DAN MAFIYA

CHAPTER 5

by @ashtar

DAN MAFIYA 🧛‍♂️


#CHAPTER_5


By ✍️ Malik al-Ashtar


Tuni aiki ya kankama, kuma bari na faɗa muku idan mutum ya kai wannan matakin, cewa ya janye ƙafa ya fasa ba ƙaramin babban kuskure ba ne.


“Zuciyar kare? Kuma bayan haka ma tana...”


“Shiiiit! Ba a ɗaga mana murya a nan ! Zaka ci ne ko a'a?”


“A'a gaskiya ba zan iya ba ! Ba zan iya cin wannan abun ba.”


Zan iya amincewa na ci lafiyayyen abinci ba tare da nayi wata tambaya ba amma yanzu, a gabana zuciyar kare tana bugawa har tana zubar da jini, inaaa ba zan iya ba..


Wani mugun kallo yayi min kafin ya fita daga ɗakin. Ban san me yasa na ƙi bin bayansa ba, ina nan zaune na wasu ƴan mintuna kafin ƙofa ta buɗo, ba shi ba ne, wannan mutumin nan ne da muka zo tare.


A fusace yake sosai...


“A'a, a'a ba zaka watsa min ƙasa a ido ba Adamu !! Ba zan yarda da wannan ba. Ka san me yasa muka zo nan da kuma abinda ya kamata ka yi.


”Amma ya nemi da na ci zuciyar...”


Ban ma kai ƙarasawa ba ya daka min tsawa..


“TOH KA CI MANA !! EH ZUCIYAR DA YA BAKA !! KAFI KOWA SANIN ME KE FARUWA DA KAI A WANNAN LOKACIN... DAN HAKA DA NA KAWO KA DAN KA YI ABINDA AKA CE NE !!”


Cikin tsawa sosai yake magana da nayi tunanin duka na zai yi. Na yi shuru ban sake cewa komai ba.


“Zai dawo kuma zaka yi duk abinda ya ce!”


Ban san ta yaya ba sai na tsinci kaina ina mai gyaÉ—a kai alamar toh... Ya fita bayan wasu Ć´an mintuna mutumin ya dawo, babu alamar fara'a ko kaÉ—an a fuskarsa.


Ya sake ɗaukar zuciyar inda ya ajiye ta ya sake miƙo min ba tare da ya ce komai ba wannan karon... Na tara hannuna na karɓi zuciyar. Ina mai tabbatar muku ikon Allah ne kawai yasa ban yi amai ba.


“Ci!!”


Na kai zuciyar wajen bakina da ke buɗewa a hankali, wani iska na ji ya dakar min fuska... alamu na ina dab da shiga hannun baƙaƙen sheɗanu ne, suna ƙarasa cire min duk wani sauran imani da ya rage min...

Na saka zuciyar cikin bakina lokaci guda na haÉ—iye ta ba tare da na tauna ba...


“Kana shiga sabuwar duniya kuma baka san me ya dace ka yi ba. Nan ba inda ka sani ba ne. Kai ma ba wanda ka sani ba ne a baya.”


Kalaman da ya faɗa min kenan... Sannan ya cigaba da faɗar kalaman tsafin sa yana kewaya ni ba tare da ya ƙetaro wannan jan kewayen da nake ciki ba.


Cen ya faɗi wasu kalamai da ƙarfi, lokaci guda na ga kaka ta bayyana gurin... Tsorata nayi amma na ga mutumin yana bai wa fatalwar kaka umurni.


“Kada ki sake bayanna a idanunsa ! Kin yi rayuwarki kuma kin yi lokacinki dan haka ki ɓace bana son sake ganin ki.”


Kaka da hawaye a idanunta, har yau tana cigaba da kallo na. Tana ciki damuwa. A bayyane yake da ka gan ta ka san tana shan wahala. Ba a ɗau lokaci ba Kaka ta ɓace.


“Shikenan, fito daga zagayen !”

Yace da ni.


Na fito daga cikin jan kewayen, na ji ni na daban. Ina jin wani ƙarfi tattare da ni... Karon farko na ji ina iya taka uban kowa.. sai dai har yanzu ban san ta yaya zan yi amfani da wannan sabon ƙarfin nawa ba.


Na fito daga cikin É—akin na tarar da mutumin da muka zo tare a waje, murmushi yayi min irin ko ni fah yanzu da nayi biyayya.


Lokacin da na ƙaraso kusa da shi, ya ɗan bubbugi kafaɗata sannan ya ce min

“Daga yau ka dinga saurarar sharuɗɗan da aka gindaya maka, idan ka yi hakan ka yarda da ni babu makamancin haka da zaka aikata.”


“Toh, kenan shikenan ba zata sake zuwar min ba?”


“Ranar da ta sake zuwar maka, ka manta da ka taɓa sani na. Na yi maka alƙawarin ba zaka sake ganin ta ba!!”


A daidai lokacin, na ji wani kwanciyar hankali ya saukar min, kuma abinda nake so kenan ! Cigaba da rayuwata ba tare da na sake ganin ta ba.. duk da kakata ce, tana tsorata ni sosai lokacin da take zuwar min.”


Duk da fari ban yarda ba, na ɗauki yardata na basu. Har gida ya raka ni yana sake tabbatar min da na kwantar da hankalina babu abinda zai ƙara samu na.


Rashin babu inda zan je, dole na koma gidan da wai kakata ce ta bani.. lokacin da na shigo gidan, na duba kowanne lungu na gidan dan na tabbatarwa kaina ba zan sake ganin ta ba.


Kuma abinda ya faru kenan, ban sake ganin kaka ba...


Dan haka na cigaba da ƴar rayuwata da ƴan kuɗaɗen da na tarar a gidan saidai sun fara ƙarewa. Nayi amfani da su wajen buɗe ido a gari, wurare na gani na faɗa. Ban san me yasa ba amma abubuwan ƙyalƙyali da kyau sun fi ɗaukan hankalina.


Ban faɗa muku irin ƙarfin ikon da na samu ba, irin nicknames na masu kuɗi da ake kira na da su, haɗaɗɗun ƴan mata da kullum suke manne a jikina kuma ba kowanne ba.


Tuni ƙaurin sunana ya ratsa ko'ina na birni.. cikin ƙanƙanin lokaci na dawo matashin saurayi wanda ko'ina maganarsa ake... Bana iya zuwa wani guri ba tare da na janyo hankalin mutane ba.


Har aka zo lokacin da kuɗi suka fara ƙarewa. Daidai lokacin da zan ƙara ɗaura ɗamarar shiga sabuwar rayuwar da na zaɓawa kaina.


Mutumin nan da har yanzu ban san sunansa ba, yazo daidai lokacin da nake yiwa kaina tambayar ta yaya zan cigaba da rayuwa yanzu...


Kamar ya sani...


“Toh ya kake Adamu?”


“Lafiya nake ɓangaren lafiyar jiki, kakata bata sake fito min ba, dan haka lafiya lau nake zaune.”


“Good, toh bayan wannan babu wani abu?”


“Na tarar da wasu ƴan kuɗaɗe lokacin da na zo gidan nan, amma sun ƙare bayan nayi amfani da su.”


“Eh wannan haka ne, ana amfani da kuɗi dan biyan buƙata ! Ba dan a ajiye su ba. Kuma dole ne su ƙare kuma idan sun ƙare dole ka nemi wasu. Je ka shirya, zan kai ka wani guri.”


Na shiga É—aki na shirya, muka shiga mota ya kai ni cikin wata babbar ma'aikata... Muka shiga, ya kai ni wajen babban oga sannan ya ce

“Gashi nan ! Ya shirya kuma zai iya farawa !!”


Shekaruna 24 a lokacin...


TO BE CONTINUED...