SAHLA a Paris

Coustaliye

by @azizat

TOP-NOTCH.....the touch of excellence just for you.

✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

010...Coustaliye...

***

A inda Faruk ya ajiye key ɗin mota ko kallon wajen Alhaji bai yi ba.

"Aliyu aure nake so kayi. Duk wani Alheri da zaka min ba zan ji daɗi ba kamar ka ajiye iyali. Ka kalleka, ka kalli kaninka Mustafah. Ba ka ganin nitsuwa a tattare da shi. Kwanan nan ya saka Kamal ɗinsa a makaranta. Aliyu ba mota nake so ba, ba gida nake so ba, ba kuɗi nake so ba. Aure nake so kayi. In dai farin cikina kake so to aure zaka yi."

"Dad ka dena comparing ɗina da Mustafa. Kowa da kaddararsa. Zan yi aure idan Allah ya nufa"

"Haka kake faɗa duk shekara. So kake sai an yi auren su Abbas kafin kai kayi aure. Minene matsalar ne?"

"A kara min lokaci. Zan yi aure"

"Al'amarinka Faruk sai addu'a. Ni kam babu abinda za ka yi ka burgeni sama da aure. Da Allah nake rokon ka idan akwai wata matsala ne da bamu sani ba ka gaya mana"

Faruk ya girgiza kai.

Alhaji ya cigaba "An nuna maka 'yan mata cikin dangi da abokai amma duk babu wacce ta maka. Ance ka fitar da mace ka ki. So kake da girmanka mu maka auren dole ne"

Faruk yai shiru. Babu abinda zai iya cewa. Ba za su gane matsalarsa ba. Kila aure baya cikin kaddararsa.

Yana fitowa daga sashen Alhaji ya wuce sashen Kaka. Itama ɗin ya san duk kanwar ja ce. Dan duk abinda Alhaji ya faɗa itama shi zata maimaita. Amma dolensa ne ya je ya mata ta'aziyya tunda shine musabbabin zuwansa kasar.

Ya so zuwa a lokacin rasuwan amma babu dama saboda aikinsa, infact a South Africa yake lokacin da aka yi rasuwar.

Kaka na kishingiɗe akan tabarma hannunta da mafifici tana fiffita. Ya tsugunna ya gaisheta.

"Faruku ne?"

"Kaine a gidan namu. Sannu da zuwa"

Ina Sahala take ta ɗauko maka kujera a ciki.

"Sahala" ta kwala mata kira. Amma shiru

"Haka nake fama da ita fa, yanzu haka kallo ta je yi a ɗakin Rafee'atu"

Ta ɗan tashi ta zauna tareda mika masa mafificin hannunta.

Gaskiya rasuwan 'ya'yanta biyu ya taɓa Hajiya Kaka. Gaba ɗaya ta rame masa compared to wancan zuwan da ya ganta.

"Na ce ko zaka zauna a tabarma kafin Sahala ta zo"

Ya girgiza kai, bai saba zama a kasa haka ba. Yana mamakin yadda mutane ke iya zama a kasa har su harɗe kafafunsu. Shi idan ka ga ya zauna a kasa to sallah ne.

"Hajiya yaya hakuri"

"Hmm Umaru da Bintu sun tafi saura ni. Ance Umaru da shahada a bakinsa ya cika. Kaga kuwa ya huta. Allah yai musu gafara"

Faruk ya amsa da Amin.

"Yanzu Faruku kai kenan haka zaka cigaba da zama babu aure. Ko dai.. Sahala, ya haka?"

"Wallahi sai dai ayi asaran abinci a gidan nan. Haka kawai ku maida ni 'yar iska. Wallahi sai anyi meeting a gidan nan yau. Babu 'yar iskar da zan sake yiwa aiki"

Tana tafe niki-niki da katuwar tukunya akanta ta yi wani katon gammo da gyalenta.

Shi da Kaka suka zuba mata ido. Tana zuwa tsakiyarsu tace Kaka Dan Allah tayani na sauke wannan tukunyar.

Kaka ta mike da sauri ta kama mata suka sauke tukunya.

Kaka ta buɗe marufin tukunyar, tururi ya baza wajen.

"Minene wannan Sahala?"

"Ba Mama bace za ta maida ni taɓaɓɓiya. Na dawo daga wajen registration ɗin JAMB da uban yunwa wai abinci ya kare. Tace na je na dafa mana couscous guda biyu ni da su Abbas da su Hanifa dan suma ba su ci abinci ba. Shinefa na ga ta ɗaura ruwan kayan miya a wuta yana tafasa. Da farko dana zuba ledan couscous biyu a ciki sai naga yayi ruwa, shine na shiga store na ɗauko biyu na kara a kai, shima couscous ɗin kamar magani ya ki shanye ruwan. Ni kuma na ɗauko ledan taliya guda uku na juye a kai.

"To wai yanzu sai dai ni na cinye abinda na dafa, kuma zata faɗawa Alhaji na mata almabazzaranci da abinci. Wallahi ta faɗa, nima zan faɗi abubuwan da take mini, ai na jima ina tarata"

Faruk yai murmushin gefen baki. Yarinyar nan ba randa zai shigo gidan nan bata saka shi dariya ba. Idan za ta fara comedyza ta yi kasuwa.

Ga dai gwaten taliya da couscous yana kallon Kaka da Sahala suma suna kallonshi.

"To yanzu Sahala da kika cicciɓoshi kika kawo nan ya kike so ayi da shi"

"Cewa ta yi idan ban ɗauke daga kitchen ɗinta ba zata zuba min wanka da shi"

"To shiga ciki ki kawo min cokali na taɓa na ji ko zan iya ci"

Da Kakan da Sahlan duk sammakal. Kaka ta taɓa abincin tace "amma Sahala wannan abincin ai ba zai ciwu ba. Taliyar fa bata dahu ba"

Sahla ta karɓi cokalin ta ɗebo abincin ta kai baki. Shi ba kunu ba, shi ba gwate ba, ga shi nan dai.

"Yanzu ya za ayi da abincin nan. Kema Sahala baki kyauta ba"

"To Kaka sai kin faɗa a gaban shi ne, salan ya je ya gayawa Yaya Yusuf"

"Kawai barin je na samu Baba Maigadi nace ya nemo mana almajirai. Yau za su ci coustaliye. Uncle Far, ai, Uncle F Kay sunan abincin yayi kama da abincin 'yan Paris ko?"

"Hajiya barin shiga na gaishe da mutanen gida" yai maganar yana ajiye mata kuɗi damin dubu ɗaya.

"To Faruku Allah ya maka albarka. Allah ya sa ka auru kwanan nan"

"Kaka ya auru kuma sai kace mace"

"Yo tunda ya ki neman auren ba sai na masa addu'ar Allah yasa mace ta auro shi ba"

Shi kam tuni ya bar barandar ya wuce sashen matan gida.

Kowacce mata sai daya shiga yai mata gaisuwa. Mama ko kallon kirki bata masa ba tana ta faman yiwa yaranta masifa akan abinda Sahla ta yi. Wai ya aka yi suka bari ma Sahla ta buɗe store har ta ɗauko mata kayan abinci.

A wajen Anty Rafee'ah ne ma ya ɗan jima su kan taɓa hira. Duk maganar dai bai wuce yaushe zai yi aure ba. Sai kuma maganar Sayyidahda suka yi. Sun rabu da mijinta amma ta ki dawowa gida Nigeria.

Anty Rafee'ah ta masa nasiha akan ya lallashi Sayyidah ta dawo gida dan Alhaji baya jin daɗin zamanta a America.

Yai mata alkawarin zai yiwa Sayyidah magana. Duk da kuwa ya san taurin kan kanwar ta sa. Shi kuma ga shi mutum ne da baya iya shiga harkar mutane balle har ya takura musu bisa ra'ayinsu.

Lokacin daya fito compound ɗin gidan ya ga jerin Almajirai na shigowa gidan. Tausayinsu ya kama shi. Yau lallai za su ci abinda zai rikita musu ciki. Da wannan ne ma ya fara tambayar kansa wai har yanzu a kasar Hausa ana almajiranci. A bar yaro ya dinga garari a titi neman abinci. Eating leftovers daga ko'ina. Gaskiya Allah ke kiyaye yaran nan, if not da yawansu da sun mutu ta hanyar food poisoning. Yana fata watarana za a samu chanji. Kowanni ɗa zai zauna gaban iyayensa yai karatu. Shi shaida ne na illar rashin kulawar iyaye a kan 'ya'yansu musamman idan suna shekarun kuruciyarsu.

Shi gashi a gaban iyayensa ya taso amma rashin kulawarsu, sakacinsu ya haddasa masa damage ɗin da har yanzu yana fama da shi kuma bai san ranan samun sauki ba.

Lokacin da aka yaye Hasina Maami ta bada rikonta ga yayarta da ke London. Ta focusing hankalinta akan karatunta thinking sai ta gama zata sake haihuwa kwatsam sai ga cikinsa. Tun da aka haife shi ya ke karkashin masu aiki. Infact ance ko nono baifi na wata biyu ta bashi ba ya koma shan madara.

Zai iya kwana biyu, uku bai yi magana da iyayensa ba sama da good morning da kuma good night.

And all of a sudden aka kawo Julius...

Matsalar Sayyidah ma baya rasa nasaba da rashin kulawar iyaye. Bayan rabuwar auren Maami da Dad ɗinsu, kulawarta ya koma hannun babysitters ko kuma gidan makotansu turawa. Maami tana yin degree ɗinta na uku, ga kuma rabuwar nasu ya taɓata.

Dad ya dawo Nigeria da zama gaba ɗaya su kuma sun makale a kasashe daban-daban.

Shi yanzu yana France. Hasina da mijinta suna London. Sayyidah na America.

Idan ya zo Nigerian ma gidan na su ba a haɗe yake ba. Bai taɓa tunanin Dad zai iya ajiye mata har huɗu ba. But then abubuwa da dama sun canja da shi bayan an bashi sarautan Ubandoma.

Sarautan ne ya sa shi kara aure ko kuma dama ra'ayinsa ne? Bai san amsar ba. Bai kuma san ya ake ji idan anyi aure ba balle har yai tunanin wasu mazan ba za su iya rayuwa da mace ɗaya ba.

Yana da burin yai aure watarana, yana da burin ya zauna da mace ɗaya har karshen rayuwarshi. Sai dai kuma wannan buri ne da ba zai taɓa zama zahiri ba.

For now, sai dai ya ga ana aure, ana haihuwa, and the circle continuous.

Bai jima a tsaye ba ya ga almajiran nan na fitowa daga chan gefen Kaka, robobinsu cike da Coustaliye...

Yai murmushi mai tsayi daga chan kasan ransa ya furta sunanta. Sahla..

Litattafan TOP-NOTCH na kuɗi ne

Abinda ya baka TSORO---Ramlat MaiDambu

Bani da LAIFI--- Shatuu

SAHLA a Paris---Azi_zat

Guda ɗaya 350

Biyu 700

Uku 1000

Account details

3091721807

Aisha Kwalam Hassan

Firstbank

Za a iya tura shaidan biya ga ɗaya daga cikin nambobin nan:

***

***

***

Ga masu turo katin MTN kuma zasu tuntuɓi numban Zahran Adda Ramlah:

***

'Yan Niger kuma su tuntuɓi Nana A'ichah:

+ 22784506476