WATA ƘADDARA

WATA ƘADDARA 6&7

by @shamsiyyamanga

*WATA ƘADDARA*!!!




*NA*




*SHAMSIYYA MANGA*




*MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION*





*_BISSIMILLAHIR_* *_RAHMANI_ _RAHIM_*




*Page* 6️⃣&7️⃣




*بسم الله الرحمن الرحيم*


( *والسارق والسارقة فاقطعو* *أيديهما جزاء بما كسبا نكالا من* *الله،والله عزيز حكيم* ).{سورة المائدة} اية٣٧.


[ *Allah maɗaukakin sarki ya faɗa a cikin alƙura'ani mai girma cikin suratul* *MA'IDA* , *aya ta 37* ]


{ *DA ƁARAWO NAMIJI DA ƁARAUNIYA MACE IDAN KUN KAMASU KU YANKE* *MUSU* *HANNAYEN SU GUDA ƊAYA GWARGWADON ABUN DA SUKA AIKATA NA GAME DA SATA, ALLAH MAI GIRMA NE* *KUMA MAI HIKIMA* }


_________________________

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_


_*infection*_

_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

_***_



"""""""""""""""""""Kallon kallo kawai ake tsakanin Deede da MUBARAK kowanne zuciyar shi da abun da yake saƙawa,ƙarfin hali MUBARAK ɗin yayi sannan ya haɗiyi wani yawu da tun ɗazu ya tsaya mishi a wuya kafin ya juya ya kalli RAMLAT da har a sannan bata juyo ta kalle su ba kamar ma bata san mai suke faɗa ba kawai dai ta ƙurawa waje guda ido.


"""""RAMLAT wai bakiji abun da ake faɗa bane ba,ki juyo ki faɗa mana gaskiyar abun da yake shirin faruwa?""""" Cewar MUBARAK ɗin yana kafe RAMLAT ɗin da ido kamar zai cinyeta.


Har a sannan RAMLAT bata da niyyar juyowa infact ma alamu sun nuna mind ɗinta baya tare dasu.


Zagayowa MUBARAK yayi ta gabanta sannan ya kamo kafaɗunta ya jijjigata tare da cewa.


"""""RAMLAT what's going on? ki sanar damu ana magana kinyi shiru"""""


Sai a wannan lokacin RAMLAT ɗin ta ɗago da idanunta amma bata bari sun haɗa ido da MUBARAK ba juyawa tayi tare da kallon ma'aikatan Mall ɗin sannan tace


"""""Kuna da damar da zaku iya caje ni tun daga sama har ƙasa,idan har kun samu abun da kuke zargin cewa na ɗauka muku to daganan ku ƙira ƴan sanda su tafi dani,sannan idan har kuma baku samu abun da kukace na ɗauka ba to nikuma sai nasa an kulle shagonnan sannan sai nayi Shari'a daku saboda ƙazafi kuka mun"""" tana gama faɗin haka ta miƙo musu jakarta.


Su kuwa masu Mall ɗin mamakin ƙarfin halin RAMLAT ɗin suke yi bayan sun kamata read handed har tana da bakin da zata iya magana,karɓar jakar sukayi sannan suka zzazzage duk wani abu da yake ciki,da sauri suka ɗago suna kallon RAMLAT ɗin fuskar su da mamaki sannan suka kalli CCTV camera ɗin,aikuwa mamakin su bai ƙara tashi ba sai gani da sukayi fuskar wata mata daban ta bayyana a cikin Computer ɗin instead of fuskar RAMLAT ɗin,cigaba sukayi da bincika jakar RAMLAT ɗin amma ko sama ko ƙasa basu ga kayan da RAMLAT ɗin ta ɗauka ba,ƙara kai dubansu sukayi ga CCTV camera ɗin amma still fuskar wancan matar suke gani,tashin hankali!!.


Suma MUBARAK da Deede sai a sannan suka kai dubansu kan CCTV camera da take can a saman Mall ɗin sannan suka kalli computer ɗin da take gaban ma'aikatan Mall ɗin suma fuskar wata daban suka gani,duk wani binciken duniya ma'aikatan Mall ɗin sunyi a kan RAMLAT ɗin amma ko ƙasa ko sama sun rasa kayan da sukaga ta ɗauka ɗin kuma fuskar matar da take cikin computer ɗin a bincika kaf cikin Mall ɗin amma ko mai kama da ita basu gani ba,sosaima ma'aikatan Mall ɗin suka cika da mamaki tare da tsoro ya ɗarsu musu to mai yake shirin faruwa haka.


Shikuwa MUBARAK ganin da yayi ba'a samu kayan da akace RAMLAT ɗin ta ɗauka ba shiyasa ranshi ya fara ɓaci ganin suna shirin ɓata mishi suna dashi da matar shi aikuwa cikin ɓacin rai ya fara magana


""""Mai kuke shirin aikatawa haka? Ku waɗane irin mutane ne waɗanda basu san aikin su ba ku rasa wadda zakuyiwa sharri sai matata to wallahi ku shirya karɓar hukunci dan bazan yadda ba"""" ya faɗa cikin tsananin ɓacin rai.


"""""Bawan Allah mufa bamuyiwa matarka sharri ba,mu da bamu sanku ba daga kai har matartaka to mai zai sanya mu mata sharri abune mun gani ta ɗauka da idanunmu muka ganta kuma ko a yanzu ma ni ban yadda cewar kayannan baya tare da itaba""""Wani daga cikin ma'aikatan Mall ɗin ya faɗa shima cikin ɓacin rai.


"""""Oh watau ku har yanzu bakinku bazai mutu ba,to in hakane sai ku nunamana evidence mu gani ai ita dai Camera bata ƙarya to meyasa bamu ga fuskar RAMLAT ɗin a cikin Camera ɗin ba sai fuskar wata daban""""" cewar MUBARAK ɗin cikin tsawa


"""""Kaga MUBARAK dan Allah kayi haƙuri mubi komai a sannu duk wannan abun bana tada jijiyar wuya bane kaga har an fara taruwa a kanmu"""" Cewar Deede da tunda suka fara abun ta kasa magana sai yanzu.


""""""Haba Deede yakike maganar cewa abi komai a sannu saboda ni ba ƴarki bace ko da har anmun sharrin sata amma kike maganar wai abu komai a sannu to wallahi baza'a bi komai a sannu ba yanzu haka zan ƙara Dad ɗina gwanda yasan halin da ake ciki tunda naga kede bazaki iya tsayawa ki ƙwatar mun haƙƙina ba""""RAMLAT ɗin ta faɗa tana mai zaro wayarta a jaka tare da ƙoƙarin ƙiran Dad ɗin nata.


""""""Haba RAMLAT wannan wace kalar magana kike haka tsakani da Allah wannan fa mahaifiyata ce sannan karki manta Deede bata taɓa nunamiki wani abu na muzantawa ko makamancin haka ba duk yadda zatayi tana ƙoƙari wajen ganin ta kyautata miki,amma ruwanki ne idan zaki ƙira Dad ɗin naki bazan hanaki ba ki ƙirashi ɗin""""


Ko kallon shi RAMLAT ɗin batayi ba ta cigaba da dialing number ɗin Dad ɗin nata saidai kuma not reachable,tsaki tayi sannan ta maida wayar jaka.


Murmushi Deede tayi sannan ta kalli MUBARAK tace


"""""MUBARAK karki damu da abun da RAMLAT ɗin ta faɗa ni nasan ɓacin raine ya sata faɗin hakan,kasan yadda ƙazafin sata yake da ciwo""""" Deede ɗin ta faɗa amma ƙasan zuciyarta ɓacin rai ne fall a ciki.


MUBARAK ne ya kalli RAMLAT ɗin sannan yace


"""""RAMLAT yanzu faɗamun ya kike so ayi?"""".


Shiru RAMLAT ɗin tayi kamar bazata amsa ba kafin kuma ta saki wani murmushi da ita kaɗai ta san ma'anar shi sannan tace


"""""MUBARAK kawai ƙyalesu daman ni buƙatata kar abun da suke zargina dashi ya tabbata to gashi yanzu sune da jin kunya dan haka karka damu mu tafi kawai"""" ta ƙarasa maganar tana mai nufar ƙofar fita daga Mall ɗin.


Kallon ma'aikatan MUBARAK ɗin yayi sannan yace wallahi kunyi bala'in bani mamaki kuma kun bani kunya ku rasa wadda zaku yiwa sharri sai matata bayan kun sanni kun san ba yau muka fara zuwa siyayya shagon ku ba inda matata ɓarauniya ce ai da tuntunin ta gwada muku halin nata amma bata taɓa ba sai yau zaku bita da sharri kun bani mamaki wallahi""""


"""""Kaga malam MUBARAK mufa ba sharri mukayiwa matarka ba kuma zan iya rantsewa da Allah akan cewar naga matarka ta ɗaukar mana kaya amma koma menene mun barta da mai sama"""" cewar ɗaya daga cikin ma'aikatan Mall ɗin cikin ɓacin rai.


"""""Ko kuma mu muce mun barku da mai sama ba Allah ya isarmana,kuma muda shagonku har abada wallahi koda kuwa ku kaɗai kuka rage masu shago a duniya"""" MUBARAK ɗin ya faɗa tare da kama hannun Deede suka nufi hanyar barin cikin Mall ɗin.


"""""Muma bama buƙatar mugun iri a cikin Mall ɗin mu kuje can ku ƙarata dakai da ɓarauniyar matarka"""".


Shidai MUBARAK bai ƙara tanka musu ba suka fice domin in yace zaiyi magana zai iya shaƙe ɗaya daga cikinsu,saboda MUBARAK irin mutannannan ne masu shegen zuciya bashida faɗa amma zuciyar shi a kusa take.


A mota suka tarar da RAMLAT tana jiransu shiga sukayi don tafiya,har MUBARAK zai tayar da motar sai RAMLAT ta dakatar dashi


""""Dan Allah MUBARAK nayi mantuwa a ciki ko zaka ɗakko mun?""""


Kallon ta MUBARAK ɗin yayi a sheƙeƙe bai cemata komai ba juyawa da yayi yana kallon titi,ganin hakan da RAMLAT ɗin tayi ya sanya ta buɗe murfin motar tare da fita sannan ta nufi cikin Mall ɗin,bata shiga ciki ba sai ta nemi waje daga gefe ta tsaya rufe idonta tayi sannan ta fara motsi da bakinta bansan mai tace ba amma dai ta ɗan ɗauki tsawon lokaci a haka kafin ta buɗe idon wani farin haske ne naga ya fito daga idon nata ya nufi cikin Mall ɗin, murmushin mugunta ta sake sannan ta juya ta bar wajen ba tare da kowa ya lura da abun da ta aikata ɗin ba,motar ta koma inda ta tarar da su Deede ɗin suna jiranta,tayar da motar MUBARAK ɗin yayi sannan suka nufi gida,a hanyane Deede tacewa MUBARAK ɗin ya kaita gidan gwaggo Halima mahaifiyar SALMA,da yake SALMA ɗin ƴar ƙanwar Deede ɗin ce.


Sun isa gidan su SALMA ɗin a ƙofar gidan suka tarar da SALMA zata tafi kasuwa itada wata ƙawarta kasancewar bikin SALMA ɗin saura sati ɗaya suna ta shirye shiryen bikin,saida ta tsaya suka gaisa dasu Deede ɗin kafin suka kama hanyar tafiya kasuwar.


Fitowa sukayi daga cikin motar sannan suka nufi cikin gidan RAMLAT sai wani ya tsuna fuska takeyi,duk abun da take ɗin MUBARAK yana ankare da ita tarata yake sai sunje gida zai sauƙemata farrillan rashin mutunci,a haka suka shiga gidan su SALMA ɗin wanda yake madaidaici daidai gidan masu rufin asiri.


Da sallama ɗauke a bakinsu suka ƙarasa shiga cikin gidan inda suka tarar da Umman SALMA ɗin da kuma wasu mata su Uku a zaune a madaidaicin falon su SALMA ɗin mai ɗauke da kujeru guda shida,ƙarasa shiga cikin falon sukayi da fara'a Umman SALMA ɗin ta taso tanayiwa su Deede ɗin sannu da zuwa,akan kujera Deede ɗin ta zauna inda shikuma MUBARAK ya nemi waje a gefe shima ya zauna.


Ita kuwa RAMLAT tsaye tayi ƙiƙim kamar wata soja bata da alama ko niyyar zama,sai wani cika take tana batsewa a dole ita bataso akazo gidan su SALMA ɗin ba,daman jinin su baya haɗuwa da Umman SALMA ɗin,kallonta Deede tayi sannan tace


"""""RAMLAT ya kika tsaya a tsaye ki zauna mana ga waje""""" ta faɗa tana nunawa RAMLAT ɗin kujerar gefenta.


Ko kallonta RAMLAT ɗin batayi ba balle Deede ɗin tasa ran cewa zata amsa mata.


""""Haba Deede meye naki na magana da ɓata yawun bakinki kekam ba kin zauna ba sai kibar mutum ai ke ba baƙuwa bace a sanin halin RAMLAT dan haka karki wani damu"""" Cewar Umman SALMA ɗin tana bankawa RAMLAT ɗin harara.


Wani baƙin ciki ne ya turnuƙe zuciyar RAMLAT ɗin tare da jin tsanar mahaifiyar SALMA ɗin lalle ma matarnnan da alamu sai na miƙe tsaye a kanta, RAMLAT ɗin ta faɗa a zuciyarta.


"""""Sannunku da zuwa fa,ai tun ɗazu muke zuba idon ƙarasowar ki ashe kuna tafe"""" inji Umman SALMA ɗin


"""""Eh wallahi kinga mun biya ta wajen shopping ne kinsan MUBARAK yau zai wuce wajen aiki""""


"""""Lah haka fa yau Sunday ashe""""


"""""Wallahi kuwa yana ta shirin komawa wajen aiki"""" Cewar Deede ɗin.


"""""Ki sawa maganar ki jam'i domin kuwa wannan karan ba isa ya tafi ya barni ba wallahi tare zamu tafi ni nasan daman akwai masu zugashi ai tunda ni an tsaneni, to nagaji wallahi eheee""""" RAMLAT ɗin ta faɗa tana mai girgiza kamar wata tarwaɗa


Takaicine ya ishi MUBARAK ganin irin tozarta shi da RAMLAT ɗin take shirin yi,har ya buɗi baki zaiyi magana sai maganar Umman SALMA ta katse shi


"""""Lalle RAMLAT ashe rashin kunyarki da ake faɗa ake labari da gaske ne?,ashe ke tantiriyar marar kunya ce to wallahi ki iya bakinki in Deede ta ɗauki abun da kike mata to nikam bazan ɗauka ba""""".


"""""Kaga malam in zaka tashi mu tafi ka tashi in kuma bazaka tashi ba to ni kaga tafiyata domin kuwa wallahi nagaji da jin wannan cin mutuncin da ake mun kaikuma ka kasa yin magana""""" ta faɗa tare da juya ta nufi mota.


Sunkuyar da kai kawai MUBARAK yayi yana jin wani mugun ɓacin rai, lalle RAMLAT ta taro match shikuwa yau zai nuna mata cewar mahaifiyar shi ba abar wulaƙantawa bane ba,nan gaba ko wata a cikin dangin shi akace taciwa mutunci bazata yi ba,miƙewa yayi fuuu cikin tsananin ɓacin rai ya fice a ɗakin ƙiranshi Deede take amma ko alamar juyowa baida.


A mota ya tarar da ita ko kallonta baiyi ba ya shiga cikin motar sannan ya figeta a guje suka bar unguwar,kariyar Allah ce kawai ta kaisu gida,horn yayi inda mai gadi ya fito da sauri ya zo ya buɗe gate ɗin.


Yana shiga ko daidaita parking bai yiba ya kashe motar ya fita ya nufi falo,bin bayan shi RAMLAT ɗin tayi a falon ta tarar dashi a tsaye ya juya bayanshi,ko kulashi batayi ba ta nufi ƙofar ɗakin ta,cikin wata iriyar kaussasshiyar murya ya ƙira sunanta.


Turus taja ta tsaya amma bata juyo ba,ƙarasawa yayi inda take tsayen sannan ya juyo da ita cikin masifa ya fara magana


"""""RAMLAT ashe baki da tarbiyya ashe daman baki san darajar mutane ba,rashin mutunci naki har ya tashi daga kaina ya koma kan mahaifiyata,duk irin ƙoƙarin da mahaifiyata take wajen kyautata miki amma bakya gani saboda baki gaji tarbiyya ba"""""


Itama RAMLAT ɗin cikin masifa ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga mishi hannu sannan tace


"""""Karka fara Wallahi MUBARAK karka kuskura ka zagarmun iyayena kace basu bani tarbiyya domin kuwa a rashin tarbiyyar tawa kaje ka auro ni ai, da kai baka san ƴar gidan wa ka auro ba to wallahi ka......


Ai tun kafin ta ƙarasa maganar da take ɗin MUBARAK ya sanya hannun shi ya ɗauketa da wani mahaukacin mari har saida ta sunkuya tana ɗagowa ko bari baiyi ta dawo daidai ba ya ƙara ɗauketa da wani marin a ɗayan gefen har saida ta faɗi a ƙasa durƙusowa MUBARAK yayi daidai saitin fuskar RAMLAT ɗin sannan ya sanya hannun shi ya ɗago da fuskar RAMLAT ɗin suka fara kallon juna ido cikin ido,saurin runtse idonta RAMLAT ɗin tayi saboda yadda taga idanun MUBARAK sun koma jajawur kamar garwashin wuta cikin tsananin ƙunar rai har wani huci yake ya fara magana


"""""This should be the first and the last time da zaki ƙara buɗe tssatssaman bakinki ki faɗi abu marar kyau akan mahaifiyata,ke bama ita kaɗai ba duk wani a cikin familyna wannan ya zama na ƙarshe da zaki ƙara musu rashin kunya ko kallon banza kika musu wallahi sai na sanja miki kammani,karki ga ina ƙyaleki kina mun duk abun da kika ga dama wannan tsakanina ne dake kuma ya tsaya a iya kaina amma wallahi uwata uwatace duk wanda zai taɓata nikuma sai inda ƙarfina ya ƙare akanshi banza kawai shashasha"""" ya faɗa yana mai hankaɗata gefe tare da kama hanya ya nufi ƙofar barin falon domin kuwa ji yayi bazai iya zama a gidan ba idan kuwa har ya zauna to zai iya illata RAMLAT ɗin dan haka gwanda ya bar mata gidan,har ya kama handle ɗin ƙofar zai buɗe sai kuma ya juyo ya kalleta sannan yace


""""And magana na ƙarshe da zan faɗamiki shine tafiyana Abuja kamar yadda na saba ni kaɗai zan tafi kuma babu uban da ya isa ya sanja mun ra'ayi dan haka in zaki zauna ki zauna inkuma ba zaki zauna ba ga ƙofanan""""


Yana kaiwa nan a maganar shi ya buɗe ƙofar falon ya fice a gidan gabaɗaya ya barta a zaune a wajen.


Tsananin mamakine da firgici ya rufe RAMLAT ɗin ganin abun da MUBARAK ɗin ya mata wai yau ita MUBARAK ya mara mutumin da ko kara ta ajiye tace karya tsallake to bazai tsallake ba amma yanzu har shi zai ɗaya hannu ya mareta,a take idanun RAMLAT ɗin ya fara sanja kala zuwa zuwa baƙi gabaɗaya idanun ya koma baƙƙikirin baka ganin komai a idon sai baƙi,wata kururuwa tayi tare da buga kanta a jikin Centre table ɗin da yake tsakiyar ɗakin take ya tarwatse itakuma jini ya fara zubowa daga goshinta amma ko a jikinta haka ta tashi da wannan jinin goshin nata ta nufi hanyar ɗakinta tana shiga ta ɗakko key ɗin motar ta sannan ta fito daga cikin ɗakin ta nufi harabar gidan,motarta ta ɗauka ta figeta a guje da gudu mai gadi yazo ya buɗe mata gate ɗin saura ƙiris tabi ta kanshi,da kallo mai gadin yabi motar yana mamakin halin da iyayen gidan nashi suke ciki domin shima MUBARAK haka ya fita a fusace to ga itama RAMLAT ɗin addu'a yayi Allah dai ya sanya lafiya.


**************


""""""""""""""A ɓangaren yaya ABDUL ɗin SALMA kuwa tunda aka shiga satin bikinsu yake fama da wani irin matsanancin ciwon ciki duk wani abu da yake dauriya kawai yake domin kuwa kullum abun ci gaba yake amma babu wanda ya sanarwa ko SALMA saboda baya son hankalinta ya tashi,asibiti kuwa yaje yafi sau a ƙirga amma sai suce masa bakomai,kullum cikin turashi gwaje-gwaje ake amma duk result ɗin gwajin da ya fito sai ya nuna babu komai a cikin nashi.


A haka ya daure yayi ta maza yacigaba da hidimar bikinshi amma kana ganin shi kasan akwai abun da yake damunshi idan aka tambaye shi kuma sai yace kawai stress ɗin biki ne amma babu komai,yayi baƙi ya rame ya fita a hayyacin shi,ita kanta SALMA ɗin duk ta shiga damuwa ganin halin da yake ciki ɗin kullum idan yazo sai ta matsa mishi da tambayoyi akan mai yake damun shi amma sai yace mata babu komai,yauma kamar kullum suna zaune a ƙofar gidan su SALMA ɗin ƙarfe tara na darene lokacin SALMA ɗin ce ta ɗago ta kalli yaya ABDUL ɗin sannan tace cikin rawar murya.


"""""Yaya ABDUL ni nasan cewar akwai abun da yake damunka amma kaƙi sanar dani,yaya ABDUL idan baka faɗa mun damuwar kaba a wa zaka faɗawa,ko kanada wacce ta finine bayan iyayenka?,dan Allah yaya ABDUL ka sanar dani nasan kanada damuwa saidai kuma idan bazaka faɗamun ba sai ka sanar dani"""""" ta ƙarashe maganar cikin fashewa da kuka.


Tausayin SALMA ɗin ne ya kama yaya ABDUL ɗin amma har ga Allah shi bazai iya sanar da ita cewa bashida lafiya ba domin kuwa yasan halinta yanzu sai ta ɗaurawa kanta damuwa, murmushin ƙarfin hali yayi sannan ya dubeta yace


"""""SALMA ki Yadd dani babu abun da yake damuna dan Allah ki share hawayenki banason ganin kukanki wallahi ko kaɗan"""" ya faɗa yana sanya hannunshi tare da goge mata hawayen nata.


Haka dai yacigaba da rarrashinta har ya samu tayi shiru,tashi yayi sannan sukayi sallama ya tafi,ita kuma ta shiga gida.



*COMMENT SHARE* *SABIDA ALLAH*



*MANGA*✍️ ....