CHAPTER 6
by @ashtar
DAN MAFIYA 🧛♂️
#CHAPTER_6
By ✍️ Malik al-Ashtar
Tambayar da nake yiwa kaina ita ce akan me na shirya, me yake nufi da zan iya farawa...
Ogan ya kalle ni daga ƙasa zuwa sama sannan ya cewa mutumin
“Okay ! Zamu gani abinda yake iya yi ! Toh ka san ai inda ya kamata ka kai shi.”
“Eh na biyo ne kawai dan sanar da ke zai fara kasancewa tare da mu.”
“Barka da zuwa yaro fatan za'a dage da ƙoƙari ! Ka kasance a koda yaushe kanka tsaye idan kana son wani abu, kada ka ji tsoro. Daga yau kai ma nan gidanku ne.”
Godiya nayi. Har wannan lokacin ban san akan me ake magana ba, abinda kawai na sani shine na shirya kamar yanda wannan mutumin ya faɗa.
Muka fito daga ofishin oga muka shiga wani ofishin da muka tarar da wani mutum... Wani mutum dattijo da babu alamun kirki gare shi. Har yanayin yanda yake ɗaga ido ya kalle ni abin tsoro.
Dole ni nayi ƙasa da nawa idanun har zuwa lokacin da mutumin da na zo tare da shi ya taɓa kafaɗata alamar na kama jikina.
“Kun je wajen Alhaji Batagame ne?” Mutumin ya tambaye mu.
“Daga cen muke kai tsaye shi yace na kawo yaron nan.”
“Okay, ya zauna kafin na gama wani aiki.”
Aka nunan kujera sannan mutumin da na zo tare da shi yace min
“Ka yi abinda ya ce maka... Zan zo na duba ka gobe.”
Na amsa da okay. Ya fita ya bar ni da wannan mutumin da alamu suka nuna hankalinsa yana kan abinda yake yi. Na yi amfani da hakan wajen ƙarewa ofishin kallo, na ga abubuwa da dama a ofishin na al'ajabi, ƴan kananan gumaka, lambobin yabo, wasu abubuwan ma ban san ma'anarsu ba...
“Kana da binciken ƙwaƙwaf da alamu.”
Ya faɗa alhali idanunsa na ga takardun hannunsa..
“Na kusa ƙarasawa sai mu yi magana. Kafin nan...”
Wannan karon ya ɗago kansa ya kalli wani wardrobe sannan ya ce
“Je ka cen, ka fiddo jar kwalba ka ɗauki kofi ka sha.”
Na tashi, na buɗe wardrobe ɗin, na ga jar kwalbar da ya ce, na ɗauko. Na ɗauki kofi, abinda ke akwai ciki kalar ja ne mai ɗan duhu amma hakan bai dame ni ba.
Na zubawa kaina rabin kofi sannan ya ce
“Ni ma zuba min please. Ni ma na jiƙa maƙoshina.”
Ya faɗa da ɗan murmushi a fuskarsa.. har zuwa wannan lokacin, ban gane ba, ban kuma san abinda nake yi ba nan.
Sai da na kalle shi ya sha, kuma ganin yanayin yanda yake shan sa da alamu zai yi daɗi, dan haka ni ma nayi kamar shi.
Ban san meye ba.. amma akwai daɗi, mutum kama ta wanda ya saba fita zuwa wurare na ƙasaita, da son yin ƴan shaye-shayen nan, ban taɓa shan abu mai daɗin irin wannan ba... Barasa ce ko me oho.
“Zaka iya ƙara zubawa kanka! Ina jiran wasu kwalaban yau da yamman nan dan haka zaka iya shanye wannan.”
Gyara zama na yi na fara shan jan abun nan sannu a hankali.. ban iya hana kaina ƙarar da kwalbar ba tsabar na ji daɗin abun!
A daidai lokacin shi ma ya ƙare sannan ya kalle ni tare da yi min murmushi sannan ya ce
“Yauwa na ida, toh yaya ka ji?”
Na ce masa akwai daɗi sosai.
“Na sani yana da daɗi kuma kowa ya sha zai ji daɗinsa!”
Ko barasa abun shan nan, ya yiwa wani haɗin da ya saka ta wannan daɗin ko kuma wani sabon juice ne da su kaɗai manya ya fara zuwar ma...
“Well, bari na tura wannan report ɗin sai mu je.”
Ƴan danne-danne ya yi bisa na'ura, ba a ɗau lokaci ba ya gama.. ya nemi da na bi bayansa muka fita daga office ɗin, muka shiga motarsa ya ɗauki hanyar da shi ya san inda zamu je.
Agogo na duba na ga kusan ƙarfe shidda ne na yamma...
Tuƙi yake, muka iso kusan wata restaurant, maimakon mu shiga ta ƙofar restaurant ɗin kamar kowa sai na ga an bi da mu ta wata hanya, cikin ƙasan restaurant ɗin... Muka sauka ƙasa, nan muka tarar da wani guri wanda daga gani vip ne na musamman.
“Barka da zuwa sir? Good evening sir!”
Mutane har wani rusunawa suke suna gaishe da mutumin da muka zo tare, da alamu mutum ne da ake so kuma ake mutuntawa.
Muka je muka zauna wani guri mai ɗan duhu, sannan yayi odan abinda za'a kawo mana ta hanyar yin raɗa a kunnen ɗaya daga cikin ma'aikatan gurin.
Sannan ya juyo kaina tare da tambaya ta
“Toh yaro meye sunanka?”
Na bashi amsa da sunana Adamu.
“Yayi kyau Adamu, ni sunana Alhaji Balla, ni ne zan kasance mai gidanka kuma abin koyinka a wannan masana'anta ! Ni ne zan koyar da kai wasu abubuwa da dama wanda zasu sa kai ma ka zama wani babba. Zamu dinga yin komai tare, kuma zaka dinga yin duk abinda na ce ka yi...”
“Toh Alhaji.” Na amsa masa.
Daidai lokacin abincinmu ya iso. Ina faɗa muku haɗaɗɗen plate ne, da kaɗan bai kai Buffet ba, masu aikin suka ɗora mana bisa table tare da yi mana fatan a ci lafiya.
Shi ya yi musu godiya tare da yin saurin fara zubawa kansa abincin kamar ba dan shi aka yo shi ba... Tsikar jikina duk ta tashi, tsoro kuma ya kama ni lokacin da na fara ɗaga wani irin nama a cikin abincin.
Kaɗan na ɗeba na ɗora a plate ɗina, lokacin na ga ya kalle ni, tare da girgiza kai sannan ya yi murmushi.
Na fara ci, shi ma naman akwai daɗi kamar barasar da na sha ɗazu... Ci muke, muna sha.. nan muna gamawa ya ce da ni
“Toh yaya? Ka ji da daɗi ko?”
Na amsa da eh akwai daɗi sosai.
Ban ankara ba ashe hall ɗin ya cika da mutane iri-iri.
“Abinda ya kamata ka sani, wannan gurin shi ne gurin da mutane irin mu ke haɗuwa... Nan ne matasa da dama irin ka suke fara yin takun farko na shiga duniyarmu. Ka san ko meye ka gama ci yanzun nan?”
Na amsa da
“A'a.”
“Naman mutum.”
“Mene? Ban fahimta ba!”
“Yanda ka ji, a ofishi kuma jini ne ka sha.”
Wayyo Allah na ! Amai na ji ina son yi... Na yi ƙoƙarin amayo duk abinda na ci ! Na kama maƙoshina kamar ina son tuƙe kaina.
“Haka ne da farko, amma kar ka damu zaka saba. Shi yasa tun farko ake fara muku da hakan amma ka sani lokaci na tafiya a hankali har ka saba.”
Ji nake kamar wasa yake min, amma a zahirin gaskiya.. haka ne.
“Daina wani wayencewa, ka san akwai daɗi. Ka ji daɗin cin sa dan haka ka daina wannan yakunar bakin.”
Ko magana na gagara yi, ban san me zan ce ba. ƙyanƙyamin kaina kawai nake. Abin tashin hankalin, dubu ɗari biyar ya biya a matsayin kuɗin abincin.
Na lura wannan restaurant ɗin kawai maɓoya ce ta mutane marasa gaskiya da marasa imani...
“Mu je.” Ya ce da ni.
Ina son na koma gida, amma aikina da kuma ganin abubuwan al'ajabina yanzu suka fara... Wata babbar hotel muka je, babba sosai da kuma tsari. Bai ko tsaya a reception ba, kai tsaye muka wuce cikin lifter sannan muka wuce cikin wani babban ɗaki wanda zai iya amsa sunan wani gidan.
“Yi kamar kana gidanka ! Saki jikinka. A nan zamu kwana.”
A natse nake a koda yaushe, amma babu abinda zan iya yi kamar a gidana...
Shi kuma, wucewa yayi banɗaki ina jin sa yana wanka yana shewa... Bayan wani lokaci zubar ruwa ya tsaya, na ji fitowarsa daga banɗaki, juyawan ga da zan yi na gan shi babu kaya jikinsa...
Mutumin nan yana tsaye zindir haihuwar uwarsa a gabana.. ganin wannan al'amari nashi na kwararo idona jin me yake yi babu kaya jikinsa a gabana, shi ma a lokacin alamun mamaki ne da shi gani na ina mamaki.
Sannan ya tambaye ni
“Yaro me kake yi har yanzu da kaya a jikinsa?”
TO BE CONTINUED...
Sorry na rashin samun posting cikin dare, ina cikin rubutun bacci ya ɗauke ni 😁
Like, comment and share domin ƙara min ƙwarin gwiwa nagode 🧐