DAN MAFIYA

CHAPTER 4

by @ashtar

DAN MAFIYA 🧛‍♂️


#CHAPTER_4


By Malik al-Ashtar


Wannan ne karon farko da haka ta faru da ni, kallon ta nake. Gata nan a gabana, ko a cikin dubu zan iya gane kakata, ita ce da kanta.


Wani sanyi na ji ya ratsa duka ilahirin jikina, tuni jikina ya ɗau kyarma da na gane ta. Ko kalma ɗaya ta gagara fitowa daga bakina, ita kuwa kara matsowa inda nake kawai take yi, har yanzu hannunta ɗaya kan ɗaya kamar tana son tambaya na wani abu... Kamar tana roƙo na na bata wani abu.


Wata ƙila ƴancinta...amma ban fahimci hakan ba tun yanzu... Abinda kawai nake ji shine tsoro.


Komawa nayi da gudu cikin gida, na rufe ƙofa da makulli sannan na koma kan window ina leƙon ko zan gan ta amma ban gan ta ba.


Ban samu runtsawa a wannan daren ba... Kowanne motsi na gidan firgita ni yake... Ji nake kawai zata iya bayyana a gabana kowane lokaci.


Ina cikin safa da marwa cikin gidan, lokacin da na ji wani babban sauti ya fito ta baya ɓangaren kitchen.. sautin sosai ne da ya sa ni bayan na firgita na kusan saka ƙara kafin na yanke shawarar tafiya na duba cikin kitchen ɗin.


Cikina ya ɗuri ruwan tsoro har ma sun kawo min wuya, domin yanda zuciyata take bugawa kamar zata fasa ƙirjina ta fito.


A hankali nake nufar cikin corridor mai zuwa kitchen.. bisa diga digin ƙafafuna nake tafiya. Matsawa nake, ina takawa cikin sanɗa, ina kai wa cikin tsoro na tura ƙofar shiga kitchen ɗin a hankali sannan na duba cikin kitchen ɗin babu kowa, amma taga a buɗe take.


Na duba ko'ina cikin kitchen É—in na duba ban ga kowa ba... Na shiga ciki domin rufe tagar...


Toh fa, ku sani tagogina irin masu murafen nan ne wanda ke a waje, dan haka na fitar da hannuna domin kamo murfin tagar na janyo shi zuwa gare ni, sa'in da lokaci guda na ji wani ya riƙe min hannu..


Ban sani ba ko tsoron kar a janye ni ta taga ne, ko tsoron sanin wanda ya danƙe min hannu, tunanin cewa kakata... ban san wane daga ciki yafi saka ni yin ihu ba.


Saidai ni kaɗai a cikin ƙaton gidan, hatta mai gadin nan ma da na tarar yayi tafiyarsa..


Ihu nake da iya ƙarfina ina kokowar ganin na ƙwaci hannuna saidai shi ma wannan mutumin ko wannan aljani ko kuma fatalwar da ta riƙe min hannu bata zo da wasa ba.


Bayan kwashe tsawon wasu mintuna muna dambarwa, daga ƙarshe nayi nasarar ƙwatar kaina... Da gudu na koma ɗakina. Ni da nake tunanin na tsira, nayi kiciɓus hanci da hanci da kaka zaune bisa gado tana kuka kuma kamar ɗazun tana nuna min hannayenta.


Abun yayi yawa, na fice da gudu daga gidan gaba ɗaya. Ban tsaya ko'ina ba sai gaban wani ƙaramin restaurant da suke ƙoƙarin rufewa, da yake kusan ƙarfe uku da rabi ne na dare.. Kallo mutanen restaurant ɗin suke bi na da shi, da tunanin me nake yi a wannan lokacin waje. Sai ma da nace a haɗa min shayi.. nayi kamar lafiyata ƙalau dan kar na jawowa kaina zargi, sannan na zauna ina sake nazarin abinda ke faruwa da ni. Ina tunanin ta yaya zai yiwu a ce ina ganin kaka, ko dai ta mutu ne ba a wata duniyar take ba?


Haka safiyar Allah ta tarar da ni a waje, sannan na koma gida.. Shuru babu motsin komai. Babu wani baƙon abu na tsoratarwa.


Kwantawa nayi bacci domin a gajiye nake sosai. Nayi bacci da tunanin komai ya ƙare ...


Saidai nayi kuskure babba... Ba ma ɗan ƙarami ba...


Ina zaune a falo, ina kallon tv, lokacin da na ga kamar giftawar mutum a tsakar gida.


Hallau dai kaka ce ta dawo...

Miƙewa nayi da sauri amma ban gudu ba, ina kallon ta, eh kaka ce dai da kanta. Na kalle ta da kyau cikin idanunta duk jini.. na sake guduwa wannan karon ma na tsaya a waje.


A kwana na uku lokacin da na sake ganin ta, tana riƙe da bulala a hannunta tayi ta bi na da gudu. A kwana na huɗu, da wuƙa ta biyo ni. Haka sauran kwanaki.. dan haka ina cikin babban haɗari.


Gajiya kam na gaji, buƙatata kawai na gudu na tsira da raina. Na gaji da zama a gidan nan. Na ce wa kaina kawai wannan mutumin ya damfare ni ne ta hanyar yi min alƙawarin farin ciki...


Na shirya barin gidan kenan lokacin da na ga wata babbar mota ta faka a gabana. Tsayawa nayi ina kallon waye zai fito daga ciki. Mutumin nan ne da ya taimaka min lokacin da na kasa biyan hamsin É—in koko.


Galala na saki baki ina kallon sa, ƙarasowa ya yi kusa da ni sannan yace da ni na biyo shi zuwa cikin gida. Na bi bayansa ba tare da wata gardama ba.


Muka shiga ciki, ya zauna sannan ya nemi da na bashi ruwa.. na ce da shi

“Me yasa ka damfare ni?”


“Akan me kake magana?” Ya faɗa da mamaki a fuskarsa.


“Ka faɗa min kakata zata kula da ni idan na binne ta da ranta kuma na yi, tsawon mako guda kenan tana fito min har tana ƙoƙarin son kashe ni.”


Yanayin fuskarsa ne ya sauya, kuma abu na farko da ya tambaye ni shi ne

“A ina ka binne kakar taka?”


“Bayan gidanmu.” Na bashi amsa.


“Bayan gidanku fa ka ce? A nan dai inda na sani? Gurin yana da sirri ne?”


Sai a lokacin na tuna da ban binne kaka guri na sirri wanda ni kaÉ—ai na sani kamar yanda ya umurce ni. Kuskuren nake faÉ—a muku kenan na yi wancen karon..


Amma bari na faÉ—a muku wani abu mai firgirtarwa... Duk wannan cikin shirinsu ne.. sun san cewa ba zan yi kamar yanda suka ce ba kafin su aikata nasu plan É—in a kaina...


“Amma...” Na so yin magana amma ya katse ni.


“Baka yi yanda na faɗa maka ka yi ba Adamu! Baka bi sharuɗɗana ba!”


Ya shiga kallon ko'ina na gida cikin tsoro...kafin ya ƙara da cewa

“Kana da sa'a ma. Da da daɗewa ya kamata a ce ta kashe ka. Kada ka zauna a gidan nan kafin mu gama abinda zamu yi, ka zo tare da ni !”


Da jin haka, na yi tunanin ga mafita na samu. A alhali ƙara tsunduma kaina ne zan yi !


Na fito tare da shi muka shiga mota... Ya shiga gudu kamar zamu bar ƙasar! Sosai hankalinsa yake ga tuƙi. Muka isa wajen wani mutum da zubin sa yayi min kama da bokaye.


“Jira ni ina zuwa.” Mutumin da na zo da shi ya ce min.


Ya matsa kusan mutumin, suka fara magana mai zubin bokayen yana yi yana kallo na. Kuɗi na gani mutumin da na zo da shi ya fiddo ya zuba cikin ƙwarya. Kafin ya juyo kaina ya ce

“Bi bayan shi.”


Matsawa nayi na bi inda mutumin ya nufa da tuni har ya kusan kai wa wani É—aki... BuÉ—e É—akin yayi da cikinsa yake da launin ja. Nuni yayi min da hannu akan na shigo..


Na shiga.. ya rufe ƙofa.. ɗakin duhu ke gare shi sosai amma da yake akwai wutacen kyandir, ina iya ganin ƙwanƙwamai ko'ina jikin bangon ɗakin. Da hannuwan mutune har ma da idanuwa.


Abubuwa na ban tsoro birjik a cikin ɗakin. Sannan yace da ni na shiga cikin wani zagaye. Ban ga jan zagayen da ke ƙasa ba har sai da ya nuna min. Na shiga, ya fara karanto wasu kalamai da ban san ma'anarsu ba. Ji nayi kamar wani abu na fita daga cikin jikina. Kamar ana zuƙe duka ƙarfin jikina, kamar wani abu na sakin ruhin jikina.


Bayan wani É—an lokaci mutumin ya matso kusa da ni..


“karɓi ka ci!”


Ya miƙo wani abu a hannunsa, wani abu da yake bugawa kuma lokaci guda yake zubar da jini...


“Meye wannan?” Na tambaye shi.


“Zuciyar kare ne kuma zaka cinye ta tun tana bugawa, ta hakan ne kawai miyagun fatalwu zasu shafa maka lafiya...”


TO BE CONTINUED...