya na yanke hukunci, aikatawa da sauri kafin lokaci ya ƙure mini. Tashi nayi na ɗauki felu da kwashe na nufi bayan gida, na shiga haƙar rami.
Ban kwashe ko awa biyu ba na haƙa katon rami. Ji nayi kamar wasu mutanen ɓoye suna taimaka min.
Wanda hakan tana iya yiyuwa domin an riga da an zaɓe ni, kuma ya kamata na shiga ƙungiya...
Na gama haƙa rami, na koma cikin gida na tarar da kaka, bacci take domin har yanzu ina iya jiyo bugun zuciyarta.
Amma da rauni a cikin bugawar zuciyar tata dan haka nayi saurin takawa da ita zuwa bakin ramin... Ba kamar lokacin da nake kaita banɗaki ba, wannan karon sai na ji ta batada nauyi.
Na isa bakin ramin da ita, ko idanu ta kasa buɗewa saboda azabar ciwo da kuma gajiya. Na saka ta cikin ramin a hankali cikin kulawa.
Ba zan taɓa mantawa da kallon da ta yi min ba a wannan daren.
Farin watan da ke haskawa a daren, gajimare sun ɓoye shi. Sama tayi baƙi kamar za a yi ruwa amma ba haka ba ne. Hanyata ce, alamu ne na shigata sabuwar rayuwa...
Ɓakar rayuwa...
“Sai wata rana kaka!” Na faɗa a hankali.
Sannan na shiga mayar da ƙasar ramin.. felu bayan felu... Har sai da na gama rufe ramin ɓaki ɗaya...
TO BE CONTINUED...
#al_ashtar_novels