SAHLA a Paris

My goal

by @azizat

TOP-NOTCH.....the touch of excellence just for you.

✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈

013...My goal..

***

Wayata Gionee ta dawo ga kuma iphone 6. 'Yan bakin ciki sai su mutu arzikin Sahla ya zo.

lokacin dana ɗaura layina a sabuwar waya. Naci karo da texts ɗin Affan guda uku.

1- Sahla dear, i didn't mean to. Ba halina bane, soyayyar dana ke miki ya sa na rasa nitsuwata a kanki. Dan Allah ki kunna wayarki mu yi magana.

2- i'm sorry Amal ta dawo ta ga abincin da kika kawo, na san za ta gayawa Mom. Kiyi hakuri da faɗan da Mom za ta miki. Ki amsa wayata please...

3- kin san ke kanwata ce ba zan taɓa cutar da ke ba. Abinda ya faru was a mistake Dan Allah kar ki gayawa Abbanmu ko Alhaji...

Shege ashe ya ji tsoro. To ko na faɗawa Alhaji ne. To na ce me ?

' Alhaji na kaiwa Yaya Affan abinci shine ya tsareni a ɗaki wai zai ciremin kunya'

Wata zuciya tace min 'Hmm Sahla ki yiwa kan ki faɗa ki rike abin nan a ranki'

Allah zai saka min. Kuma sai na rama koba daɗe koba jimawa...

Ban san ana min bakin ciki ba a gidan nan sai da iphone ta shigo hannuna. Takanas na je falon Alhaji na nuna masa wayar da aka bani na ce ya tayani yiwa Uncle Faruku godiya. Ya ce sai in yi hankali da ita dan iphone ba Gionee bane.

Wallahi ko zaman minti biyar a ɗakin Kaka ba aka aiko wai a kirani.

Mama da Ummi ne suka haɗa zama.

Amal, Hanifah da sauran duk suna nan.

Ina shigowa Mama tace

"Yawwa. Sahla zo nan. Ance Faruk ya aiko miki da waya ko?"

"iphone 6 ya siya mata fa" Hanifah ta faɗa. Da wani katon bakinta a wajen.

"Lokacin da aka chanja muku waya duk tare aka haɗa aka siya muku. Dan haka ba zai yiwu yanzu ace ke kina da sabuwar waya su kuma basu da shi ba. Hanifah kin ce kuɗin wayar ya kai nawa?"

Kafin ta bada amsa Amal tace " Mama wallahi shige masa ta yi, na san rokon Uncle F Kay ta dinga yi. Sahla ba dai kwaɗayi ba. Haka ta samu Akhi wai tana son shi harda kai masa wani shirmen abincinta"

Raina yai matukar ɓaci. Ga ɓacin ran Affan ga kuma wannan fin karfin da ake son yi min.

Na ɗaga musu wayar nace " ga dai wayata nan original iphone 6 ne kamar yadda kuka gani" na nuna musu tambarin gutsirarren apple dake jiki.

"Wacce ta ke ganin roko nayi aka bani Dan Allah itama tayi rokon ta gani ko za a siya mata"

"Waya kuma in banda Alhaji banga wanda ya isa ya hanani amfani da ita"

"Sahla rashin kunya zaki mana. To wallahi sai kin bayar da wayan nan"

"Ayya! Ummi ina ce akwai Likita mai zuwa wajen Hanifah. Ku ce masa ya siya mata iphone"

"Wannan wayar dai farar kafata ce ya kawo min".

Na juya na tafi abina ina jinsu sunata masifa ko a jikina.

Dana shigo ɗaki na fara mamakin ya akayi suka san Uncle Faruku ya siya min waya.

Ikon Allah. Ashe munafurfur ɗin gidan ne. Lokacin da naje Umma Bilki na falon tana yankawa Alhaji lemo.

Munafuka ta je ta gulmata musu ta makale a ɗaki kamar ba ta yi komai ba. Kai ta Allah ba taki ba Umma Bilki...

***

Lokacin da Alhaji ya shigo ɗakin Rafee'ah a zaune ya sameta akan sallaya ta ɗaga hannu tana addu'a tana kuka.

Ya samu bakin gado ya zauna yana jiranta. Bai taɓa nuna mata ba amma ya damu kwarai da rashin haihuwarta. Musamman ma da ya san har yanzu da lafiyarsa tunda ga shi Zainab (Ummi) tana nan da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe.

Bata daina addu'arta ba duk da kuwa ta ji shigowar shi.

"Allah kai ka bawa Zainab haihuwa har ta buɗi baki take min gori akan baka bani ba. Allah kaine ke bayarwa a lokacin da ka so kuma a yadda ka so, Allah ka bani haihuwa. Allah ko da sau ɗaya ne nima kasa na samu na ɗauki ciki na haihu. Allah kace idan aka shiga cikin kunci a tuntuɓeka domin kaine mai yaye kunci. Allah ka yaye min wannan kunci, ka maida min shi da farin ciki..."

Ta dinga nanata kalamai masu taɓa zuciya.

Alhaji yana zaune yana jinta. Jikinsa yai sanyi. Yayi alkawari yai bayan Maryam ba zai sake saki ba saboda illar sakin daya gani tunda gashi har yau baya da wani iko akan yaran da Maryam ta haifa masa, yana matsayin Uba ne a garesu amma babu shakuwa ta Uba da 'ya'ya a tsakaninsu. The last time da Rafee'ah ta masa maganar mutuwar auren Sayyidah takanas ya shirya ya tafi chan US ɗin. Amma Sayyidah tayi girman da bata bukatar taimako ko soyayyar shi. Kiri da kiri ta nuna mishi ba zata iya zama da shi a Nigeria ba.

"Idan na koma Nigeria bani da 'yanci sai abinda kuka ce kai da Kaka. Na san aure zaku ce zaku mun, ni kuma ba zan iya auren ɗan Nigeria ba. Ba zan iya zama da namijin da mace ɗaya ta masa kaɗan ba. Na saba da nan ba zan iya komawa Gombe da zama ba. Ka yi hakuri ka barni a nan"

Yana kauda kai ne a lamarin Zainabu saboda 'ya'ya dake tsakaninsu. Duk cikin halayenta babu wanda ya ke kyamata sama da sata. Alhamdulillahi yana iya kokarinsa wajen wadatasu da komai duk da 'yankoma baya da aka samu a kasuwancinsa. Amma Zainabu. Yayi masifar yayi hukuncin amma duk da haka lokaci lokaci yana kamata da laifin sata. Akwai lokacin da ya horata kusan shekara ya hanata shiga sashensa, saboda idan kuɗi bai ɓata ba agogo ko hula zasu ɓata. Irin satan da take masa tun farkon aurenta har yanzu yasa shi banbance satan da su Abdullahi da su Abbas ke masa da kuma wanda take yi.

To ya zai yi. Banda hakuri. Shi ya gani yace yana so. Abin kamar magani, tunda ya auri Aishatu sai zuciyarsa ta kwaɗaitu da cika sunnah zuwa mata huɗu. Zainabu kanwar wani abokinsa ne da suka taso tare.

Bilkisu ya haɗu da ita a gidan Radio. Tayi NCE Hausa tana aiki a nan. Bayan aurensu ya hanata aikin saboda wasu maganganu da ya ke ji akanta.

Rafee'ah? A rasuwan Sulaiman ya ganta lokacin tana bautar kasa a Asibitin da aka kai gawar Sulaiman. Sai da yai bincike ya gane ashe 'yar'uwar Maryam ce. Alhamdulillah gasu nan yau aure ya bawa shekara goma shauku baya.

Bai tanka mata ba har ta gama addu'o'inta ta shiga nannaɗe sallaya.

Wayarsa ce ta shiga kara ya ɗauka da sauri ganin mai kiran.

"Eh tana nan. Gamu nan zuwa ranka shi daɗe"

Yana gama wayan ya kalli Rafee'ah wacce itama shi ɗin take kallo.

"Maimartaba ne. Akwai wani case na haihuwa, ana bukatan ki"

Bata tambayeshi karin bayani ba ta cire hijabin sallarta ta buɗe closet dan ta ɗau ko wani hijabin tunda babu halin chanja wani kayan.

***

Tabbas Allah yana amsa addu'a a lokacin da ya so, a yadda ya so.

Rafee'ah ta sake kissing goshin yaron wanda har lokacin bacci yake. Bata taɓa jin karɓan ɗan wani ba. Kanwarta Hadiza ma ta mata tayin Ihsan ɗinta amma ta ki. Idan ta karɓa na kwana nawa ne za a zo a karɓa ko kuma a fara mata gori. Ta jure zama ita kaɗai iya waɗannan shekaru amma tun daga haihuwar yaron nan ta ji son shi ya shigeta. Ya sha wahala sosai.

Ba ta iya shiru ba lokacin da suka baro Asibitin ana maganar za a kai yaron gidan marayu. Tace Alhaji ya mata alfarma ta adopting yaron.

Mahaifiyar yaron mahaukaciya ce. Nakuda ta fara aka kaita Asibiti abin ya zo da complications shine aka gayawa Sarki ana bukatan kuɗin da za a mata aiki.

An mata aikin but she didn't make it. Ta jima tana yawon hauka. Akwai lokacin da aka ce har a Fada tana kwana. Daga baya kuma ta gudu ba a sake ganinta ba kusan shekara biyu sai gata nan kumadu amma wannan karan har da tsohon ciki.

Ta kissing kumatun yaron tareda kiran sunansa 'Ayman'

***

Ina zama a aji na ajiye jakata a gefe ina murmushi. Yau zamu fara lectures. Duk da ban samu course ɗin dana ke so ba amma wannan ɗinma ya min. Zan karanta abinda mahaifina ya karanta kuma sai nayi suna sama da Mahaifina. Ina ga ma yin Allah ne ya sa ban samu first choice ɗina ba sai second choice dana zaɓa wato English and Literature.

Wata budurwa ta zauna gefena tareda mikomin hannu muka yi musabaha.

"My name is Nazifa"

"My name is Sahla"

"Wow nice name"

Nace "Thank you"

Ba a jima ba lecturer ya shigo muka fara lectures ɗinmu na farko.

Kai Jami'a akwai daɗi. Ina tafiya a cikin school ina jin kaina nima wata ce. Ina tsakiyan sabbin friends ɗina Nazifa da Alheri, muna tafiya muna taɗi. Kowa da burin daya saka a gaba.

Ni nawa burin na yi karatu mai zurfi na zama professor of English. Wai! Har na hangoni ana kirana da Professor Sahla.

Wannan burin na saka a gaba kuma sai na cika shi. I will make my late father proud. I will make Alhajinmu proud.

Mun gama lectures fa tuntuni amma muka yita yawo har hostel. So nake na ga Jami'a, Jami'a ta ganni.

Ni kaɗai ne a GSU. Hanifah ta samu ABU amma maimakon Pharmacy sun bata Biochemistry. Ita kuma Safiyya dama JAMB ɗinta bai yi kyau ba balle har tayi tunanin samun admission.

Da farko Hanifah tace ba za ta je ba sai an chanja mata course amma chanjin course bai yiwu ba dan haka da ta bari admission ya wuceta sai ta hakura ta je tayi registration.

Safiyya kuma wai za a nema mata admission a Fed Poly Bauchi.

Ni kam ina ruwana ina son GSU ɗina. In je lectures in dawo gida in haɗu da tsohuwata.

Tun bayan rabuwar mu da Affan na hana kaina kula samari. Shegu kaman ance na shiga GSU dan samari ne. Bini-bini Sahla ina so mu zama friends, Sahla ina son ki. Sahla ki bani chance na zo gidan ku.

A ajinmu idan ka cire Ma'aruf sai kuma course rep ɗinmu Hassan babu namijin da nake kulawa. Kowa sese ne tsakanina da shi.

A gida kuma Yaya Yusuf ne yake takura min. Watarana takanas ya zo ya ɗaukeni bayan mun gama lectures ya kaini wani restaurant har ina tunanin abin kirki yasa shi zuwa ɗaukana ashe da nasa manufar.

Muka zauna ya tsige mun abinda ke ran shi. Wai sona yake. Wai da gaske idan na bashi dama aurena zai yi. Wai ya jima yana dakon soyayyata.

To ni na bashi dakon ne da zan biya. Shi ya ga zai iya shiyasa ya ɗauka.

Ya gama I love, I die, I live, I mad ɗinshi na ce masa yai hakuri ni na dena soyayya. Ko zan yi soyayya ma ba zan kara yi da ɗan gida ba, Allah ya kiyaye, ɗan bakara.

Mun jima a wajen yanata yi min karatun so amma na ki ɗaukan darasi ko ɗaya. Toshe kwakwalwa na nayi karma ta yi munafurcin ɗaukan karatun ba tareda na bata izini ba.

Imba Yaya Yusuf bama, sai daya gama zane nin zai wani biyo baya wai yana dakon soyayya na. Wallahi irin dukan da ya min ko Yaya Mustafah iya kaci.

Cewa yai zai bani lokaci na yi tunani kafin mu kare first semester ɗinmu. Na ce masa kar ya sa rai. Haka kawai, ba a soyayyar dole...

*

Karatu ya fara nisa dan assignment da presentation muke yi ta ko'ina. Book review da ake bamu kuwa kamar bamu da abinyi sai karatun littafi.

Mr Thomas ya bamu review ɗin littafin Jaguar Nana, shi kuma Mr Akilu ya bamu review na Chinua Achebe. Ga Malam Mukaddas ma ya bamu kusan littafi uku yace mu rubuto mishi review ɗinsu.

Yanzu Karatu nake kamar zan yi hauka wani lokaci dai sai ka ganni da novels huɗu a lokaci guda ina karantawa.

Sai da muka shigo tsakiyar semester na gane cewa Jami'a ba wasa bane, ashe daɗin suna garai ba daɗin yi. Ni da Nazifa da Alheri da Ma'aruf muka haɗa clique ɗinmu, muna taimakawa juna da tutorials. Abin dai kamar na hakura da burina. In dai haka first degree yake da wahala to da alama ba zan kai matakin Professor ba. Kai Ya Allah...

Litattafan TOP-NOTCH na kuɗi ne

Abinda ya baka TSORO---Ramlat MaiDambu

Bani da LAIFI--- Shatuu

SAHLA a Paris---Azi_zat

Guda ɗaya 350

Biyu 700

Uku 1000

Account details

3091721807

Aisha Kwalam Hassan

Firstbank

Za a iya tura shaidan biya ga ɗaya daga cikin nambobin nan:

***

***

***

Ga masu turo katin MTN kuma zasu tuntuɓi numban Zahran Adda Ramlah:

***

'Yan Niger kuma su tuntuɓi Nana A'ichah:

 + 22784506476