DAN MAFIYA

CHAPTER 7

by @ashtar

DAN MAFIYA 🧛‍♂️


#CHAPTER_7


By ✍️ Malik al-Ashtar


GARKUWA WRITTERS ASSOCIATION đź’«


Book on Wattpad 👉 ***

On Arewabooks 👉 https://arewabooks.com/book?id=6350e2ebfd0f045b385cfaf1

For more Novels 👉 ***


Baki sake nake kallon sa... Ina tambayar kaina, me yake yi tsaye a gabana babu kaya kuma me yake nufi da har yanzu da kaya a jikina?


“Ban gane ba.” Na faɗa da alamar tambaya.


“Adamu, na faɗa maka ni zan kasance malaminka duk wani abu da kake son ka zama, ni ne zan koyar da kai...yanzu muna a matakin da zan gwada maka iko, mallakewa da kuma samun nasara.”


Ban san ta yaya ya yi nasarar barin gabana ba, ya dawo ya zauna kusa da ni inda ya fara shafar kafaɗa a hankali yana yin ƙasa...


“A yanzu yarjejeniya ce zamu ƙulla tsakanin ni da kai.”


“Ta yaya kenan ake ƙulla wannan yarjejeniyar!?” Na faɗa rai a ɗan ɓace.


“Ka kwaɓe kayanka tukuna sai na nuna maka.”


“A'a, a'a ! Ba zan fidda kayana ba!!”


Na yi sauri na miƙe tsaye lokacin da na ga al'aurarsa ta fara sauyawa.. abu ɗaya nake ji a lokacin shi ne son yin amai.


A wani ibtila'i kuma na kawo kaina? Tambayar kaina nake shin wannan mutumin da ya kawo ni nan ya san da wannan abun, sannan na cewa kaina ta yaya ma zai rasa sani, tun da shi ya kawo ni nan.


“Ka sani Adamu, idan aka shigo wannan harkar, abu ɗaya da ke iya fitar da mutum shi ne mutuwa, kuma ka yarda da ni mutuwar da nake faɗa ba irin wacce kake tunani ba ce.”


A haka ya fara yi min barazana.


“Ka san matasa nawa suke son kasancewa a matsayin ka a yanzu? Ka san matasa nawa suke a shirye da su rasa ɗuwawunsu dan kawai su samu rayuwa mai kyau da dukiya? Toh bari ka ji ya zamar maka dole ka yi biyayya saboda tun da ka yi wannan zaɓin dole ka yi abinda ake so... A cen waje, sun san kana tare da ni, kira ɗaya kawai zan yin su gane ka ƙi yin biyayya. Ka san abinda muke yiwa mutanen da ke ja baya? I prefer not to tell you.”


Zuciyata ta shiga bugun uku-uku, sassan jikina suka fara rawa jin kalamansa... Lokacin da ya lura da tsoro ya shige ni, sai ya sassauto ya dawo sigar lallashi.


Kamar wani dodo haka nake ganin sa yanda ya sauya lokaci guda ya ce

“Adamu, yi tunanin rayuwar da zaka samu, ƙarfin iko, irin mutanen da zasu ji tsoranka.. yi tunanin irin sauyin da rayuwarka zata samu... Ka san wani abu yaro, mu ma da kake gani sai da muka bi ta nan kuma duba yanda muka dawo yanzu. Babu wanda zai san kai wanene, ko kuma abinda kake yi ! Zaka yi rayuwarka cikin kwanciyar hankali..”


Ban ma san wane irin tunani nake yi ba, gani tsaye, shi kawai nake sauraro. Za a iya cewa kamar yana gusar da tunanina da kalamansa masu ratsa ni..


Ban san ta yaya zan muku bayani ba, kawai sai tsintar kaina na yi wandona a ƙasa, na yi kamar ruku'in sallah. A hankali na ji yana min massage, sannan na ji kamar yana zuba min wasu ruwa masu yauƙi a jiki.


“Meye kuma wannan?” Na faɗa ina ɗagowa cikin tsoro.


“Kar ka damu, lubricant ne kawai dan kar ka ji zafi...”


Abin ƙazanta da ƙyama, ba zan so baku labarin wannan baƙin gurin ba...


Ina jin yanda yake kusanto bayana, na rufe idanu, cikin ƴan daƙiƙu yarjejeniya ta ƙullu tsakanin ni da sabon malamina..


Na sha kuka saboda tsana da ƙyamar kaina da nake ji, na ji babu abinda nake so da ya wuce na kashe kaina.

Lokacin da ya gama, ya ce min

“Daga yau kai na hannun damana ne. A komai daga ni sai kai.”


Wata ƙatuwar akwatin kuɗi ya fiddo ya ajiye min... Mai ɗauke da miliyan ɗari biyar cif.


“Ga wannan, je ka sha shagalinka, ka zaga duk inda kake so !”


Tuni yanayina ya sauya.. ƙarfin kuɗi kenan.. kuka ya koma dariya. Daga ƙarshe ma cewa kaina na yi, ba komai ma tun da buƙata ta biya.


A zahiri Alhaji Balla, bai san yana shirin ƙirƙirar baƙin dodo ba ne.


Washe gari na koma gidana, mutumin nan ya dawo ya tambaye ni idan komai lafiya, na amsa masa da eh. Ya yi min bayanin cewa daga yau zan kasance a koda yaushe kusa da Alhaji Balla domin a haka tsarin yake.


Dalilin hakan, ya sa koda yaushe ina tare da Alhaji Balla. Ya mayar da ni kamar matarsa, a cewar sa ana yi ne ɗan ƙara ƙarfafa ƙarfin iko.


Na yi tafiye-tafiye a ƙasashe da dama na duniya sannan na dawo. A lokacin ne fah abubuwa suka fara rincaɓewa a masana'anta...


Hassada ta shiga, mutane na tambayar me ya sa sabon shiga ya samu matsayi haka kuma ta yaya nake jan hankula har haka..


Da yake tsinanniyar duniyar ce da mu, wacce ta kasance kowa mugu ne a cikinta, na fara fuskantar jifa ta baƙin tsafi.. gashi sabon shiga ne ni, ba wani ƙarfi ne da ni ba duk da ƙoƙarin kare kaina da nake amma wasunsu sun fi ƙarfina..


Ciwo na yau daban na gobe daban... Alhaji Balla kuwa ya nuna halin ko in kula, asibiti kawai nake iya zuwa inda babu su kuwa babu wani magani da suke iya yi min..


Mutumin nan ne kaɗai da ya yi silar shigata ƙungiya ya bani shawara, wata rana ya ce min

“Adamu, yanzu kai ba irin sauran mutane ba ne, ya kamata ka je ka nemi yanda zaka kare kanka, domin baka sani ba fah, mutane ba son ka da alkhairi suke yi ba koda kuwa suna nuna maka haƙoransu !”


“Toh ina kake ganin zan je na nemawa kaina kariya?”


“Zan kai ka wajen wani hatsabibin matsafi... Zai baka duk wata kariya da ya kamata.”


Ku ji fah, tun da na shigo ƙungiyar babu wanda ya taɓa min maganar akwai kariyar kai da mutum zai nemawa kansa, dan haka gare ni wannan labari ne mai daɗi... Babu wani dogon tunani na amince !


Cikin daren ranar na ga tashin hankali... A wannan daren kai ka ce mutanen da ke neman cutar da ni sun ji zan je neman kariya.


Na ga musifu a daren... Farmaki ta ko'ina. Ina kwance zan ji ana tafiya ko gudu a cikin gidan, ko kuma na ga mutane na fitowa suna ɓacewa a gaban idanuna.


ƙadangaru da ƙyanƙyansu kala kala na ban tsoro bisa katangu. Da ƙwari masu mugun wari na yin amai.


Akwai lokacin da ma na ji wata irin ƙara ta fashewar wani abu, ina zuwa falo na tarar TV ta ce ta yi bindiga ita kaɗai. A kitchen ma wuƙaƙe da tukane ke ta dukan juna kamar a maƙera.


Haka na daure har gari ya waye na yi sa'a mutumin nan ya zo da sassafe, ya faka motarsa sannan ya ce mu tafi.


Ban san ina zamu je ba... Bayan tafiyar kamar awa ɗaya, muka yanka ta wani daji, wata hanya marar kyau, mai kwazazzaɓo wacce ba kwalta ba ce... Allah ya taimaka ya iya tuƙi, ya san hannunsa.


Muka iso gaban wani tsohon ɗaki na ƙasa wanda shi kaɗai ne a tsakiyar dajin, wani mutum muka ga ya fito daga ciki, tarin ganye ne kaɗai ɗaure a ƙugunsa, a hannayensa kuma layu sai saman kansa gashin kaza.


Babu takalmi a ƙafafuwansa kuma bai da haƙora bakinsa, zaka yi zaton a tsugunne yake alhali tsaye yake, kawai jagarta ce gare shi.


“Wannan shi ake kira ƙurungu mutumin aljanu.. zo mu je mu gan shi !!!”


To be CONTINUED...