DAN MAFIYA

CHAPTER 3

by @ashtar

DAN MAFIYA 🧛‍♂️


#CHAPTER_3


Abu ɗaya da nake da tabbacinsa, canji na rayuwata.. duk da har yanzu a zahiri ina a ni ɗin, amma ina jin sauyi a cikin jikina da kuma rashin wani babban ɓangare nawa da nake ji...


Kakata, mutuniyar kirki kakata wacce a yanzu haka take turbuɗe a cikin ƙasa kuma ba zan sake ganin ta ba, duk da na san zata cigaba da kasancewa da ni kamar yanda wannan mutumin yace faɗa.


Sai dai ba a nan gizo ke saƙar ba, kada ku manta kowane abu da zamu aikata yanada sakamako. Baku lura ba, amma ban cika ka'idojin da mutumin nan ya gindaya min ba...


Zaku fagimta nan gaba.. amma bari na cigaba da baku labari.


Ina tsaye gaban tudun kabarin da na yiwa kaka lokacin da na ji waƙa da kiɗa na tashi daga sama. Ban san daga ina kiɗan ke fitowa ba amma kamar daga nesa nake jiwo shi. Har yau ina tuna wasu daga cikin baitocin «Kutu kutu absisko..kudum..gadam..»

Ga kuma sautin kiɗa dake tashi kamar ganguna. Kamar irin kiɗan borin nan, na shiga neman inda kiɗan ke fitowa amma kamar ƙara kusanto inda nake yake yi..


Tuni tsoro ya shige ni, na zubar da komai na ruga ɗaki dan na ɓuya, saidai har cen ɗin ma ba tsira zan yi ba. Na ƙaraso bakin ƙofar ɗakin na shiga na garƙame da sakata, ko'ina na jikina rawa yake tsabar tsoro.


Jikina ya bani kamar ba ni kaɗai ba ne a ɗakin, kuma haka ne... Ban san ta yaya ya shigo ba, kawai sai ganin sa nayi zaune bakin gado kusa da kujerar da nake zaune.


Firgita nayi cikin tsoro tare da ja da baya, shi kuwa bai motsa ba. Mutum ne sanye da irin doguwar rigar nan baƙa wacce ta rufe shi duka daga ƙafa har fuska, ba yanda za a yi na san waye yake gabana, koma dai meye wannan ba mutum bane kamar kowa.


Da ka gan shi kasan za a yi tsantsar rashin imani a gurin.


Lokaci guda babu hanyar guduwa, kuma cikin jikina na ji kamar an sakawa ruhina linzami akan dole sai na yiwa wani abu ko wani biyayya.


“Barka da zuwa cikinmu.”


Abinda yace min kenan.. muryarsa tana kama da ta mutumin da ya tsufa sosai wanda magana ma wahala take masa, da jin muryar zaka san akwai gajiya ga mamallakinta.


“Ka zaɓi sabuwar rayuwa kuma ba zaka yi nadama ba!! Ga abinda zaka yi..”


Wani abun kuma hallau..?


“Zaka je cikin birni sannan zaka je anguwar GRA, idan ka isa cen ka gabatar da kanka a matsayin mamallakin gidan da aka rubuta na siyarwa ne daga nan za a baka makullan gidan... Bayan ka karɓi makullan a cikin gidan zaka samu abubuwan da zaka yi rayuwa... Kwana uku gare ka!!”


Yana gama faɗar haka.. ya ɓace ɓat.


Tambayar kaina nayi idan ya dace na yi biyayya akan abinda ya faɗa.. in ɗauki ƙafa in tafi cikin birni wannan baya cikin tsarina... In je garin da ban san kowa ba? Na fara sabuwar rayuwa?


A'a ban shiryawa wannan ba. Saidai na manta da wani abu...

Washe gari na zauna baƙin ƙofar gida tsawon yinin ranar, ina tunanin abinda na aikata.. Ƙuzari da tsoro ne suka min ƙaranci na zuwa ganin inda na binne kaka har ma na tono ta. Toh ko zan tarar da ita har yanzu da rai? Bana tunanin haka!! Ina ganin mafita ɗaya ce na bar ta cen cikin ramin wanda shi ne makwancinta na har abada...


“Wai Adamu ina kaka? Tun safe har yanzu bamu gan ta ba.” Wani maƙocinmu ne ya katse ni ta hanyar tambayata inda kaka take.


“Kaka...? Ban...sani ba! Ina bacci lokacin da ta fita.”


“Ta fita? Ita da batada lafiya.. Jiya ma fa na leƙa da yamma, ban tarar da kai ba har tace na ɗauko mata magungunanta...”


Tuni na bada kaina, faɗin kaka ta fita ba dabara bace mai kyau. Amma da yake ba zan iya dawowa bisa maganata ba, dan haka dolena na ƙara yi masa wata ƙaryar.


“Eh..am..ta samu sauƙi! Jiya ɗin ma magungunan ne na je samo mata.”


“Ah toh madallah.. zan sake dawowa zuwa dare sai na gan ta.”


Da dare na rufe ƙofa lokacin da suka dawo. Suka yi ta bubbugawa har suka gaji amma na ƙi buɗewa. Saidai dandanan labari ya baza anguwa kamar wutar jeji... Kowa ya shiga tambayar ina kaka, har zuwa washe gari da safe, ƴan unguwa suka taru suna min barazanar na fiddo inda na kai kaka idan ba haka su kai wa ƴan sanda ni.


Ban san duk wannan matsin na meye ba.. har sai daga ƙarshe na fahimci duk cikin shirin baƙaƙen sheɗanu ne dan su same ni...


“Mun baka nan da gobe ka fiddo ta inda ka kaita. Idan ba haka ba zaka gani!”


Washe garin ma suka dawo, na sha barazana sosai da yasa na cewa kaina mafita ɗaya da nake da, ita ce na gudu.. na bar garin nan...


Toh amma ina zan je?...


Sake tunawa nayi da maganganun wannan mutumin mai baƙaƙen kaya sannan na ce wa kaina, zuwa birni wata ƙila ita ce mafita gare ni...


Dan haka wajen ƙarfe uku na dare na fito daga gida lokacin kowa na bacci na gudu. Ban damu da me zai biyo baya ba idan sun wayi gari sun ga bani nan..


Dan haka na ɗauki hanyar birni tare da ɗari biyar ɗin da na samu cikin wani tsohon kwagirin kaka...


Na isa birni, na yi tambaya da unguwar da wannan mutumin ya faɗa min. Aka min kwatance tare da sanar da ni lallai akwai nisa unguwar. Toh ina da wani zaɓi ne ni? Na take ta a ƙafa, na isa unguwar wajen ƙarfe takwas na dare. Na yi tambaya da gidan aka gwada min.. Irin ƙaton gidan nan ne.. villa guda, akwai mai gadi, wanda da alamu ni yake jira.


“Ina wuni malam? Kai ne Malam Adamu?” Cewar mai gadin.


“Eh ni ne.” Na amsa masa.


“Dama kai nake jira ! Ga makullan gidan.”


Na kasa yarda! Cikin sauƙi haka! Ban yi tunanin sauƙin har haka ba... Ban faɗa muku irin tsari gidan da ke gabana ba.. Ku kira shi Masarauta!


Karɓar makullan nayi, yayi min iso zuwa ƙofar gidan. Na buɗe ƙofar na shiga.


Komai akwai !


Tunda nake a rayuwata ban taɓa ganin gida na alfarma ba irin wannan.. lokaci guda na manta da duk wata wahalata da ƙuncina.


Mai gadin yace min

“Kakarka tace...”


Ban bar shi ya ƙarasa ba.

Nace

“Wa ka ce? Ka ce wa tawa?”


“Wata dattijuwa ta zo nan, ta ce kakarka ce ita.”


Dandanan na tuna da maganar wannan mutumin da yace kakata zata cigaba da kula da ni, amma sai na binne ta da ranta.


Na tabbatar abinda yake faruwa yanzun kenan.


“Nagode zaka iya tafiya.” Na sallami mai gadin.


Ya fita ni kuma na tsaya a cikin gidan, wannan ƙaton gidan.. na shiga duba ko'ina na gidan, ban ƙara jin daɗi ba sai da na ga ɗakina, banɗakina da duk wani abun da kuka sani na jin daɗin rayuwa...


Har da rafas na kuɗi masu yawa cikin drawer na.


Saidai murnata ta koma ciki, domin bayan sati ɗaya da dawowata... Tsakiyar dare na farka daga bacci saboda zafi, na yanke shawarar fitowa waje dan na ɗan sha iska.


Ina yin hakan akai-akai tsawon lokaci, dan haka har na saba...


Na fito tsakar gida, ina miƙa tareda hamma lokacin da na ɗaga kaina zuwa ƙofa idanuna suka sauka kan kakata...


Tana sanye doguwar farar rigar, hawaye da jini na fita a idanunta... Hannunta ɗaya kan ɗaya tana roƙo na... Dalili?


Ban sani ba...


TO BE CONTINUED...


Comments da like ɗin ku suna ƙara karfara min gwiwa nagode sosai da sakonninku