CHAPTER 8
by @ashtar
DAN MAFIYA 🧛♂️
#CHAPTER_8
By ✍️ Malik al-Ashtar
GARKUWA WRITTERS ASSOCIATION📚✍️
Book on Wattpad 👉 ***
On Arewabooks 👉 https://arewabooks.com/book?id=6350e2ebfd0f045b385cfaf1
For more Novels 👉 ***
Da fitowarsa bai ko kalle mu ba ya ɗauki hanya cikin daji, mutumin ya ce na bi bayansa.
Na shiga bin bayan ƙurungu mutumin aljanu da ke ta nusar daji ba tare da ya waiwayo ko sau ɗaya ba, ni kuwa ina biye da shi, ina saka ƙafata duk inda ya saka tashi.
Ba tare da mun furta ko kalma ɗaya ba har muka iso bakin wani babban fili mai ɗauke da ciyayi kamar wani ɗan ƙaramin ƙauye.
Tambayar kaina nake ta yanda aka yi guri irin wannan yake ɓoye a nan da nisa. Zaka iya bin gurin tsawon shekaru a bayan ɗan ɗakin da ƙurungu ya fito ba tare da ka yi tunani akwai kyakkyawan gurin a nan ba. Kyakyawan guri amma mai haɗari domin da ka gani ka san guri ne da ake yin tsafi.
“Jira ni nan. Kar ka motsa, kar ka je ko'ina !”
Na tsaya kuma a daidai lokacin na fahimci ashe ina tsakiyar wasu bishiyu ne wanda aka ɗaurawa jan ƙyalle a jikin kowanne.
Na kalli gabas na kalli yamma, zuciyata na dukan uku uku.. ina tambayar kaina me ya kawo ni nan..
Ya ƙara yin ƴar tafiya gaba sannan ya dawo ɗauke da zakara a hannunsa. Zakaran ɓaki ne daga jikinsa har idanunsa... Kamar.. ban sani ba amma dai da ka gani ka san wannan ba zakara ba ne.
Ya miƙo min zakaran sannan ya fiddo wuƙa da kuma ƙwarya ba tare da na ga ta ina ba sannan ya ce
“Ka yanka, ka sha sannan ka yi wanka da shi.”
Kar ku damu na fahimci me yake nufi ! Aikatawar dai shi ne matsala...
Zakaran yana kallo na cikin idanu, na riƙe shi da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuwa na riƙe wuƙa. Ita kanta wuƙar abar al'ajabi ce.
Dga baya da na yi tunani... Sai na ga bani da wani zaɓi... Rayuwata ke cikin haɗari, dan haka na riƙe zakaran, na sa wuƙar na yanke wuyansa farat ɗaya.
Jinin ya fara zuba cin ƙwaryar, baƙi ƙirin yake jinin kamar ba zai daina zuba ba. Ga wani ƙarni marar daɗi da ke fita cikin jinin.
Lokacin da jinin ya gama zuba, sai ya nemi da na ci kayan cikin zakaran, irin su ƙoda, hanta da ƴan hanji.
Da ƙyar da ƙyanƙyami na yi nasarar saka su bakina, sannan ya nemi da na sha baƙin jinin na zakaran, shi ma hakan na aikata sannan ya juye min sauran a jikina.
Tun daga kai zuwa ƙafa.
Kuma haka yi kamar kullum na ƙara jin wani ƙarfi da son mallaka suna ratsa sassan jikina... Dandanan na ji ina buƙatar ƙara matsayi da ƙarfi.
“Ka tafi yanzu.. jinin da na zuba maka, jinin duk mutanen da suke takurawa rayuwarka ne kuma zaka ga sakamako.”
Na juya bakina ɗauke da galmin hanji da kuma jikina da yake ƙarnin jini. Na tarar da mutumin bakin mota muka juya muka tafi.
A cikin bayanin da ya yi min, kwana uku ke gare ni ba tare da na yi wanka ba ko na ci wani abu domin hakan ne zai sa a samu biyan buƙata.
Dan haka a cikin kwanaki ukun, na ga abubuwan al'ajabi...
A wajen aikina, akwai abokan aiki wanda muke mutunci da su sosai, ashe su ne ke neman kashe ni dan su maye gurbina...
“Duk wanda zaka gani toh ba shi ne, iska ne kuma kar ka yafewa kowa.”
Bayani na ƙarshe da Ƙurugu ya yi min kenan.
Rana ta farko da muka dawo daga wajen wajensa, maguna suka taru bakin ƙofata... Suna kuka, suna yakushin ƙofar, kuma kukan nasu irin na mutane..
Abin da ban tsoro har zuwa lokacin da suka daina...
A kwana na biyu, wajen ƙarfe takwas na samu baƙuncin wata abokiyar aikina, sakatariyar Alhaji Balla... Na bar ta ta shigo duk da ina tune da ka'idojin da aka gindaya min.
Nunawa ta yi kawai ta kawo min ziyara ne, ta fara min maganar aiki da wasu abubuwan marasa ma'ana, ko wanda basu shafe ni.
Bayan wani ɗan lokaci, na tambaye ta gaskiyar abinda ya kawo ta, nandanan ta fara kuka sannan ta fara bani labarin yanda da farko ita bata amince ba amma sauran ne suka yi ta zuga ta..
Sannan roƙi na janye abinda na tura musu sun tuba
“Ciwon baya da ka dinga fama da shi aikin wane ne, ciwon ƙafafu silar wane kaza ne, haka ma ciwon kai, ni ciwon ciki kawai na saka ma, kuma har akwai shirin son makantar da kai nan gaba.”
Abun akwai tsoratarwa duk da ban san wani aike take maganar na yi musu ba, na nuna mata na fahimta, sannan na ce mata zata iya tafiya..
“Sauran ma suna nan tafe ganin ka, mun yanke shawarar duka bayyana kan mu.”
Abinda kuwa aka yi kenan kafin kwana ukun, ni kuwa aikin korar su kawai na yi ta yi duk lokacin da suka zo.
Bayan kwanakin ukun sun cika, mutumin nan ya zo gidana, na bashi labarin abinda ya faru, ya bayyana min cewa Ƙurungu, shi kaɗai ya san me ya tura wa ko wannensu.
Daga baya kuma hukunci ya biyo baya, ko wannensu zaɓi biyu gare shi, kai da kake son ka kore ni, ko ka ajiye aikin naka ko kuma ka zauna ka rasa ranka ko ka kamu da wata babbar cuta.
Wanda basu kai ga aikatawa ba ma, sai da suka zo suka nemi gafarata gudun kar wani abu ya same su... Kaɗan daga aiki Ƙurungu kenan.
Wata biyu bayan komai ya dawo normal kuma har yanzu mai gidana ko na ce Alhaji Balla yana cigaba da mallaka ta (kusanta ta), wani mugun tunani ko na ce wani tunani mai kyau ya zo mini na son ƙwace matsayi da maye gurbin Alhaji Bala...
Komawa na sake yi wajen Ƙurungu na yi masa bayanin abinda nake buƙata, tambaya ta ya yi
“Ta yaya yake yi wajen mallakar ka?”
“Yana samu na ta baya ne..” Na bashi amsa.
“Kai ma ka yi nasarar samun sa ta bayan, zaka gani ! Idan ka aikata hakan ka dawo nan gurina ni kuma zan faɗa maka sauran abinda zaka yi.”
Alhaji Balla ya kasance shahararre kuma tsohon matsafi ne, bai yarda da kowa ba...
Ko fitowa bai cika yi ba sai idan zai je cin abinci.
Dan haka sai da ya ɗauke ni kusan shekara ɗaya sannan na samu wata dabara...
Mun fita cin abinci a restaurant namu wanda muka saba wata rana da yamma kuma kamar yanda muka saba, muna gamawa muka je gidansa domin aikata abinda muke yi, sai dai abinda Alhaji Balla bai sani ba, a wannan ranar ni ma na zo da nawa wani shirin...
Ba tare da ya fahimci me yake faruwa ba, gajiya da kuma baccin da ya zo masa lokaci ɗaya, ya yanke shawarar ɗab kishingiɗawa saman doguwar kujera, ba a ɗau lokaci ba bacci ya yi awon gaba da shi...
Sai gashi bayan kwashe shekara ɗaya ina planning yau Alhaji Balla ya shigo hannuna...
TO BE CONTINUED...