MAHASEEM

Chapter 2

by @ummubasheer

*_MAHASEEM_*

       

{ ```Heart``` ```Touching``` ```Story``` }



_NA_

*_UMMU_ _BASHEER_*


```HASKE``` ```WRITER'S``` ```ASSOCIATION``` ...💡






 *Page 02*





 ```Maitama Abuja```





 _Kyakyawan_ Saurayi ne ya fito daga cikin wata had'adiyar mota fara mercedes wato Wanda akafi sani da benz (C300), dogo ne mai fafad'ar kirji, jikin shi na mazaje ne masu k'arfi, fari ne, yana da manyan ido, dogon hanci tare da pink lips kamar wanda ya shafa lipstick saboda yanda yayi pink sosai, sanye yake cikin navy blue suit, hannun shi rik'e da labcoat, dayan hannun kuma briefcase ne, cikin takun kasaita haka yake tafiya zuwa Cikin gidan wanda ya had'u iya haduwa Mansion ne domin bangare daban daban na gani, nan ya bud'e wani kofa mai kyau ya shiga, wata matace fara na gani tana saukowa daga stairs, Murmushi ta saki tana cewa"Habibi nah ka dawo"


Murmushi yayi mata wanda ya kara mai kyau tare da zama a kujera ita ma zama tayi, yace"Mom Barka da warhaka"


 "Yauwa Habibi ya aikin?"


 Zai bata amsa sai ga wata Kyakyawar budurwa ta shigo da gudu sanye cikin Uniform ta fad'o kan Mom, wani irin tsawa ya daka mata da sai da ta mik'e"Nawwal kina hauka ne zaki shigo haka"


 Mom ce tace"Aa kyalen min Auta nah, kinji je kiyi shower kizo kiyi lunch Dan nasan ba kiyi ba a school "


Kallon shi tayi tace"Sorry Broh _NIBRAS_ ya aiki"


Ko amsa ta baiyi ba ya dauki wayar shi yana dannawa ganin haka ta nufi upstairs jiki a sanyaye.


Mik'ewa yayi domin tafiya side dinshi Mom tace ya tsaya yaci abinci yace Nawwal ta kai mai zaije ya huta, nan ya fita,wani bangare naga ya nufa Dan karamin flat mai kyau ya shiga masha Allah nace ganin haduwar  sky blue and white komi na parlour, straight bedroom ya shiga nan ma fa ya hadu domin komi white ne zallah, ya dad'e yana wanka sannan ya fito ya shirin cikin wasu kananan kaya, jin knocking yasa ya nufa kofar yana budewa yaga Nawwal rik'e da basket na abinci matsawa kawai yayi taje ta ajiye a dining ta Fita,bayan yaci abinci yaje massalaci sai da yayi isha'i ya shigo gidan, wani side naga ya nufa, yana shiga naga wata tsohuwa a zaune kan kujera ta tasa TV a gaba, idanun ta sanye da medical glass, murmushi yayi ganin gaba daya hankalin ta na kan TV din, zama yayi kusa da ita hannu tasa a baki alamar yayi shiru, hannu yasa ya fara matsa mata kafafu, kallon shi tayi"ai koh kamar kasan ina neman mai matsa min kafa duk sunyi tsami"


"Kina shan magungunan ki kuwa?"


 Tsaki taja"kai raba ni da wannan magungunan sai dacin bala'i"


Mik'ewa yayi yana cewa"Still dai ya kamata ki dinga sha saboda lafiyar ki"


Hararan shi tayi"toh likita bokan turai"


Murmushi yayi tare da mata sai da safe daidai zai fita sai ga wata matashiyar budurwa ta shigo cikin matsatsen doguwar riga bako gyale, tana ganin shi tayi wani fari da ido"Ya Nibras two days ban ganka ba"


Tsaki kawai yayi ya bar gurin, haushi taji ta kalli Granny tace"tsohuwa kinga abinda Yayi min koh?"


 Dak'uwa tayi mata"Amshi nan uwar kice tsohuwa, wallahi Naila ki kiyaye ni"



Tsaki tayi ta juya tana cewa"Dan ma kin samu nazo gaishe ki shine zaki wani wani mttsssss...." Ta fita tana guna guni.


Ita ma tsakin taja ta cigaba da kallon ta.







Familyn Kabeer Yero sanane ne, Alhaji Kabeer babban mutum ne Dan kasuwa ba Wanda bai San Family Yero ba, d'an Kaduna ne anan yayi aure matar shi daya ce Safiya, ta haifa mai yara maza uku daga nan bata sake haihuwa ba, Akwai Sultan, Aliyu sai Lawal, Sultan yayi karatun likitanci ne a kasar Sudan acan ya had'u da wata balarabiya Sunan ta Nimrah soyayya suke sosai amma iyayen ta sunk'i yarda ta auri Dan Nigeria haka ya koma Nigeria amma gaba daya yana cikin damuwa, lokacin daya koma kanin shi Aliyu yayi aure yana aiki a kamfanin baban su, lokacin da Sultan ya dawo mahaifin su ya bude mai hospital, nan ya fara aiki ya had'a harda kasuwanci ai nan fah ya fara kud'i, sosai ya damu da Nimrah har ya sanar da mahaifiyar su nan ta fad'a ma Baban mussaman ko Baban ya shirya shida wani yayan shi da aminin shi da Sultan din su kaje har Sudan suka nemar mai auren Nimrah ganin iyayen Sultan sai suka amince bayan wasu yan bincike aka sa ranar aure acan akayi auren aka kawo ta Nigeria, ba'a Dade ba da auren mahaifin su Sultan ya rasu inda ya bar musu tarin dukiya, bayan wasu kwanaki da rasuwan shi aikin kasuwancin ya maida Sultan Abuja acan ya ya gina wani baban Hospital, Ba'a dauki lokaci ba lawal Shima yayi aure, Nimrah duk ta damu da rashin samun haihuwa saboda two years kenan da auren su amma shiru ga matar Aliyu ta haifi namiji, Sultan ganin kowa da gidan shi a kaduna ga mahafiyar su ita kadai a gida sai mai aiki yayi tunanin gina musu gida a Abuja, gadan gadan aka fara aiki, lokacin Nimrah ta samu ciki, ai koh ba karamin farin ciki su kayi ba, bayan wata tara ta haifa kyakyawan d'ant ranar suna yaci suna Nibras ba'a Dade ba matar Lawal ma ta haifi danta Hibban, bayan wasu shekaru Alhaji Sultan ya kammala gini, gida ne na gani na fad'a babban gida ne mai dauke da side daban daban akwai side dinshi sai na Lawal da Aliyu, sai na mahaifiyar su, sai kuma wani flat da yayi guda uku masu kyaua jere na y'ayan su Maza, tare da taimakon kannen shi suka had'a kai aka kamala komi hatt da furnitures komi sabo, amma Alhaji lawal yace ba zai iya barin aikin shiba amma zasu dinga zuwa Hutu, Alhaji Sultan baiji dadin hakan ba, haka suka tare a gidan su dake Maitama Abuja, 




Bayan wasu Shekaru, Alhaji Sultan ya zama babban attajiri, karshe ma kanin shi Aliyu ya daura a company shi, Yaran su biyu yanzu Nibras sai kanwar shi Nawwal, sai Alhaji Aliyu yaran shi uku akwai Salman, Naila,sai Hibban wanda yake sa'an Nawwal, shekara d'aya ne tsakanin Naila da Hibban,sak'o ne kullum cikin fad'a suke, sai Alhaji Lawal danshi Fawwaz sa'an Nibras sai kannen shi uku mata, Sa'adat, Nihla sai Safina, Ummie(mahaifiyar Nibras)tana son yaran ta sosai tana ji da Nibras ba kadan ba take sonshi, haka Nawwal ta shagwab'a ta dayawa, Ummie bata da wata matsala akwai kirki sai dai bata son talauci ko kadan tana da high taste, Matar Aliyu wato Mom bata da mutunci akwai ta da son abin duniya ga hassada da bakin ciki ko kadan bata shiri da Ummie dama tunda aka auro ta basu shiri tana bakin cikin ta fita kyau, gashi kuma mijinta yafi nata mijin kud'i, bare kuma yanzu da mijin nata ke aiki karkashin Abie(Alhaji Sultan) sosai take bakin ciki, gashi duk ta bata yaran ta bata tsayawa ta basu tarbiyya, baban Dan nata Shaye shaye yake ga neman mata kuma ta sani,bata damu ba, Naila kuwa bata da nutsuwa akwai shigar banza ita dai bata bin maza amma fah bata da kunya ko kadan, tana da kyanta daidai, tana bala'in son Nibras amma shi baya son ta, kowa a gidan yasan yanda take son shi, Hibban ba ruwan shi domin yanzu yake da 24yrs,yanzu ya gama ABU Zaria inda ya karanci Law,Hibban yana da kyau,yana da haske domin duk yafi su Naila haske duk da ba fari ne sosai ba, shida Nawwal suna shiri sosai, Mom tana jin haushin yanda suke shiri kusan ko yaushe Yana side dinsu Nawwal, sau dayawa shine yake koya mata Karatu, tsakanin Naila da Hibban ba nisa shekara d'aya ne tsakanin su,Mom ba karamin haushin Naila take ji ba yanda take son Nibras, Kullum sai ta zauna tana musu hud'ubar tsiya, Salman ne kawai yake daukan hud'uban ta sauran koh anan zasu watsar dashi, Salman yana jin haushin yanda baba shi ke aiki kasan Abie gani yake kamar su ba'a son sune.





Nibras kyakyawa ne saurayi Dan kimanin shekaru ashirin da tara, yayi karatun likitanci inda yanzu ya zama cikaken Doctor mahaifin shi ya daura shi matsayin shine Babba a hospital dinshi, inda mahaifin ya koma harkar kasuwanci lokaci zuwa lokaci kuma yana Dan duba hospital din, Nibras mutum ne mai son tsafta, miskili ne baya son hayaniya, yana da aboki guda daya Sahal shima doctor ne tare suke aiki, Nibras mata basa gaban shi domin bai tab'a yin soyayya ba cewa yake waste of time ne, yana son aikin shi domin taimakon Al'uma, Suna shiri shida Fawwaz, lokaci zuwa lokaci shida iyayen shi sukan je Sudan domin gaida yan'uwan mahaifiyar su suma kuma sukan zo wani lokacin.





 ```Please ina son a dinga comments sosai, more comments more Typing```





 ```TAKU CE UMMU BASHEER```