Chapter 1
by @ummubasheer
*_MAHASEEM_*
{ ```Heart``` ```Touching``` ```Story``` }
_NA_
*_UMMU_ _BASHEER_*
```HASKE``` ```WRITER'S``` ```ASSOCIATION``` ...💡
*Alhamdulillah I'm back my Fan's,Ina ma Allah godiya daya bani ikon fara rubuta muku Wannan labarin mai suna MAHASEEM, Sannan ina Mik'a sak'on gaisuwa ta gare ku massoya na,aduk inda kuke.*
*Bamu Dace Da Juna Ba*
*Akan* *Kanwata*
*Zuri'a* *D'aya*
*Ke* *Haske* *Ce*
*Mahaifiya* *Ta*
```Wa'inan littafan nawa duk zaku same su a Arewabook, kuyi searching sunan akwai su complete, pls kuyi Following na
```
*Page 01*
_Wata_ Kyakyawar yarinya ce wacce ba zata wuce Shekaru goma sha bakwai ba na gani ta shigo cikin gidan a guje kamar wacce aka biyo, wata mata dake zaune kan turmi ita ma naga ta tashi ta shige daki a guje, Yarinyar naga ta d'au buta ta shige bayi, Can naga matar nan ta leko ta window ganin ba komi sai ta fito dakin daidai nan yarinyar ta fito bayi tana dariya matar cikin bacin rai tace"Wannan yarinyar akwai fitinaniya inace biyo ki akayi ashe tsabar rashin nutsuwa ne kika shigo a guje"
Dariya ta k'yal k'yale dashi sai ga wata mata ta fito daga dayan dakin tana cewa" _Mahaseem_ meke faruwa ne"
Wacce aka kira da Mahaseem ta fashe da dariya harda rik'e ciki tana nuna dayan matar dake hararar ta"Inna Jummai wai daga shigowa ta kawai naga Inna ladi ta shige daki a guje, aradu ta ban dariya"
Wacce aka kira Inna ladi tace"shegiyar yarinya mai kama da Aljanu kinyi ma kanki"tana fad'in hakan ta shige d'aki.
Inna Jummai ta kalle Mahaseem"A ko yaushe ina fad'a miki ki dinga nutsuwa ke yanzu ba yarinya bace"
Turo baki Mahaseem tayi"Ni wai mene nayi,kawai Inna ladi matsoraciya ce"
"Yanzu dai shiga daki ki canza kayan makarantar"
Mahaseem dariya tayi tare da shigewa cikin daki, ta canza kaya ta fito da sauri inna Jummai tace"ina kuma za kije ko abinci ba zaki ci ba, baki ganin yamma tayi ne"
"Aradu gidan su laure zanje, ina binta bashi yau sai ta biya ni ko inyi mata na jaki" ta fad'i tana tafa hannaye.
Ko kafin Inna jummai tayi magana har Mahaseem ta fita a waje taci karo da Wata yarinya kawai naga ta d'aka mata duka ta ruga a guje, yarinya kara tasa ta shige cikin gidan a guje, Inna ladi ce ta fito hankali tace"Bibalo waye ya dake ki ne"
Bibalo na kuka tace"Mahaseem ce kawai banyi mata komi ba ta d'aka min duka"
Cikin massifa Inna ladi ta shiga surfa massifa"Wannan yarinya ta fitini kowa, shegiya irin mayu zat dawo ta same nine ai"taja yarinyar zuwa d'aki.
Mahaseem tana tafe tana yar wak'ar ta taje gidan su laure a kofar gida ta tsaya ta aiki wani yaro tace yace ana kiran laure inji Habu, nan yaron ya shiga ya fad'a ma laure ai ko da sauri ta tashi ta yab'a gyalen ta saboda Habu saurayin tane,sai dai mai, tana fita tai karo da Mahaseem cikin tsoro zata juya, Mahaseem ta shak'o wuyar ta"Ai yau ba zaki gudu ba, nasan dama ba fitowa zakiyi ba idan bance Habu bane, aradun Allah yau sai kin biyani kud'i na"
Laure gaba daya a tsorace take"sake ni toh in kawo miki ai naira hamsin ce"
Sakin ta tayi ta rik'e mata hannu"toh mu shiga gidan naku ki dauko min kar ma ayi tunanin wani ai mu k'awaye ne koh?"ta fad'a tana daga mata gira
Sanin halin Mahaseem yasa Laurr ta d'aga kai, a haka suka shiga gidan ta shiga d'aki ta dauko naira hamsin ta bata, murmushi Mahaseem tayi tace"Kawata laure sai anjima" ko kulata ba tayi b ta fita,daga nan wucewa tayi wani guri inda ake saida dussa ta siya ta nufa gida tana zuwa ta nufa gurin wata akuya tana cewa"Yar Akuya ta zo kici dussa"ta zuba mata a wani kwano tana shafa jikin akuyar, da bala'i Inna ladi ta fito jin muryar Mahaseem"uban mai Bibalo tayi miki kika dake ta"?ta nufe ta ganin hakan yasa Mahaseem ta shige d'aki a guje ta rufe kofa Inna Jummai na tambayar ta meya faru bata kulata ba ta nufi window tana tsalle tana cewa"ba dai Ubana ba wallahi, Bibalo kuma sai na dake ta tunda ta raina ni"cike da tsiwa take fad'a yayin da Inna ladi ke massifa sosai. Kin bude kofar tayi haka Inna ladi ta gaji ta bar gurin, Inna Jummai ce ta kalle ta"wai ke meke had'a ki da Bibalo ne? "
Tsalle tayi ta haye gado tace"Wallahi ta rainani, nace dazu taba akuya ta ruwa, shine Dan tana gaban Innar ta wai tak'i din dama nace kwarankwatsi sai na dake ta"
Inna Jummai girgiza kai tayi kawai domin tasan Mahaseem da shegen tsokana ga tsiwa.
Wace ce Mahaseem?
Asalin ta y'ar wani k'auye ne Mai suna Rahaama dake Jihar Kaduna,iyayen ta fulani ne Mahaifinta Malam Habibu su biyo iyayen su suka haifa daga shi sai kanin shi Malam Ayuba, iyayen su suna da arzik'i irin na kauyen nan domin baban shi manomi ne,ba'a Dade ba ya rasu inda aka raba musu gado shi Malam Habibu yayi ta tatala gadon shi, a haka ya had'u da wata bafulatana soyaya ya shiga tsakanin su, zance ya kai gaban manya aka daura musu aure, sunan ta Na'ima rugar su tana da Dan nisa daga kauyen nan, tallar nono take kawowa nan, bayan auren su ba'a Dade ba shima Ayuba yayi aure anan kauyen ya samu mata Jummai, a gidan su duk suke zaune, Ayuba shagalin shi kawai yakeyi da kudi duk ya cinye gadon nashi, Malam Habibu yana yawan mai fad'a akan ya dinga tatali sai yace aa shifa gara yaci kudin shi, ana haka Na'ima ta samu ciki,ita da Jummai suna shiri sosai kasancewar gida daya suke,wata rana aka wayi gari mahaifiyar su Malam Habibu ta rasu, sosai suka ji mutuwar ta, bayan wasu watani Na'ima ta haihu ta samu y'a mace aka sa mata suna Mahaseem, Sosai sukayi farin ciki, nan fa malam Ayuba ya fara damuwa ganin jummai ita ko b'atan wata bata taba yi ba, a haka Mahaseem ta shekaru biyu, lokacin Malam Ayuba ya had'u da wata ladidi ta, sosai take son shi amma shi baya sonta, da asiri da kissa tasa ya aureta, tunda akayi auren babu zaman lafiya tsakanin ta da Na'ima da Jummai domin ta tsane su, sai dai ita ma shiru ba haihuwa har tsawon shekaru biyu, lokacin Mahaseem shekarar ta hud'u a duniya, mahaifiyar ta na dauke da wani cikin wata rana suka shirya tafiya rugar su, Jummai ta dauki Mahaseem tace Dan Allah su bar mata ita tunda Mahaseem din ta dage ba zata bisu ba, nan suka tafi suka barta tunda aranar zasu juyo, Allahu Akbar ashe wannan tafiya bata dawowa bace domin a hanyar su ta dawowa sukayi hatsari ba wanda ya rayu a motar, Malam Ayuba ya shiga tashin hankali na rasa dan'uwan shi, Mahaseem bata da wayau amma ko yaushe sai tace yaushe iyayen nata zasu dawo, sosai Jummai ke kuka idan tace hakan saboda akwai shak'uwa sosai a tsakanin ta da Na'ima, Malam Ayuba yace shi zai rik'e Mahaseem saboda gadon da aka bar mata, sannan ladidi bayan ta gama takaba yazo ya nema auren ta Dan kawai ya samu dukiya tunda ita ma an bata nata gadon, Ladidi ganin dagaske sonta yake kawai sai ta amince ta aure shi, amma ta tsani Jummai da Mahaseem, ana yin auren kuma sai ta samu ciki ai nan fa ta fara ma Jummai gorin haihuwa ita dai bata kulata domin ita mace ce mai kirki da hakuri, a haka ta haihu ta samu ya mace aka sa mata Habiba ana cemata Bibalo, Malam Ayuba haka yaketa had'ame dukiyar marainiya Mahaseem kuma ba sonta yake b yafi son y'ar shi kawai baya son nunawa ne a gari kar ace gadon Mahaseem yake so shiyasa yake nuna yana sonta, Ladidi ko ba karamin haushin hakan yake ba, shi ko cemata yake kawai saboda mutane yake yin hakan ai shima ba sonta yake ba, ita ma ladidin duk ya cinye mata nata gadon.
A yanzu shekarar Mahaseem Goma sha bakwai, kyakyawa ce ajin farko, doguwa ce mai kyan diri gata fara sol, tana da dogon hanci da bakin ta Dan daidai, hakoranta a jere farare kal ga dimples idan tana magana yana lotsawa, ga gashin ta baki ne sosai mai santsi domin bata ma kitso sai dai Inna Jummai ta dinga gyara mata shi, tana da cikar gira da gashin ido, Mahaseem duk kauyen nan ba wanda ya kaita kyau da tsafta ga ta da son kwaliya, mussaman Kawu Ayuba ya siyan mata kayan kwaliyar, Mahaseem tayi Primariya yanzu tana secondary SSS 1 take akwai ta da kokari, ga son zuwa makaranta, tana zuwa Islamiyya, nan ma Jummai na kokari tana bata tarbiya tunda ita ma tana da ilimin ta, Malam Ayuba yayi kokari ne yasa Mahaseem a makaranta kar yan kauyen su zage shi akan rashin kula yar marainiyar, Mahaseem akwai shegen surutu, ga rawar kai da shegen tsokana amma sai tsoro, kawayen ta biyu laure da Indo amma tafi shiri da Indo, duk sa'oin juna ne,ita da Indo ajin su a makaranta, Inna Ladi ta tsani Mahaseem baran ma yanda taga ta cika tana zama budurwa, tun tana karama take sa Mahaseem aiki, lokacin tana tsoron ta haka za tayi ta bata wahala, amma tunda ta fara girma sai tana k'i, idan Aiken ta tayi sai ta gudu taki zuwa, aikin gidan ko idan ba dukan ta tayi ba ba tayi, Inna Jummai idan tayi magana sai Inna Ladi ta hauta da massifa, shiyasa ma bata shiga harkar ta, Mahaseem ta tsani Inna Ladi, shiyasa idan tayi mata wani abin sai ta huce akan yarta Bibalo, habawa ai nan za tayi ta bala'i an taba mata y'a dan tunda ga kanta bata sake haihuwa ba, yanzu Bibalo shekarar ta sha biyu, Mahaseem duk Wanda ya tab'o ta bata hakura sai ta rama, Malam Ayuba yayi fad'an har ya gaji domin ana yawan kawo mai karar ta, Inna ladi ma har abin na bata haushi sai tace yafi son Mahaseem akan y'arshi, toh amma fah shima idan ta bashi haushi kulle ta a daki yake ya nakad'a mata dukan tsiya.
~Wannan kenan~
*_TAKU CE UMMU_ _BASHEER_*