The Plan
by @azizat
TOP-NOTCH.....the touch of excellence just for you.
✈✈✈SAHLA a Paris✈✈✈
014...The Plan...
Ina zaune ina rubuta review Anty Amarya ta yi sallama. Kaka na zaune ta yi nisa da tunani.
"Sahla dan Allah ga Ayman nan ki kula min da shi kafin na dawo. Muna da surgery ne ba zan iya tafiya da shi ba. Akwai abincin shi a nan, idan akwai abinda na manta ban saka ba ga key nan ki je ki ɗauka"
Tab. Anty Amarya ce da barin key ɗin ɗakinta. Kai ashe reno na chanja mutum.
Na karɓi Ayman ina mishi wasa. Lokacin da aka kawo shi Alhaji ya tara dukka gidan aka yi meeting yace mana Ayman ɗan Anty Rafee'ah ne dan haka ɗansa ne. Ko bayan ransa bai yafe ba wanda yaiwa Affan kallon ba ɗan Kabiru Ubandoma bane.
I remember har sunan Ummi da Umma Bilki ya kira ya ja musu kunne akan duk wacce ta yiwa Ayman gorin asali a bakin aurenta. Alhaji yayi faɗa sosai.
A ranan sunansa anyi shagali sosai. Bayan sati biyu da sunan shi Ummi ta haifi 'ya mace. Ta sha burin namiji zata haiho amma Allah ya turo mata 'ya mace.
Tun kafin ayi suna aka fara rikici da ita akan Alhaji ya ki sake hannu ayi shagalin suna kaman yadda aka yiwa Ayman. Rabon da ayi haihuwa a gidan ai an jima. Alhaji yace ba za ayi shagali ba.
Ita dai yarinyar ba a saka mata suna Fatima ba sai aka saka mata Khadijah muna kiranta Baby Dijah...
"Kaka ta yi bacci ne?"
"Ki bar Kaka fa. Kuna magana yanzu zata bige miki da bacci"
Anty Rafee'ah ta fita bayan ta yiwa Ayman kiss a goshin sa.
Yaron kyakykyawa da shi, idan ba a faɗa maka ba baza ka taɓa sanin ba Anty Amarya ta haifeshi ba. Shima fari ne sosai kamarta.
Da na ga yaron zai hanani rubutu sai na ɗaura shi akan gado, ya ɗan yi kuka kaɗan yai shiru ya fara bacci.
Ina rubutu Kaka tace " Sahala yanzu wai Kabiru da AbdulKarimu ba zasu biya mini kujerar Makkah ba. Anya ba zan sai da Tumakai da Awaki na ba?"
Na yi dariya nace " Kaka kenan, kuɗin jirgi fa ba kuɗin motar Gombe zuwa Abuja bane. Kaka kema ki hakura da maganan nan, kwanan nan fa kullum sai kin yi korafin kafanki"
"Kema goya musu baya zaki yi. Ai ina gani a TV masu lalurar kafa na zuwa Hajji, zaka ga ana turasu a keke"
"Kaka idan aka ce za a biya miki kujera ma ni zan ce kar su biya. You are so obssessed..." kwal na ji sanda a kaina.
"Amma Kaka Allah, Allah kina cin zalina, nifa marainiya ce"
Ta ɗaga sanda za ta sake kwaɗamin na yi saurin jan littafina na gudu...
*
Su Abba zasu dawo Nigeria da zama. A bakin Kaka na ji yau dana dawo daga lectures.
Na yi ko oho da labarin. Ni ina ruwana da su, idan ka cire Abba dukkansu ba ruwana da sha'aninsu.
"Ni kam ba zance kuke da Afan ɗinba"
"Allah ya kiyaye na yi zance da shi. Ni fa Kaka ki barni, karatu zan yi mai zurfi sai na ga karshen biro"
"A'a ki zama Alhudahuda karshen karatu kenan. Ke da nake so ki shirya da Yusufa nayiwa Kabiru magana a yi 'yar gida nan da farkon shekara mai zuwa"
"Kaka karatu zan yi. Ba ruwana da aure. Mai ake yi a aure banda cire kunya"
"Auren ne ba amfani. Ita Asiya data sha boko ta koshi gashi har yanzu babu mashinshini. Ina raye ba zaki karisa boko ba sai a ɗakin mijinki. Ba kya ganin Asiya ne"
"Kaka kenan, ke kika ce jifa aka yiwa Anty Asiya yanzu kuma kince boko ya hanata aure. Da aure da mutuwa duk lokaci ne. Ke ya ba ki mutu ba da Inna Sadiyya ta rasu."
"Amma Sahala zan ci..."
"Sulaiman yana can kabarinsa. Kila ma yana jiran zuwanki gobe"
"Sahala!"
Na kyalkyale da dariya. Tsohuwar tawa bata son zancen mutuwa.
Ko sati biyu ba ayi ba da maganan da muka yi da Kaka su Abba suka dawo. Ance Affan yana chan saboda zai karisa masters ɗinsa. Ita kuma uwar yanga Amal ance transfer za a mata ta dawo private university, ko wannene ohon musu.
Da alama Mom ɗinsu ba ta so dawowarsu ba. Daga baya naji gulma a cikin gida wai bata so su zauna a Gombe ne, ta fiso su koma Abuja.
Matar nan tunda suka dawo ita da 'ya'yanta sai sun ga dama suke shigowa su gaida Kaka.
Ni ko ina ruwana babu abinda na saka a gaba sai karatu dan mun kusa fara exams...
Abinka da kawancen munafurci. Ummi da Mama sai da suka yi kaca-kaca akan Mom.
Matar nan sai wani shishshige mata suke yi ita kuma tana koransu kamar kuda. Idan ka cire Anty Rafee'ah babu wacce take gani da wani daraja. Girman kan tsiya ne da ita ga rashin son mutane ko nace talakawa.
Akwai wani rana da kunnena naji Mom ɗinsu Amal tana kiran su Ummi da 'ya'yan matsiyata.
A raina nace madallah, maganin masu kwaɗayi kenan.
*
Alhamdulillahi mun yi jarrabawa mun gama. Kuma ina da yakinin ba zan samu matsala ba dan mahaukacin karatu nayi, duk kwaɗayina da son cin abincina a lokacin exams ɗin nan wani lokaci sau biyu nake cin abinci, kuma ba wani abincin kirki ba.
Muna cikin hutu daf za a yi resuming school ASUU ta fara yajin aiki. Kamar wasa aka yi yajin aikin sati biyu. Sati biyu ya kare aka sake shiga yajin sai Baba ta gani.
Tun ina tsammanin dawowa har na fara jiran maatayyassara kawai.
Ana wannan zaman shirun ne na fara koyon cake a wajen Anty Rafee'ah. Kila nima cake ɗin zan fara tunda boko ya gagara. Ko ince mu 'ya'yan talakawa Boko ya gagaremu.
A wannan zaman ne aka haɗa auren Asiya da wani abokin Baffanmu Abubakar. Ɗan kasuwa ne yana da mata biyu ita zata je ta uku. I'm very sure Anty Asiya ta amince da auren nan ne saboda maganar mutane. Mutumin fa idan bai yi sittin ba to saura kiris, gashi wani luti da shi. Astagfirullah.
Bikin dai anyi ne amma babu wani armashi. Anty Asiya tace ba za ta yi events ba banda walima. Su kuma Mama da Ummi da ya kamata su haɗa kai ayi komai har yanzu basa magana.
Aka gama hidiman biki aka kai Amarya gidan mijinta a chan Kano.
Muka sake zama a gida muna jiran tsammanin Man Rabbuka. Amma shiru.
Ranan kamar an tsikare ni ina zaune ina latsa iphone ɗina wani abu ya faɗo min.
"Kaka" shiru
"Kaka"
"Na'am"
Ta amsa min da kyar.
Allah Sarki, ta saka damuwa sosai a ranta yanzu bata da wani energy kamar da. Idan ana abu a gidan ma ba kasafai take shiga ba.
"Kaka ina da wani plan. Amma sai kin dage plan ɗin zai yiwu"
"Minene kuma pillow?"
"Kaka Plan ba Pillow ba. Ko dai kunnenki ma ya fara taɓuwa ne"
"Bana son shiririta Sahala. Minene?"
"Ba kina son zuwa Makkah ba. To akwai yadda za ayi hakan ta faru"
Kaka ta mike zaune da sauri jin maganan Makkah.
"Kinga Uncle Faruku yana da kuɗi. Idan kika masa magana zai biya miki kujerar Makkah. Amma wani hanzari ba gudu ba. Idan su Alhaji suka ji labari ba zasu bari ba"
"Eh hakane. To ya za ayi"
"Ai ki dage musu kafarki na ciwo kuma kina son ki chanja Asibiti, likitocin Egypt dana Nigeria duk basu iya aiki ba. Ke yanzu wajen Faruku zaki je ya nema miki likitoci masu kyau a Paris"
"Kina ga zasu yarda?"
"Zasu yarda Kaka amma sai kin yi abu ɗaya"
Kaka ta buɗe ido tana saurarona.
"Duk rintsi kice musu da Sahla zaki je. Kice idan ba da ni ba kin fasa"
"Kai amma Sahala Bokon ki yayi amfani. Ai muna zuwa can wajen Farukun sai mu dage sai ya kaini Makkah ko?"
"Peww. Kaka ni da ke sai mu lula Paris kawai"...
Step 1- shine Kaka ta langaɓe ta kuruta ciwonta. Hakan kuwa aka yi da Alhaji ya shigo ta langaɓe tana masa complain iri-iri. Yace bari ya ɗau mota a kaita asibiti tace masa ita ba ta gane asibitin nan. Dake dama ta kwana biyu ba a kaita Egypt ba sai yace zai yiwa Abba magana a fara shirin tafiyarta Egypt.
Step 2- Kaka ta kekasa kasa tace allanfir ta gaji da Egypt ɗin nan. Duk yadda za ayi kawai a chanja Asibiti. Shekara da shekaru tana zuwa Egypt amma sai dai ciwo ya lafa ya sake dawowa.
Alhaji ya nace dai Egypt ɗin za a kaita.
Step 3- Kaka ta fara emotional blackmail ɗinsu. Kun san dai yadda manyan mutane basa wasa da iyayensu. Abba ne ma ya fi rikicewa. Alhaji kaman ya so gano shirinmu amma da Likita ya confirming jinin Kaka ya hau sosai sai ya ɗan saduda.
Step 4- sun amince zasu yiwa Faruku magana, idan ya amince sai Abba ya rakata Paris. Kaka tace sam babu wanda zai rakata sai Sahala.
Alhaji ya ce ai ina zuwa makaranta. Kaka tace kusan wata uku kenan ana yajin aiki wayasan yaushe za a dawo.
Step 5- anyi meeting. Ance Yusuf ko Sulaiman ne zasu rakata. Sulaiman yana law school an cire shi. Yusuf ya bada uzuri saboda shima zai rubuta professional exams ɗinsa na zama cikakken Medical Lab Scientist. Abdullahi ba shi da nitsuwa. Abbas da Abbas ba hankali. Sahla, Sahlan dai to ya za ayi...
Duk abinda ake ciki na yi likimo kaman ban san komai ba har sai da aka gama kai ruwa rana akace an amince zan raka Kaka jinya.
Abba ne ya kaimu Abuja inda za a min passport da sauran documents na tafiya.
Oh my Goodness. Sahla zata je Paris. Let me scream. Jama'a zan je France, zan bar Nigeria zan je Paris, France.
Hanifah har ɗaki ta biyoni tana min kumfar baki. Na mata kwalele nace aga-aga waye zai fara shiga jirgi a cikinmu.
Aka gama kananun maganganu, aka gama gulman aka zuba mana ido. Na zama Sahla ikon Allah.
Ban san ya aka kare da Uncle Faruku ba amma tunda aka fara shirye-shiryen tafiyarmu na san cewa ya amince. To ya ma isa yace bai amince ba.
Ni kam tuni na bazama sunday market na siyo kayan sanyi dayawa. In Allah yasa na bar Nigeria to ni da dawowa sai na kammala karatuna. Ni ASUU zasu ciwa mutunci. Ko sun ki ko sun so sai na kai matsayin Professor.
Anty Amarya da ta zo ta ga kayan tayita min faɗa wai sai kace me shirin kaura. Ai ba haka ake ba. Ta shiga rage min kayan, zuciyata kaman zata fashe. Ko dai itama tana bakin ciki da tafiyata me. Kai amma Anty Rafee'ah bata da mugun zuciya.
Abuja aka kaimu ranan Monday, ni ina tunanin nice zanyi jagoran tafiyar kawai aka taka min birki wai Uncle Faruku na jiranmu a Abuja.
Bamu haɗu ba sai safiyar da zamu tafi.
Na gaishe shi ina kokarin yi masa godiyar iphone ya shige mota abinsa.
Inaga jifa aka min daga Gombe. Sai da muka zo airport na tuna cewa ashe baro jakar da aka saka mana documents ɗinmu a gidan Baffanmu Ɗahiru.
"Uncle Farukkk Dan Allah a tsaya nayi mantuwa"
Ba tareda ya juyo ba yace " minene?"
"Visa na manta a gidan Baffa"
"Laa. Sahala ba ance ki bawa Baffanki takardun ba idan muka iso"
"Mantawa nayi Kaka"
Ya ɗau waya ya kira Baffanmu ya gaya masa abinda ya faru. Muka tsaya kusan minti goma kafin ya kira yace an gani za a kawo.
Juyowa yai ya kalleni. Muna haɗa ido na ji wani tsoron shi ya shige ni. Anya banyi kuskuren biyo Kaka ba. What if shima kaman Affan ne, gashi nan tsohon tuzuru da shi.
Allah dai ya taimakemu da aka kawo jakar backpack ɗina aka samu documents ɗin a ciki dan har na fara wasu-wasin ko dai ba a ciki suke ba.
Dake mun ɓata lokaci ko minti goma bamu yi ba aka fara kiran passenger jirgin da zamu shiga. Na riko hannun Kaka muka fara binshi a baya dan tuni yayi gaba ya barmu.
Yau dai zan shiga jirgi, yau dai sai Paris...
Litattafan TOP-NOTCH na kuɗi ne
Abinda ya baka TSORO---Ramlat MaiDambu
Bani da LAIFI--- Shatuu
SAHLA a Paris---Azi_zat
Guda ɗaya 350
Biyu 700
Uku 1000
Account details
3091721807
Aisha Kwalam Hassan
Firstbank
Za a iya tura shaidan biya ga ɗaya daga cikin nambobin nan:
***
***
***
Ga masu turo katin MTN kuma zasu tuntuɓi numban Zahran Adda Ramlah:
***
'Yan Niger kuma su tuntuɓi Nana A'ichah:
+ 22784506476