SAHLA a Paris

Miyan kyankyaso

by @azizat

TOP-NOTCH.....the touch of excellence, just for you.

✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

***

005 ...miyan kyankyaso...

"Ban yafe abinda kuka yiwa Sahala ba. Gashi nan yarinya ta kasa tafiya tun shekaranjiya"

"Hajiya Kaka wai duk abinda Sahala tayi kina goyon bayanta. Wallahi ko yanzu na sami dama sai na sake punishing ɗinta"

"Koma mi ta yi sai ku karya mata kafa"

"Hajiya babu wanda ya karya mata kafa. Iskanci ne ya hanata mikewa"

"Wallahi ka kiyaye ni Mustafah. Ina faɗa kana faɗa"

"Yanzu dai kiyi hakuri ki saka mana Albarka, yau zan tare a sabon gidana"

"To, to, Allah ya shi Albarka. Shi kuma Farukun yaushe zai aje iyali?"

"Hajiya ki taya shi da addu'a kawai"

"Ina addu'ar zata karɓu ya je ya makale a kasar ɗagutu"

"Hajiya aiki yake yi fa. A UNESCO ya ke aiki)

"Ummisko? A mace yake wa aiki kenan"

"Hajiya ba Ummisko na ce ba kar ki masa sharri"

Fitsari nake ji amma na kasa tashi saboda bana son gaida Yaya Mustafah. Washegarin ranan da suka saka ni tsallen kwaɗo na tashi da kumburarrun kafafu, kafana suka rike, na kasa motsa su. Kaka ta sa aka faɗawa Alhaji. Da kansa ya zo ya ɗaukeni sai da muka fito zamu tafi Abban Egypt ya karɓeni yace ya bari shi zai kaini Asibiti.

Sarai Alhaji ya ji labarin abinda ya faru amma yace a rufe maganar a cigaba da shirye-shiryen ɗaura aure kawai.

Bayan mun dawo daga Asibiti babu inda nake zuwa, ko banɗaki zan je sai Kaka ta dafa min. Duk wanda ya shigo gaida Kaka kuwa sai ya gaya min magana. "Badluck kawai. Mai farar kafa. 'Yar asara" suna dai kala-kala.

Ban san lokacin da Yaya Mustafah ya fita ba, balle har naga shigowan Uncle Faruku.

Marata ya murɗa, na rasa ya zanyi, kamar ma dai wani jiqa-jiqa nake ji a pant ɗina. Da na kasa daurewa sai na tashi zaune.

"Kaka zan yi fits..." na tsaida maganar dai dai lokacin da idanunmu suka haɗu. Yana zaune akan kujerar dake kallon gadon Kaka. Yau bai saka gilashi ba dan haka na samu damar ganin fararen idanunsa.

"Za ki iya tashi ne ko sai na tallafa miki?"

Ban amsawa Kaka ba na diro da kafafuna kasa na fara tafiya. Ina wucewa ta gaban Kaka ta daka salati. "Sallallahu Alaihi Wa Sallam"

Zani ta jawo da sauri ta zo ta rufe min bayana. Ta jawo hannuna muka wuce banɗakin tare.

Yau dai na zama 'yanmata nima. Dama duk cikin sa'annina nice ban fara ba. Haniefah ma dana girma da shekara ɗaya ta fara wancan hutun da suka zo gida.

Sai da muka dawo ɗakin na lura da inda na kwanta ashe duk ya ɓaci da jini.

Na ɗan rufe fiskata. kenan Uncle Faruku ya ga jinin ɗazu dana tashi.

"Shi kuma Farukun ina yai? Ana masa zancen aure ya tashi ya gudu"

***

Malam Salim shine Malaminmu na integrated science. Yana da kyau, ɗan fari da shi, ga gemu da kasumba. Idan yana mana darasi a aji sai na ga kamar ni kaɗai yake kallo. Idan muka haɗa ido sai na ji wani kunyarsa ya kamani.

Malamin Maths ɗinmu ɗan bautar kasa ne. Uncle Zaid shima yana min irin kallon da Malam Salim ya ke yi min. Shima yana burgeni musamman idan ya saka kayansu na bautar kasa. Wayyo ni Sahla! Malaminmu na hadda ma yana burgeni kuma ina son kanshin turarensa. Idan na zo ba da hadda ma sai na matsa kusa da shi sosai dan na shaki kanshin da kyau.

Ban san mi yake damuna ba. Maza masu kyau suna saurin burgeni. Malamin English ɗinmu ne kawai bai min ba. Leɓensa kamar ganda, idan yana darasi na dinga dariya kasa-kasa kenan. Idan ya ce Verb sai kaga leɓen sunyi sama sun baje kasa, kamar yace 'waaab'.

Yanzu ba ni kaɗai ke zuwa makaranta ba. An dawo dasu Haniefah da Safiyya gida bayan Safiyya ta kwaso Aljanu, ita kuma Haniefah ciwon ulcer ya yi mata lahani. Daɗin abinma duka a JSS 3 aka saka su saboda ba su yi junior waec ba a chan makarantansu aka ciresu. Hanifah ba karamin jinya ta sha ba bayan an dawo da su gida, satinta kusan uku a Asibiti, wai ulcer da typhoid suka mata mugun kamu.

Duk da gidanmu gidan yawa ne, amma har yau bani da wadda muka shaku da ita irin sosai ɗin nan. Nasiba, Safiyya, Hanifah da kuma Zuhriyya duka sun haɗe kansu waje guda. Zuhriyya tana SS 2 mu uku muna JSS 3 ita kuma Nasiba tana JSS 2.

Ni kam daga ni sai Kaka. Duk iya shege na akwai abinda bana iya faɗawa Kaka. Ina so na tambayeta ko abinda na ke ji gameda su Malam Salim dai dai ne. Ina so na tambayeta ko yawan kallon kaina da nake a madubi abin damuwa ne. Ina so na tambayeta ko abinda na ke ji a raina idan nayi mafarkin Affan ko na Uncle Zaid dai-dai ne.

Ina son sanar da su Safiyya amma ina tsoron kada su min dariya. Kada su dinga tsokalata kamar yadda suka saba.

Matan gidan kuwa kowa 'ya'yanta ta sani. Wani sabon salon iskanci da suka samu tunda sun ga na fara ɗan hankali bana kiyuwar yin aiki sai su dinga sani aiki son ransu. Ko Kaka da muke ɗaki ɗaya bata bautar dani kamar yadda su ke yi.

***

Yau kwana ɗaya kenan ya saura ayi Mauludi.

Hajiya Kaka tana celebrating wannan rana a kowacce shekara. Duk da akwai yaran mazan gidan da suke ja da bikin da ake a ranan amma hakan bai hana yin hidima a wannan rana ba a kowacce shekara. Takanas Alhaji ke ware kuɗi ya bawa Hajiya dan ta yi hidima da shi. Ayi girke-girken sadaka da wanda za a raba kyauta wa 'yan anguwa.

Girkin yau ya faɗa hannun Ummi dan haka ita Kaka ta damkawa lamarin girke-girken da za a yi.

Ita da Kaka sai da aka zauna aka yi lissafe-lissafen abubuwan da za a siya da adadin abinda za a bukata amma duk da haka sai da matar nan ta rage abubuwa. Aka ce ta auno shinkafar da za ayi masa da shi mudu goma shabiyu, matar nan ina kallo ta auna mudu tara ta bani. Ban yi magana ba dan bana son zafin kai nima fama nake da kaina, wannan shegen bakon da yake zuwa duk wata ya hana ni sakat.

Naman da aka kawo za ayi miyan taushe da shi. Kaka ta ware wanda za a soya a kawo mata da kuma wanda za a silala a zuba a taushe. Ita kuwa Ummi ta kwashi rabin naman bayan an silala ta saka a wata tukunya tace Hanifah ta kai mata karkashin gado. Muna haɗa ido tace " miye? Na ajiye ne saboda baki na musamman da basa zuwa sai chan yamma"

"Ummi ni ban ce komai ba. Kema kin san in ba dan ciwon kafa dake damun Kaka ba ba zata bari ki gudanar da komai ke kaɗai ba, tunda ta san halinki. Ki yi abinda kika ga dama. Amma kar ki manta dan soyayyar Manzon Allah ake wannan sadaka"

"To Malama Sahala. Ja mana aya ki mana wa'azi"

Na kauda kai na cigaba da yanka Alayyaho. Kwanan nan dubun matar nan zai cika ta ga abinda zan mata a gidan nan.

Karshe dai hidimar Mauludin bana da walle-walle aka tashi tsakanin Ummi da Kaka da kuma sauran matan banda Anty Amarya.

Masan da aka toya bai kai yadda ake yi ba. Jollof ɗin shinkafa itama bata kai ba. Balle uwa uba nama. Mama da Kaka haka suka shiga har kitchen ɗinta suka dinga neman inda ta ɓoye nama amma basu gani ba. Da kamar na faɗa musu a karkashin gado take sakawa sai na yi shiru nace zan yi maganinta ai na san ya take da su. Ko dai ta soya ta dinga ɗauka ɗai ɗai duk lokacin da za ta ci abinci ko kuma ta yi stew da shi ta ɓoye a fridge ɗinta ranan da ba girkinta ba idan an kawo mata abinci ta buɗe stew ta ɗebi nama ta watsa a saman abincinta.

"Sahla dan Allah yi min jajjage mana, zan yi 'yar sos (sauce) ce kaɗan, gobe na ɗan ci shi da biredi. Kwana biyu na gaji da cin biredi da shayi zalla"

Ba musu balle gardama na ce mata to. Yaranta suna falo suna kallo, ni ce boyi-boyinta ko?.

Na zuba kayanmiya a cikin turmi sannan na ɗauko farar leda dana ɓoye a bayan kofar kitchen ɗinta na zazzage kyankyasan da ke ciki tas a ciki. Dama kyankyasan wanda take kiwo a ɗaki da kitchen ɗinta ne na ke tattara mata su, to yau ga ranan su. Na haɗa su da kayan miya na dake su da kyau suka karawa kayan miyan ja.

Dana gama na zuba a munafukar tukunyarta da take satan nama da shi.

Da na gama na fito falo na ce na gama. Na zauna a falon nima ina kallo zuciyata fal da tsoro. Anya kyankyasai goma basu yi yawa ba? Dan manya ne sosai, sun sha kiwo sun koshi.

Ta tashi ta je ta ɗauko naman da ta ɓoye a ɗaki ta wuce kitchen da shi.

Sai dana tabbatar ta gama miyar sauce ɗin sannan na musu sallama na wuce ɗakinmu.

Da ke Ummi akwai kwaɗayi, tun a daren ta fara taɓa miyar. Ta ci shi da farar shinkafan da ta dafawa yaranta dan ba ayi girki ba yau bayan abincin Mauludi.

Allah ka yafeni. Daga Salamu Alaikum ɗin sallar Asuba aka wuce da Ummi Asibiti saboda gudawan da take tun da tsakar dare.

Na yi kum da bakina. Amma ina addu'ar Allah yasa dai kada ta mutu. Ba abinda ya samu yaranta tunda suma abinda ta basun bai taka kara ya karya ba.

Zuwa karfe shabiyu na rana aka sallamota bayan ta sha ruwa leda huɗu.

Kaka ta dinga yi mata madallah, wai naman sadaka da ta sace ne ya sakata gudawa. Ni dai ina jin su na yi kum da bakina. Da yake na tsorata sosai da aka kaita Asibiti na saci jiki na je sashinsu na ɗauko tukunyar miyar na wanke sauran miyan na zubar. Naman kuma dama saura kaɗan na zuba a leda na fito waje na yar a dustbin ɗin da ke waje.

Matar nan kafin dare ta fara Zage-zage wai an shigo an mata sata a kitchen. Na ce bata daddara ba kenan.

Yanzu ko gaisheta na yi sai na ji dariya ya taho mini idan na tuna cewa taci miyar kyankyaso 😂😂😂

***

Litattafan TOP-NOTCH

Abinda ya baka TSORO---Ramlat MaiDambu

Bani da LAIFI--- Shatuu

SAHLA a Paris---Azi_zat

Guda ɗaya 350

Biyu 700

Uku 1000